Showing 345001 words to 348000 words out of 363274 words

Chapter 116 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2607

da kan ta kasa har suka isa asibitin ba wanda yace da wani kala.
Tun daga nesa ta hango bgs a parking space na hospital ɗin ta tsorata da ganin yanayin da yake ciki duk ya sauya har yar rama sai da yayi bgs da bala'i tsabta amma yau shi ne yake tsaye jikin sa duk jini kuma bai damu ba lallai ba karamin tashin hankali yake ciki ba lokacin guda taji hawaye sun zo mata kokari ta yi ta danne su Shahram na tsaida mota kafin ya fito ya buɗe mata bgs dake tsaye a wajen ya sa hannu ya buɗe mata kofar motar cikin sauri ta fito tare da faɗa wa saman kirjin sa a tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, kasa kasa yace "I missed you My pleasure" kara shige wa jikin sa tayi da kyau ta shagwaɓe murya tana faɗin "Ni ma nayi kewar ka sosai" buɗe motar Shahram ya yi, ya fito ya bar wajen ya nufi ɗakin da Aryan ke kwance.

Sun ɗan jima manne da juna kafin ya raba jikin su ya ruko hannun ta yana faɗin "Muje" "Yaya Prince bari na ɗauko jaka ta da basket ɗin abincin a cikin mota" sakin hannun ta ya yi, ya buɗe motar da kan sa ya fito da basket ɗin tare da jakar ta ya rufe motar tare da miƙa mata jakar ta shi kuma ya rike basket ɗin da hannu ɗaya, ya rike hannun ta da ɗayan hannun sa suka nufi ɗakin da Aryan ke kwance sosai bgs ya ɗan samu sauki a ransa tun lokacin da Hiyana ta sa shi sukayi salati tun lokacin ya cigaba da ambato sunan Allah a ransa lokacin guda yaji damuwar sa kaso 60 cikin ɗari ya gudu ya samu sauki sosai a ran sa. Da sallama suka shiga ɗakin su Aryan ɗin, Aryan na kwance saman gadon marasa lafiya duk da yana sume ya rame sosai yayi wani irin hasken wahala kallo ɗaya bgs ya masa ya kawar da kai dan bai san ganin Aryan a halin da yake cikin nan da sauri Hiyana ta karisa wajen da sauri Shahram dake zaune kusa da Aryan ya mike ya koma bakin kofar shigowa ya tsaya ajiye jakar ta tayi ta kwance nikaf ɗin fiskar ta, ta ajiye ta zauna a gefen gadon Aryan a hankali ta fara karanto addua'o'i tana tofa masa zuba mata ido bgs ya yi yana kallon. 30mins ta ɗauka tana yi wa Aryan addua'o'i kafin ta ɗago ido ta kalli bgs cikin sanyi murya tace "Yaya Prince ba wani allura da zaka masa ko wani magani da zaku bashi ya farka" shiru ya ɗan yi kafin yace "sharp brain kin tunamin akoi allura sai dai alluran da dadewa gomnatin ta hana amfani da shi shiyasa yanzu babu shi amma kamar ba zamu rasa a gida ba dan a baya muna yiwa sojojin mu idan irin haka ta faru da su, idan Allah yasa ma muna da Alluran ko na masa zai kai kwana biyu kafin ya farfaɗo bari na kira Yusuf ya bincika min tsofaffin magani gida mu gani" ya kai karshen maganar tare da ciro wayar sa daga aljihun sa ya laluɓo number Yusuf. Bugu ɗaya Yusuf ya ɗaga bgs na kokarin yin magana Yusuf ya katse sa da cewa "Ka dawo da Aryan gida akoi sauran alluran kwali ɗaya na duba basu yi expire ba" katse kiran ya yi ba tare da ya yi magana ba ya dubi Hiyana dake kallon sa tana jiran taji an samu alluran ko yaya kashe mata ido ɗaya ya yi tare da ɗaga ma ta gera ɗaya kasa tayi da kan ta dan taji kunya "Me ki ke kallo na?" Zazzakar voice na shi ya katse ta cikin sauri ta ɗago kai tana faɗin "Nifa ba da wata manufa na kalle ka ba kawai ina jiran in ji an samu alluran ne" "za kiyi bayani da kyau ne" ya yi maganar yana kokarin cirewa Aryan ruwan da suka sa masa shiru ta yi ita ma bata sake magana ba har ya gama cire wa Aryan komai da suka sa masa yana kokarin ɗaukan sa Dr ya shigo yana magana cikin harshen turanci "Tun ɗazun muke jiran ka kasa mana hannu mu fara yiwa Aryan aiki amma kayi shiru" ko kallon in da Dr yake bgs bai yi ba ya saɓi Aryan a kafaɗar sa ya nufi waje yana faɗin "Eshat muje" da sauri ta ɗauki jakarta, ta bi bayan sa ta bar musu basket ɗin abincin awajen.
idan da sabo Dr ya saba da halin bgs shi baya tsayawa wai a sallami mara lafiyar da ya kawo abun da ya ga dama kawai yake. Dr ya tsaya yana tunani shi kuwa bgs ya wuce da Aryan wajen motar su Hiyana na biye da shi da gudu Shahram ya buɗe masa motar ya kwantar da Aryan a gidan baya ya gyara masa kwanciya da kyau sanna ya fito ya rufe motar ya kama hannun Hiyana suka shiga ɗaya daga cikin motocin sojojin da suka rako su asibin da kan sa ya ja su daga shi sai ita yayin da Shahram ya tuka Aryan.


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai


























[8/19, 8:52 PM] SAFIYYA: 💋Duk Karfin izzata 💋




By
Star Lady


Page 62


....."Me ya kawo ka gidan mu kuma?" Kallon su Abba ya yi kafin yace "Yaya ina ka san wan nan matar?" "Meke faruwa ne ku mana bayani mana" cewar yaya Abdussalam sarkin zuciya "Aliyu meke faruwa ai na kasan Fateem?" Cewar Abba ƙasa uncle Aliyu yayi da kai kafin ya fara magana "A saudiya na santa tun ranar da na fara ganin ta na kamu da son ta na bita amma sai tace min tana da Aure na ɗauka karya kawai take min bata son yimin magana ne hakan yasa nayi ta bibiyar ta ina ta kura mata har daga karshe dai na gane da gaske tana da Aure lokacin da nake bibiyar ta tayi ta zagina da faɗa min maganganu marasa daɗi dan kare mutuncin Auren ta ni kuma naki dai na binta har sai dana tabbatar da gaske tana da aure naji ciwo a rai na sosai maganar dana ke muku wajen shakara 6 baya kenan Fateema itace mace ta farko dana fara so arayuwa ta na bita, tun da na gane tana da aure shike nan ban sake jin son wata a rai na ba shi yasa kuke ta min zancen Aure na share ku dan ni a rai na ita kaɗai nake so ita kaɗai ne a rai na shiyasa na ki yin Aure na cigaba da zama na kawai" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje yana faɗin "Yaya muje ni bana son ganin Fateema dan matar aure ce ni kuma zuciya ta har gobe akoi son ta a ciki bana son ganin matar wani" ya kai karshen maganar tare da ficewa ya bar palon kallon Abbo Abba ya yi yace "To Abbo munzo da kokon bara a baku Auren Fateema amma karku sanar da shi sai ta gama takaba zamuzo a ɗaura aure ba tare da ya sani ba bazata zan masa dan shekara da shekaru ina matsa masa yayi aure yaki sai yanzu Allah ya ƙaddara" murmushi Abbo yayi yana faɗin "Na bashi Auren Amina har abada Allah ya kai mu lokacin" da fara'a Ammi ta amsa zancen da cewa "To sai a bar ta ta gama takabar ta a nan sai munzo biki kawai sai mu tafi da ita yanzu ba zancen yin wata ɗaya ta dawo ta zauna da yan uwan ta sai munzo ɗaurin Aure sai mu wuce da ita kawai bayan an ɗaura" kasa Hajj Fateema tayi da kan ta miƙewa Abba yayi yana faɗin "Muje kar muyi tafiyar dare". Har wajen motocin da zasu kai su Abba airport su Abbo suka rakasu suna sumu sallama tare da tunatar da Abba akan kar su manta batun turo su Hiyana da mazajen su da fara'a Abba ya amsa da In Sha Allah ba zasu manta ba zasu zo ba jimawa. Da haka sukayi sallama su Abba suka shiga mota suka wuce Airport daga nan suka hau jirgin da ya kawo su suka koma Naija cike da tsarabar Sudan sai murna suke.

Nigeria

Suna dira Nigeria suka samu mummunar labarin mutuwar mijin Aunty Maryam wato Major haka washe gari suka shirya suka wuce Gombe dan zuwa gaisuwa. Kwanan su uku a Gombe suka juyo tare da Aunty Maryam dan ta dawo gida tayi takaba.

A ɓangaren Inna kuwa su Abba basa nan Yusuf yasa aka rataye ta bayan dawowar su Abba ne suka samu labari Abba da kansa ya ansa ɗan da ta haifa ya miƙa wa Ummi yace ta rike sa da amana da murna ta ansa ɗan aka fara bashi madara yaron kyakkyawa da shi kamannin sa ɗaya da bappan su yaya Bello yana cike bulbul abun sa Ummi bata da matsala ta amsa ɗan ta san cewa laifin wani baya shafan wani Abba ya hana a faɗa wa su Diyana ɗan inna ne dan yasan idan suka sani yaron ba zai taɓa tashi cikin jin daɗi ba dan haka sai ya sanar da su akan ɗan Inna ya rasu ya bawa Ummi akan idan sun zo sun tambayi ɗan waye Ummi tace musu daga Katsina ta ɗauko shi da haka Abba ya rufe maganar.

After 2 days Aliyu Haidar takwarar uncle Aliyu wato Haidar ɗin Ammi ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa saudiya sai murna yake sun dai dai ta da Fariza sai murna yake sosai ya dawo tare da Hindu mai aikin Hajj Fateema suna shiga gida kai tsaye palon Abba ya wuce da Hindu nan ya samu su Abba gaba ɗaya suna zaune suna tattaunawa akan bikin Ahmad da Omar dan tare za'a haɗa da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo palon nan idon gaba ɗaya jama'ar palon ya dawo kan sa wuce wa ya yi kusa da uncle Aliyu wato takwarar sa dake zaune kusa da Abba ya zauna yana faɗin "Wayyo na gaji" Abba na kokarin yin magana Aisha da Sadiq suka miƙe a tare suna faɗin "Mama" sunyi maganar suna kallon Hindu mai aikin Hajj Fateema kallon Hindu Abba yayi kafin ya dawo da kallon sa kan su Sadiq kallon su Hindu take ta kasa magana mamaki ya kama gaba ɗaya jama'ar palon sun kasa magana Ammi ce tayi ta maza tace "Aisha maman kuce?" Da sauri Aisha tace "Eh Ammi itace maman mu ina da hoton ta tun bamu girma sosai ba ta tafi aiki a saudiya ta barmu bata kara dawowa ba" ta kai karshen maganar tare da sakin kuka mai tsuma rai alama Ammi ta mata da hannu akan tazo da sauri ta tafi ta faɗa jikin Ammi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sosai Ammi ke rarrashe, shi kan Sadiq ya kasa magana zubewa kasa Hindu tayi tare da sakin kuka tana faɗin "Wallahi na san ban kyau ta muku ba akan neman duniya nayi watsi da ƴaƴana ku yafe min" jinjina kai Abba yayi kafin yace "Eh gaskiya kam Hindu baki kyau ta ba ko kaɗan in da hanyar kyau tawa ma yabi baki bishi ba har da ƴa mace kika watsar kika tafi dama dai mazane dukkan su biyu to da da ɗan sauki kin san haɗarin da mace take da shi kuwa? Har alkawari Allah ya yiwa wadda ya samu ya mace Ubangiji yace duk wanda ya haifi ƴa'ƴa mata uku ya basu tarbiya har ya aurar da su basu taɓa zina ba ya wa wanna mutumin alkawarin gidan aljanna ƴa mace ce ke kai iyayen ta wuta farat ɗaya haka kuma ita ke iya zama sanadiyyar shiga aljanna iyayen ta farat ɗaya ƴaƴa mata ba abun wasa bane abun a sa musu ido da basu kulawa ne kamar yarda manzon Allah (SAW) yace mata na sa rauni hakane dayawa daga cikin mutane idan akace musu mata na da rauni suna ɗukan abun, kamar mace bata da karfi ko bazata iya yin abun da na miji yayi ba, to ba haka annabi yake nufi ba abun da annabi yake nufi da raunin mace zuciyar su mata suna da abubuwa biyu zuwa uku a zuciyar su wadda shi annabi ke nufi da raunin mace, abu na farko mace na da kawa zuci abun da ake cewa kawa zuci ya kunshi tausayi san yan uwan ta, mace ba zata iya tafiya waje tayi sati tana lafiya ba tare da ta nemi gida taji halin da suke ciki ba saɓanin ɗa namiji wadda zai iya tafiya yayi shekara ba tare da ya tambayi ina kanin sa wane aa ina wane amma mace tana kiran gida sai ta lissafo ɗaya bayan ɗaya ta tambaya suna ran ta a ko da yaushe mace ce tana da tausayi fiye da namiji dan shi namiji yana da dakakkiyar zuciyar da ko abu ya bashi tausani zai iya jurewa ya hakura ya cire abun ya watsar saɓanin ita mace da duk yadda ka kai da yi mata abun da ba daɗi idan abun rashin daɗi ya same ka sai ta tausaya maka barina ɗauki misali da su Diyana yanzu haka duk abun da Habiba ta musu nan muddin aka ce musu Allah sarkin yaron nan bai da kowa zai taso cikin wahala da rashin jin daɗi wallahi da wuya na gama rufe baki basu yi rige rigen cewa zasu ansa yaron ba duk wani abun da mahaifiyar yaron ta musu zasu mance da shi wanna shine kalan raunin da annabi ke nufi bawai mace ba zata iya yin wani aiki da namiji yayi da sauran su ba yanzu zaka iya sarrafa zuciyar mace ko mai girman ta kuwa abu kaɗan zaka mata ta sauya daga yadda take shakara da shekaru wanan ɗaya ne daga cikin babban haɗarin barin yar ki mace ki tafi neman wani abu wai shi kuɗin, abun da a duniya zaki bar shi ki sani ƴaƴan nan da kike gani kamar ke kike da hakki a kan su to suma suna da hakki a kan ki kuma ki sani ɗaya bayan ɗaya sai Allah ya tambaye ki ya kika kula da su a ranar da baki baya karya dole ki faɗi duk wani abu da kika musu tarbiyyar su da sauran su, wan nan babban kuskure ne ya kamata ku gyara ku ja ƴaƴan ku mata ajiki ku zama tamkar kawayen su kuyi wasa da dariya da su ta yadda zaku saba ya zamto bata ɓoye miki komai nata a matsayin ki na mahaifiyar ta karki wani nuna kamar kin haifeta kin girme mata aa ki jata a jiki ku zama kawaye dan duniyar yanzu ta wuce tunanin mai tunanin ba dan Allah ya tsare yaran nan da karinyar sa ba kina tunanin a zaman nin nan zaki dawo ki same su ne? To ya kamata wan nan ya zama izini gare ku mata Allah ya kyau ta" Abba na yin shiru Ammi da Ummi suka ansa sai da suka wa Hindu faɗa mai ratsa zuciya sanna Ammi ta umarci Aisha da ta rakata ɗakin su taje tayi wanka ta huta wucewa Aisha tayi tana kuka ta fita jiki ba kwari Hindu ta bi bayan ta tana mai danasanin abun da ta aikata sai kasa take da kai dan kunyar ƴaran nata take kallon su Ammi Abba yayi kafin yace "Kuje zamu karasa maganar bikin da daddare" yana kai karshen maganar ya mike ya wuce bedroom na shi da haka su Ammi suka fice kowa ya koma part na shi uncle Aliyu ma ya wuce part na shi.

After 4 month

Us

Tsaye suke Yusuf Aryan Fahad Khalid a bakin labour room da Lamrat ke ciki tana nakuda sai safa da mar wa Yusuf yake yana ta faman haɗa zufa shiru su Khalid suka tsaya suna addu'ar Allah ya sauke ta lafiya dai dai lokacin bgs ya iso shida Hiyana dake ta masa kuka sai ya kawota taga Lamrat shi ne ya bar wajen aiki dole yaje gida ya ɗauko ta ya kawota kallon Aryan yayi yana faɗin "Ta haihune?" Girgiza kai Aryan ya yi yana faɗin "A'a tun da suka shiga da ita likitocin basu fito ba" "Ok ni zan koma kome yake ciki ka sanar da ni awaya ga Eshat nan" ya kai karshen maganar tare da dafa kafaɗar Yusuf dage zagaye wajen yana faɗin "Addu'a zaka nitsu ka mata ba zagaye ba" ɗago idon sa da suka rikiɗe suka yi jaa Yusuf yayi yana kokarin yin magana Dr ta fito hannun ta rike da baby boy tana ta murmushi da sauri Hiyana ta tari Dr tana murmushi tasa hannu da nufi ta ansa baby zuba mata ido Dr tayi Hiyana ta ruɗe ta rasa ta yadda ake rike baby dan bata taɓa ɗukan jinjiri ba girgiza kai Dr tayi san nan ta wuce ta ta nufi wajen bgs da gudu Hiyana ta shiga ɗakin da dr ta fito wato in da Lamrat ke kwance. Dr kuma ta tana zuwa wajen su bgs ta miƙa wa bgs dan a tunanin ta shi ne baban baby kasan cewar taga babyn ya ɗan yi kama da shi hannu yasa yana son ansan baby bai iya rikewa ba mamaki Aryan yake wai yau bgs ne har da kai hannu zai ansa baby tab Allah mai iko abun da basu taɓa tunani ba arayuwar su bgs ɗin da bai son ganin babyn da ya kai shekara ɗaya ma bare jinjiri ko lokacin da Aunty farida ta Haifi Junior ba yadda ba'ayi da shi ba yaje yaga baby yaki shi idan ba yaro ya kai 4 years ba baya ko ɗaga ido ya kalli yaro ba wai kuma dan baya son ƴaƴan ba haka ra'ayin sa yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login