Showing 300001 words to 303000 words out of 363274 words
a kakar ta sannan ta ɗauki wani bakar jallabiyar sa suka fito suka nufi gidan su yaya bello dan ita Hajj fateema batama san wacece inna habiba ba da sallama ɗauke a bakin su suka shiga gaba ɗaya su inna suna tsakar gida inna habiba ciki ya bayyana ya girma dan akalla zai kai wata 6 zuwa 7 suna zaune suna hirar su,jin sallama yasa suka ɗago kai Innar yaya Bello naganin Hajj fateema ta gane ta zaro ido tayi da mamaki muryan ta har rawa yake wajen furta "Ummi kece nake gani ko mafarki nake" murmushi Hajj fateema ta saki kafin tace "nice inna" da sauri Innar yaya Bello ta taso suka rungumi juna suna murna kafin su saki juna inna ta musu iso kan tabar da suke zaune,zama su Hajj fateema sukayi dama da ita da Aunty mardiya Aunty salma Aunty Maryam suka zo sai baya baya Aunty maryam take da Hajj fateema ta kasa sakin jiki da ita dan abun da tayiwa su diyana abaya ita kuma Hajj fateema bata daku ba ta yafe mata sai janta take a jiki tana nuna mata komai ya wuce,cikin harshen fullanci Innar yaya Bello tace "Inna buba dake da habiba ga maman su hiyana ke innar buba ma ai kin san ta ko? Jin innar yaya Bello tace ga maman su hiyana ne yasa inna habiba mikewa zaune da kyau har sai da cikin ta ya wani mugun murɗawa cikin rawar murya tace "ma ma ma hiya diya" ta kasa faɗin maman hiyana da diyana tsabar ruɗu da tashin hankali da ta shiga nan fa kallo ya koma kanta da mamaki Hajj fateema tace "lafiya muryan ki ke rawa kika kasa kiran sunana!? "Tana mamakin ganin kine ai" cewar innar yaya bello "me yasa zatayi mamakin gani na ni ban ma waye taba wacece? "Habiba ce fa kin manta tata ko da yake lokacin da kika bar kauye bata girma sosai ba tana yarinya itace matar baban su hiyana da ya aura bayan tafiyar ki" zubur Hajj fateema ta miƙa tare da ɗaure fuska sosai a hasale ta fara magana "cemin zakiyi wadda ta kusan kashe min ƴa'ƴa ta cutar min da miji azzaluma wlh bama zan kyale ki ba dole hukuma su hukun ta min ke" ta kai karshen maganar tana kokarin juyawa ta bar gidan,da sauri Aunty salma ta rike ta tana faɗin "kiyi hakuri yanzu dai ki zauna mu tattauna da ita" cikin fushi Hajj fateema tace "salma ki kyale ni bawani kagana da zanyi da wannan makira shaɗaini yar" "kiyi hakuri dan Allah ba dan muba ki bari ina son yi mata tambayoyi ne idan yaso in na gama sai ki kira hujumar"tsaki Hajj fateema taje ta koma ta zauna ba dan taso hakan ba a tare suma su Aunty salma suka koma suka zauna "bai wa Allah me yasa kika cutar da su hiyana!? Cewar Aunty salma cikin sauri Hajj fateema tace "aa ba baiwar Allah ba wanna baiwar sheɗan ce" sosai inna taji zafin kalmar Hajj fateema dan yanzu imani ya shigeta sosai ta san Allah cike da nadamar abubuwan da ta aikata ta fara basu labari "tun ina yar shaka 14 na fara son bappan su hiyana shikuma ko kallon in da nake bai taba yi ba sau da dama ina zuwa wajen sa a gona a chan nake wuni amma bana jin ya taba ɗaga ido ya kalle ni abun na min ciwo sai na bawa kawata na kauyen makoptan mu labari ranna da muka haɗu a dandali da ita na kai tallan nono ita kuma tallar gyaɗa,nan take sanar dani akoi wani malami idan ka fita kauyen su aikin sa na da kyau sosai ta fara bani labarin yadda ta kori kishin yar ta ta zauna ita kaɗai naji dadi sosai na amince mata gobe zamuje ina dawowa gida na ce da bappan su bello ni gaskiya asai da ɗan maraki na ɗaya ko rago Aban kuɗin ya tambaye ni me zanyi da kuɗin nace masa bikin kawarmu zamuje kauyen gaba da mu bai damu ba ya sai da ya bani kuɗin da murna na ansa kuɗin a lokacin kuɗin shanun Naira 100k dai dai haka washe gari mukaje wajen malamin nan tashin farko ya ansa 30k sanna yace sai na bashi budurcina sai na bashi kai na ban damu ba na bashi kai na ya kwanta da ni ya min pata pata lokacin nayi kuka kamar ba zan yi rai ba kawata tayi ta bani hakuri tana faɗa min itama da haka ta fara ranar farko da mukaje bayan na bashi kai na da kuma kuɗin sai na faɗa masa aikin da zai min akan ya haukata maman su hiyana ta shiga duniya kowa ya manta da ita sai ya sawa baban su hiyana sona haka ko akayi ban wuci kwana uku da dawowa ba ranar da maman su hiyana ta haifi amrat aranar ta bar gidan ta bar kauye gaba ɗaya,nan muka sake komawa wajen bokan arana ta biyu ma sai da na bashi kai na sanna ya amince ya mana aikin mallaka min baban su hiyana sai yadda na yi da shi a takaice dai bayan munyi Aure da baban su hiyana na mallake sa sosai baya kula kowa sai abun da nace har ƴaƴan sa baya kulawa to akoi lokacin da asirin da na masa ya karye hankali na ya tashi dan alokacin ya sake ni da yake ya kamu da ciwon kafa baya iya komai sai ce masa nayi babu inda zanje a gidan zan zauna Allah sarki bawan Allah haka ya rabu da ni nayi kokarin komawa wajen bokan da kawata sadiya ta haɗamu dan ni tun lokacin da yamin aiki nayi aure daga shi har sadiya ban kara bi ta kan su ba atunanina ba zan bukaci komai ba kuma,dana isa wajen bokan sai aka cemin ai ya jima da mutuwa wai wani aiki yayiwa wata aka kunce aikin sai ya dawo kansa aikin,dan da yazo mutuwa yana ihu yana faɗin habiba kin cuceni kinsa nayi aikin da aka warware sa ya dawo kai na jin hakan yasa na gane aikin da yayiwa maman su hiyana ce ta dawo kansa na girgiza ainun na ji tsoron kar maman su hiyana ta dawo ban gama kwashe dukiyar Ahmadu ba nan na fara tunanin ya zan ɓullo wa lamarin na fara tunanin kashe Ahmadu sai na tuna ko na kashe sa ban isa in taɓa dukiyar sa ba kowa ya sani al adar kauyen nan ne,baka isa ka taɓa dukiyar mutun idan ya mutuba har sai an raba gado gwarama yana yare zaka iya taɓa wa wanna a gaban sane nayi tunani da dama ban samu mafita ba daga karshe na yanke shawarar ziyartar Sadiya kawata ko zan samu ta bani shawara lokacin danaje gidan sadiya kishiyar ta ta sanar dani asirin sadiya ya tonu ta gudu ta bar kauye ta tafi dan kar mutane su kashe ta ta tafi birni neman kuɗi jiki ba kwari na juya na dawo gida nazo dai dai zan shiga gida na haɗu da Innar buba na tsaya muka gaisa to dama muna shiri da ita sosai da Innar bello ce bama shiri dan ita innar bellon nan ta cika wa'azi dayawa bayan mungama gaisawa take tambaya ta lafiya ta ganni haka ina ɗari ɗarin gaya mata dan karta faɗa wa yaya na amma sai na daure na faɗa mata ina gama bata labari ta kwashe da dariya ta riko hannuna tace muje,ba musu na bita muka kutsa cikin daji nan ta kaini wajen nata bokan wadda ya min cikin nan da farko nace ina son yayiwa baban su hiyana asiri ta yadda zai ban dukiyar sa dukka da kansa ya gwada ya gwada abun yaki yiwuwa yace min hakan bazata yiwuba domin baban su hiyana yana da tsari a jikin sa sosai bello ya masa maganin tsari ajiki a lokacin,nace ya bani maganin da zan kashe shi da kai na dan inason muci gadon sa,sai yace ba wani magani da zai kamasa sai dai in dai da kai na zanje na yankasa da wuka ko na dannesa da pillow haka muka kamo hanya aiki bai samu ba jiki ba kwari muka nufi gida a hanya innar buba ke sanar dani mu kashe bappa sai mu aurawa hiyana buba cikin ruwan sanyi sai mu kashe diyana amrat lamrat ita kuma hiyana sai ta haifi yaro ɗaya sai mu kashe ta daga baya mu kashe yaron dan bamu bukatar jinin su dukiya zai zamo namu da murna na amince da shawarar ta ido na ya rufe da son duniya bayan na dawo gida na kara ninka wa su diyana azaba kan wanda nake musu duk dan wuya ta kashe su Allah sarki Allah yasa suna da tsawon rai watanar jummaa babu kowa a gida na shiga ɗakin bappan su yana kwance saman yar gadon sa yana barci da a wawtata da wuka zan yanka shi sai Innar buba ta hana tace mu danne sa da pillow dan kar asirin mu ya tonu haka ko akayi yana barci nasa pillow na danne sa na haye saman ruwan cikin sa tunyana yunkurin kwace kansa har ya saduda ya fara furta Kalmar shahada bappa na da taurin rai sai da na ɗauki wajen 15mins ina danne da shi baya numfashi sanna ya mutu farkon dannesa da nayi ina iya jiyo me yake faɗe banda sunan maman hiyana da su hiyana ba abun da yake kira daga karshe ne daya tabbatar mutuwa zanyi ya fara furta kalmar shahada ina kashe sa na fice naje na sanar da innar buba mukayi ta murna a tare a gari kuwa nayi kamar ban san komai ba bayan rasuwar sa nayi kokarin a ɗaura Auren hiyana da buba ta hanyar zuwa wajen bokan mu ya rufe mun bakin jama'ar kauyen ta yadda za'a ɗaura auren ba tare da cececuce ba haka ko akayi boka ya rufe bakin kowa akan mutuwar bappa da auren hiyana ana gab da za'a ɗaura auren Aisha yar baban su hiyana tazo ta ɗauke su suka tafi birni tunda suka zo sau ɗaya har yau ban sake ganin su ba amma duk da haka ban kyale su ba sai da nasa aka haukata diyana akan kunce tsarin da bappan su ya musu,wanna shine takaitacen abun da na aikata" salati gaba ɗaya wajen yasa a fusace Hajj fateema ta mike tana faɗin"da iya cutar da ƴaƴana kikayi zan iya hakuri na barki da Allah amma kin cutar dani dayawa daga karshe kika kashe min mutumin dana fiso fiye da kowa aduniya na gudu na bar iyaye na saboda shi na bar komai na saboda shi na bar cikin masarautar mu saboda shi kin cuceni dayawa habiba dole ki ansa hukunci"tana kai karshen maganar ta mike da sauri ta fice daga gidan tana kukan kashe bappa da inna abiba tayi.
Kallon Aunty salma Aunty Maryam tayi tace "muje koh?"a tare suka mike suka bi bayan Hajj fateema chan jikin mota suka hangota tana tsaye ta dukar da kai kasa tana cikin matsanancinyar damuwa,karisawa wajen sukayi Aunty maryam tace "muje ne?"girgiza kai Hajj fateema tayi kafin tace"aa nayi waya da Abba zai yi magana da sarki yola za'a turo jami'an tsaron su wuce da habiba da uwar buba sai na ga tafiyar su sanna zan wuce"da sauri Aunty mardiya tace"gaskiya kamata yayi Yusuf ko Aryan ne zasu basu hukunci dan inna ce Prince ba makawa kashewar parad ɗaya zai musu" "eh zancen ki gaskiya ne idan yan sanda sun kama su sai a wuce dasu kano Yusuf ya musu hukunci"cewar Aunty salma shiru wajen yayi basu sake magana ba kowa da abun da yake tunani
Iya comments iya read more ba dai wadda zatace bai yi update ba daga yau na dai na Long page sai an dawo yin comments gobe idan Allah ya kai mu 1 read more zaku samu sanna na kashe update na weekend ❌
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
💋 Duk Karfin Izzata 💋
💋The talent troupe writer's 💋
By
Star Lady
Page 49
KANO
ABBA & AMMI
zaune suke a palon sa su biyu suna hira cikin nitsuwa Abba yace "Aisha ina son ki bani hankalin ki sanna ki bani nitsuwar ki ki sa aranki komai ya faru da bawa mukaddari ne daga Allah sanna ki ɗauki hakan a matsayin jarabawa" shiru Ammi tayi ta tattara hankalin ta dukka ta bawa Abba kirjin ta na dukan uku uku dan tun da taji Abba yace hakan tasan ba lafiya ba,cigaba da magana Abba yayi "kuskure dai mun riga munyi duk da cewa haka Allah ya kaddara amma nima ina da nawa laifin ni nake hana ki zuwa kallon yan uwan ki har abubuwa suka rinƙa faruwa wallahi rashin zumunci bai yi ba kwata kwata,ko da sau ɗaya ne a sati ya kama ka rinƙa wai wayan yan uwanka ko ka kirasu awaya dan jin ya suke amma ke na hana ki zuwa wajen yan uwan ki tsawon shakara 7 zuwa 8 ina mai baki hakuri ta wanna ɓangaren ki min afuwa" ita dai Ammi shiru tayi ta zuba masa ido zuciyar ta na dukan uku uku burinta kawai taji me Abba ke son sanar da ita "fateema ta sanar min ɗazun habiba ita ta kashe mahaifin su hiyana da hannun ta yanzu mun sa jami'an tsaron sun kama ta" zubur Ammi ta mike tana faɗin "what!? Habiba ne ta kashe Ahmadu da hannun ta!!?no ba wasu yan sanda da Za'a haɗa ta dasu ni da nake da hukuma da doka gaba ɗayan ta a gida dole ta karɓi hukunci dai dai da abun da ta aikata a ɗaure min ita ba wanda zai mata hukunci sai Safras shine dai dai zai iya hukuntata akan abun da tayi"mamakin yadda Ammi ke magana har da kiran sunan bgs ya hana Abba magana da alama yau Ammi ta fusata sosai ta fita hayyacin ta"A'isha koma ki zauna" ba musu ta koma ta zauna tana faɗin"ban yarda kowa ya taɓa habiba ba idan ba Safras ba shine zai iya yi mata hukunci dai dai da abun da tayi dan bana son amata kisan farat ɗaya" "A'isha habiba tayi laifi dayawan da dole ta ansa hukunci kisa ni da kai na nace a rufe ta sai komai ya dai dai Safras ya dawo hayyacin sa ya mata hukunci habiba ita ta haukata Hajj fateema sanna ta haukata diyana ta azabtar da su hiyana bayan nan ga laifin zina ga shirka babban laifi fiye da komai a duniya haɗa Allah da wani wa iya zubillah bayan nan ga kisan kai ai dole habiba ta karɓi hukunci kisa taje can lahira ta samu Ubangiji data haɗa da wani ya mata nashi hukunci,shirka shirka shirka babban laifi ne number 1 a duniya wadda idan kana aika tashi ka mutu ba makawa jahannama kai tsaye zaka tafi babu wanda Allah ya tsine masa sau biyar a Qur'ani sai boka ai idan mutun yana da hankali ma wallahi ko sau ɗaya Allah ya tsine wa mutun bazaka kusancesa ba bare har sau biyar kai jama'a ya kamata murinƙa tunawa zafa mu mutu muje mu samu Allah da kuke haɗawa da wani awanna lokacin shi kan shi wanda ka haɗa da Allah neman ta kansa yake yana neman Rahman Allah kuma ba samu zai yi ba daga shi har masu binsa zasu samu azaba mai tsanani basu samu Rahman Ubangijin ko ɗigo,ya Allah ka kiyashe mu haɗa Allah da wani Allah ka bamu ikon rike ka kai ka ɗai" "Amin ya Allah" Ammi ta amsa da shi,cigaba da magana Abba yayi "sanna magana ta gaba Aisha yau kwanan 16 ke nan da accident na su Safras ina son ki sani ba accident su kayi ba zan faɗa miki hakan ne ba wai dan ki tada hankalin ki ba ko kice zaki shiga tsakanin mata da miji zan faɗa miƙi ne dan ki kaiwa hiyana agaji dan har yanzu bata ko motsi idan har na isa da ke karki tofa wani magana mara daɗi cikin maganar nan dan Safras yayi nadama abun da bai taɓa a rayuwar sa saboda son hiyana ya kwanta a hospital nan dukka yaran nan a tunanin su na haifesu ne kawai basu san cewa dasu nake kwana dasu nake tashi a rai na ba duk abun da suke akan ido na suke komai abun da ya faru Safras ya kusanci hiyana cikin fushi bayan haka baya cikin hayyacin sa shine aka samu matsala yanzu tana gidan sa na us karki nuna musu kamar kin san komai ki kyale su a matsayin accident ɗin yanzu ki shirya kije ki kula da hiyana tana bukatar kulawar uwa kusa da ita duk da cewa har yanzu bata farka ba amma komai na jikin ta ya dai dai ta bugun numfashi ta ya dai dai ta sai dai ciwo da bazaa rasa ba zata iya farkawa akowani lokacin awanna lokacin tana bukatar kulawar uwa da kuma soyayya kin san irin wanna abun idan ya faru da mutun wuya mutun yake rayuwa idan ya rayu kuma wani sai kiga ya farka da taɓin hankali saboda razana da yayi bana fatan hakan ya faru da ita ina fatan ta farka lafiya lau nasan zataji tsoron Safras sosai karki bari wani magana na Safras ya je kunnen ta kisa ta manta da Safras har sai komai ya dai dai ta sai ta samu sauki sosai a hankali zamu komar da ita dai dai kuma mu nuna mata Safras na son ta da gaske"tsabar tausayin hiyana Ammi bata san lokacin da hawaye ya fara bin kumatun ta ba"haba Aisha menene abun kuka addu'a zaki mata ki shirya da wuri amma ina son ki san wani abu ɗaya duk in da Safras yake zai zo wajen ku dan yanzu ma bai yarda hiyana ta mutuba yanzu haka yana gadon asibitin ma yana bincike akan ta tabbas zai zo duk da nasa a canzawa hiyana gida Aryan yayi