Showing 279001 words to 282000 words out of 363274 words

Chapter 94 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2578

kamar ansa kwai mai haske a cikin sa ko aina baban mu ya samo ɗan akwatin nan oho" kallon key ɗin dukka jama'ar palon sukayi.

Hannu Aryan ya miƙa wa Ammi alamar ta bashi key ɗin,ba musu ta miƙa masa,ya ansa tare da mikewa yana faɗin "bari na ajiye sa awajena zuwa gobe" ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita

sai da ya kai bakin kofar fita ba tare da ya juyo ba yace "my jidda ki same ni a ɗaki na ina son magana da ke" da sauri tace "yaya Aryan nifa bana iya tafiya sosai ko ka manta ne? Yanzu ma nan da ɗakin Ammi bana iya zuwa kuma wlh har yanzu zafi wa....bata kai karshen maganar ba tayi shiru sakamakon juyowa dayayi a sukwane ya watsa mata harara.
kasa sukayi da kai a tare daga shi har ita kasan cewar sunga jama'ar palon na kallon su,shafa gashin kansa yayi cikin jin kunya yace "Aunty mardiya pls ki taimaka mata zuwa ɗaki" ya kai karshen maganar tare da juyawa yana kokarin fita da sauri diyana ta kuma cewa "yaya Aryan nifa wlh ba zanzo ɗakin kaba salon ka sake kara y....bata kai karshen maganar ba Ammi ta daka mata tsawa "wai ke diyana yaushe zaki yi hankali ne? ya Allah kasa akoi maganin hankali cikin akwatin bappan nan dan na gaji da haukan kin nan!!" sunkuyar da kai Aryan yayi ya fice da sauri dan diyana na neman tona masa asiri.

wani irin bakin ciki da kishi ne yaya Bello yaji ya tokare masa makoshi dan dagaji yadda diyana tayi magana yasan in da zancen nata ya dosa duk da cewa yasan ba samun diyana zai yi a matsayin mata ba tariga ta masa nisa amma yana bala'i son ta da kaunar ta kuma dole yaji kishi


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


💖The talent troupe writer's 💖




💋Duk Karfin Izzata 💋

By Star Lady






Page 40

Yau hiyana ta cika 2 days kwanche bata ko motsi,ba karamin tashin hankali bgs ya shiha ba,ya rame ya sauya har wani duhun wahala yayi baya zuwa ko ina kullun yana zaune kusa da gadon ta dan gani yake kamar idan ya tafi zata farka ba'a gaban saba, Aryan yana kokarin wajen kwantar masa da hankali. Khalid kuwa ya samu sauki ya warke sumul har ya fara jinyar yaron cikin jikin sis love ɗin sa. A ɓangaren Yusuf ma kulawa ta musamman yake bawa baby lamrat dan ji da cikin nan nashi yake kamar me. Ahmad kuwa soyayya babu kama hannun yaro tsakanin sa da hajjon sa yanzu ya sata a makaranta shi da kansa yake kai ta ya kuma ɗauko ta. fahad da Amrat zuba soyayya suke suma iya son ransu sai dai har yanzu Fahad na ɗaga mata kafa. Ba yadda ba'ayi da diyana ba akan ta koma part ɗin yaya Aryan amma taki har da kuka tana rantsuwa akan ba zata koma ba,haka Abba yace a kwale ta zuwa gaba kaɗan ta ɗan kara hutawa sosai Aryan ya shiga damuwa dan yana kaunar jiddan sa yana bukatar ɗumin jikin ta yana son ganin ta kusa da shi,amma haka ya hakura ya kyale ta ya sai mata waya dan su rinƙa hira amma ko ya kira tana gani bazata ɗauka ba idan ya shigi Part ɗin Ammi sai ya gudu ta ɓuya tun yana iya ɓuyewa har abun ya fara bayyana dan har rama yayi Saboda tunanin jiddan sa ita kuma jidda wasan ɓuya ma take da shi yanzu ko ajikin ta sai kiba take tana kara haske duk wasu albarkatun jikin ta sai kara girma suke.

Yau tun safe Abba yayi kiran family meeting. 9am gaba ɗaya family suka haɗu a palo har da Aunty Amarya Aunty Maryam Aunty farida da bata da lfy ma an ɗauko ta hiyana ce dake sume bata zoba.
Cikin nitsuwa Abba ya fara magana "ku bani hankalin ku, yanzu tun da Allah ya sanya Ahmad ya samu lfy zai koma kan kujerar mulkin sa dan na gaji" kasa da kai Ahmad yayi cikin karyewar zuciya yace "Abba dan Allah kabawa uncle Aliyu mana" "aa Ahmad Aliyu ba zai ansa mulki ba meeting ɗin nan ma danace yazo cemin yayi bashi da time dan haka ku kyale batun Aliyu next week zaka koma kan kujerar mulkin ka" shiru palon yayi ba wanda ke magana yaya bello yana son yayi magana akan hiyana amma yana bala'i tsoron bgs dan yaga yadda bgs ke bawa hiyana kulawa kuma fuskar bgs babu alamar wasa ko kaɗan kallo ɗaya zaka masa ka gane mutun ne mai bala'i zafin rai.
"Akoi mai magana a cikin kune!?" Cewar Abba Ammi na kokarin yin magana sukajiyo voice ɗin hiyana kasa kasa da kyar ta furta "Assalamu alaikum" a sukwane bgs ya ɗago kai tare da kai kallon sa bakin Kofar shigowa,tabbas itace tana tafiya tana dafe bango sai taga taga take kamar zata faɗi,a zafafe ya miƙe ya nufeta,kamar wata yar baby haka ya ɗauko ta ya dawo da ita saman sofar da yake zaune ya kwantar sa ita yana faɗin "kar ki tashi dan baki gama warkewa ba" hararar sa ta kasan ido tayi kafin ta kawar da kanta daga kallon sa

Alhadulillah Alhadulillah shine abun da jama'ar palon ke faɗin,ba tare da Aryan yayi magana ba ya miƙe ya bar palon.

jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da akwatin bappa da key ɗin kusa da hiyana yazo ya mika mata,kafin ta ansa bgs ya rigata ansa yana faɗin "ne menene wanna ɗin!?" "Ka bata zata buɗe mana ne" cewar Ammi dan tasan tana ce masa magani zaa ɗauka wa Aunty farida zai iya hanawa yace sai dai a kira likita. Ba musu ya mikawa hiyana akwantin ansa tayi ta yun kura zata mike,cikin sauri ya mikar da ita a hankali ya zaunar da ita tare sa saka mata pillow a bayan ta, a kule tace "kar ka sake taɓani yaya Prince!" a sukwane ya waro manya manyan idon sa waje yana kallon ta ba shi ka ɗai ba kowa na palon ya girgiza da jin maganar hiyana barin ma Abba da Ammi, ita ko hiyana ko ajikin ta ɗaure fuska sosai ta kara yi tana faɗin "Ammi taya ake buɗe a kwanakin?" Zama bgs yayi kusa da ita yana kallon ta har yanzu mamaki yake me yasa tace kar ya sake taɓata ko dai zafin ciwo ne ya sanya tace hakan?.

"Bello ka nuna mata ta yadda zata buɗe" cewar Ammi mikewa yaya Bello yayi ya nufota yana faɗin "to Ammi" bai kai ga karisawa wajen ba bgs ya ɗaga masa hannu yana faɗin "ni bana bukata in dai sai wani ya nuna mata yadda ake buɗewa to sai dai kar a buɗe" ya kai karshen maganar tare sa ansan a kwanakin yayi wurgi da shi,shiru palon yayi duk kan su suna tsoron yiwa bgs magana jiki ba kwari yaya Bello ya koma wajen zaman sa ya zauna.

girgiza kai Ammi tayi ta miƙe da kan ta ta nufi akwatin ta tsugunna tana kokarin ɗauka sai ganin bgs tayi ya rigata ɗauka ɗaure fuska tayi tana kokarin yin magana idon ta ya sauka kan Abba dake girgiza mata kai alamar tayi shiru,ba musu tayi shiru ta koma saman sofan da ta tashi ta koma ta zauna.
Miƙa wa hiyana akwatin bgs yayi yana faɗin "ba sai wani ya nuna miki ba ki buɗe da kan ki" ansa tayi tana bin wajen sanya key ɗin da kallo
Daga karshe ta ɗauko key ɗin a hankali ta zura a ramin tana zurawa key ɗin ya kwace kansa yayi cikin akwatin ɗan karamin kara akwatin yayi alamar yana buɗuwa. Ya ɗau tsawon yan mintoci yana yar kara kafin ya tsagaita jim kaɗan akwatin ya buɗu wani daddaɗar kamshin turare ne ya fara fitowa daga akwatin nan take ya gauraye palon.

mikawa Ammi akwatin hiyana tayi Ammi ta ansa ta mikawa yaya Bello, ya ansa ya fara fitar da abubuwan dake ciki wani magani ya fito da shi kalar ruwan ganye ɗagowa yayi ya kalli Ammi cikin nitsuwa yace "Ammi babu maganin da zai karya asirin nan sai dai maganin da zai juya asirin ya koma kan wanda ya mata hakan" shiru Ammi ta ɗan yi kafin tace "aa Bello bai kamata mu zama irin ɗaya da su ba bai kamata mu mai da musu kan su ba ka dai kara dubawa" cike da jin haushi Aryan yace "kai zoka haɗa mata maganin ya koma kan nasu mana ba susuka haɗa ba suje chan su karata ai zasu san hanyan da zau bi su warware idan ma ya kamasu" da sauri Khalid ya ansa zanchen da cewa "kana da gaskiya Aryan tun da su basu da imani har suka iya mata wanna abun tofa ya zama dole su ansa hukunci ka mai da musu da kayan su kan su" gyaran murya Ummi tayi kafin tace "ranka ya daɗe me kace ya za'ayi!?" gaba ɗaya palon kallo ya koma kan Abba. Shiru ya ɗan yi na yan mintoci kafin yace "ayi yadda Aryan yace dan sun nuna ainihin rashin imani dan haka a mai da musu da kayan su" kallon yaya Bello Aryan yayi yana faɗin "sai ka fara aikin ko" "ku bani ruwa a roba tukun nan" cikin sauri amrat ta miƙe ta nufi waje.

Jim kaɗan ta dawo hannun ta ɗauke da ruwa a roba mai ɗan faɗi, gaban yaya Bello tazo ta ajiye masa tana faɗin "yaya Bello gashi nan".
Jawo roban ruwan yayi ya fara karanto nasi falaki kulhuwa Ayatul kursihu yana tofawa cikin ruwan yana zuba garin maganin,bayan ya gama sai ya karaton ayoyi goma cikin ruratun bakara daga shafin 8 na farko ya karanta sau biyu sanna ya rufe da amanar Rasuluh.

Bayan ya gama haɗa komai ya ɗago ya kallin su Ammi yace "to ku shirya kuma duk ku fara addu'a a ranku dan shaiɗanun aljanu aka haɗata da su idan sun fita zasu iya komawa kan ɗaya daga cikin ku" jin haka ya sa diyana ta miƙe a sukwane ta koma kusa da Aryan ta zauna ta kankame hannun sa tare da kwantar da kanta a kafadar sa,saura kaɗan dariya ya kubce masa saboda razanar da diyana tayi ashe dai akoi abun da take tsoro Fahad kuwa rungume amrat ɗin sa yayi tare da kwantar da kan ta saman faffaɗar kirjin sa, kallon hiyana bgs yayi ya ga hankalin ta ma baya kansa "sister ki rufe kan kin nan da kyau" ko kallon in da yake hiyana bata yi ba sai ma kara ɗaure fuska tayi sosai ta kawar da kanta gefe duk abun da suke kan idon Ammi da Abba suke mamaki Abba da Ammi keyi to meke faruwa?.

A hankali yaya Bello ya ɗago kan Aunty farida yana faɗin "ku buɗe min bakin ta" sakin diyana Aryan yayi yana kokarin miƙewa diyana ta fasa kara tana faɗin "ni wlh tsoro nake ji!" alama da ido bgs yayi masa akan ya koma ya zauna ba musu ya koma ya zauna ya rungumo jiddan sa, miƙewa bgs yayi ya kariso wajen ya tsugunna ya sanya hannun ya ɗan buɗe bakin Aunty farida da sauri yaya Bello ya fara zuba mata ruwan maganin,
ihu ta fasa tana kokarin kwache kan ta
da karfi yaya Bello yace "ku rinƙe ta da kyau lokacin da zakuyi faɗa da sheɗanun aljanune yayi ku gwada musu karfin ayar Allah" gaba ɗaya mutanen palon sai da suka girgiza ganin yadda Aunty farida ke kokarin faɗa da bgs tana son kwace kan ta, wani wawan damka bga yayi mata a wuya yana kokarin mai data ya kwantar da sauri Ummi ta miƙe zata bar palon dan bazata iya ganin abun dake fatuwa ba "Hauwa'u ki dawo ki zauna ayi komai a gaban ki" cewar Abba Ummi kamar zatayi kuka haka ta dawo ta zauna ta sunkuyar da kanta kasa.

Ganin Aunty farida na neman tafi karfin bgs ne ya sanya Aryan mikewa a sukwane ya kariso wajen suka haɗa karfi suka danne ta,kuka sosai su Aunty mardiya keyi har da Aunty Maryam awan nan karon tayi hawaye. da kyar suka samu Aunty farida ta nitsu amma duk ta kukkije musu jiki ta jiwa Aryan ciwo a wuyar sa duk dauriya irin na Ammi sai da tayi hawaye Abba ma daurewa kawai yake ya sunkuyar da kansa kasa Aunty mardiya Aunty salma kam baa magana sunyi kuka har idon su ya sauya.

Bayan Aunty farida tayi shiru kamar mai barcine suka sake ta dukkan su suka koma suka zauna suna mai da numfashi kallon yaya Bello Abba yayi yace "yanzu sai me kuma bawan Allah" "babu komai Abba In Sha Allah tana tashi zata dawo dai dai Kum.....bai karisa maganar ba Aunty Amarya ta fasa ihu ta faɗi kasa tana birgima tana faɗin duk abun da ta aikata daga farko har karshe,kallon kallon juna suka farayi gaba ɗaya jama'ar palon sun ma kasa magana masu kuka sun tsai da kukan nasu chak.

sai da Aunty Amarya tayi surutan ta daga farko har karshe sanna tayi shiru tana kallon sama, mutuwar zaune Aryan yayi ya kasa magana gaba ɗaya palon ba wanda ya iya cewa komai almost 30mins sanna Aryan ya miƙe tare da dafe sai tin zuciyar sa ya nufi hanyar fita yana faɗin "uwar da ta haifeni ita ta kashe min ɗan uwana da hannun ta ta jefamin yan uwana cikin tashin hankali ta haukata min matata ta haɗa Ahmad da bala'i ta haɗa Aunty farida da ciwo innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Allah ka ɗauki raina na huta dan ba.... Bai kai karshen maganar ba numfashi sa ya ɗauke diff rai yayi halin sa ya yanke jiki zai faɗi a sukwane bgs ya kariso wajen ya taro sa yana kiran sunan sa a ruɗe "Aryan!!! Aryan!!! Aryan!!! Kada kamin haka kada kamin haka Aryan kayi wa Allah karkasa hakan a ranka kar ka cutar min da kan ka" yana magana cikin fitar hayyaci cikin tashin hankali "Aryan kasan dai nima bazan iya rayuwa ba tare da kai ba ko? Pls my blood ka tashi karka min haka" ya kai karshen maganar tare da shinfiɗe Aryan a kasa yana danna masa kirjin sa da karfi karfi, ganin bgs ya fita hayyacin sa yana kokarin yiwa Aryan illa ne ya sanya su Khalid suka kariso wajen da gudu suna kokarin jan bgs baya a fusace yayi watsi da su ya koma kan Aryan yana bubbaga masa kirjin sa yana kiran "no Aryan no i said no!!? Kuka sosai su Aunty mardiya suke Aunty maryam kam tama kasa kukan tayi mutuwar zaune sumar zaune Omar yayi.
yaya Bello kuwa lallaɓawa yayi ya kamo hannun hasana da hajjo suka bar palon, tashin hankali ya hana Abba yin magana Ammi Ummi duk bakin su ya mutu sun kasa ko motsi daga in da suke,runtse ido hiyana tayi tana hawaye ba karamin tausayi yaya Aryan ya bata ba Yusuf Khalid jiki ba kwari suka miƙe daga watsi dasu da bgs yayi suka koma kusa da matan su suka zauna dan wanna bala'i yafi karfin tunanin su Haidar ma hawaye yake Fahad kuwa ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa ko motsi

mikewa Aunty Amarya tayi ta rarrafo zuwa kusa da Aryan ta tsugunna cikin kuka tace "kayi hakuri ɗana ka yafemin ni da kai na na kashe yaya dukka biyu wayyo Allah na shiga uku na" ta kai karshen maganar tare da kai hannun ta saman kumatun Aryan, wani wawan damka bgs ya mata a wuya ya zaro idon sa da sukayo jaa kamar jini cikin tsawa yace "idan kika sake taɓa min ɗan uwa wlh ba abun da zai hanani kashe ki azzaluma kin cuci rayuwata wlh idan Aryan bai tashi ba sai na miki kisan wulanci" waro ido waje Ammi tayi dan bata taɓa ganin bgs cikin tashin hankali haka ba ganin sa a haka ba karamin tsoro ya bata ba gaba ɗaya ya canza lokacin guda fuskar sa tayi jaa kamar jini gashin jikin aa duk sun mimmike idon sanna kamar jini haka ya zamo jiyoyin kansa kamar zasu fito wajen gashin kansa ya watse sai cije lips yake da karfi.
gaba ɗaya family dake palo sun tsorata ainun da ganin yananin da bgs ya shiga.

Zaro ido waje Aunty Amarya tayi kamar idon nata zasu faɗo kasa saboda shakar da bgs ya mata gashi kuma yaki sakin wuyar nata
Cikin sanyin murya da tausayin ƴaƴan nata dan tasan yadda bgs ke bala'i son Aryan kamar ransa Ammi tace "ka sake mata wuya kaji? zata iya mutuwa fa" "ta mutu mana ta mutu Ammi menen amfanin ta aduniya daman wlh idan Aryan bai tashi ba da kai na zan mata kisan wulanci saboda neman duniya ta tarwatsa mana farincikin rayuwar mu saboda son duniya ta kashe min ɗan uwana kuma ɗan cikin ta tir da shaiɗaninyar zuciya ya Allah duk in da muke dagani har yan uwana ya Allah ka tausaya mana ka bar mu da imani" ihu diyana ta fasa ta miƙe da sauri ta dawo kusa da Aryan tana faɗin "yaya Aryan karka mutu ka barni dan Allah ka tashi" wurgi da Aunty Amarya bgs yayi ya miƙe ya ɗauki Aryan ya saɓa sa a kafaɗa ya nufi waje da shi sai lokacin Abba ya samu damar yin magana yace "Safras ka dawo da shi nan karka kaishi ko ina" ba musu bgs ya dawo da shi ya shinfiɗe sa saman sofa mai zaman mutun 3.

Ihu Aunty Amarya ta farayi tana murkusoso ba wanda ya kulata sai Ammi da Ummi su suka nufe ta suna karanto mata addu'a cikin ihu take faɗin "ƴaƴa na ku yafe min na shiga uku ni da kai na na kashe Aiman yanzu gashi na sa Aryan ya haɗiye zuciya ya mutu me ya rage min innalillahi nayi nadamar zuwata duniya sadiya kin cuce ni kin gama dani inna...bata kai karshen maganar ba rai yayi halin sa zuciyarta ta buga, kallon Ummi Ammi tayi kafin su juya a tare su kallin Abba yayin da shima su yake kallon, girgiza masa kai sukayi a tare alamar shikenan ta tafi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login