Showing 264001 words to 267000 words out of 363274 words
zaune a palo ya isko Aryan da dadyn Junior ba tare da ya zauna ba yace "Aryan ya kamata muje ko?" Miƙewa Aryan yayi tare da fito da wayar sa daga aljihun sa dan ya kira Shahram a sukwane yace "what auta 3 miss call lfy kuwa?" cikin zafin nama ya fara kiran layin nata a kashe ɗago ido yayi ya kalli bgs dake tsaye ya tsare sa da ido yana jiran yaji menene
Ganin kamar Aryan bai da niyar magana ya sanya shi saurin ciro wayar sa a aljihu waro manya manyan idon sa waje sosai yayi lokacin da yayi karo da miss call ɗin Zahra har uku na Ammi biyu da sauri ya fara kiran layin Zahra amma a kashe layin Khalid ya kira wayar tana ta ringing baa ɗaga ba ɗago ido yayi ya kalli Aryan yayin da shima Aryan ɗin shi yake kallon lokaci guda suka ja dogon numfashi
A tare suka fara kokarin kiran Ammi dan suna da tabbacin ba lfy ba auta ta musu miss call har 3 kai ina ba lfy
Call ɗin Aryan ne ya fara shiga wayar Ammi tana kwance saman gadon ta cikin sauri tayi picking tana faɗin "hello Aryan" jin voice ɗin Ammi lfylou ya sanya ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya yana faɗin "Ammi ya gida? Kowa lfy ko?" ciro wayar tayi daga kunnen ta dan ta tabbatar Aryan ɗin ne da gaske ya yake tambayar ta ya gida bayan a gidan suke jin haka ya sa tace "Aryan meke faruwa?" da ya fahimci ba komai sai ya nemi ya waske dan kar hankalin Ammi ya tashi
da kyar ya samu suka rabu da Ammi tana cikin kwanciyar hankali dawo da kallon sa yayi kan bgs dake tsaye,waro ido waje sosai Aryan yayi yana kallon sauya wan da bgs yayi lokaci guda idon sa sun kaɗa sunyi jaa sosai jijiyoyin kansa duk sun tashi sai huci yake ya kafe idon sa a kan wayar sa da alama wani abun yake kallo tun da ya ga bgs a wanna hali yasan ba lfy ba
Ba tare da yayi magana ba ya wuce bedroom na Aunty farida jim ka ɗan ya fito ɗauke da ita a kafaɗar sa suka nufi waje,cikin zafin nama da taku irin na jaruman maza Bgs ya fice daga palon
daga gidan Aunty farida kai tsaye Airport suka nufa Aryan na son tambayar bgs meke faru amma ya hakura dan ya san bgs ba zai faɗa masa komai a gaban Aunty farida ba kasan cewar bata da lfy
A ɓangaren jabir kuwa kafaren guest house na dadyn sa suka wuce da Zahra
Suna isa ya sanya aka fito da ita yaran baban nashi suka kewaye gidan da bindigu matsowa kusa da ita jabir yayi ya fara magana
"Ke ina hiyana na?" Zahra da muryan ta baya fita sosai saboda kukan da ta sha tace "wasu sun ɗauke ta" mari mai lfy jabir ya sakar mata a kumatu kafin yace "ni ba dake nake gaba ba hiyana da yayan ku nake nema dan haka yanzu ki bani number ɗaya daga cikin yan gidan ku domin na kirasu su kawomin hiyana su anshe ki" cikin sauri Zahra ta fara karanto masa layin bgs yana sanyawa awayar sa
Sau biyu yana kiran layin Bgs amma bai ɗaga ba kasan cewar bgs baya ɗaukan new number
Mari mai karfi ya sake sakar wa Zahra cikin faɗa yace "ni zaki rai na wa wayo? ki bani number da ba zaa ɗaga ba maza ki bani number da kika san ina kira zaa ɗaga" already Zahra ta sha kuka har ta gaji yanzu gaba ɗaya kukan ma ya dai na fita zuciyar ta ta bushe bata jin komai wani tunani ne ya faɗo mata "jabir wawane bai yi karatu ba ba abun da ya iya a school sai shirme dan haka bari nayi amfani da wawancin nashi na kafa masa tarko ta yadda yaya prince zai cin masa cikin sauki" katse mata tunanin da take yayi ta hanyar kara mata mari yana faɗin "ba dake nake magana bane?" Cikin dakiyar zuciya tace "number da na bakan nan shi ka ɗai ne number wan da na riƙe a kai na sai dai ka masa massage dan nasan baya kusa da wayar ne idan ka masa massage idan yazo zai gani" "good idea" ya faɗa kafin ya fara typing massage kamar haka "na ɗauki Zahra tana hannu na akawomin hiyana azo a anshe ta" yana gaba typing ya turawa bgs
Nauyayyar ajiyar zuciya Zahra ta sauke lokacin da taga ya turawa bgs sakon addu'ar allah jikan sa take masa a ranta dan tana da tabbacin ko ina yaya Prince yake nan da 30mins zai bayyana a nan.
Umarni zabir ya bawa yaran baban sa akan su ɗaure masa Zahra a jikin itacen mango dake cikin gidan
a take suka ɗaure ta itakam ko a jikin ta dan burinta ya gama cika jabir tashi tazo karshe matikar yaya Prince yaga massage ɗin nan shikenan kuma
Jirgin su na sauka a Airport basu wani ɓata lokaci ba suka fito Aryan ɗauke da Aunty farida a kafaɗar sa dadyn Junior na bayan su
"Aryan ku wuce gida ina zuwa sanna idan su Ammi suka tambaye ka ina auta Khalid da sister kace muna tare"cewar bgs yana kai karshen maganar ya nufi wajen motocin su
ansan key ɗin motar dake hannun Abdol yayi ya shige motar da kan sa yaja da gudun gaske ya bar airport ɗin.
Mamakin abun da ke faruwa Aryan yake har suka shige cikin motocin su suka bar Airport ɗin.
Gudu suke da motar su kamar zasu tashi sama cikin kankanin lokaci suka fita garin kano,sunyi tafiya mai nisa tsakanin su da garin kano kafin su kutsa cikin daji da motar, nan ma tafiya mai nisan gaske sukayi kamar wayan da zasu bar dunuyar kafin su iso wani ka ta faren gida
ta cikin gate ɗin gidan suka kutsa motor su
bayan suyi parking ne suka firfito tare da fito da Khalid da hiyana da gaba ki ɗaya sun jiggata barinma hiyana
waya ogan su ya fitar daga aljihun sa ya danna kira jim kaɗan ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Oga yau fa mun fara aiki a cikin hotuna huɗu da ka baku munyi nasarar kama mutun biyu saura biyu suma mun sa musu ido muna ganin motsawar su daga gidan zamu kama su" daga ɗayan ɓangaren ogan yace "good yanzu abun da nake so da ku ita macen nan ina ganin kamar tana da mahimmanci sosai tun da har bgs da kan sa ya ɗauko ta a saman kafaɗan sa to ku kula da ita sosai shi kuma na mijin daman mun san already yana ɗaya daga cikin mutane shida da bgs ke matikar kauna dan haka ku masa azaban da sai ya gwammaci mutuwa kafin na shigo kasar macen ku barta sai na karisa bincike na tabbatar wacece ita yanzu abu ma na farko da na manta ban faɗa muku ba shine ku charje su ku raba su da duk wani abun dake tare da su dan nasan wanene bgs ku zauna cikin shiri dan zaizo tabbas zaizo ina son idan yazo ku haɗa su ku musu kisan mummuke ammafa ku kula kuma ina kara jaddada muku akan ku chire duk wani abun da kuka gani a tattare da su bgs ba na wasa bane" yana kai karshen maganar ya karse kiran juyowa ogan nasu yayi ya kalli su Khalid kafin yace "ku ɗaure mace shi kuma namijin ku kai she ɗakin horo amma kafin nan ku bincike su ku cire komai dake tattare da su ku kona" cikin dakiyar zuciya Khalid yace "dan Allah oga kayi hakuri kubar sister ta tafi ni ku riƙe ni ko kashe ni zakuyi ku kashe ni amma ita dan Allah ku kyale ta" wani mugun dariya ogan yayi mara daɗin ji
sai da yayi dariyar sa mai isar sa sanan yace "daman muna tantama akan macen shin tana da mahimmanci a wajen kune ko bata da shi yanzu ka tabbatar mana tana da matikar mahimmanci mungode da ka bamu amsa ba sai mun sha wahala ba kai ku ɗauki mace ku sanya ta a ɗakin duhu shi kuma ku kai min shi ɗakin horo bari na ɗan wasa jini a kan sa kaɗan ita kuma macen zuwa dare damuyi ferfesun ta yau akoi sharholiya
Ko alamar tsoro babu a furkar hiyana cikin dakiyar zuciya tace "dan Allah ina son inyi sallar azahar kafin ku kai ni in da zaku kai ni" cikin fushi ogan nasu ya juyo zai zabga mata mari Khalid yayi saurin shiga tsakanin su yana faɗin "dan Allah oga kayi hakuri bata da lfy ne amma In Sha Allah ba zata sake magana ba" tsaki ogan nasu yaja cikin tsawa yace "ku sani nan ba gidan wasa kuka zo ba duk wan da ya sake kawomin shirme sai na fasa kan sa da bindiga yasin"
hararar sa hiyana tayi ta kasan ido a cikin zuciyar ta tama faɗin "karamin mara kunya ne kai tun da ba zaka iya tinkarar yaya Prince da kan shi ba sai ka sato wayan da yake kauna dan ku cutar da shi ai cikakken namiji gaba da gaba yake tinkarar yaki ba ta baya ba" tayi nisa cikin tunani taji wani kato yana kokarin cire mata hijabin jikin ta da niyar su chajesu a zuciye ta rufe ido ta zabga masa wani wawan mari cikin fushi tace "duk wan da ya sake yun kurin taɓa jikina a gidan nan wlh sai dai mu mutu tare mutuncina yafimin rayuwata jikina dan mijina kawai akayi shi ni jinin fulanin daji ne tsoro baya cikin jinin mu ni kuma kanwace ga babban soja da babu irin sa jarumin namiji ɗaya tamkar da million wadda shi kaɗai yake tarwatsa rungunar yan ta'adda komai girman ta ina son kusani tafasasshen jinin dake gudu a jikin bgs shine nima a jikina karkarinta dai kuce zaku kashe ni to idan kun kasheni ku kuma ku tabbata a duniya karku mutu" waro ido Khalid yayi yana kallon ta dama sister tana magana haka lallai mace mai mutun macece ban taɓa jin sister tana magana haka ba amma yau da zaa taɓa mutuncin ta dubi yadda take magana ko tsoro babu wato da a taɓa mutuncin ta gwara ta mutu In Sha Allah babu abun da zai sameki sister da izinin Allah tun da kekaye yun kurin kare mutuncin ki Allah ba zai taɓa bari aci mutuncin naki ba
Khalid yayi nisa cikin tunani bai ankara ba sai gani yayi wannan mutumin da hiyana ta mara ya ɗauke ta da wani gigitatchiyar mari tare da kwashe kafafunta ta zube kasa ta buga kanta a kasa,gadan gadan mutumin yayi kanta da niyar dukan ta da sauri Khalid ya sha gaban sa yana kokarin bashi hakuri da karfi mutumin ya ɗaga gindin bindiga ya bugawa Khalid a kai kan kace me jini ya fara zuba kamar famfo zubewa kasa Khalid yayi baya ko motsi cikin tsawa mutumin yace "mutunci ko to yau zakiga mutunci kai ku samin ita a ɗaki yau sai kin gane shayi ruwane!!"
To masu karatu nima na tafi inje inyi nawa sharholiyar domin wanna lamari yafi karfina sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu more love lodi lodi 🥰
[7/23, 1:44 PM] Maman Aslam: 💖The talent troupe writer's 💖
💋Duk Karfin Izzata 💋
By Star Lady
Page 36
....suna kokarin kamata ogan su ya daka masu tsawa "kai kuma da hankali kuwa!!? Kunsan me kuke shirin aikatawa kuwa!? kuwuce ku bani waje hai" wadda hiyana ta marane yace "haba oga baka ganin yarinyar nan marina tayi ne? ɗaure fuska ogan nasu yayi kafin yace "bana son shirme adam idan ka taɓa yarinyar nan kana tunanin oga zai barmu da rai ne?ae, ko me ta maka hakuri zakayi sai oga ya bada umarnin hukuncin da zaa mata sanna kai ma ka ɗauki naka fansan yanzu gashi ka sumar da wanna bayan oga yace mu bashi horo mai kyau amma karmu kashe shi to yanzu dai ba halin mu horar da shi sai dai ma mu bashi kulawa ta yadda zamu tsayar da jinin nan idan ba haka ba zai iya mutuwa dan jinin sosai ne ke zuba daga jikin sa ku ɗauke sa ku kai sa treatment room Auwal ya duba shi a samu a tsai da jinin nan kafin mu fara bashi horo ita kuma yarinyar ku kai ta ɗakin kunama ku ajiye ta" yana kai karshen maganar ya wuce ya bar wajen.
guntun tsaki hiyana taja a ranta tana faɗin "ba ɗakin kuna ma ba ko ɗakin aljanu zaku kai ni ta Allah ba taku ba ato duk wan da ya rike Allah shi kaɗai baya taɓa taɓewa a duniya na rigaku nace Allah wlh ba wanda ya isa yamin abun da Allah bai min ba ba kuma wanda ya isa ya hana abun da Allah ya min makarya tan banza matsoratan wofi" tayi nisa cikin zancen zucin ta sai ganin wasu jibga jibgan maza tayi suna kokarin ɗaga ta rintse ido tayi ta daka musu tsawa "karki kuskura ku taɓani!! juyowa ogan nasu dake tafiya yayi yana kallon su yana mamakin dakiya irin na hiyana gashi basu isa su mata wani abu ba tare da ogan su ya basu izinin yin hakan ba
dawo yayi wajen cikin umarni ya fara magana "adam ku kira matan nan masu mana girki su chaje yarinyar tun da bata son maza su taɓa ta shi ma na mijin kuyi saurin charje shi" sai lokacin hiyana ta tuna da nauran da yaya Prince ya bata wadda ta barosa saman mirror ɗakin sa ji tayi kamar zatayi kuka yanzu ta ina yaya Prince zai nemo su amma ba komai Allah nanan domin Allah ba azzalumin bawan sa bane sai dai bawa ya zalunci kan sa.
Haka ko akayi wasu mata ne sukazo suka charje hiyana tsab daga sama har kasa basu samu komai a jikin ta ba
Haka suka ja ta zuwa ɗakin kunama suka kulleta
Shima Khalid charje sa sukayi tsab sunyi nasanar jiro na'urori guda biyu a jikin sa cikin sauri ɗaya daga cikin su ya shiga cikin mota ya fice da nauran daga gidan
Adam da kan sa ya ɗauki Khalid zuwa ɗakin da suke duba kansu idan basu da lfy
Hiyana kuwa suna shigar da ita ɗakin wasu jigba jihab kunamu ta fara cin karo da su ko ajikin ta juyawa tayi a ɗakin ta nemi Wajen kasa mai ɗan tsarki taje tayi taimama,duk da bata san inane gabas awajen ba haka ta tada sallah tana sallah tana jin kunamun suna hawa kafar ta amma bata damu ba bama tayi ko da motsi ba dan tasan ba abun da zasu iya mata ai ba aban za suke zaune a dajin su ba su da suke rayuwa da kaciji da kunama kullun.
Bayan ta idar da sallah ne ta zauna tafara jero wa Allah kirari da addu'a akan Allah ya kare su ya kare mata mijin ta daga sharrin duk wani abun halitta
Tana cikin addu'a ne wata kunama ta hauro saman kumatun ta tana jin sa sai yawo yake mata a kumatun ta
Sai bayan da ta kammala addu'ar ne ta sanya hannu ta kusa da kunamar tace "bawan Allah kayiwa Allah ka sauka jiki na idan ma wani laifi na maka kayi hakuri" bin hannun ta kunamar yayi ya gangaro har wajen tafin hannun ta a hankali ta sauko da hannun nata kasa kunamar ya sauka,ba karamin mamaki ta shaba ita dai a iya sanin ta tasan kunama na harbi to ya akayi bai har beta ba? Tunawa da maganar bappa tayi lokacin da yake faɗa musu ba kowani dabba bane yake cizo da gangan wani yana cizone dan ya kare kan sa wani kuma yana ciwo ne idan akan matsa masa amma ko wani irin dabbane idan dai ba sheɗani ba annabi yace idan ka haɗashi da Allah ka masa magana ba zai cutar da kai ba sai dai in sheɗanin aljani, lokacin guda taji tsoron Allah ya kara ninkuwa a ranta lallai duk wanda baya jin tsoron Allah ya taɓe ya shiga uku ya lalace ko kwayar idon ɗan Adam ka gani ya isa ya saka ka kara sanin girman Allah ya Allah duk halin da zamu shiga Allah ka tausaya mana ka barmu da imanin mu.
Sai tunani take ta tunano wanna ta tunano wacan har barci wahala ya fara ɗaukan ta gyara wa tayi ta kwanta a wajen ba jimawa barci yayi awon gaba da ita
A ɓangaren Zahra kuwa
gaba ɗaya ta gaji da ɗaurin da jabir ya sa akamata da kyar da kyar take numfashi ga yinwa da kishin ruwa sun addabe ta gashi rana ya iso wajen da take sai zufa take haɗawa
Da dai taga su jabir basu da niyar kulata ko zata mutu su suna zaune a inuwa suna buga whot idan sun gaji su koma lido da alama ma sun manta da ita awajen
Rai a ɓace ta ɗaga murya tace "jabir kazo ka bani ruwa na sha kishi nake ji" ba musu ya mike ya tare da ɗaukan roban ruwan dake kusa da shi yazo gaban ta kamar abun kirki ya buɗe bakin robar ruwan kamar zai bata a baki sai kuma ya watsa mata a face nata tare da shekewa da dariyar mugun ta girgiza fiskar ta tayi tana mai nadamar tambayar sa ruwan da tayi hannu ya ɗaura saman wuyar ta ya gangaro da shi a hankali,yana faɗin "ashe kema Zahra ba baya ba wajen kyau shine na kafe sai hiyana ai da tun ɗazun ni da yarana mun ɗan huta da ke ka ɗan ai" yana magana yana gangaro da hannun sa saman kirjin ta.
Kamar daga sama yaji tas an harɓi hannun nasa da gun,ihun azaba ya saki ita kuwa Zahra ihun murna ta saki dan ko ba a faɗa mata ba tasan yaya Prince ne ya iso, a guje yaran dadyn jabir suka miƙe suna kokarin ɗaukan gun nasu
Kafin su kai ga ɗaukan gun ɗin bgs ya harɓi mutun uku daga ciki cikin zafin