Showing 282001 words to 285000 words out of 363274 words

Chapter 95 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2601

kawar da kansa gefe yayi alamar ko in kula

after some minutes

Palon yayi shiru ba abun da kake ji sai sautin shesshekar kukan diyana ta kankame hannun Aryan sai kuka take,
ruwan sanyi roba uku bgs ya zubawa Aryan amma shiru shiru Aryan bai farfaɗo ba,dafe kai bgs yayi da kyar ya iya buɗe bakin sa saboda bacin rai yace "Abba dan Allah ku ɗauke gawar matar nan ban son ganin ta tana kara bakan tamin rai tana kara sani naji kamar zuciyata zata fashe ta fito waje" cikin karyewar zuciya Omar yace "Abba muje mu sallace ta ko?" "aa Omar ni bazan sallaci Hajara ba sai dai ku" shiru Omar yayi yana mai tausayin mahaifiyar tasu a kule Ammi tace "idan na isa da ku ku tashi kuje ku shirya makara akira mai mata wanka ku sallace ta ku kai ta ma kwancin ta" a sukwane bgs ya ɗago kai yana kallon Ammi ɗaure fuska sosai Ammi tayi alamar bawa sa a tattare da ita mai da kansa yayi ya sunkuyar.
jiki ba kwari su Khalid suka mike suka fice daga palon ya rage daga matan sai bgs da Abba.

After 3 days

Har yau Aryan bai fargaɗo ba tashin hankali ba kaɗan ba bgs ya shiga dan zuciyar Aryan gab take da bugawa gashi bai farfaɗo ba bare su bashi hakuri su taushe sa. Ko yaushe diyana tana kusa da shi tana kuka anyi rarrashin duniya taki yin shiru kuma taki matsawa kusa da shi.

Yauma kamar kullun misalin karfe 8 na safe tana kwance kusa da shi tana kuka kasa kasa,idon ta duk sun kunbura ta sauya kamar ba ita ba bgs na zaune gefen ta ya zuba musu ido yana jin tausayin su na ratsa shi Aunty farida na gefen bgs tasamu lfy sumul sumul abun ta. Su Khalid kuwa suna wajen ansan gaisuwar rasuwar Aunty Amarya

A hankali Aryan ya waro idon sa waje tare da ɗaga hannun sa ɗaya ya ɗaura bayan diyana dake kwance kusa da shi ta bashi baya tana kuka l. kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace "my jidda me ya sanya kike kuka? Ko so kike ki ƙaramin ciwo kan ciwo ne? kin san fa kukan ki ciwo ne agareni a yanzu bayan Abba bgs Aunty farida ke kaɗai nake kallo naji daɗi a raina ki dai na kukan nan haka ya isa, ji nake kamar kina chakamin mashi a zuciya ta idan kina kuka" a sukwane diyana ta juyo cikin shessheka tace "yaya Aryan dole zan yi kuka ba kai ne ka... Bata karisa maganar ba ya rufe mata baki da hannun sa tare da jawo ta jikin sa yana ɗan bubbuga bayan ta sai lokacin idon da ya sauka kan bgs da Aunty farida,yana kokarin yi musu magana bgs yayi saurin ɗaga masa hannu alamar yayi shiru dawo da kallon sa kan diyana yayi cikin zolaya yace "my jidda ba kince baki so na ba me kuma ya saki kuka dan zan mutu?" "Yaya Aryan ka dai na faɗin haka wlh bazaka mutu yanzu ba kuma Ni bance bana son ka ba ina son ka mijina ina son ka sosai" "eyeee babyn yaya Aryan yau ta dai na jin kunya har da cemin miji da ina da lfy danayi sujudur shukur na godewa Allah" miƙewa bgs da Aunty farida sukayi suka bar ɗakin dan sunga Aryan da diyana sun fara sakin layi.
Rungume ta sosai Aryan yayi yana rarrashin ta ita kuwa sai zuba masa shagwaɓa da kalaman love take "my jidda waya koya miki kalaman soyayya" ya tambaya yana gyara mata kwanciya ɓoye fuskar ta tayi a girjin sa kafin tace "a littfin Romeo na Princess Teema na koya" shafa gashin kanta ya fara yi yana faɗin "wayace ki rinƙa karanta Novel?" "Yaya Aryan ina karanta Novel ne dan na koyi yadda zan rike ka" waro ido waje yayi tare da sakin ta yana kokarin mikewa zaune,da gudu ta mike ta bar ɗakin,bin bayan ta da kallon yayi har ta fice murmushi ya saki kafin yace "Nagode wa Allah daya nunamin ranar nan da jidda ta ta sauya har da zubamin kalaman soyayya" ya kai karshen maganar tare sa zuro kafar sa kasa ya mike da kyar yana taga taga har ya fice daga ɗakin ya nufi wajen Abba.

Yau ne Abba ya kira meeting na karshen akan issue marigayya Aunty Amarya, gaba ɗaya family sun taru a palon.
Abba cikin nitsuwa Abba ya fara magana "Aryan na san baka sani ba Allah ya yiwa mahaifiyar ku rasuwa tun shekaran jiya ina fatan kuma zaku yafe mata abun da ta aikata muku? Ni dai har ga Allah na yafe mata haka Aisha da Hauwa'u suma sun yafe mata kuma zan zo naji kun faɗa da bakin ku kun yafe mata sanna ku cigaba da neman mata gafara wajen Allah" a tare suka amsa da "Allah ya yafe mu tare Abba mun yafe mata" ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin ya cigaba da cewa "to sai batu akan mulki munyi magana da Aliyu zai dawo Nigeria next week ya ansa mulkin sanna na sanya antona asirin da Hajara ta binne a kan mulkin nan,gaba ɗayan ina mai sallamar ku akan ku koma bakin aikin ku tun da komai ya dai dai tun" "no Abba komai bai dai dai tu ba dole na kama wanda ya sanya aka kama su Khalid" cewar bgs jinjina kai Abba yayi kafin yace "haka ne to Allah ya bada Sa'a akoi wani mai magana!? Shiru palon yayi Aryan ya sunkuyar da kai kasa yana mai takaicin rasuwar da Aunty Amarya tayi ba tare da ta nemi yafiyar mutanen da ta cutar a rayuwa ba.

"Abba ina da magana" cewar hiyana nan take kallon ya dawo kanta "to hiyana ina jin ki menene maganar taki faɗi" sunkuyar da kanta kasa tayi cikin jin kunya ta fara magana "Abba kasa yaya Prince ya sake ni bana son shi bana son zama da shi mugune" a sukwane bgs ya ɗago yana kallon ta gaba ɗaya su Khalid kara waro ido waje sukayi suna kallon ta Abba da Ammi ba karamin girgiza da jin maganar nata sukayi ba daurewa Abba yayi yace "lfy hiyana kike son yayan ki ya sake ki!? "Abba ba lfy ba yaya prince ya cutar da ni arayuwa ta sosai nayi hakuri har nagaji bazan iya ba wlh Abba yaya Prince yana gab da kashe idan kuka sake bari na da shi" nan hiyana ta shiga basu lbr duk abun da ya faru na muguntar da bgs ya rinƙa yi mata daga farko har karshe.

Tirkashi nan take ainihin ɓacin rai da tashin hankali ya bayyana karara a kan fuskar Abba da Ammi cikin fushi Abba yace "tabbas babu makawa Safras zai sake ki yanzu kuwa ba sai anjima ba" waro ido waje bgs yayi tare da sunkuyar da kansa saka kamar mai tunani wani abu "Auta ku tashi ku je ɗaki bari muyi magana" cewar Aunty farida mikewa Zahra hiyana diyana amrat lamrat sukayi suka bar palon,kallon Omar da Haidar Aryan yayi tun bai yi magana ba suka mike da sauri suka fice.

"Safras ina mai umartan ka da ka rubuta takardan sakin hiyana ka kawomin yanzun nan" cewar Abba Aunty farida na kokarin yin magana Abba ya dakatar da ita yana faɗin "kar wanda ya samin baki a maganar nan dole ya sake ta ashe Safras zaka iya kashe yar uwar ka dan kiyayya kajefota daga sama ta faɗa cikin ruwa sanna duk bai isheka ba sai ka harɓeta da bindiga? To wlh ka rubuta sakin ta yanzun nan ka bani a nan na aura mata wanda take so" mikewa bgs yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "bari na kawo maka Abba" mutuwar zaune su Aryan su kayi lallai bgs wato ma bai damu ba bari ya kawo akar dan sakin tab


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By
Star Lady

Ina godiya da rashin comments da ba ku min 2 days kwata kwata kun dai na comments ko to yayi Allah ya bar zumunci 🙄

Wanna page ɗin naku ne maman amir da Aisha baita jidda my mum Allah ya bar kauna🥰


Page 44

Aryan

"Hello Aunty farida pls ki taimaka min ina cikin damuwa wlh my jidda gudu na take bata yarda mu haɗu da ita ba yadda ban yi da itaba akan ɗazun ta kawomin coffee amma taki" daga dayan ɓangaren Aunty farida tace "oh Allah ku dana ke ganin na gama da case na kunma kenan? To bari ina zuwa yan zun nan zan ta zo kuwa" murmushi yayi kafin yace "tnks my lovely Aunty shi ya sa nake son ki" murmushi itama tayi tana faɗin "ai ni burina komai ya dai dai ta tsakanin ku da matan ku ku samu ku haifamana baby's muzo mu ɗauka dan duk wanda matar sa ta fara aihuwa to baby awaje na zai zauna" cikin sauri yace "aa Aunty farida nan fa ɗaya ni gaskiya na riga da babyn Yusuf sai dai ki jira na bgs" tsaki Aunty farida taja kafin tace "bgs ko ɗan albarka zanyi bayani ne" "eh gaskiya Aunty farida naji daɗi da kuka masa haka yanzu zai san darajar sister" girgiza kai kawai Aunty farida tayi dan tasan da bgs da Aryan bakin su ɗaya yanzu ba karamin aikin Aryan bane idan ta faɗi wani maganan yaje ya mai da wa bgs "kai dai bari na turo maka jiddan ka" bata jira amsar sa ba ta katse kiran dan tasan wani tambayar zai jefo mata.

A palo ta isko diyana hiyama Zahra A'isha Zainab suna hira "my diyana tashi kozo muyi magana da ke" da sauri ta mike ba nufi Aunty farida hannun ta Aunty farida ta kama suka wuce ɗakin Ammi zaune suka isko Hajj fateema saman gado tana latsa waya,cikin harshen larabci Aunty farida ta sanar da hajj fateema abun dake faruwa na diyana taki yarda da Aryan,a fusace Hajj fateema tace cikin harshen larabci "gaskiya ku kuke biyewa yaran nan sati uku mijin ta na binta tana guduwa ina kuke son yasa ransa da wanne ɗaya zai ji rashin uwa ko rashin mata kai jama'a kuma Ammi sai ta zuba musu ido? To ni wanna iskanci ba dani ba tun wuri yaran nan su kwanshi kayan su yanzun nan ba sai anjima ba su kuce ɗakin mazajen su yau naji tsiya to waje suke son mazajen suje su nemi mata ne? Shima Aryan ɗin da nashi laifin tun yaushe ka make ta amma sai ka tsaya ka biyewa yarinya tana juyaka kai daɗi soyayya ko? To su diyana dai basu yi hankalin sanin soyayya ba idan ka biye musu gasuwa zakayi" "oh god ke Hajj fateema gaskiya kin cika zafi ai dake da Prince ɗin ba banbanci wajen zafin rai nifa yanzu na kawo tane mu mata nasiha kuma mu mata dabara yadda zata rike mijin ta" guntun tsaki Hajj fateema taja kafin ta mike ta nufi waje tana faɗin "ke ki zauna ki lallaɓata ni bari ki gama naje na kora su lamrat su wuce ɗakin mazajen su ga garinma da hadari ban iya ɗaukan iskan cin nan nasu" ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, girgiza kai Aunty farida tayi dan daman tasan halin hajj Fateema da ɗaukan zafi akoi ta da zuciyar bala'i. "Aunty farida me ya faru na ga Ummin mu tana masifa da larabci" ɗan buge mata baki Aunty farida tayi kafin tace "baa cewa uwa tana masifa kice meya sa take faɗa ko me ya ɓata mata rai kinji? Karki sake cewa babban mutun yana masifa" gyaɗa mata kai tayi tana faɗin "to" "yauwa yanzu kin san me nake so dake" girgiza kai tayi alamar a'a "yauwa kin san dai ni mai son ki ce ba zan so ai miki wani abun da ba dai dai ba yanzu na jiyo kishin kishin yaya Aryan naki yana neman wata mata zai kara aure wai tun da ke baki son shi baki bashi kulawa kina gudun sa" ihu diyana ta fasa tana faɗin "Aunty farida dan Allah kice masa ni bana son kishi kishiya muguwa ce ba kin ga abun da inna habiba ta mana ba dan Allah ki faɗa wa yaya Aryan ina son shi kuma kome yake so wlh zan masa ni bana son ya kalli ko wace mace sai ni ka ɗai wayyo Allah zan mutu idan akan min kishiya" abun ma dariya yaso bawa Aunty farida su diyana har da cewa zata mutu oh wanna yarinya "my diyana kiyi shiru kiji me zan faɗa miƙi" dai na ihun tayi amma bata dai ma hawaye ba "yanzu kin san me? Girgiza kai tayi alamar a'a "good ai yanzu kece kawai zaki iyasa Aryan ya fasa neman Auren da yake idan kika fara bashi kulawa kina nuna kulawan ki akan duk wani abun da yake so ki rinka gudun duk wani abun da baya so kirinƙa zama kusa da shi ko wajen Ammi sau ɗaya zaki rinƙa zuwa a rana da safe kuje ku gai da Ammi Abba Ummi shike nan ki koma kusa da mijin ki ki zauna daman ke ba sai an miki magana akan kwalliya ba kin iya sai dai yanzu ki rinƙa sawa yaya Aryan kana nan kaya irin yan wando zuwa cinyan nan da yar riga karama sanna ki rinƙa yi masa shagwaɓa kamar dai yadda na san kin nan karki yarda ki rinƙa zama saman kuje idan kuna tare ajikin sa zaki rinƙa zama,wani lokaci idan kuna zaune kice masa ya tashi ya goyeki cikin shagwaɓa fa zaki faɗa masa hakan kirinƙa yi masa kalamai masu daɗi ki dai na shirmen da kike ɗin nan ki nitsu ki kama kan ki sanna cikin wasa ki rinƙa saka kananan kayan sa wani lokaci haka idan kuna tare nasan kasan ku da sanyi to idan kun koma idan ya sa manyan kayan sanyin san nan in kuka kwanta a gado ki rinƙa shigewa cikin rigan nashi cikin shagwaɓa kice yaya Aryan sanyi nake ji idan ya dawo wajen Aiki ki ansa abun dake hannun sa ki cire masa ta kalma ki masa oyoyo first tare da bashi hot kiss sanna ki cire masa ta kalma karki yarda ki barshi yana wanka shi kaɗai tare zaku rinƙa yi idan kika barshi yaje wanka shi kaɗai zai fara tunanin baki son shi har ya fara tunanin wata mace to karki yarda ki bashi chance da zai tuna wata idan kunyi wanka ki rinƙa taya shi goge jikin sa ki taya shi sa kaya idan kuna cin abincin ki rinƙa bashi a baki kina masa hira mai daɗi kina haɗawa da shagwaɓa" tun da Aunty farida ta fara magana diyana tayi shiru ta sunkuyar da kai kasa kamar malama "my diyana kar kiji kunyata ni Auntyn kice muje next topic dukka kannena nasan halin su fiye da tunanin ki na san abun da suke so da wanda basa so Aryan bgs Fahad mutane mai matsananciyar sha'awa sosai sai kun daure ni nama yi mamakin da har yanzu dake da hiyana da Amrat baku samu ciki ba to dai yanzu daurewa zakuyi har ku saba sai magana ta gaba idan kuna tare a gado karki rinƙa kwanciya shiru ki kyale sa sai dai shi yayi ta wasa da ke ba,duk abun da ya miki kema ki mai da masa da martani karki bari ya fiki idan kina bari yana finki to zai karo miƙi kishiya nasan bazaa rasa gumba Larabawa da kayan mata a jakar Ummin ku ba dan duk zuwan da zatayi tana kawo min bari na duba muku zan sa a ɗauko muku kayan gyara da turaruka da sabulan gyaran jiki daga Maiduguri yanzu dai tashi kije kiyi wanka ki tsala kwalliya da kayan barci masu kyau yadda na sanki da bulbula turaren nan haka zakiyi ki tashi kan yaya Aryan karki bari yayi tunanin wata kinji? gyaɗa mata kai tayi tare da mikewa duk jikin ta ya mutu Aunty farida ta kashe mata jiki tana kokarin fita Aunty farida ta kuma cewa "my diyana kar ki manta duk lokacin da mijin ki ya nemeki kika ki biya masa bukatar sa zaki shiga tsinuwar Ubangiji sanna ina kara tunatar da ke akan duk abun da yake so matikar bai taɓawa Allah ba ki taya shi son wanna abun Allah zai baki lada kuma ya saki a aljanna idan kuma kinga mijin ki yana kokarin kauce hanya kiyi gaggawar dakatar da shi da nuna masa illar hakan ta yadda zai fahimter a ta kai ce dai ki mai da mijin ki tamkar baby sabon aihuwa jeki shirya da wuri" to ta amsa da shi sanna ta fice da sauri ajiyar zuciya Aunty farida ta sauke kafin tace "to na gama da matsalar Aryan saura na Prince bari na samu hiyana in jarraba mu gani ko a dace Allah ka dai dai ta mana la muran nan" ta kai karshen maganar tare da mikewa ta binciki trolley Hajj fateema ta fito musu da kayan gyara ta nufi waje tana faɗin "diyana manya zakiyi bayani yau ai da Prince da Aryan da Fahad matan su sai sun haɗa da sallan dare da hakuri musamman Prince ina tausayawa hiyana baiwar Allah zakiyi bayani har da cewa baki son shi bari ya rike ki a rannan ne zakice baki son shi da tushe yar kani".
Saman kadon ɗakin su diyana ta ajiye musu kayan gyaran ta dubi Kofar toilet da diyana ke ciki tana wanka tace "my diyana idan kin fito ga naki a kan gado ki ci kaɗan kaɗan ki ajiye sauran karfa kici dayawa to idan ki kaci dayawa babu ruwana bari na kaiwa su Auta nasu" daga cikin toilet diyana tace "to" "ah ah haf my diyana wayace miki ana magana a toilet idan kikayi magana a toilet Mala'ikun Allah zasu tsine miki karki sake" daga cikin toilet ɗin ta kuma cewa "to Aunty farida ba zan sake ba"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login