Showing 18001 words to 21000 words out of 363274 words

Chapter 7 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2526

bai amsa ba Hiyana tasa hannu ta taɓa shi ko motsi bai yiba a firgiche tafara jijjigasa tana ihu tana kiran sunansa Amma shiru
Chikin kiɗima hiyana tafito daga ɗakin tayi waje tana ihu



London United Kingdom

Tsaye yake a tsakiyar babban palon su hannun'sa ɗaya na rike da trolley ɗayan hannun kuma yana rike da wayarsa yana latsawa, sanye yake chikin black jeans da blue t-shirt ya rage tsawon gashin kansa, yanzu gashin bata wuche zuwa iya wuyar'sa ba, yana sanye da booth black colour a kafarsa dakuma p-cap shima baki hannun sa na ɗaure da wani haɗadɗen agogon daimon mai kyau da tsada fiskar nan kuwa babu alamar annuri akanta a taure take tam kamar an aiko masa da sakon mutuwa amma yayi kyau sosai laɓɓansan nan kuwa kamar yasa jan baki jaa sosai ga sajen sa a kwanche yasha gyara bakaramin kyau yayiba, faffaɗar kirjin san nan kuwa a tsaye dam dam kamar zai fashe ga damtsen hannun sa a chike kamar zasu yaga hannun rikar, almost 10mnt yana tsaye

A hankali Aryan ke sauko daga saman stair ɗin shima shigarsa iri ɗaya dana DON abun mamaki shima ya yanke gashin kansa ya rage mata tsawo, rike da trolley shima yana ja sauko wa yayi yazo dai dai inda DON ke tsaye, da wan nan sexy voice nashin ya furta sorry bro,DON bai tanka saba yaja trolley sa yanufi kofar fita, da sauri Aryan yabi bayan sa sukayi waje tare, da gudu rundunar jibga jibgan sojojin masu ji da lfy da karfi sunsha trenin suka nufosu, da sauri abdol ya karɓi trolley hannun DON, Shahram kuma ya karɓi trolley hannun Aryan, suka samu su a chikin haɗaɗɗun motachin, da akajera musu dan tafiyar

Aryan yadubi DON yace "muje a mota ɗaya koh,DON batare daya amsa ba yace "wai ina Aiman da Ahmad ne "ae tunjiya suka wuche naija Aryan yabashi amsa yana kallan fuskar sa kama hanya kawai DON yayi batare daya sake magana ba yanufi motar, da sauri abdol yabuɗe masa kofar motar, slowly ya shiga ya zauna, ɗaga hannu Abdol yayi ya sara masa san nan ya rufe kofar motar, zagayowa ta ɗayan kofar motan Aryan yayi, da sauri Shahram ya buɗe masa kofar a nitse ya shiga ya zauna Shahram ya sara masa san nan yarufe kofar motar
Da gudu sojojin suka hau nasu motochin su suka tadasu, da matsakai chin gudu suka nufi gate ɗin tun basu kariso ba security suka wangale masu gate ɗin, da gudu suka danna hanchin motochin waje,motar sojoji 2 a gaba sai motar su DON a tsakiya sai motochi 2 na sojoji a baya gudu suke shararawa a kan mikakkiyar titin

Aryan ya dubi DON yace sai dai fa mutafi da jet ɗinka dan kuwa nawa yana naija dashi su Ahmad suka tafi "Ok kawai DON yache, chikin kankanin lokachi suka isa Airport Already angama shirya komai su kawai a ke jira, batare da ɓata lokachi ba suka fito daga chikin moton su suka nufi kyakkyawa kuma haɗaɗɗen privet jet ɗin DON mai ɗauke da tambarin sunan'sa PRINCE SAFRAS suna shiga batare da ɓata lokachi ba jirgin yaɗaga sai malam Aminu Kano international Airport Kano Nigeria



More comments and share pls


*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*



💖 The talent troupe writer's 💖

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai


*Episode 5*


DON

Misalin karfe 5 na yamma jirginsu yayi landing a malam Aminu information Airport kano, wasu dan kare dan karan motochi 5 sukazo ɗaukansu ga motochi 3 chike da sojoji, basu wani ɓata lokachi a chikin jirgin ba suka fito tare suka jera, sai wani kara ɗaure fuska suƙe da ka gansu kaga wayan da akawa zuwa dole, musamman DON nashi daban ne, Abdol da Shahram suna biye dasu a baya,rike musu da trolley sojojin nan na ganin fitowar su suka jinro daga nasu motochin suka nufe su, Fahad na ganin fitowar su ya nufesu da sauri, yana ɗan murnushi hugging na DON yaje yayi yana faɗin "Wellcome back bro, hannu DON yasa yayi taying ɗin yana faɗin "missed U my blood "missed U too yayi maganar yana zare jikin sa daga jikin DON, yajuya yayi rungume Aryan ma, yana faɗin yaya Aryan nayi kewar ku sosai, rungume sa sosai Aryan yayi yace "nima nayi kewar ka sosai my blood, ganin DON yayi gaba ya barsu ne yasa Fahad ya saki Aryan da sauri sukabi bayan DON wajen motochin nasu suka nufa,nan take su Haidar suka fara musu sannu da dawowa ko kallan in da suƙe DON bai yiba bare su saran zai amsa musu, ya shige motar ya zauna yana yamutsa fuska, Aryan ma shiga mota yayi riƙe da hannun Fahad sai da suka zauna san nan ya dubi kannen nasu yace "yauwa to ku shiga mota muje gd koh sai mu gaisa a chan zaifi, da sauri suka koma chikin mota, drivers su kama motochin key da gudun gaske suka bar Airport ɗin gudu suƙe shararawa sosai a kan mikakkiyar titi, sai da suka kusa da bakin gate ɗin gida suka rage gudun motochin, batare da ɓata lokachi ba security daƙe tsaron gate ɗin su wangale musu gate ɗin a nitse suka kutsa chikin gd, kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin, Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar da gudu su kazo suka buɗewa DON da Aryan kofar motar, a nitse DON ya zuro kafafun'sa waje kafin ya fito gaba ɗaya bai bi ta kan kowa ba yanufi ɓangaren sa, Aryan ma ɓangaren sa yanufa riƙe da hannun Fahad suna tafiya suna hira, Yusuf ya karɓi trolley DON daga hannun Abdol yabi bayansa da shi Ahmad ma ya karɓi na Aryan daga hannun Shahram ya nufi ɓangaren Aryan ɗin, su Haidar kuwa kowa yakama kansa yayi part nasa

Ammi na zaune akan kujera a palan'ta tasha kwalliya chikin wata ɗankarekiyar lace baki da ratsin ja mai shegen kyau ga wasu gwala gwalan data zuba a wuya da hannu ta,ba karamin kyau tayiba inka ganta kace bata,wuce 25 years ba, Aunty farida tashigo da sallama ɗauke a'bakinta, da fara'a Ammi ta amsa mata sallamar, shigo chiki palon tayi ta zauna saman sofa mai zaman mutun 2,tana fuskantar Ammi "feeda dayake haka Ammi ke kiran Aunty farida feeda,ina junior yake "Junior yana wajen mardiya chewar Aunty farida " ok kawai Ammi tace tana kallan face ɗin Aunty farida "Ammi magana nakesan muyi dan Allah "ae feeda tun shigowar'ki Na fahimchi hakan, badamuwa ina jinki "Ammi daman, magana che a kan price, tun!bata kai karshen maganar ba Ammi ta ɗaga mata hannu, tana faɗin a'a feeda, kinsan dai bazan saka bakina a maganar bako,babu ruwana, dan kuwa kinsan mai martaba idan yayi magana baya chan'zawa "Ammi mun san Abba idan yayi magana baya sau'yawa, amma ae ke ki nasashi ya sauya magana koh, dan Allah Ammi, ki samana baki pls takarisa maganar kamar zatayi kuka "aa feeda babu ruwa'na wai ni ina ruwa da wani prince, ae wan nan ɗan Ummi ne ba ɗa naba kije kisamu Ummi ita tashiga masa amma ban dani "dan Allah Ammi kinfasan Abba yafi sauraren maganarki fiye da kowa a gidan nan" Feeda kin dai san in nache bazanyi abuba tofa bazanyin bane koh dan haka kibar maganar kawai,"to shike nan Ammi na barta barinaje namusu sannu da zuwa "baki Ammi ta taɓe tana faɗin eh lallai feeda ɗaure wa karya gindi,su da suke kannenki basu zasuzo su gaida kiba ke zakije ki gaida su lallai yaran nan suna abun dasu ka gadama
Aunty farida tamike tana faɗin kai Ammi kedai babu ruwan ki tsakanina da yan uwana ko inche yayyuna dan yanzu nabasu girma takai karshen maganar tana kokarin fita daga pallan bata tsaya ta jira amsar Ammi ba ta wuche abunta tana fita tayi part ɗin DON

Da sallama tashiga palan nasa babu kowa, kai tsaye betroom ɗin sa tanufa, yana tsaye gaban mirrow yana gyara gashin kansa,sanye yake da bakar jallabiya, da alama wanka yayi, jin sallaman ta yasa yaɗago green eyes nashi ta chikin miron yana kallan'ta, batare da ya juyo ba "yace Aunty babba yanzu nake tunanin inje in ganki, kafin inyi barchi
Harara wasa Aunty farida ta wurga masa tana fadin "daka ganniba dole kafaɗi haka nasan da banzoba ba zuwa zakayi ka nemeni'ba, slowly ya juyo ya zuba mata green eyes nashi nan kafin yace "a'a Aunty farida ae kema kinsan dole na nemeki


Karisa shigowa chikin ɗakin tayi tai, a bakin katafaren gadansa dake shinfiɗe da White bet shit ta zauna tana faɗin,"to ya hanya "Tafiyar da bada san ranmu mukayotaba Tafiyar dole,ya kae karshen maganar yana ɗaure fuska , guntun murmushi Aunty farida tayi kafin tace, "hmmm yanzuma nagama magana da Ammi kafin nazo nan, kara ɗaure fuska yayi yana faɗin "ai dama baki mata magana ba, da baki ɓata bakin ki bama dan nasan baza ta saurare mu ba jinjina kai Aunty farida tayi kafin tache,mudaiyi addua karkadamu inshaa allah komai zaitafi yadda kakeso,tana kae karshen maganar tamike,bari na dubo Aryan, batare da ta jira amsar saba tayi waje dan tasan ba amsa war zai yiba,"juyawa yayi yachi gaba da abun daya'keyi


Tana fita ɓangaren DON tanufi ɓangaren Aryan bakin ta ɗauke da sallama tashi palon babu kowa a palon sai sanyi A.c dake ratsa jikin betroom nashi tanufa, sallama tayi a bakin kofar kafin ta tura kofar tashiga kwanche ta same sa akan katafaren gadansa,idon sa a lumshe da alama barchi,yafara ɗaukan, jin an taba kofar ne yasa ya buɗe idon'sa da kyar, yana ganin ta ya dan saki fuska yana da kyar ya buɗe baki da murya irin na mai barchi yace "Allah ya barmana ke aunty mu wlh naso nazo,na dubaki amma barchi ya hanani, murmushi tayi tana faɗin "an dawo lfy my tagar "lfy lau lovely Aunty "to bari na kyale kayi barchin ka daman dai ina san inzo inji an iso lfy ne tun da lfy ba wata matsala ayi barchi lfy sai mun haɗu awajen chin abinchin dare ahuta gajiya,tana kae karshen maganar ta juya tanufi waje juyawa yayi shima yana fuskantar gefen dama yachigaba da barchin daya fara"

Misalin karfe 8 nadare gaba ɗaya family Abba sun haɗu a palon, dan chin abinchin dare, banda Aryan DON da kuma Fahad, sun zauna shiru suna jiran fitowar Abba, Ammi che ta katse musu shirun da chewa "nikoh meyasa mairo da salma basu zo bane kodai basu da lbr meeting martaba ya shirya
A tsiyache Aunty amarya tace ke Aisha kidaina ɓatamin su nan yarinya, kuma ina ruwanki da zuwar ta inba muna furchiba
"haba Aunty amarya daga tambaya chewar Ummi "ke Ummi baa kasa dake ba idan kemaɗin muna furchinne sai naji akule Aunty mardiya tache "a'a wlh ya isheki haka gaskiya bazaki zauna kina zagin iyayen mu, a gaban mu'ba tayi maganar tana nuna Aunty amarya ta hannu, hannu Aunty farida tasa ta ɗan buge bakin Aunty mardiya, tana faɗin to ke ina ruwanki ae dukkan'su iyayen'mune wan nan fadar'sune tsakanin'su
Umar ya ɗago rai a ɓache yana faɗin "to ae gashi muma Aunty mardiya rashin kunya kike neman kiyiwa mahaifiyar tamu, A'kule haidar yache "haba Umar kai bakaji abun da Aunty amaryan ke faɗe bane, dafe kai Khalid yayi yana faɗin, to ya isa haka ae kuyi shiru, amma ina ba wan da ya saurari Khalid sunki yin shiru wan nan ya faɗa wan nan ya faɗa abun hat'tafara zama kamar faɗa
Dafe kai kawai Ammi da Ummi sukayi suna kallan ikon Allah kowa kokari yake yakare ma haifiyar'sa wan nan abu dame yayi kama" sai faman kache na che suke abu har ta fara zama kamar faɗa

Kamar daga sama sukaji gyaran murya daga bayan su nan take, sukayi tsit dan kuwa ko basu juya ba sunsan mai wan nan voice ɗin tsaye yake a bakin kofar shigowa palon, yazura hannu a aljihun wandan,sa' yana kallon su fuskar nan tamkar batasan menene dariya'ba a daure take tam, a nitse yafara takowa izu chikin palon,wajen table ɗin yanufa,da sauri Haidar yamike, yaɗan jamasa kujeran zaman, baya tayadda zaiji daɗin zama gaba ɗaya matasan suka mike,ban da Khalid da Aiman da Yusuf jiki na kerma sukafara "faɗin sannu da fitowa yaya Aryan zama yayi batare daya amsaba yana binsu da ido jiki ba kwari suma suka koma suka zauna, murya na rawa Zahra tache "sannu da dawowa yaya Aryan
ko kallan in da take bai yi ba bai kuma amsa sannu nata ba ita ma,nan take kowa a chikin su yasha jinin jikin sa kallon fiskokin su yake sosai kamar mai karantar wani abu a tattare dasu

"me za'a zubamaka ne Aryan Ammi ta tambaya tana kallan fiskar sa, sai lokachin yadawo da kallansa kan Ammi kana yaɗan saki fuska calmly yace "abun daya dache kawai "ok to bintu kuzuba masa ferfesu kayan chiki da fraid rice Ammi tabawa masu aikin umarni, da sauri suka fara zaran plate dan su zuba masa,hannun su har rawa yake dan tsoran sa da sukeji suna kokarin zuba masa abin chin'ne
Aunty amarya ta daƙa musu tsawa "bashi zaku zuba masaba dan babu wanda ya isa ya zabawa ɗa na abun, da zai chi sai ni dana haife'sa kowa a gidan nan yana da nashi ɗan ae to kowa ya kula da nashi ba ruwan shi dana wani,dan haka tuwon shinkafa zaku zuba masa
Shiru yan aikin sukayi sun rasa umarnin wa zasu bi "kamar daga sukaji Aryan yana faɗin ku bar'shima kawai am ok, Aunty amarya zatayi magana sukaji takun tafiya ta bayan su dukkan su suka juya ban da Aryan, tafiya suke chikin kwanchiyar, hankali sun jero kamar ,sanye suke chikin jallabiya dukkansu Fahad bakin DON kuma fari tas, fiskar sun nan dukkansu babu wasa a ɗaure taku suƙe irin na chikakkun maza, kamar wasu yan biyu haka suka jero dan dai kawai DON yafi Fahad tsawo dakuma chika sai kuma kalar kwayar ido daya ban ban tasu Fahad kwayar idon sa baki ne DON kuma green amma ban da haka kaman'nin su ɗaya

A take palon yayi tsit suka kara nitsu wa dan duk gidan idan ka chire Abba Ammi da Ummi Aunty farida sai Aryan to kowa na gidan tsoran DON yake, har Aunty amarya tsoran sa take kamar me dan tasan DON ba wasa ba'a kawo masa wargi yanzu zai sumar da mutun, bakaramin tsoransa Aunty amarya ke jiba, da sauri Haidar yamike ya gyara musu kujerar da zasu zauna, a nitse suka zauna slowly DON ya ɗago yafara gai da iyayen nasu, da fara'a suka amsa masa, da sauri kannen nasu suka fara ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar kowa daga chikin su ba sai ma wayar sa daya chiro daga aljihun sa yafara latsawa
"prince me Za'a zubama,Ummi ta tambaya tana kallan face nashi, shiru ya ɗanyi kamar mai tunani sai kuma ya dawo da kallan sa kan Aunty farida,batare dayayi magana ba, Aunty farida ta gane me yake nufi da sauri tace,da masu aikin "ku zubawa kowa ferfesun kaji da chips kawai
Chikin sauri, suka fara zaran plate suna zubawa suna mika musu

A hankali Aryan ya ɗau spoon yafara shan ferfesu, wani kululun bakin chikine ya tokare wa Aunty amarya makoshi tana san tayi magana tana tsoran DON a zuchiyar ta take faɗin wai komai farida tace a gidan nan ko, basaso sai sun yarda, gashi dai ni tana haifi yaran nan amma bani da wani iko da su, maganar farida tafi nawa muhim manchi dole nayi maganin abun wlh bazayyiwu'ba

Da Sallama Abba yashigo palon yana sanye chikin jallabiya fara tas kai tsaye table ɗin yanufa,tun bai karisa zama ba suka fara gaishesa,Sai da duk suka gama gai'dashine ya haɗesu yabasu amsa ɗaya da sauri bintu mai aiki ta rari plate ta zuba masa abinchin zaɓin Aunty farida wato ferfesun kaji da chips
Tunda Abba yaga irin abinchin'ne a plate ɗin kowa dake wajen yagane zaɓin Aunty farida ne dan haka shima karba kawai yayi yafara chi

(sai yanzu nasan a inda yan gidan suka gado rashin magana dan kuwa shima Abba baya magana shiru shirune)

Shiru kake jin palan ba mai magana sai karan spoon kawai zakaji,da sautin A.c dake tashi

Bayan sungama chin abinchin ne DON ya mikewa ya nufi hanyar fita daga palon, harya kai bakin kofar sai kuma ya juyo yana faɗin "dukkan ku mazan nan kusameni a ɗaki,ke kuma Zahra karfe 10 dai dai ina bukatar ganin ki bai jira amsar su ba yayi waje, da sauri suma suka muke sukabi bayan'sa
Suna fita Abba ya dubi su Ammi yana faɗin "sun aikata wani abun da ba dai dai bake nan,Ammi dai shiru tai bata bashi amsaba hakama Ummi
aunty amarya che tache "zagina mana sukayi, Shiru Abba yayi dan yasan halinta sarai yanzu haka ita ta takalo faɗan "ranka shidade inasan magana dakai chewar Ammi, Abba zaiyi magana
Aunty amarya tarigashi dache'wa "to ae yau ba ranar ki bane bake kike dashi ba sai ki bari sai yadawo dakin ki, shiru Ammi tai dukkansu ba wanda yasake magana

DON na shiga dakin sa ya zaune a gefen katafaren gadon sa yana jiran kannen nasu
Da sallama suka shigo gaba dayan su
Aryan ya wuche ya zauna a kusa da DON a bakin gadan, shi kuma Fahad hayewa yayi kan gadon abunsa ya kwanta ya dauko wayarsa yafara latsawa,domin kuwa yariga da yasan dalilin kirannasu to shi baya chiki maganar

Dukkan su zama sukayi a saman sofan dake ɗakin Khalid ma agefen gadon yazauna suka sa DON a tsakiya shida Aryan ryan
Almost 10mnt DON bai che dasu komai ba kamar ma baisan da zaman su a ɗakin ba, shiru sukayi suna tunanin me yasa ya kira'su kodai yaji abun daya faru a palo ne calmly yafara magana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login