Showing 135001 words to 138000 words out of 363274 words

Chapter 46 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2590

ga wani sihirtachen kamshin dake tashi ajikin ta, yauma kamar kullun ta Chi kwalliya sosai kamar ka sa che ta gaje ka ajiyeta ka yita kallon ta kamar madubi dan kyau, sanye take chikin wata dan kareriyar lace Sky Blue da zanen fulawa baki a jiki, ɗinkin riga da sket ba ƙaramin zama kayan sukayi a jikin taba kamar daman a jikin nata akan ɗin kasu, ga wani haɗaɗiyar high heel baki da ta sanya

jama'a ya kuke ganin farin kafa da bakin takallama? sai ɗaukan ido kafar nata yake ga kunbar (farche) kafar ta nan yasha gyara fari tas dashi sai sheki yake ta sanya mayafi baki kalar takalmin ta ta zuba wasu ɗankara ɗankaran sarka da abun hannu na gold wadda Aunty farida ta bata, jakar ta ta ɗauka ta nufi waje

Taku take a hankali sai wani yauki da yanga take kamar bata son taka kasa ta fito harabar gidan, Aiman dake zaune chikin mota tun daga nesa ya zuba mata ido yana kallon yadda take taku chikin yanga da yauki har ta iso wajen motar ba tare da ya ankara ba, fitowa wajen Aunty farida tayi daga chikin nata motar tana faɗin "wan nan irin kwalliya haka my diyana dole namiki" murmushi kaɗan diyana tayi san nan tace "ngd Aunty farida"


Chiro wayar ta daga chikin jaka Aunty farida tayi tace "to my diyana gyara na ɗauke ki, gyara tsayuwa diyana tayi Aunty farida ta fara ɗaukan ta hoto har kala 10 ta ɗauke ta san nan tace "to ya isa haka shiga da wuri muje dan kar lokachi ya kure jirgi ya tashi ya bar yaya Aiman a nan"

"Aunty farida na shiga motar ki ne ko kuma naje na yaya Aiman? "Duk wan da kike so my diyana" "to bari na shiga na yaya Aiman, bata jira amsar Aunty farida ba ta buɗe gidan baya ta shiga kusa da shi ta zauna, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke wadda sai da yasa diyana juyowa tace "yaya Aiman lfy murmushi kawai yayi mata dai dai lokacin driver's suka tada motochin, da gudu baba mai gadi ya wangale musu katafaren gate ɗin chikin ni tsuwa suka danna hanchin motochin waje
Sunyi nisa da tafiya yaya Aiman ya juyo da kallon sa kan diyana da kyau ya fara magana

"baby diyana in son ki bani hankalin ki magana mai muhimmanci nake son muyi" ɗago blue eyes nata tayi tana kallon sa chikin sanyin murya tace "to yaya Aiman in jin ka

"Ni ba zan ɓoye miki ba gaskiya ina son ki Auren ki kuma zanyi kuma na san kin san da hakan ko? Sun kunyar da kai kasa diyana tayi tana wasa da yan ya tsun ta "baby diyana ko baki so nane? Yayi maganar yana ɗan dukar da kansa kasa yana leken fuskar ta
"Ina son ka mana yaya Aiman kai fa yayana ne idan ban soka ba waye zan so? "Baby diyana ni fa ba irin wan nan soyayyan ba soyayya irin na Aure nake nufi ba na yaya da kanwa ba" "eh yaya Aiman soyayya irin na Aure'n ina son ka Nima.

Wani farinciki kine ya lullɓe sa ji yake kamar ya jawota ya rungume ta ajikin sa ko zai samu saukin a zuchiyarsa

A ɓangaren diyana kuwa, kuka take a zuchiyar ta tana faɗin "No yaya Aiman me yasa zaka min haka ni wlh yaya Aryan nake so ba kai ba, amma ba zan iya chewa bana son kaba kuma bazan iya chewa yaya Aryan nake So ba, Ni ban ma sani ba shin yaya Aryan yana sona ko dai kawai a matsayin kanwa ya ɗaukeni ni yanzu ya zanyi da rayuwata wayyo Hiyana ta kizo ki che cheni awan nan bala'i daman kin saba taimako na, ya Allah ka kawo min mafita

"Baby diyana tunanin me kuma ki ke yi? "Babu komai yaya Aiman " "ya zaki chemin babu komai bayan nayi magana har sau biyu baki jiba"
"Babu komai wlh kawai kewar su hiyana nake ne shiyasa" "to ki dai na damuwa kinji? naji Abba yace jibi Aunty farida ta mai daki gida ai" "Da gaske yaya Aiman" "eh mana shiyasa ma ai zan koma ban damu ba dan nasan jibi kema zaki dawo gidan badan zaki dawo ba ai da nima bazan koma ba, yayi maganar dai dai lokachin da driver's ke parking na motochin a Parking space na Airport.

Da sauri Aiman ya fito yana faɗin "my wife saura 5mnt jirgin mu ya ɗaga sai munyi waya, bai jira amsar taba ya wuche ya nufi motar Aunty farida dai dai lokacin itama ta fito daga chikin motar, sallama sukayi ya wuche ya nufi jirgi yana tafiya yana waigo diyana mamaki ne ya kamashi tunani ya shigayi "me yasa diyana bata fito daga chikin mota ta masa bye bye ba, ɗayan ɓangaren na zuchiyar sa yace "kila kunyar ka takeji ne Shiyasa kabari sai ka koma ka kirata awaya, sai kaji dalili, da wan nan tunanin ya shiga jirgin sai da Aunty farida taga tashin jirgin su san nan ta koma chikin mota

A ɓangaren diyana kuwa tun da Yaya Aiman ya fita daga chikin motar take kuka hawaye sharɓe sharɓe, gaba ɗaya hawayen ya wanke mata fuska,surutu ta rinkayi shi dai driver yana jinta amma ko ɗago ido bai yi ya kalleta ba dan yana tsoron kallon nata saboda Aunty farida ta musu gargaɗi akan duk wanda aka kama yana kallon diyana zai karɓi hukunchi mai tsanani daga wajen mijin ta, hakan yasa gaba ɗaya masu aikin gidan suna tsoron idon su ta sauka a kan ta koda kuwa ta bayan tane.

Key driver's ɗin sukawa motochin suka tayar suka nufi gida


KANO

kwanche yake saman katafaren gadon sa yana kallon sama yayi shiru kamar mai tunani hannun sa ya ɗago ya duba time a jikin dan ƙareriyar agogon gold dake manne a hannun sa, karfe 4:45pm mai da hannun nasa yayi gefe yana kwaɓe fuska karar wayar sa da ya jine alamar shigowar sako hakan ya sashi sa hannu yana lalubar wayar, chan daga ɗan gefensa ya jiyo wayar

Ɗauko wa yayi ya kawota dai dai sai tin fuskar sa,tare da kunna hasken screen ɗin ganin number da diyana ta kirashi shekaran jiyane ya bayyana akan screen ɗin hakan ya sa shi saurin meƙewa zaune tare da chire password ɗin wayar hannun sa har rawa yake wajen shiga massage

wow zafafan hotunan da Aunty farida ta ɗauki diyana ɗazun da zasu raka Aiman Airport ne aka turo masa sai dai an sanya wa hotunan backgrau an sanya wasu flower daga gefe gefe anyiwa hotunan kwalliya,ta yadda mutun ba zai gane a in da aka ɗauki hotunan ba zubur ya miƙe tsaye, tare da kurawa wayar ash eyes nashi ya kankame wayar sosai kamar wani yace zai kwache masa ita, daya bayan ɗaya yake kallon hotunan.

...nan take yaji jikin sa na rawa sai wani tsuma yake, ji yake kan sa ta masa nauyi gaskiya ina bukatar ganin matata a kusa dani dafe kan sa yayi ya koma ya zauna a gefen gadon a hankali ya fita daga wajen massage ɗin ya shiga contact ya fara kokarin kiran layin diyanar amma a kashe, wurgi yayi da wayar tasa saman sofa, da karfi ya fara magana

"Wai wanene ya ke min wasa da hankali haka ne!? Abba da alama awan nan karon kashe ni kake son yi da kan ka, oh my god!! Kwan chiya yayi a saman gadon rabin jikin sa na sama kafafun sa kuma na kasa, haka yayi ta surutu har barchi yayi awon gaba dashi.


Washe gari misalin karfe 5:5Am kamar dai kullun yauma lallaɓowa tayi ta fito daga part ɗin Ammi ta nufi ɗakin da yaya Ahmad ke kwanche, da sallama ɗauke a bakin ta ta shigo kakar kullun yana kwanche saman gadon sa yau dai idon sa a lumshe kamar mai barchi

Gefen gadon hiyana taje ta zauna a hankali tafaɗa karan to masa addu'oe tana tofa masa jin motsin mutun a kusa dashi ne yasa ya waro manya manyan fararen idon sa akan kyakkyawar fuskar sai shekin alwala fuskar nata yake

"Yaya Ahmad ya jikin naka, abun mamaki sai taga ya girgiza mata kai alamar yana samun sauki, mikewa tayi tsaye da sauri tace "yaya Ahmad yanzu kana iya motsa jikin ka!? Hannun sa yaɗaga mata alamar ta gani yana iya motsa wasu daga chikin gaɓoɓin sa, murmushi tayi wadda yasa dimple nata ya lotsa tace "Alhadulillah kasan me yaya Ahmad? saura kwana ɗaya na gama haɗa maka ruwan addu'a ka kuma nasan kana sha In Sha Allah zaka samu sauki, amma yanzu in kawo maka wani abu ne? Ɗaga mata kai yayi san nan yamata nuni da hannun sa alamar ruwa yake son sha, da sauri ta fice daga ɗakin ta koma part ɗin Ammi ta ɗauko masa ruwan faro mai sanyi daga fridge ta fito ta nufi ɗakin.

Tun daga nesa ta hango Bgs yana kokarin shiga ɗakin yaya Ahmad ɗin, ɓata fuska tayi alamar bata ji daɗi ba dan taso tabawa yaya Ahmad ruwan addu'ar nan ya sha zai tai maka masa, amma babu hali dan kuwa bata isa ta shiga ɗakin Bgs na chiki ba juyawa tayi jiki ba kwari ta koma part ɗin Ammi


Ƙarfe 7 dai dai suka gama shirin zuwa school suka zauna a palon sama suna jiran yaya Khalid, sai ƙarfe 7:10 yaya Khalid ya shigo palon Ammi da Sallama ɗauke a bakin sa har suna haɗa baki wajen amsa masa Sallamar zama yayi saman sofa yana kallon su ɗaya bayan ɗaya chikin sanyin murya ya fara magana

"Yau ba zuwa school domin Abba ya karɓa muku transfer later za'a Chanza muku makaranta Amma sai ranar Monday yanzu dai kuje ku chire uniform ɗin ku shirya muje muchi abinchi" to kawai su kache san nan suka wuche suka nufi ɗakin su, shi kuma ya miƙe ya fice daga palon ya nufi palon Abba dan zuwa yin breakfast


Karfe 8:20 gaba ɗaya family Abba sun haɗu a palo dan yin breakfast ban da Aryan da Bgs, abin chi suke chikin nitsuwa da kwanchiyar hankali ɗan gyarar murya Abba yayi ya dubi Fahad da hiyana ya fara magana "kai Fahad je ka kuramin babban yayan ku, ke kuma hiyana je ki kiramin yaya Aryan kusan tare suka miƙe suka nufi waje hiyana ta nufi part ɗin yaya Aryan Fahad kuma ya nufi part ɗin Bgs.

Da sallama Fahad ya shaga betroom nashi zaune ya same'sa saman sofa yana latse latse a laptop "yaya prince Abba na kiran ka" shiru Bgs yayi kamar bai ma san da shigowar mutun ɗakin ba aikin dake gaban sa kawai yake, zama kusa dashi Fahad yayi ya sake mai mai ta maganar "yaya prince Abba na kiran ka" nan ma shiru yayi kamar bai jiba Almost 10mnt Fahad na zaune yana jiran amsar Bgs har ya fidda rai da samun amsa yana kokarin miƙewa sai yaji Bgs yana faɗin "ae na Abban yake? nauyayyar ajiyar zuchiya Fahad ya sauke kafin yace "yana palon sa kuma ya che kayi sauri" shiru Bgs yayi bai sake magana ba, Fahad dai da yaga Bgs bai da niyar sake yin magana sai ya kama kan sa ya fice daga ɗakin dan in da sabo ya saba da rashin maganar Bgs

Abangaren hiyana kuwa da sallama ta shiga part ɗin yaya Aryan babu kowa a palon kasa haurawa tayi palon sama nan ma babu kowa, kofar betroom nashi ta nufa a hankali ta tura kofar tare da yin sallama ta shiga, tsaye yake gaban mirrow yana gyaran gashin kansa, sanye yake chikin wando jeans fari da bakar t-shirt chikin sanyin murya tace "yaya Aryan Abba na kiran ka" a sukwane Aryan ya juyo dan jin irin voice na diyana ganin hiyana che yasa yace "jeki ina zuwa, da sauri hiyana ta juya ta fice daga ɗakin tana yabon irin kirkin yaya Aryan a zuchiyar ta.

Shi kuma juyawa yayi ya chigaba da gyaran gashin sa yana tunanin diyanar sa

Kusan tare Bgs da Aryan suka shigo palon taku suke da kagan su kaga jaruman sojoji Bgs na gaba Aryan na bin sa abaya, zulaihat dake zaune kusa da Aunty amarya ta zuba musu ido tunani ta shigayi "ashe ma hoton sa da na kalla ban ga komai ba, asai a fili yafi kyau wow gaskiya guy ɗin nan ya hadu iya haɗuwa ba karya, har naji na kara son shi ga wannan faffadar kirjin nashi zai yi daɗin kwan chiya wlh kai gaskiya ayi sauri a ɗaura mana Aure in ba haka ba zan kai masa kai na, dan ba zan iya hakuri ba.

Tayi nisa chikin tunanin sai ji tayi Aunty amarya ta taɓa ta a ɗan firgiche ta ɗago ido tana kallon ta alama da ido Aunty amarya ta mata akan ta gaishe dasu Bgs, dawo da kallon ta kansu tayi chikin rawan kai ta yanga tace "hiii prince y kk tirkashi gaba ɗaya jamaa palon sai da suka ɗago suna kallon ta banda Aryan Bgs da kuma Fahad.

Murmushi Yusuf yayi a zuchiyar'sa yace "tab aiko ga wadda zata bi sahun yar sarki Zaria, Khalid kuwa dariya ma taba shi amma sai ya danne dan yasan idan yayi dariya tofa tabbas Bgs zai iya ɓaɓɓalla yarinyar nan, Haidar Umar mamaki ne ya kama su, ko su dasu kannen sa basu taɓa che masa wani hii ba bare ita da basu ma san daga in da ta fitoba kwashe kwashen Aunty Amarya ta kwaso ta, Abba kam tunani yake gai suwar mutunci ma akayi wa Safras yau she yake amsawa bare wani hii lallai su hii anji jiki

Shiru palon yayi kowa da abun da yake tunawa, hannu Zahra tasa ta ɗauki Cup ɗin ruwan dake kusa da Abba tana kokarin kawowa gaban ta kamar wadda aka bugewa hannu patal cup ɗin ya faɗi chikin plate ɗin abin chin zulaihat ruwan ya zube a chiki, chikin jin haushe da bachin rai abun da Bgs ya mata na rashin amsa hii ɗin ta da yayi ta miƙe ta zabgawa Zahra wani gigitachen mari, wani kara Zahra ta saki

Bata gama sauke hannu ba Haidar da Umar suka miƙe a tare suka wanke mata fuska da wasu gigitachen maruka a lokachi guda ta gefen dukka kuma tun ta tana kokarin sakin kara, Fahad ma ya miƙe ya mata ɗaya tamkar da dubu ta gefen kunne, wadda yasa gaba ɗaya taji duniya ya tsaya Chak kunnen ta ya dai ma ji na wunchin gadi, almost 5mnt tana tsaye tama kasa sakin ihun dan da alama bata chikin hayyachi sai da ta kara wani 5mnt san nan ta samu damar sakin wani razanannen ihu mai firgitarwa, Afusache chikin tsawa Aryan yace "get out a ruɗe ta kama hanya fita sai ihu take kamar wata mahaukaciya

Kuka Zahra take a hankali sai shessheƙa take ga shatin yatsun zulaihat kwanche akan kuma tun ta wajen yayi ja wur dashi gyaran murya Aryan yayi wadda yasa gaba ɗayan su ban da Bgs suka ɗago suna kallon sa,da hannu ya yiwa Zahra alama da tazo
Miƙewa tayi daga kujerar ta ta nufi waje sa, batare da yayi Magana ba ya mata nuni da hannun akan ta zauna kan chinyar sa, zama tayi yasa hannu ya goge mata hawayen kasa kasa yace "ya isa haka kuka kinji Auta? Gyaɗa masa kai kawai tayi alamar eh, spoon ya ɗauka ya fara ɗeban abinchi daga chikin plate na Khalid yana bata a baki.

Aunty amarya ji take kamar ta tashi ta shake Zahra dan haushi kwafa tayi a chikin ranta tana tunanin wani hukunchin ya kamata ta ɗauka akan yaran nan

Khalid kam yama kasa magana saboda bakin chikin marin sis love ɗin sa da akayi ajiye spoon na shi yayi yana kallon yadda Zahra ke chin abinchin da Aryan ke bata

Tunani Umar da Haidar suka shigayi daman yan uwan su suna son su haka dubi yadda yaya Aryan ke bawa Zahra abin chi a baki Alhadulillah Alhamdulliah

Duk wan nan abun da ake Bgs ko ɗago ido bai yiba bare kasa ran zai yi magana.

Haka zalika Fahad tun da ya mari zulaihat ya koma ya zauna ya chigaba da chin abin chinsa kawai

mikewa Ammi tayi ta fara magana "me yasa zaku mata irin wan nan maruka hakan eh!? "Ammi to me Auta ta mata da zata mare ta haka chewar Umar, shi dai Fahad kawar da kai gefe yayi dan bai ma son haɗa ido da Ammi dan bai da niyar bata amsa sai wani furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa, dawo da kallon ta Ammi tayi kan Bgs dake zaune yana kallon wayar sa "kai yanzu kana ganin yaran nan suka mari yar mutane bazaka hana suba Koh? Shiru ya ɗan yi na yan second ni kafin ya buɗe ɗan karamin bakin yace "ai dai dai sukayi Ammi shiyasa"
"Dai dai sukayi ma zaka che ko? "Haba Aisha ya isa haka gaskiya ya faɗa miki ai dai dai sukayi mana da basu hukun tata bama to ni da kai na zan hukun tata Autan tawa guda za'a mara kuma a gaba na san nan batare da tayi laifin ko mai ba ai kam wane mutun, chewar Abba komawa Ammi tayi ta zauna tayi shiru tana tunani "nima har chikin raina naji wan nan mari da yarinyar nan tawa Zahra amma dai bai kamata su haɗu mata haka ba

Abba ne ya katse mata tunanin da take yace "to na tara ku a nan ne inason yin magana daku...✍️✍️



💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)

*Baby*


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login