Showing 129001 words to 132000 words out of 363274 words

Chapter 44 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2577

Fahad, sai wayan chan marasa jin haidar da Umar, Allah ya tashi kafadun Ahmad shima yabi sahun ku" "amin kawai Aryan yace daga nan sukayi sallama, ya kashe wayar ya ajiye a gefe guda san nan ya miƙe da kyar ya nufi toilet.

Aɓangaren Aunty farida kuwa tana gama waya da Aryan tafara Neman layin Abba, kira ɗaya Abba ya ɗaga chikin zumuɗi "tace Assalamu alaikum Abba na albishir" da faraa Abba yace "goro my daughter"
"Abba yau Aryan da kansa ya furtamin yana Son diyana kuma wlh duk hiran da mukayi nayi recordined" "wow my daughter gaskiya nafi kowa murna da hakan dole namiki kyauta mai girman gaske saboda tun bayan Aihuwar ku baa taɓa bani lbr mai dadin wan nan ba" "to Abba yanzu ya kamata diyana ta dawo gida dan wlh Aryan na chikin damuwa sosai bakaji yadda naji voice nashi ba kamar bai da lfy "
"Za'a dawo da ita my daughter amma ba this week ba sai next, dan ina son in masa surprise ne. "To shike nan Abba na sai munyi waya" tana gama faɗin hakan Abba ya katse kiran, sai faman murmushi yake


Washe gari tun asuba Hiyana ta lallaɓo ta fito daga part ɗin Ammi ta nufi ɗakin yaya Ahmad, kamar dai kullum yauma haka ta same'sa, gefensa kaɗan ta zauna tafara karanto masa addu'a kamar yadda ta saba, tanayi tana hawaye sosai almost 10mnt ta ɗauka tana masa addu'a bayan ta gama ne ta ɗago kai tana kallonsa yayin da shima ita yake kallo chikin sanyin murya tace
"Yaya Ahmad kanajin sauki kuwa? Murmushi yayi tare da lunshe idon sa ya sake buɗe wa, alamar Eh ba karamin daɗi tajiba ganin yadda ya chanza yanzu har hasken sa ya fara dawowa ya fara dawowa dai dai kamar da, tayi nisa chikin tunani, kamar daga sama taji tsayuwar mutun a kanta a ruɗe ta ɗago blue eyes nata taga dai babu kowa yan waige waige tafara yi still dai bata ga kowa a ɗakin ba, miƙewa tayi chikin tsoro tana faɗin "yaya Ahmad sai gobe kuma idan nazo... Bata karisa rufe bakiba wani iska mai karfin gaske ya hanƙaɗata ta faɗi ka buge da jikin gadon, da karfi ta furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil, nan take is kan ya tsaya chak wani karfi taji yazo mata ta miƙe da sauri har tana haɗawa da gudu ta nufi waje.

Tana fita tayi karo da Bgs shi kuma yana shigowa, baya baya tayi ta faɗi kasa chikin tsawa "yace ke me kikeyi a nan!? "Muryan na rawata tace "kayi hakuri yaya prince daman nazo duba jikin yaya Ahmad ne" ɗago hannun sa yayi yana kallon ɗankareriyar agogon gold dake manne a hannun sa, karfe 5:10Am dawo da kallonsa kanta yayi duk da chewa wajen akoi ɗan duhu baya ganinta sosai hakan bai hanashi fahimtar chewa tabbas wan nan ɗaya daga chikin yaran da Ammi ta ɗauko daga Yola bane dan yasan Zahra dai bazata zo nan wajen at this time ba, batare da ya sake magana ba ya tsallake ta ya wuche ya shege ɗakin da yaya Ahmad ɗin ke kwanche

Ita kuwa jiki ba kwari ta mike ta nufi part ɗin, Ammi

Yana shiga ɗakin ya ɗaga ido yana kallon sama a hankali ya fara magana "ya kamata na samu time na duba Camera nan fa ko kuma nasa ko Fahad ne ya duba min, dan ya kama nasan suwaye da waye ke shigowa ɗakin nan, kuma meke kawosu zan yi kokari naga na binchiki Cameran gaskiya, dan ni ban yarda da kowaba.

Sauko da ido sa yayi kan Ahmad dake kwanche, a hankali ya taka zuwa wajen gadon kasa kasa yace "Allah ya baka lfy my bro, bari muje masallaci sai mun dawo yana kai karshen maganar ya juya da sauri ya fice daga ɗakin.

To kwanche tashi babu wuya awajen Allah yau dai diyana na da 2 week's a Maiduguri wajen Aunty farida dan ta

Yauma kamar kullun sanye take chikin doguwar riga abaya pink colour ta tsantsara make up ɗin ta kamar ka sache ta dan kyau, ta goge tayi kyau sosai takara haske da chika fatar jikin tannan kuwa kamar kitaɓa jini ya fito, sai ɗaukan ido take kamar madubi, taku take a hankali ta sauko daga stair case ɗin ta shigo chikin palon a tsakiyar palon ta tsaya kamar mai tunani, da ɗan karfi tace "yes yauwa na tuna jiya ai yaya Aiman ya sayamin sim card ya kamata na kira yaya Aryan tun da na san number sa, da sauri ta juya ta koma ɗakin ta

Ɗauko wayar ta tayi ta fito palo ta zauna saman sofa mai zaman mutun 3 kunna hasken screen ɗin wayar tayi, sauri sauri ta shiga contact ɗin ta babu number kowa awajen daga na yaya Aiman sai na Aunty farida, shiru ta ɗanyi na yan second ni da sauri kuma tafara rubuta number sa tana gamawa ta danna call wayar tayi ringing har ta katse bai ɗagaba, sake kira tayi nanma bai ɗaga ba sai a garo na uku ya ɗaga chikin faɗa ya fara magana

"Wai wanene ke neman ta kuramin ne? Chike da zumuɗi tace "yaya Aryan ni ne fa" zubur ya miƙe tsaye muryan sa har rawa yake yace "ke ina ki ke ina Abba ya kai..... Bai karisa maganar ba yaji an katse kirar, da sauri ya chiro wayar daga kunnen sa yabi kiran Amma ina layin akashe sau uku yana gwadawa amma a kashe wani irin raɗaɗi yaji zuchiyar sa na masa na dama ya farayi yana faɗin " dama ban ji voice nata ba da yafi min yanzu zata sake jefani chikin tashin hankali, wurgi yayi da wayar gefe guda ya dafe saitin zuchiyarsa a hankali ya koma ya zauna a gefen gadon.

Aɓan garen diyana kuwa wani wawan mari Aunty farida ta sakar mata bayan ta ansa wayar tata ta kashe chikin tsawa tafar magana "ke bakyaji ko? eh wato ni ban isa in sa ki abu ko in hana kiba koh? Sokike Allah ya isan Abba ya kamani ko? Chikin kuka diyana tafara magana "kiyi hakuri Aunty farida na kasa mantawa da yaya Aryan ne shiyasa amma namiki alkawarin bazan sake ba" nan take Aunty farida taji jikinta yayi sanyi kuma tayi na damar marin'ta da tayi Allah sarki So kenan

Zama tayi gefenta ta rungumo ta tafara magana "ya isa my diyana kinji kiyi shiru, ni banche ki manta da yaya Aryan ba ki chigaba da tunanin sa In Sha Allah next week ma zamuje gida sai kiga yaya Aryan ɗin naki kinji ki share hawayen ki ya isa haka" chike da zumuɗi da farinchiki diyana ta goge hawayen ta tana faɗin "amma Aunty farida idan mukaje gida a chan zaki barni ko? "Eh mana my diyana ai daman mai dake zanyi" dariya diyana tayi kamar ba ita bache mai kuka yanzun nan, a wan nan yanayin Aiman ya shigo ya same'su

Saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna yana faɗin "to baby diyana me kuma ya faru naga sai murna kike? "Yaya Aiman zan koma gida mana shiyasa nake murna, miƙewa Aunty farida tayi ta ɗauki wayar diyana ta wuche ta haye sama ta barsu awajen,

"Baby diyana yau kinyi kyau sosai, sun kuyar da kai diyana tayi saɓanin da, idan an che mata tayi kyau sai tafara dariya, tana farin ciki.

"Yaya Aiman nagode kuma kai ma ai kayi kyau sosai" "to taso kizo na mana hoto kinji my baby chikin nitsuwa ta miƙe ta karisa wajen da yake zaune saman hannun kujerar da yake zaune ta zauna, chiro wayar sa yayi ya rinƙa ɗaukan su pic masu kyau sai murnushi suke su dukka, bayan ya gamane ta miƙe ta koma kujerar ta ta zauna suka chigaba da hirar su

KANO

Sis Love yana ga kin rame ne kwana biyun nan Zahra dake zaune kusa dashi ta ɗago kai zatayi magana kenan dai dai lokachin Bgs ya shigo palon da sallama ɗauke a ɗan karamin bakin nan nashi, fuskar nan tashi kamar wani hadari a ɗaure take tam, sanye yake chikin wando jeans baki da t-shirt blue ba ƙaramin kyau kayan suka masa ba, asalin halittar jikin sa ya bayyana faffadar kirjin san nan a tsaye take tam, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fasa rigar saboda chika

nan take Zahra ta miƙe jiki na rawa tace "sannu da shigowa yaya prince ina wuni, shiru ya ɗanyi yana kallon Khalid dake zaune ko kallon in da Bgs ɗin yake bayyi ba dan baya son su haɗa ido chikin tsawa yace "ke wuche ki bamu waje, ai tun bai kai karshen maganar ba Zahra ta nufi hanyar ɗakin su da gudu har tana tuntunɓe

"Me kake yi a nan Khalid? Sai lokachin Khalid ya ɗago kirjin sa na dukan uku uku dan shi kanshi yana fargaban ansar da zai bawa Bgs amma kuma ya zama dole ya sanar dashi dan shi gaskiya ya gaji yana son Zahra sosai.
"Hira nazo yi wajen matata ta" tirkashi waro green eyes nashi yayi waje sosai yana kallon Khalid, yayin da shima Khalid yake kallon sa "wai Khalid kaji abun da bakin ka ya furta kuwa? "Kwarai kuwa Bgs naji mana barima na mai mai ta maka hira nazoyi wajen matata kuma kanwata farinchiki na burin raina abun alfahari muradin rai na kai in ta kai che maka itache duniyata komai nawa, mutuwan tsaye Bgs yayi yama kasa chewa Khalid komai, ganin haka yasa Khalid ya miƙe ya fice daga palon ya barshi tsaye awajen.

Yana fita tun bai yi nisa ba yace "alhamdulliah alhamdulliah alhamdulliah, yau dai na gama da duk wata matsala ta, kai Bgs kai dai wlh ina maka adduar Allah ya ɗora maka soyayya wadda bata sonka inga ta tsiya yana magana yana sauke nauyayyar ajiyar zuchiya da haka ya nufi ɗakin sa ya haye gado ya kwanta

To masu karatu sai mun hadu Ranar Monday idan mai dukka ya kaimu..✍️✍️✍️

Book 1 fa yana gab da karewa sauran page 3 ko 4



💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)



More comments an share

*💫STAR LADY💫*34

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣6️⃣*


A fusace Bgs ya juya yama fasa shiga wajen Ammin taku yake irin na jaruman maza, ya fice daga part ɗin gaba ɗaya, part ɗin Aryan ya nufa a dai dai wajen part ɗin Ummi yachi karo da Yusuf da lamrat sun fito daga part ɗin Ummi sun nufi part ɗin Ammi sai murnushi suke suna hira kamar wasu kawaye, mamaki da al ajabine ya hana Bgs tafiya kuma ya hana shi magana tunani ya shigayi wai yaushe yaran nan suka dawo hakan, yayi nisa chikin tunani sai jin yayi Yusuf yayi ya ɗan tafa kafaɗar sa yana faɗin

"Big bro me kuma ka keyi a nan? Wani mugun kallo ya wurgawa Yusuf wadda sai da yasa Yusuf ɗin haɗiyar wata yawu mai kuyar wuche makoshi, da kyar Yusuf ya iya buɗe baki ya sake chewa "my bro lfy kake kallona haka"? A fusache Bgs ya wuche ya nufi part ɗin Aryan, batare da ya chewa Yusuf komai ba

Juyowa Yusuf yayi yana kallon lamrat dake tsaye,ta harɗe hannu a kirji tana kallon su "my baby ke kam ba kya tsoron yaya prince ɗin ne? Murmushi lamrat ta yi kafin tace "to ni yaya Yusuf in ban da kaima da neman magana ina ruwana dashi, mutumin da ko magana bai taɓa yi ba, nifa ban taɓajin voice nashi ba kwata kwata, to ai kaga ba ruwana dashi"

Murmushi kawai Yusuf yayi san nan ya jawo hannunta yana faɗin "zo muje mu gai da Abba tun da kin gai da Ummi, yau so nake na gabatar dake wa kowa na gidan nan, shima yaya prince ɗin naso gabatar masa dake amma sai yayi tafiyar sa sunkuyar da kai kasa kawai lamrat tayi batara da ta che komai ba

Jan hannunta yayi har chikin fada, lamrat sai kokarin kwache hannun ta take dan kunyar Abba takeji amma yaya Yusuf ya riƙe ta sosai kuma yana jin, yadda take ta mutsu mutsu da hannun tana son kwache wa, amma yaki sakinta saima kara riketa da yayi sosai sai da suka isa gaban Abba san nan ya saketa ya samu waje saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna yana faɗin

"Sannu da hutawa Abba" da fara'a Abba ya amsa lamrat kuwa tsugunnawa tayi har kasa ta gai da Abba, sai murnushi yake ya amsa mata san nan ya ɗora da chewa "amarya tashi ki zauna saman kujera, sunkuyar da kai kasa Yusuf yayi wai irin kunyar nan, hararar wasa Abba ya wurga masa yana faɗin "au sai yanzu kasan da wani abu wai shi kunya ko"? Bari na samu Ammin ku anjima zan sanar da ita da kai da Khalid duk kar ta kara barin kushiga part nata sai ranar da aka shafa fathiha"

waro green eyes nashi waje Yusuf yayi sosai, chikin voice irin na masu shagoɓa ya fara magana "haba Abba so kake muyi chiwo ne, Allah ko kwana ɗaya ba zan iya jurewa ban ga my baby ba, da gudu lamrat ta tashi ta fice daga fadan dan ta lura shifa yaya Yusuf ɗin nan bai san kunya ba

Zuba masa ido Abba yayi yana kallon ikon Allah
"Abba kasan me wlh ina son kafin mu koma London an shafa fathihan nan sai kowa ya wuche da matar sa" "Yusuf tashi ka bani waje kuma ni ba zan yiwa lamrat Aure a yan shekarun tan nan ba kwata kwata fa she is 14 years tayi kan kanta da yawa" waro ido waje yaya Yusuf yayi kafin yace "haba Abba na pls ai zata karisa girman ta a gida na, nifa Abba banso ma a che Auren mun nan ya wuche nan da 1 week ba"

Kwafa Abba yayi yace "to ka faɗawa babban yayan kune? dan kasan ni dai ba zan maka maliyi ba shine zai maka waliyi ni kuma waliyin lamrat" a sukwane Yaya Yusuf ya miƙe ya nufi hanyar fita yana faɗin "lallai Abba baso kake nayi aure ba a wannan rayuwar, in dai sai na fadawa Bgs ya zamo waliyina to wlh nama hakura da Aure har abada ya kai karshen maganar tare da ficewa daga fadan

Dariya sosai Abba yayi kafin yace "dukkan ku nasan maganin ku ai tun ɗazun nake chewa ka tafi kabani waje kaki ka zauna kanamin surutai ba gashi yanzu chikin ruwan sanyi ka tafi ba"

Aɓangaren Bgs kuwa

Kwanche ya samu Aryan saman katafaren gadon sa, idon sa biyu yana kallon sama da alama yayi nisa chikin tunanin da yake, dan ko sallamar da Bgs yayi bai jiba.

Hayewa samab gadon Bgs yayi ya kwanto da fuskarsa dai dai face ɗin Aryan ɗin, ya kwaro green eyes nashi sosai, a chikin idon Aryan, a sukwane Aryan ya yunkura zai tashi tamke wuyar sa Bgs yayi ya mai dashi ya kwantar, yana faɗin "yan zu kuma tunanin me ka keyi?

Chikin fushi ta jin haushin tadda Bgs ya tsoratashi yace "wai dan Allah Bgs me na maka ne? bazaka kyaleni naji da damuwa taba sai ka karamin naka? komawa gefe Bgs yayi ya zauna kamar bai ji me Aryan ya faɗa ba, shiru suka zauna Almost 10mnt kafin Bgs ya juyo da kallon sa kan Aryan ya fara magana

"Ina kaunar ka Aryan duk duniya idan ka chire iyaye na ba wanda nake so kamar kai ba zan iya ganin ka a chikin damuwa ba, duk lokachin da ranka ya ɓachi ko kashiga damuwa tofa nafi kowa shiga tashin hankali, dolene na rinƙa yawan tambayar ka meke damunka, dan kai ne mutun na farko da nake kauna bayan iyaye na, daga kai sai Fahad sai Zahra Aunty Farida da kuma Khalid Yusuf Ahmad, ba zan iya ganin damuwar ku, na yi shiru ba"

Da mamaki Aryan ke kallon Bgs "wai wace Zahra kake nufi" Aryan ya jefo masa tambaya yana tsare sa da ido, guntun tsaki yaja kafin yace "daman muna da wata Zahra ne a wan nan gidan bayan Auta "amma lallai Bgs ka iya iskanchin kala kala yanzu daman kasan ana kiran Zahra da sunan Auta, eyee wato duk abun da ake a gidan nan kana sane, amma sai kayi kamar baka san komai ba ko?

"Kaga Aryan ni yanzu ka faɗamin tunanin me kakeyi ban che kamin wasu tambayoyin ba" "yanzu idan nache maka tunanin mace nake me zakache? Dogon tsaki yaja kafin yace "ka hauka che mana me kuma zan che sai na tashi na kama kai na dan ba amfanin na zauna ina magana da wanda bai da hankali, tsaki Aryan ma yaja san nan yace "hmmmm Ni bari naje nayi wanka kana nan ne ko dai in same ka a part naka? Shiru Bgs yayi kamar bai ji abun da Aryan ɗin yace ba, ganin bai da niyar magana yasa Aryan ya miƙe ya nufi toilet ya barshi awajen, Shiru yayi kamar mai tunani jim kadan ya fara magana

"Khalid yana son Auta wow nayi farin chiki da hakan gaskiya domin ko ba komai zata samu farinchiki, amma dai dole Khalid ya chanza kasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login