Showing 342001 words to 345000 words out of 363274 words
60
SUDAN
diran yamma su Abba suka yi kasan cewar Abba ya kira sarki baban Hajj Fateema ya sanar masa da zai zo kawo masa ziyara hakan ya sa sarki ya aiko motoci 5 akan a ɗauko su daga airport. Haka ko a kayi fadawan gidan sarki suka zo ɗaukan su dukkan tsofaffin cikin fadawan nan ba wan da ya gane Hajj Fateema ita kuwa duk ta waye su sai dukan uku uku kirjin ta keyi. haka suka shiga motocin gidan sarki dogarawa suka yiwa motocin key suka bar Airport ɗin sojojin da su Abba suka zo da su kuma wasu suka shiga mota ɗaya da yarage wasu kuma suka hau motar haya.
Tun daga farkon anguwar su Hajj Fateema ta waro idon ta tana kallo, komai ya sauya anyi manya manyan gine gine amma duk da gine gine da akayi hakan bai sa ta kasa gane komai na wajen ba, kallon da take wa wajen. Bugun da zuciyar keyi ya kara tsanan ta sosai lokacin da idon ta ya sauka kan tampatsetsen gate ɗin gidan su duk da anyi ginin mai kyau a rushe na baya hakan bai sa ta kasa gane gidan su bane. Horn ɗaya sukayi masu gadi suka wangale musu gate ɗin gidan suka danna hancin motocin cikin gida ji take bugun gaban ta na kara tsananta sai ambato sunan Allah take har dogarawa suka yi parking a parking space na gidan nan take sojin da su Abba suka zo da su suka bubbɗe musu kofar motocin suka fito. Bayan sun fito daga cikin motocin dogarawa suka musu jagora zuwa fadan sarki wato baban Hajj Fateema da kyar Hajj Fateema ke ɗaga kafar ta saboda bugun da zuciyar ta ke yi.
Da sallama suka shiga fadar sarki yana zaune saman kujerar sarautar sa fari tas kyakkyawa da shi kamannin sa ɗaya da Hajj Fateema duk da ya tsufa hakan bai hana kyan sa bayyana ba. Cikin girmamawa ya miƙe ya taro Abba tare da miƙa masa hannu suka gaisa kafin suka rungumi juna suna murmushi kamar sun san juna ɗaya bayan ɗaya Hajj Fateema ke kallon yan uwan ta dan gaba ɗaya suna fadan. Dum dum taji lokacin da idon ta ya sauka kan yaya Abdussalam dake zaune yana latsa waya ya kara kyau da cikan halitta yana sanye cikin jallabiya baka. iso sarki ya musu sanna ya wuce rike da hannun Abba suka koma saman kujerar mai zaman mutun 2 suka zauna wucewa su Ammi ma su kayi wajen su Maman Hajj Fateema suka zauna duk fadan ba wanda ya gane Hajj Fateema cikin nitsuwa sarki baban Hajj Fateema ya fara magana "Barkan ku da zuwa ina mai farincikin da wanna ziyara da ka kawo min Abubakar har ma tare da family ka gaskiya na yi farincikin da ba zai misaltu ba yanzu dai ga abinci can an shirya muku sanna akoi liyafa da na shirya muku na wanna ziyara gaskiya ba zan manta wanna ziyara ba muje kuci abinci a kai ku masauki ku huta zuwa dare sai mu gaisa da kyau ko?" Da fara'a Abba yace "Hakane muma munyi farincikin ganin ku cikin koshin lafiya" Abba na rufe baki maman Hajj Fateema hajjiya Hindatu ta ɗaga wa Abba gaisuwa jin muryan maman ta yasa Hajj Fateema jan dogon numfashi tare da yin kasa da kai tana sauke wa a hankali da fara'a Abba ya amsa kaisuwa nan take su Ammi ma suka gaida sarki Abdullah wato baban Hajj Fateema cikin nitsuwa yaya Abdussalam yaya Abdurahman suka gaida su Abba Abba na kokarin yin magana maman Hajj Fateema ta mike cikin ruɗu da kiɗima tace "Aminato!!" tayi maganar tana nuna Hajj Fateema a sukwane yaya Abdussalam ya ɗago kai kusan a tare suka dago kai da sarki Abdullah da yaya Abdurahman waro ido Khalil ya yi shima ya miƙe yana faɗin "Wallahi Oumma Aunty Amina ce ita ce" a tare Abdurahman da Abdussalam suka miƙe dan farko da Oumma tace Amina basu gane ta ba sai da Khalil yace ita suka lura da kyau suka ga ashe itace kasa da kai Hajj Fateema ta yi ta fara hawaye ta kasa magana Oumma na kokarin sake magana Abba yace "Ku zauna daman abun da ya kawo mu kenan akan batun Amina" ba musu suka koma suka zauna dukkan su idonsu na kan Hajj Fateema gyara zama Abba ya yi, ya fara magana shi dai sarki Abdullah ganin abun yake kamar a mafarki ita kuma Hajj Fateema sai kara nadama take a ranta tana kara jinjinawa uwa sai zancen zuci take "Duk gidan nan ba wan da ya iya gane ni sai uwata kai uwa ta daban ce duk wan da bai kyautatawa mahaifiyar sa ba ya yi asara yana cikin kunci uwa ta wuce wasa" sosai tayi nadamar sanya Oumma da tayi cikin bakin ciki. Tana cikin zancen zuci ta jiyo Abba na magana "Da farko dai muna masu baku hakuri dan neman yafiyar ku muka zo ga Amina mun taso ta a gaba ne dan tazo ta baku hakuri akan abun da ya faru kuyi hakuri ku yafe mata a kashe maganar nan tun da komai yazo da sauki hannun nagari ta faɗa" dakatawa da magana Abba ya yi yana son yaga action da zasu ɗauka kafin yaci gaba da magana. Sarki Abdullah ne ya yi gyaran murya ya fara magana "Lokacin da abun ya faru ni ban sani ba da bazan bar su Abdurahman su hukun ta mai kiwon nan ba tun da ba abun da ya yiwa Amina sai bayan ta fiyar Amina na samu labarin komai naji ba daɗi kuma na musu faɗa akan yanke hukunci ba bincike mun bi bayan Amina amma bamu same su ba na shiga tashin hankali wadda ya yi sanadiyar na samun hawan jini na ba rana ɗaya da zata wuce ban yiwa Amina addu'ar Allah ya tsare min ita a duk in da take kuma Allah ya dawo da ita lafiya munyi yawon neman Amina kasa daban daban bamu taɓa kawowa Amina na Nigeria ba sawon shakara 4 muka ɗauka muna neman ta a makwabtan kasashe amma shiru ba ita ba labarin ta mahaifiyar ta yi kuka har idon ta suka dai na gani sosai sai da muka fitar da ita waje aka mata aiki a idon san nan ta dawo gani da kyau ba zan iya misalta muku tashin hankali da muka shiga ba ga yan uwan ta maza nan har yanzu ba wanda ya yi Aure a cikin su bare na samu jikoki da zasu rinƙa ɗebe min kewar Amina khalisat ta yi Aure shekara 6 da suka wuce har yanzu bata taɓa samun haihuwa ba, in takai ce muku ko jiya sai da nayi kukan ɓatan Amina" ya kai karshen maganar tare da goge idon sa yana kokarin tare hawayen dake san zubowa. Kuka sosai Hajj Fateema take ta rarrafo akan guiwowin ta, ta kariso gaban sarki ta kama kafofin sa tana kuka tana faɗin "Na tuba Abbo kayi hakuri nayi nadama nayi dana sanin" hannu Abbo yasa ya ɗago ta yana faɗin "Ya isa haka kukan Amina ni daman ban rike ki a rai na ba na san yarinta ne ke damun ki a lokacin ni damuwata ɗaya in san in da ki ke kullun cikin yafe miki nake ki nemi gafarar Oumma ki da yan uwan ki" ya kai karshen maganar tare da sakin ta jikin ta har kerma yake ta nufi wajen Oumma tun bata yi magana ba Oumma tace "Na yafe miki Amina amma ina son sanin ina ki ka je? Tsawon shekarun nan" Hajj Fateema na kokarin yin magana Abba ya riga da cewa "Ni zan baku wanna amsa makiyayin da su Abdurahman suka kama suka rufe kanina ne shi Amina ta bi suka tafi dan tana son shi, nan Abba ya fara basu labari kamar yadda Hajj Fateema ta sanar masa tun ranar da suka bar gida har Auren su da bappa Haihuwar su Hiyana haukatata da Inna Habiba tayi da irin wahalar da su Hiyana suka sha da haɗa Auren su da su bgs da Abba ya yi da abun da Abu Abdurahman ya yiwa Hajj Fateema da rasuwar bappa duk sai da Abba ya basu labarin komai. Sun sha kuka sun tausaya wa Hajj Fateema san nan suka yi wa Bappan addu'ar samun Rahman Ubangijin nan dai a ka yayyafi juna Khalil sai murna yake ya ciro waya ya kira khalisat ya sanar mata Aunty Amina ta dawo da murna khalisat tace gobe zata kamo hanya sai murna jama'ar cikin fada ke yi. Da haka Sarki Abdullah wato Abbo yace su tashi suje su ci abinci suje su huta sai zuwa dare za'a karasa hira. Cike da farinciki suka mike Hajj Fateema rungume da Oumma ta suka nufi wajen cin abinci. Abinci ne mai rai da lafiya aka haɗa musu ba zancen pulako suka saki jiki sukaci suka sha sanna Yaya Abdurahman ya raka su masaukin baki yana tsoka nan Hajj Fateema wai tayi kiba daman zata yi kiba rungume sa ta yi tana dariya. Haka ya raka su Abba sai da ya tabbatar basa buƙatar wani abu sanna ya fito rike da hannun Hajj Fateema suka nufi wajen Oumma.
To bari mu leko su bgs mu gani me suke kafin mu dawo su Abba sun huta.
Us
....suna shiga Hospital ba ɓata lokaci turawa suka an sa su Aryan suka dukufa a kansu suka fara aikin ceto ran su. Sai safa da mar wa bgs yake a bakin kofa ɗakin da su Aryan ke kwance gaba ɗaya ya rasa nitsuwar sa. Ganin abun na neman fin karfin sa ne ya sa, ya ciro waya ya fara kiran layin Ummi bugu ɗaya Ummi ta ɗaga tsabar ɓacin rai da kyar ya iya buɗe baki ya fara magana "Ummi na san kece kawai zaki iya jurewa muna bukatar addu'ar ku Please na san Abba da Ammi duk ba zasu iya jurewa ba musamman Abba zuciyar sa ba zata iya ɗauka ba ki sanya Aryan a addu'a sosai yana cikin rashin lafiya" kallon Abba dake gefen ta Ummi tayi kafin tace "Zamuyi waya" bata jira amsar sa ba ta katse kiran dafe kan sa bgs ya yi yana mai jin zuciyar sa na masa zafin kamar zata fashe ta fito waje.
Ya jima a tsaye a wajen yana tunanin halin da Aryan ke cikin babban likita ya fito ya same sa awajen sau uku likita na masa magana bai ji ba har sai da Shahram dake ɗan nesa da su ya matso ya taba sa yana faɗin "Oga a na magana" cikin sauri ya kalli likita yana faɗin "Ya jikin na su" cikin harshen turanci likita ya fara magana "Sauran sojojin munyi nasara ceto ransu sai dai zasu ɗauki kwana biyu kafin nan su dawo dai dai amma shi kuma ɗan uwan ka maganar gaskiya sai dai a masa wankin jini dan kwayoyin sun ratsa jinin sa sosai" waro ido sosai waje bgs ya yi a ran sa yana mai mai ta maganar Dr "Wankin jini kuma Aryan no it can't be never" ya yi nisa cikin tunani da yake Dr ya taɓa sa yana faɗin "Baku da zaɓi dole kasa hannu a masa wankin jini dan da sa hannu a takarda da Halin da yake yanzu duk ɗaya ne idan kuka barshi haka mutuwa zai yi idan kuma aka masa wanki jini idan ya yi Sa'a ya rayu idan kuma ba mu yi nasara ba mu na iya rasa shi yanzu kayi sauri kasa mana hannu a takarda idan ya mutu shike nan" kwata kwata bgs baya jin abun da Dr yake faɗe ya shiga duniyar tunanin hanyan da zai kuɓutar da Aryan daga wankin jini dan hakan ba zai yiwu ba ba zai iya sanya hannu a takardan yarjejeniya mutuwar Aryan ko tashin sa ba no ba zai iya ba dafe kan sa ya yi, ya fara zagaye wajen yana tunanin mafita zuba masa ido Dr ya yi kau da fuska Shahram ya yi daga kallon bgs yana hawaye dan yasan tsananin shakuwa dake tsakanin bgs da Aryan tun da yake a duniyar nan bai taɓa kallon yan uwa masu son junan su kamar bgs da Aryan ba yasan mawuyacin abu ne bgs ya yarda ya sa hannu akan takardan yarjejeniya akan rayuwa ko mutuwar Aryan ina ba zai yiwu ba. hawaye sosai Shahram yake yana tausayin bgs da Aryan shi kuwa Dr yana tsaye yana jiran bgs ya zo ya sanya hannun a kan takarda ayiwa Aryan wankin jini. Bgs kuwa yana can duniyar tunanin mafita yadda zai kuɓutar da Aryan dai dai lokacin kiran Hiyana ya shigo wayar sa hakan ya sanya ya dawo hayyacin sa cikin sauri ya duba wayar ganin my world ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar yasa ya katse kiran ya kirata. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin raunaniyar murya tace "Yaya Prince ina wuni?" Kasa magana ya yi saboda ɓacin rai harshen sa ta masa nauyi ya kasa buɗe baki "Yaya Prince lafiya?" Shiru ya mata ya kasa magana jin yadda yake numfashi yasa ta gane ba lafiya ba tattara nitsuwar ta tayi ta kara yin kasa da muryan ta, ta fara magana cikin girmamawa "Yaya Prince duk halin da ka ke ciki ka sanya a ranka ba mai fitar da kai sai Allah duk halin da zaka shiga na kunci karka manta da ambato sunan Allah da yiwa annabi salati da yiwa Allah godiya a duk halin da ka tsinci kan ka yanzu dan Allah ba dan ni ba muyi salatin Annabi tare kaji my Habibi?" Dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya lokaci guda yaji harshen na shi ta ɗan sake maganganu Hiyana sun sa zuciyar sa ta ɗan yi san yi kasa kasa kamar mai raɗa yace "Allahumma sallahi ala muhammad waala Ali Muhammad kama sallaita ala Ibraheem wa ala Ali Ibraheema innaka hamidul maji Allahumma barik ala muhammad waala Ali Muhammad kama barakta ala Ibraheema wa ala Ali Ibraheema fil alamina inna hamidul maji" a tare suka fara salatin kuma a tare suka kai karshe yana kokarin yin shiru ta sake yin sauri faro salatin daga farko haka yasa shima ya daure ya bi bakin ta. Sau uku suna salati tare kafin tace "Yaya Prince meke faruwa?" Cikin nitsuwa ya mata bayani sama sama na abun da ke faruwa shiru ta ɗan yi kafin tace "Yaya Prince dan Allah kasa a kawo ni asibitin kaji?" "No Eshat me zaki zo kiyi?" "Dan Allah yaya Prince addu'a zan zo in yiwa yaya Aryan dan ba abun da yafi karfin Allah ya abun da bai da magani a al Qur'ani mai girma dan Allah yaya Prince ka bari nazo nayiwa yaya Aryan addu'a kaji?" shiru ya ɗan yi yana tunani shagwaɓe murya tayi tana faɗin "Haba my Habibi Allah idan baka amsa da eh ba zan maka kuka" yadda ta yi maganar har sai da ta ɗan sa shi murmushi cikin shagwaɓa tace "Yaya Prince murmushi yana maka kyau sosai" waya ce miki na yi murmushi?" "Babu wanda ya faɗa min daga zuciya ta naji" cool murmushi ya saki yana faɗin "My Eshat uwar rigima kin rama abun da nake miki kenan ko? wai daga zuciyar ki, kika ji, kaji ɗan bakin ta a wajen" turo ɗan baki nata tayi kamar tana gaban sa a shagwaɓe tace "Kai yaya Prince ai ba karya na yi ba kayi murmushi ne da gaske zuciya ta ta faɗa min ni dai yanzu dan Allah ka amsa a kawo asibitin nan idan nazo sai mu karisa maganar mu kaj" jinjina kai yayi kamar tana gaban ta yana faɗin "Ki shirya Shahram na zuwa yanzun nan ya ɗauko ki ya jikin Diyana?" "Jikin ta da sauki amma bata farfaɗo ba" tayi maganar cikin zumuɗi jinjina kai yayi kafin tyace "Kisa hijabi har kasa sanna ki sa nikaf da safan kafa da hannu kinji?" Da mamaki ta amsa da "to" kashe wayar yayi ba tare da yayi magana ba ya mai da aljihun wandon sa, ita kuwa mamaki ya kama ta aran ta tana mai mai ta maganar sa "kisa hijabi har kasa da nikaf tare da safan hannu da na kafa" a gefe guda kuma taji daɗin yadda ya bayyana kishin sa a kan ta, tunawa da tayi yace za'a zo a ɗauke ta ne yasa ta mike ta sanya hijabi a saman riga da wandon dake jikin ta ta ɗauko nikaf ta sanya tare da safan hannu da kafa kamar yadda ya umarce ta. Bayan ta gama shiri ne ta fito ta tsaya a harabar gidan tana jiran Shahram hannun ta riƙe da kyakkyawar jakar ta mai kyau da tsada baki kalan takalmin ta dake kafar ta da kyakkyawar basket na kayan abinci da ta ɗauka wa bgs.
Bata jima da fitowa ba sai ga Shahram ya danno hancin motar sa cikin gidan a gaban ta yazo ya yi parking na motar tana kokarin buɗe motar ya yi saurin fitowa ya buɗe mata gidan baya ba tare da ta masa magana ba ta shige ta zauna tare da takure jikin ta waje guda saboda sanyin A.c dake cikin motar shi ma Shahram ya shiga yayi wa motar key bai ko kallin in da take ba ma bare ya san tana jin sanyi, yaƙi kallon tane dan karya yi laifi amana take awajen sa yasan ba karamin matsayi yake da shi ba awajen bgs yanzu tun da har ya iya aikan sa ya ɗauko masa matar sa lallai ya yarda da shi sosai addu'a yake a ran sa Allah ya ba shi ikon rike musu amana.
da gudu ya figi motar suka nufin asibitin tun tana takure jikin ta har ta fara rawan sanyi duk Shahram bai sani ba. Ganin numfashi ta na kokarin yanke wa ne saboda sanyi yasa ta daure tace "Yaya dan Allah ka kashe A.c nan" a sukwane Shahram ya kashe A.c yana faɗin "Sorry madam" yayi maganar ba tare da ya kalli in da take ba har mamaki sai da ya bata ji yadda yake mata biyayya kamar wata babba shiru ta yi ta sunkuyar