Showing 228001 words to 231000 words out of 363274 words

Chapter 77 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2533

sa yayi kafin yace "ba sai na faɗa miki menene fyaɗe ba nan ba da jimawa zan miki wani abu makamancin hakan yanzu dai umarni nake baki kizo ki bawa Aunty Amarya hakuri" zatayi magana ya ɗaure fuska sosai yace "bana son wata magana kiyi abun da nace miki kuma daga yau idan kika sake chewa baki son Aunty Amarya to nima ki sa aran ki bana son ki dan ba zan so wan da baya son mahaifiya ta ba" ganin ransa ya baci sosai ya sanya ta faɗo jikin sa tana faɗin "kayi hakuri zanje kuma ai bani na fara chewa bana son taba itace tace bata son mu ita da Aunty Maryam" ta karisa maganar kamar zatayi kuka rungumota yayi ajikin sa sosai yana faɗin "tana son ki mana tana sun ku gaba ɗayan ku kamar yadda take san mu kawai rashin samun fahimtar juna ne" hannu ta tura chikin gashim kansa tana faɗin "yaya Aryan yaushe zan maka kitso ne? Gashin kan nan yayi tsawo da yawa"ɗago habarta yayi yace "kin iya kitso ne?" chikin sauri ta ɗaga masa kai alamar eh "to muje ki bawa Aunty Amarya hakuri sai mu dawo ki yimani" chikin sauri ta sake sa ta ɗauko hijabin ta ta nufi waje tana faɗin "to karfa ka tafi wani waje ina dawowa yanzun nan" "to" kawai yace mata yana kokarin zama sai wani tunani ya faɗo masa "yanzu idan diyana ta je bawa Aunty Amarya hakuri ita kaɗai zaa iya samun matsala dan idan Aunty Amarya tayi wani magana da bai wa diyana daɗi ba diyana zata iya mai da martani dan bata bari ko ta kwana" tuna hakan yasa yayi saurin mikewa yabi bayan ta dan sulhu yake nema da Aunty Amarya ba zai so a sake samun wata matsala ba

Tana gab da shiga part ɗin Aunty Amarya ya chin mata chikin nitsuwa yace "my jidda duk abun da Aunty Amarya zata che miki ban yarda ki yi wata magana ba kiyi shiru kawai ki saurare ta idan ta gama magana sai kice tayi hakuri" "to" kawai diyana tace

a tare suka shige chikin palon da sallama a bakin su kamar yadda ya bar ta haka suka shigo suka same ta saman kujera diyana ta zauna Aryan yana son che mata ta sauka kasa yana tsoron amsar da zata bashi a gaban Aunty Amarya yanzu ma yaya suke da Aunty Amarya bare kuma taji irin maganganun da diyana take masa mara kan gado ba respect tuna hakan ya sanya yayi shiru bai yi magana ba

A kufule tace "kiyi hakuri Aunty Amarya" salati Aryan ya fara yi a zuchiyar sa wai yaushe diyana zatayi hankali ne ko gaisuwa babu bare ta che ykk
harara Aunty Amarya ta wurga mata kafin tace "haka ake bada hakuri a gidan uban ki ina zaune a sama ki na zaune a sama" turo baki tayi zatayi magana sai ta tuna abun da yaya Aryan yace mata kallon sa tayi ta gefen ido taga alamun ran sa ya ɓaci sosai jiki ba kwari ta sauko kasa ta matso kusa da Aunty Amarya murya kasa kasa ta fara magana "kiyi hakuri ba zan sake ba" ba karamin daɗi hakan da tayi Aryan yaji ba ji yayi kamar yazo ya rungumeta ta dan murna Aunty Amarya kuwa wani kululun bakin ciki ne ya tokare mata makoshi rai a ɓace ta fara magana "kina bukatar samun tarbiya dan kwata kwata in da kika fito babu tarbiya ya kamata ki koma sai kin samu tarbiya sai ki dawo ki zauna da ɗana" tana kai karshen maganar ta miƙe ta wuche bedroom nata, nauyayyar ajiyar zuchiya Aryan ya sauke tare da miƙewa ya kama hannun ta ya mikar da ita kin tafiya tayi ta tsaya "my jidda muje mana" "yaya Aryan menenen tarbiyya tun da naji Aunty Amarya ta faɗi hakan to tabbas zagi na tayi kuma zagin ma da alama mara daɗi ne" ɗaukan ta yayi chak ya saɓa ta a kafaɗar sa ya nufi waje da ita dan bai san biye mata kar Aunty Amarya ta fito ta gansu a palon

Saman katafaren gadon sa ya sauke ta tare da zama kusa da ita yana faɗin "zo ki mun kitson" jin abun da yace ya sa ta miƙe tana dariya ta fara wargaza masa gashin kansa manya manyan kun bushe ta masa a tsakiyar kan sa guda uku yana zaune yana jin duk abun da take masa leko fuskar sa tayi tace "yaya Aryan na gama kaje wajen mirrow ka gani sun yi kyau" ba musu ya miƙe yaje gaban mirrw a sukwane ya sanya hannu ya goge idon sa ya sake kallon kansa da kyau tsai tsaye ta masa kitson kamar kawon shaiɗan kamar wani sabon mahaukaci haka ya dawo ji yayi tamkar ya wawwan ka mata mari amma sai ya danne ya juyo ya kalleta ta tana zaune tsakiyar gadon sai murmushi take
kakalo murmushi dole yayi yace "my jidda gaskiya kitson yayi kyau sosai ashe kin iya kitso har haka" kara washe baki tayi tana dariya tace "to yanzu dai kuje ka nunawa su Abba" ta karisa maganar tare da miƙewa ta nufoshi "aa my jidda ba sai na nunawa su Abba ba ki barshi kawai iya ni da ke" "to shikenan yanzu ni bari naje wajen Ammi na" "to" kawai yace mata da sauri ta fice daga ɗakin

Tana fita ya dafe kansa yana faɗin "na shaga uku ni Aryan to ya zanyi dole nayi kokari na gyara kayana tun da ina son ta dole ta koma school da haka ya nufi toilet dan yayi wanka ya kwance haukar da diyana ta masa

To bari mu leka yan Uk muga me suke Aikatawa

Uk

7am ta farka daga barci slowly ta waro blue eyes nata waje chikin sauri ta miƙe zaune tare da zuro kafafun ta kasa mikewa tayi ta nufi toilet a gurguje tayi wanka ta fito ta shirya chikin sauri doguwar riga ta sanya a jikin ta rigar ta kamata sosai ta fito mata da shape nata sosai rigar tana da yar siririn hannu ɗaure gashin kanta tayi ta watsa jelar a bayan ta hijabi ta ɗauko chikin kayan da sukayi shopping da yaya Khalid jiya a nitse ta gabatar da sallar asuba tana rokon Allah da ya yafe mata akan makara da tayi bata gabatar da sallah akan lokaci ba

Bayan ta idar da sallah ta jawo trolley ɗin ta ta zauna ta tsara make up abun da bata taɓa yi ba yau first time a rayuwar ta sosai tayi kyau kamar ka sache ta ka gudu mayar da kayan da ta watsa tayi ta miƙe tana tunanin ina yaya Prince ya kwana da bai kwana a ɗaki ba tana da tabbacin yau bai tafi wajen Aiki ba dan kwata kwata bata ji motsin saba na damar abun da ta masa jiya ta farayi chike da tsoro ta nufi waje tana tafiya tana sanɗo kamar ɓarauniya

tana fitowa palo ta same sa kwance saman doguwar kujera ya miƙe kafafun sa wadda suka fi kukerar tsawo kallo ɗaya ta masa ta fahimci shima ya makara bai yi sallar asuba ba a hankali ta tako zuwa gaban sa ta tsugunna hannun sa ta kamo ta riƙe chikin sanyin murya ta fara kiran sunan sa "yaya Prince yaya Prince yaya Prince" slowly ya faro green eyes nashi a kan face nata ɗaure fuska sosai yayi tare da mikewa zaune kai kallon sa yayi kan hannun sa da ta rike chikin sauri ta sake sa yana kokarin miƙewa tayi saurin rike kafar sa ta fara magana kamar zatayi kuka "yaya Prince dan Allah kayi hakuti tuba nake ba zan sake ba" chikin ɓachin rai yace "me kika yimin da kike bani hakuri!? Chike da tsoro ta kwantar da kan ta saman chikinyar sa tare da kamo hankun sa chikin nata chikin shagwaɓa ta fara magana "na maka laifi mana jiya nasa kayi fushi ka fito palo ka kwana" "tashi min kan kafa" kara kankame hannun sa tayi dan tasan yanzu ba zai bugeta ba dan Ammi tace idan ya kara bugun ta bata yafe masa ba shiya sanya yanzu bata tsoron sa "yaya Prince ni gaskiya ba zan tashi a jikin kaba har sai kache ka hakura" fisge hannun sa yayi tare da miƙewa ya nufi bedroom chikin sauri ta miƙe tabi bayan sa dai dai tsakiyar ɗakin ta rungume sa ta baya tare da kwantar da kan ta a bayan sa tana faɗin "dan Allah yaya Prince kayi hakuri mana nafa che ba zan sake ba" a fusace ya juyo tare da damkar wuyar ta da nufin yayi wurgi da ita ba shiri ya zame hannun sa daga wuyar nata sakamakon tuna maganar Ammi yana kallon face nata zaro ido waje tayi sosai tana kallon face nashi yana sakin wuyar nata ta fara tari tari ta riƙe wuyar ta
guntun tsaki yaja tare da jawota jikin sa ya ɗago habarta yana kallon face nata chikin nitsuwa ya fara magana "ke sister tace ki tsaya a matsayin ki na sister ta idan ba haka ba" bai karisa maganar ba ya sake ta ya wuce toilet abun sa jiki ba kwari ta wuce ta fara gyara masa gadon tana yi tana tunanin "anya yaya Prince zai chanza kuwa gaskiya nayi na damar hana shi wasa da ni jiyana da daddare wata kila da ya samu abun da yake so da zai iya ɗan sawa ran sa ruwan sanyi" tunani kala kala ta rinƙa yi har ta kammala masa gyaran ɗakin ta fito masa da kayan sawa ta ajiye masa saman gado ta koma ta zauna saman sofa

Ko da ya fito toilet ko kallon in da take bai yi ba ya wuche dressing room nashi tasha ruwan mamaki ganin yaki sanya kayan da ta fito masa da su, wandon jeans fari da t-shirt blue ya sanya yau ko ɗaure gashin kan sa bai yi ba da alama yana chikin bachin rai sosai

shin fiɗa dadduma yayi ya tada sallar asuba da bai yi ba,chikin sauri ta miƙe ta nufi kitchen ta ɗauko masa breakfast nashi ta dawo ta ajiye masa saman table ta zauna tana jiran sa
bayan ya idar da Sallah ya mike ya ɗauki wayar sa da system ya nufi hanyar fita daga ɗakin da sauri tace "yaya Prince ga breakfast naka" ko kallon in da take bai yi ba yayi fice warsa daga ɗakin bin bayan sa da kallon tayi har ya fice jiki ba kwari ta miƙe ta koma saman gado tare da ɗauko wayar ta tafara neman layin Aunty farida dan ta taimaka da shawara

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu zamuga wasan yadda zai kaya tayaya Hiyana zata shawo kan Bgs? Tayaya yaya Aryan zai kare da diyanar sa? tayaya Bgs zasu kama dadyn jabir? Ya za'ayi asirin Aunty Amarya ya tonu? Muje zuwa yanzu wasan ya fara


💋Duk Karfin Izzata 💋



💖The Talent Troupe Writer's 💖


💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*




Book 2

Page 26


Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga chike da damuwa hiyana ta fara bata lbr abun da ya faru dariya Aunty farida tayi bayan ta gama jin bayanan hiyana chikin nitsuwa ta fara magana "oh su Safras manya to an faɗa masa mata wasa ne wato har da wani che miki ki tsaya a matsayin ki na sister ko? Lallai zai gane shayi ruwane kinsan yanzu me abun yi? "Aa Aunty farida ban sani ba sai kin faɗa" ta faɗi maganar tana girgiza kai "na shan yau ba zai dawo da wuri ba ki tsara wanka ki shakwalliya ki shirya masa duk wani abun da kika san zai bukata kafin ya dawo,yanzu idan mun gama waya ki kirashi ki masa ya isa wajen Aiki lfy idan kuma kika kira bai ɗauka ba to ki masa massage sanna idan ya kusa dawowa nan ma ki sake kiran sa idan bai ɗauka ba ki masa massage ki tambaye sa ya Aiki sai ki kara masa da ya sawo miki chocolate a hanya idan har ya sawo miki chocolate ɗin to ba shakka ya fara son ki idan kuma bai sawo ba to fa muna da sauran aiki a gaban mu sanna idan ya dawo bayan kin gama chire masa ta kalma kin masa duk abun da ya dace idan yayi wanka ya shirya ya zauna yana hutawa sai ki tawo ki zauna a kan chinyar sa tun da yanzu ba zai bugeki ba kina da daman zama a jikin sa ba yadda zai yi da ke idan yace ki tashi karki ta shi ki kwanta a kirjin sa chikin shagwaɓa kice yayi hakuri idan ya fara yi miki tsawa ki sa masa kukan shagwaɓa tare da sanya hannun ki a wani shashe na jikin sa kina wasa da shi ko ki sanya hannun ki chikin gashin kansa kina shafawa kina masa kukan shagwaɓa,wlh dole ya sauko idan kika masa haka saura kuma kije ki masa akasin hakan kin san idan kika kure sa ya zuchiya wlh mantawa zanyi da umarnin Ammi ya miki ɗan ban zan duka kina jina ko? Tun da Aunty farida ta fara wanna bayani hiyana ta sunkuyar da kai kasa kamar a gaban Aunty farida dan take "hiyana ba dake nake magana bane nace kina jina!? Kasa kasa chikin jin kunya tace "eh Aunty farida ina jin ki kuma Nagode" "good yanzu dai ki tashi ki fara aikin abubuwan da na faɗa miki idan da dama ki shiga kitchen ki masa girkin gargajiya da kanki dan na san ya gaji da chin abincin turawan nan tukunnan ma kin iya girkin ne? kar kije ki masa shirme ko da yake Auta na nan zata nuna miki duk abun da ya dace kiyi tuwon shinkafa da miyar egusi zaki masa dan yana matikar son tuwon shinkafa da miyar egusi kinji? "Eh Aunty farida naji kuma In Sha Allah zanyi yadda kikace "yauwa nama fasa Auta tayi maki ni zan koya miki yadda ake komai ina system ɗin yayan naki? "Ya tafi da shi" "ok to tun da ya tafi da shi idan lokacin yin girkin yayi sai muyi video call na nuna miki yadda zaki yi komai yanzu dai ki tashi ki fara yin abubuwan da na faɗa miki kuma saura ki sa hijabi idan ya dawo kaya zaki sanya waɗan da dasu da babu duk ɗaya ne kina ji na?" chikin sauri tace "eh Aunty farida naji" "good to tashi kije ki fara duk abun da ya dace" "to" hiyana tace tare da chiro wayar daga kunnen ta ta katse kiran

Layin Bgs ta fata kira bayan ta kammala waya da Aunty farida sau uku tana kiran layin amma shiru bai ɗaga ba, massage ta tubuta masa kamar haka "yaya Prince ya Aiki fatan ka isa lfy? Ni dai ba zan gaji da ce maka kayi hakuri ba" Tana gama turawa ta ajiye wayar ta buga tagumi tana tunani kamar daga sama taji karar wayar alamar shigowar sako chikin sauri ta duba sakon zubur ta miƙe ganin sakon yaya Prince ne "I'm good" shine abun sa ya rubuta a sakon murmushi ta fara yi tare da rungume wayar a kirjin ta tana faɗin "kai yaya Prince shine kana ganin kirana kaki ka ɗaga ko to zaka dawo ka same ni ne Allah yau na san me zan maka
Bgs dake zaune chikin katafaren Office na shi yana kallon ta ta chikin system ɗin dake gaban sa ya waro ido waje jin abun da tace kasa kasa yayi magana wadda ina da tabbacin ko shi bai ji me yace ba lokaci guda kuma ya ja tsaki tare da kawar da system ɗin daga gaban sa ya jawo cup ɗin tea ya fara sha a hankali

Ita kuwa sai surutun ta take tana juyi a tsakiyar ɗakin tayi nisa chikin abun da take wayar ta ya fara kara tana dubawa sai taga number yaya Aryan chikin sauri ta ɗaga kira tare da manna wayar a kunnen ta chikin nitsuwa ta fara magana "yaya Aryan ina kwana? Daga ɗayan ɓangaren diyana ta kwashe da dariya tana faɗin "Kamar wata mutuniyar kirki har da kashe murya wani wai yaya Aryan ina kwana to ba yaya Aryan bane Aunty diyana ce" dafe kai Hiyana tayi kafin ta saki cool murmushi ta fara magana "amma diyana baki da kirki wai har yanzu baki hankali ba" tsaki diyana taja kafin tace "ni ba wanan ne ya sanya na kiraki ba kin san me ni so nake ki che wanan mugu mai kama da ke ɗin maza ya sake ki ki dawo gida idan ba haka ba wlh shaiɗanun yara mugaye zaki haifa" lokacin guda hiyana ta ɗaure fuska chike da jin haushi zagin Bgs da diyana tayi ta fara magana "ke diyana kina da hankali kuwa kin san wanene yaya Prince awajena? miji nane fa ina mutuwar son shi ina kaunar sa fiye da rayuwa ta ina son farincikin sa fiye da nawa bani da buri a duniya da ta wuche yau na ganni gani ga shi mun zauna muna hira idan har ba zaki tayani son abun da nake so ba to bai ka mata ki zageshi a gaba na ba ni ina son kaya na a haka ke in ta kai ce miki komai yaya Prince yayi burgeni yake komai nashi kyau yake min komai idan yayi kyau take masa kamar dan shi akayi abun Kum.... Bata karisa ba diyana tace "ya isa haka hajiya soyayya sai yanzu na gane chewa nayi kuskure yanzu dai ba abun da zanche sai dai in che ki chi gaba dan son yaya Prince Allah ya sanya ya soki shima ko dan maraicin mu da wahalar da kika sha a kan mu Allah ya miki zaɓi mafi alkhari" ajihar zuciya hiyana ta sauke kafin ta chi gaba da magana "amin diyana ki rinƙa tayani da addu'a Allah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login