Showing 261001 words to 264000 words out of 363274 words

Chapter 88 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2585

Fahad gashi diyana ta sa dole ta bishi,kumbura kumatu tayi a ranta tana faɗin "shi yaya Fahad ɗin nan sai yayi ta matse mutun baya gajiya ko kaɗan" ta shagala da tunanin sai jin sa tayi ya sureta sama ya saɓa ta a kafaɗa ya fice da ita
suna fita diyana ta gyara kwanciyar ta saman kujera tana faɗin "haka kawai zaki dameni ni kam Allah ma ya sa yaya Fahad ɗin nan ya miki abun da yaya Aryan yamin kila kyayi hankali, rumtse idon tayi kamar mai barci.

To masu karatu sai muleka yola muga me suke ai katawa

Yola

Yaya bello kamar zai yi kuka haka suka fito shi da hasana riƙe da bakkon kayan su su inna suna biye da su a baya har wajen motar da Ammi ta aiko akan a ɗauko su sukaje gaba ɗaya jama'ar kauye sun fito yimusu sallama kuka hasana take sosai dan ita gani take kamar idan taje birni ba zata dawo ba.

gidan baya na motar yaya bello ya shiga hasana kuwa tana tsaye tana kuka,dafa kafaɗar ta innar bello tayi tana faɗin "ba komai In Sha Allah ki shiga ku tafi" juyowa tayi ta rungumi inna cikin shesshekar kuka tace "inna dan Allah ki sa baki a bani hajjo mu tafi da ita" kallon maman hasana dake tsaye rike da hannun hajjo innar bello tayi kafin tace "inna wuro dan Allah ki bata kanwar tan nan mana tun jiya aketa ta rokon ki amma kinki ba abun da zai faru tun da kika iya barin hasana ta tafi itama hajjo zaki iya bada ita" shiru maman hasana ta ɗanyi kafin ta saki hannun hajjo tana faɗin "to kije Allah ya tsare min ku" da murna hasana ta rungumi hajjo yarinya yar shekara 14 suna ta farinciki suka shiga mota. gaba ɗaya jama'ar kauye sai addu'a da fatan alkhari suke musu,sai da motar ta kurewa ganin su sanna su inna suka koma cikin gida.

Maiduguri

Koda suka isa gidan Aunty farida kwance suka sameta saman katafaren gadon ta idon ta buɗe tana kallon sama ko motsi bata yi kallo ɗaya bgs ya mata ya fahimci irin ciwon Ahmad ne kallon dadyn Junior dake zaune gefenta yayi calmly ya fara magana "Aryan zai cire mata ruwan nan da aka sa mata zamu wuce da ita kano anjima yanzu dai ina zuwa"yana kai karshen maganar ya fice da ga ɗakin
miƙewa Aryan yayi ya cire mata ruwan dake jikinta suka fito palo shi da dadyn Junior.

To kunji halin da Aunty farida ke ciki mu waiya kano kuma muga wani waina su hiyana ke toyawa

Kano

Zahra hiyan Sun gama shirin su tsab yaya Khalid da kan sa ya ja su a cikin motar sa suna tafiya suna yar hira Zahra a gaba mota hiyana a baya "yaya Khalid ayya zaka kai mu wajen lallema idan mun gama gyaran gashin?" chewar hiyana kallon ta yayi ta cikin mirror motar kafin yace "yanzu haka addu'a nake Allah ya sanya kar bgs ya nemiki har muje mu dawo nayi gangancin fita da ke ba tare da izinin sa ba sai yanzu ma nake nadamar yin hakan" "to ai yaya Prince bay...bata karisa maganar ba tayi shiru kasan cewar ta tuna tun da yaya Prince bai sanar da yaya Khalid akan tafiyar su ba to tafiyar sirri ce bai kamata ta sanar wa kowa ba amma ta sha ruwan mamaki ya akayi yaya Prince bai sanar da yaya Khalid ba ya sanar min?
tayi nisa cikin tunani Khalid ya taka wata wawan birki wadda ya sanya sai da kanta ya bugu da jikin kujerar gabar motar.
A zafafe ta ɗago kai dan taga me ya sanya yaya Khalid taka irin wanna birki haka,wata mota ta gani kirar siyasa baka mai bakin glass ne ta sha gabar su kan kace me jibga jibgan bakaken mutane sanye da bakin kaya sun rufe fuskar su baka iya ganin komai sai ido ne suka fito daga cikin motar
Khalid na kokarin ɗaukan wayar sa babban cikin su ya buɗe kofar motar nasu ya damko Khalid ya fitar waje ba tare da ɓata lokaci ba suka tura Khalid cikin motar su sanna suka fito da hiyana da Zahra nan fa suka ruɗe sun rasa wacece ogan su yace su kawo dan Zahra da hiyana da bgs duk kamannin su ɗaya sak kamannin Ammi suka ɗauko. Fito da wani hoton ogan nasu yayi da wata murya mara daɗin ji ya dubi su Zahra ya nuna musu hoton yana faɗin "wacece wanna a cikin ku? Murya na rawa hiyana tace "ni ce" da sauri Zahra tace "ba ita bace ni ce" tsawa ya daka musu tare da fito da bindiga ya saita su yace "idan baku faɗa min wacece ba sai na harbe ku dukkan ku biyu!!" "wlh karya Aunty Zahra take ni ce ba ita bace" chewar hiyana damko wuyar hiyana yayi ya turata cikin mota suka shiga suka tada motar da gudun gaske suka bar wajen

durkushewa kasa Zahra tayi ta saki kuka mai ban tausayi tana faɗin "me yasa zaki ce kece Aunty Hiyana? why ba zaki bari su tafi da ni ba tun da yaya Khalid na hannun su ni nasan yaya Prince ya fara son ki yanzu idan suka kashe ki shike nan ba zai sake son wata mace ba" tana kuka tana surutai kamar mahaukaciya.

Sai da tayi kukan ta mai isar ta san nan ta miƙe ta koma cikin motar su cikin sauri ta ɗauko wayar ta tafara kiran layin Bgs sau uku tana kiran sa bai ɗaga ba kiran layin Aryan tayi shima har sau uku bai ɗaga ba juyawa tayi gabas da yamma hanyar shiru babu motsin kowa lokacin guda mugun tsoro ya dira a ranta gashi ita bata san haryan komawa gida ba dan ba fita take ba ko school kai ta ake kuma a ɗauko ta chan wani dabara ya faɗo mata akan ta kira layin Abba
cikin sauri ta fara kiran layin Abba shima bai ɗaga ba ihu ta saki tare da yin wurgi da wayar gefen titi dan bakin ciki
tarwatsewa kaca kaxa wayar yayi,sai bayan da ta fasa wayar ne kuma ta fara nadama yanzu dame zata nemo gida akan azo a ɗauke ta fita tayi daga cikin motar ta fara tafiya da kafa tana tafiya bata ma san in da ta nufa ba tanayi tana kuka kamar zararriya.


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu to masoyan yaya Khalid masoyiyan hiyana masoyan Zahra aikin tsayuwar dare ya ganku fa amusu addu'a gashi zaku nan gidan Abba basanan suna Maiduguri akoi chakwakiya fa hmmmm



[7/23, 1:44 PM] Maman Aslam: 💖The talent troupe writer's 💖




💋Duk Karfin Izzata 💋

By Star Lady







Page 35


Sosai take kuka har voice nata ya dai na fita sosai ta fara ganin dishi dishi takalman kafar ta ta cire ta riƙe a hannu ta cigaba da tafiya har ta ɗan yi nisa da motar su,kaɗan kaɗan ta jiyo ringin watar yaya Khalid da ya bari cikin motar su tana kokarin juyawa ta koma wajen motar wata katuwar jib baka mai glass baki tayi parking a gaban ta tsayuwa tayi tana kallon motar bata ankara na sai ganin jabir tayi a gaban ta juyawa tayi tana kokarin komawa wajen motar su dan tayi picking call ɗin da ake kiran yaya Khalid. Wasu jibga jibgan fararen mutane kiran turawa ne suka sha gaban ta kallon su take ɗaya bayan ɗaya
Waya jabir ya ciro daga aljihun sa ya danna kiran tare da manna wayar a kunnen sa

Jim kaɗan akayi picking call ɗin "hello dady" daga ɗayan ɓangaren dady yace "hello jabir burinka ya cika ko ka kama yarinyar da kake son ne?" dogon tsaki yaja cikin faɗa yace "dady ni fa ban gan taba sister ta kawai na gani wato dady daman da ka kirani kace min ga yarinyar ta fito wato rai na min hankali kayi ko? To wlh bakayi hakan aban zaba zaka biya" cikin muryan rarrashi dady yace "calm down my son kasan dai ba yadda za'ayi na baka wrong information ko? Kamar yadda na faɗa maka haka yarana suka faɗa min kasan shekara nawa sukayi suna min aiki wajen tsare hanyar fita gidan Abubakar saraki dan suga mai shiga da mai fita? kasan tsawon lokacin da na ɗauka ina aiki da su kuwa? basa bani information akan abu har sai sun tabbatar dan haka ka tambayi ita yarinyar da kace ita kaɗai ne awajen kaji ko kuma ka ɗauko ta ka taho da ita sai ka kirasu awaya..... jabir bai bar dadyn sa ya kai karshen maganar ba cikin tsiwa yace "dady ni zaka koyawa yadda zanyi aiki nane? ba ruwan ka da yadda zanyi tun da kai ka gaza ni zanyi kaya na" yana gama faɗin hakan ya katse kiran tare da tura wayar aljihun sa ya dubi yan daban nasa "kai ku kama min ita ku sata a mota mu wuce da ita" jin haka ya sanya Zahra ta fasa ihu tana kokarin gudu dan tasan halin jabir,damko ta yan koran nasa sukayi suka turata cikin mota suka shiga suka bar wajen da gudun gaske.

Katafare parking space dake gidan Abba motar su yaya bello tayi parking buɗe kofar motar yayi ya fito hasana ta biyo bayan sa riƙe da hanmun hajjo
Tsayuwa sukayi suna kallon gidan ba karami tsorata hasana tayi da ganin gidan su Ammi ba kankame yaya bello tayi suna bin gidan da kallo shi dai yaya bello bai ruɗe sosai ba kasan cewar yana shiga birni.
sun shagala da kallon gidan Haidar ya katse da cewa "muje ko?" dawo da kallon su kan haidar sukayi cikin sauri hasana tace "laaa kaga mai kama da baban su diyana" kallon Haidar da kyau yaya bello yayi aiko zancen hasana gaskiya ne Haidar kamannin sa ɗaya da baban su hiyana Allah bai iko jini ɗaya ya wuci wasa
ganin kamar basu da niyar tafiyane ya sanya Haidar yayi gaba yana faɗin "idan kun gama kalle kalle naku zaku iya shigowa" cikin sauri suka bi bayan sa kai tsaye part ɗin Ammi suka wuce

zaune saman sofa mai zaman kanta 2 suka isko Ammi tasha kwalliya da dankareriyar kace pink color wuyar ta da hannun ta cike yake da gwala gwalai ta sanya alkyabban ta baki a saman kayan nata sai kyalli take tana ɗaukan ido kallon ɗaya zaka mata ka gane tana cikin kwanciyar hankali.

A kasa saman lallausan karpet ɗin palon su yaya bello suka zauna hasana sai kallon palon take
cikin girmamawa yaya bello yace "inawuni Ammi?" "Bello ku tashi ku zauna saman kujera mana" ba musu suka tashi suka zauna
Suna zama hasana ta miƙe zubur tana faɗin "lumewa nakeyi ba zan zauna ba zan nitse kasa,shi kan sa yaya Bello daurewa yake ya kame jikin sa waje guda ji yake kamar shima ya miƙe amma kasancewar yaga Ammi a zaune bata nitse bane ya sanya ya daure ya cigaba da zama bai tashi ba
Murmushin Ammi tayi kafin tace "to hasana zauna a saman karfe ɗin ba damuwa" zama tayi suka gaisa da kyau ba karamin daɗi sukaji ba sai kallon Ammi hasana da hajjo ke yi
waya Ammi ta ɗauko ta fara kiran layin Zahra amma sai taji wayar a kashe mammaki ne ya kama tayaya zaa ce wayar auta a kashe abun da bai taɓa faruwa ba
ganin tunani bashi da wata mafita ne sai ta kira layin Khalid shi kuma ta kira bai ɗauka ba
sau biyu tana kiran sa shiru shiru hasbunallahu waniimal wakin take mai mai tawa a ran ta dan tun safe takejin faɗuwar gaba yanzu data kira layin su Zahra sai ji tayi faɗuwar gaban ya karu ko sunan Zahra ta tuna a ran ta sai taji kirjin ta na dukan uku uku
Yaya Bello ya lura da halin da Ammi ta shiga lokaci guda ganin hakan ya sanya ya tattara nitsuwar sa cikin girmamawa ya fara magana "Ammi lfy naga yanayin ki ya sauya?" Ammi ta san wanene yaya bello dan haka bata ɓoye masa komai ba ta sanar da shi faɗuwar gaban da take ji tun safe sanna idan ta tuna sunan Zahra ko hiyana sai taji faɗuwar gaban ya tsanan ta .
"to Ammi ina Zahra da hiyana nan suke?" Chewar yaya "ina ganin kamar suna wajen mazajen su ni ban sani ba nan na tafi na barsu suna hira amma kafin na tafi ita hiyana mijin ta ya kirata kaga kenan suna tare kiran su nake akan suzo ku gaisa kafin a kai ku gidan ku amma bari na kira shi ɗin" tana kai karshen maganar ta shiga kiran layin bgs,sau biyu shi ma tana kiran layin sa bai ɗaga ba wani tunani ne ya faɗo mata "anya wayan nan ba suna tare da matan su ba sai kiran layin su ake sun ki ɗagawa to bari na kyale su na kira Yusuf su lamrat suzo su gaisa" da sauri ta kira layin Yusuf
kira ɗaya Yusuf ya ɗaga yana faɗin "hello Ammi" "Yusuf ka turomin su lamrat suzo su gaisa da yayan su" "to Ammi gasu nan zuwa" katse kiran tayi ta ajiye wayar suka fara hiran kauye da yaya bello

Da sallama Ahmad ya shigo palon Ammi,kusa da ita yaje ya zauna yana yamutse fuska "Baban hiyana ya akayi naga sai yamutse fuska kake ne?" guntun tsaki yaja kafin yace "Ammi ni wlh na gaji da zama ni kaɗai kawai ki samo min mata ni ma,kila zan rage raɗaɗin rasuwar Aikam bani da wani Aiki fa sai tunanin sa" murmushi Ammi tayi kafin ta fara magana "aa baban hiyana garadai ka samo matar ka da kan ka kamar zai fi" "Ammi nifa ban san ina zan samo mata ba kai nifa ba zai iya tinkarar yarinya ince ina son taba gaskiya kawai dai ni ai mini irin Auren su bgs domin inaga.....bai kai karshen maganar sa ba idon sa ya sauka kan hajjo dake zaune kusa da hasana ta takure waje guda "wow Ammi da alama yanzu kam zan iya cewa mace ina son ta fa" ita dai Ammi tayi shiru tana kallon ikon Allah "ke zo" yayi maganar yana yiwa hajjo alama da hannun sa,kankame hasana tayi tana ɓoye fuskar ta murmushi Ammi tayi ba karamin daɗin hakan taji ba "baban hiyana ka rabu da ita ba zata zo yanzu ba sai an kwana biyu ta saba da mutane yanzu dai bari su lamrat suzo su gaisa sai ka kai su gidan su akoi yan aiki da duk wani abun bukata a gidan" "Ammi gaskiya ni bazan ɓoye miki ba ina son wanna yarinyar tamin" dawo da kallon sa yayi kan yaya Bello ya cigaba da cewa "kai ne yayan ta ko? to ina son kanwar ka amma zan iya hakuri sai gaba zaa samin ita a school ina fatan baa mata miji a garin ku bako? girgiza kai yaya Bello yayi kafin yace "baa mata miji ba" "good haka nake son ji yanzu dai muje na kai ku gidan ku gobe zanzo in sata makaranta da kai na" dogon salati Ammi tayi kafin tace "sannu baban hiyana wato ko kunya ta baka ji bako kai da nake gani mai kunya ɗazun da safe yan uwanka sukazo nan suka karemin rashin kunya iya rashin kunya wai dan tsiya hirar nasuma a nan zasu min kamar basu da ɗaki daga mai miƙewa yace asame sa a ɗaki sai mai matsowa yana wa matar sa raɗa daga gefe kuwa ga saura a zazzaune suna ta harkan su,ni ina gama sun mance da ni awajen wato kai ma yanzu zaka ɗaura daga in da suka tsaya ko?" murmushin yayi ya sunkuyar da kai kasa tana ɗan shafa gashin kan sa dai dai lokacin su amrat suka shigo
Kusa da Ammi sukaje suka zauna "laaa yaya Bello kai ne?" Cewar amrat da sauri lamrat ta juyo
cikin girmamawa suka gaida yaya Bello da fara'a ya amsa sanna suka gaida hasana

Miƙewa yaya Ahmad yayi yana faɗin "muje na kai ku gidan naku wai Ammi inane ma gidan nasu?" "A lallai baban hiyana daman baka san gidan nasu bane kake wanna sauri sutashi ku tafi sannu ka da kokari" murmushi yayi yana faɗin "Ammi na ai farincikin na samu mata ne ya sanya hakan dukka" "eh lallai lokacin da zan hana ku shigowa part ɗi na yayi eyeee" gaba yayi yana faɗin "dan Allah Ammi inane gidan?" "gidan da Abban ku ya saiwa baban hiyana nan ne" "ok to mujen ku ko? Yana kai karshen maganar ya fice su yaya bello suka bi bayan sa.


Suna fita Abba ya shigo palon Ammi a ɗan ruɗe yace "Aisha na bar wayata a ɗaki tun safe yanzu nazo na samu miss har uku na auta nakira layin nata baya shiga na kira na mijin ta bai ɗaga ba ina take? miƙewa Ammi tayi cikin nitsuwa tace "ina ganin yaran nan suna tare da mazajen su ne fa domin nayi ta kuran layin shi shima bai ɗauka ba" "aa Aisha akoi abun da yake ba dai dai ba auta bata taɓa kashe wayar taɓa ina Yusuf yake? Lokacin guda tashin hankali ya bayyana a kan face ɗin Ammi cikin tsoro tace "to ka kira Aryan ko Yusuf kaji ina su baban suke" juyawa Abba yayi gaba ɗayan sa a kiɗime ya nufi hanyar fita yana faɗin "bari na nemo Yusuf muji kafin nayi magana da Safras" yana kai karshen maganar ya fice daga palon,
Komawa Ammi tayi ta zauna tana mamakin ina su Khalid suka je "Ammi ina Aunty Zahra ɗin?" chewar lamrat dawo da kallon ta Ammi tayi kan lamrat ɗin ta zuba mata ido sosai kafin tace "lamrat wanna watan kinyi period kuwa?" cikin kunya ta girgiza wa Ammi kai tana faɗin "aa Ammi" cool murmushi Ammi ta saki kafin tace "ku tashi kuje ɗaki kuyi hira da Aisha dan ta saba da ku" "to" sukace kafin su tashi a tare su shige ɗakin su,miƙewa itama Ammi tayi ta wuce nata ɗakin cike da zulumin ina Zahra da Khalid.


Maiduguri

Sai 3pm bgs ya dawo gidan Aunty farida


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login