Showing 114001 words to 117000 words out of 363274 words

Chapter 39 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2582

tun da har Aryan bai ji kunyar idon ki ba yazo yace baya son ganin yar ɗan uwanki to wlh sai nayi maganin sa, "tayaya zakayi maganain sa to? Ai naga shi yace bai son ganin ta to kaga idan ta tafi ai sai yafi kowa murna da hakan "Aisha ke nan yanzu kina nufin bakisan chewa Aryan na Son diyana ba, to idan ma baki sani ba yau kin sani, kuma So bana wasa yake mata ba "amma yana Son ta kuma yace baya son ganin ta a gidan nan?

"Kedai ba ruwanki kuyi abun da nache muku wlh duk wadda tasake ta faɗi inda diyana take to sai na ɓata muku, kutashi kuje, my daughter yanzun nan ku tafi kuma karki bari kowa yaga kin fita da diyana, "to kawai Aunty farida tace sannan ta miƙe tanan murna sosai dan ambata diyana atare suka fito fada da Ammi

Yola

Ihu take tana faɗin nashiga uku na ku kawo min agaji zan mutu, da gudu yaya bello ya fito daga chikin gonar sa ya nufi gonar bappan su dan daga nan yake jiyo ihun,

"Subhanallah innar buba lfy? Chikin ihu da kuka innar bubu tace "Bello mutuwa zanyi na shiga uku kumurchin machijine ya sareni a kafa, chikin sauri bello ya kai kallonsa kan kafar nata, gaba ɗaya kafar ta kunbura sundum, girgiza kai Bello yayi yana faɗin "shike nan dafin yagama shiga jikin ki wlh ko kinsha magani yanzu ba lallai ki chigaba da takawa da kafar ki ba, dan dafin ta riga ta illata namar kafar taki

"Bello ka taimake ni mutuwa zanyi wayyo Allah, da gudu yaya bello ya juya ya koma chikin gonarsa ya tsinko wasu ganye ya nufi rafi ya wanke su tas, san nan ya ɗauko wani ɗan kwarya, ya dawo wajen innar buba, murje ganyen bello ya shigayi chikin kwaryar sai da ta fitar da ruwa san san nan ya bawa innar buba, ruwan akan tasha ganyen kuma ya manna mata awajen chizon machijin.

Tana shan maganin ta fara amai, amai sosai ta amayar da dafin machijin, amma kafar ta kuma har yanzu a kunbure yake gashi yayi wani green dashi, ɗaukan kwaryar yaya Bello yayi ya koma rafin ya ɗebo mata ruwa ya dawo ya bata tasha, san nan ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗar sa ya nufi hanyar gida

Da sallama ya shiga gidan hasana na tuƙa tuwo ganin yaya Bello ɗauke da innar buba a kafaɗar sane yasa hasana miƙewa da sauri ta ɗauko ta barma mai kyau daga ɗakin ta ta shin fiɗa a tsakar gidan.

A hankali yaya Bello ya kwantar da innar buba a kan ta burman, san nan ya dubi hasana yace "kiyi sauri ki kammala abinchin ki zuba mata, to kawai hasa tace Sannan ta miƙe ta koma wajen girkin nata, innar buba kuwa sai hawaye take saboda azabar da kafarta ke mata,


Masu karatu na muku wan nan ɗan takaitaccen page ɗin ne saboda nasan kuna chikin zullumin ya diyana da Bgs zasu kare, shayasa na muku amma gobe ba update sai Monday shiyasa ma ban tsaya awajen da zaku shiga tunani ba 😸😻


💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)





More comments an like pls

*💫STAR LADY💫*

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣1️⃣*

Aunty Amarya che zaune a bakin gadon ta tana waya da hajj sadiya

"To yanzu hajj sadiya ya ki kayi dashi ne nifa wlh na matsu, banson ganin yaran nan a gidan nan, daga ɗayan bangaren hajj sadiya tace "haba hajj hajara sai kace yau muka fara aiki da gagarabadau, ki kwantar da hankalin mana yanzu zan miki bayani ai tun da ki kaga na kiraki kam kema kinsan akoi bayani "to hajj sadiya ki faɗamin da wuri mana dan na matsune naji ai

"Jiya naje wajen sa, yana faɗamin chewa Aiki na tafiya yadda ya kamata, dan yache ma akoi wani shu umin malamin da basu san daga ina yake ba yana taimaka musu sosai, shima yana bibiyar rayuwar yaran ne, ahalin da akechiki yanzu yama kusa kunche tsarin dake jikin yaran saura kaɗan, amma fa yace ita babban wlh ba wanda ya isa ya mata wani abu asiri ba zai kamata ba, aljanu ma bazasu iya shiga jikin taba, dan tana karatun qur'ani tana askar, bata wasa da sallah kuma tana sallan dare gashi bata shiga harkan kowa, yaso shiga jikin ta last month da tana period ma amma sai dai kas bai yi nasara ba, domin duk da tana period, tana askar, kuma tana zama da alwala,ba ta yadda zaiyi ya shiga jikinta, su kuma sauran nan da two weeks, malin Chan in ya gama kunche tsarin jikin nasu, yana gama kunchewa shikuma gagarabadau zai ɗaura nashi aikin a kansu
Dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace "to shikenan Allah ya kaimu "amin Hajj Hajara karki damu ke dai ki kara hakuri saura kaɗan yauwa baki bani lbr sabon sarkin ku ba ya ake chiki? " Hmmm ke dai hajj sadiya bari wani sarki wlh ranan da ya fara hawa kujerar mulkin nan tun ranar ya fara rashin lfy baya magana baya motsi, sai dai numfashin sa kawai da zakiji shine zai tabbatar miki da bai mutuba abun gwanin ban tausayi,
Wani shewa hajj sadiya tayi ta chikin wayar kafin tace "ai albishir ya kamata kimin hajj Hajara kiche aikin gagarabadau yayi kyau,
zubur Aunty amarya ta mike muryar ta har rawa yake wajen faɗin "hajj sadiya kenan ke kikayi wa Ahmad wan nan abun? ke nan daman ba chiwon Allah da annabi bane ya kamashi? tsaki Hajj sadiya taja kafin tace.

Kamar ya ni na masa, ke dai kika masa ba niba, dafe kirji Aunty amarya tayi ta zaro ido tana faɗin "ni kuma hajj sadiya a yaushe na masa hakan, "Hajj Hajara wai lfy ki?, watoma kin manta aikin da kika sani naje na sa gagarabadau ya miki akan, idan ba mijin ki ko ƴaƴan ki ba, ba wanda zai karɓi mulkin nan duk kuma wan da yayi kuskuren hawa mulkin tofa mutuwa zakiyi

Girgiza kai Aunty amarya ta shigayi tana faɗin "aa hajj sadiya ni dai gaskiya banche a kashe kowa ba ni dai to a kunche aikin nan dan wlh bakiga yadda Ahmad ya koma bane Allah ko ke kika ganshi sai kin masa kwalla,ni su Ahmad basumin komai ba,su diyana ne bana so, su nakesan a haukata min, amma ban da su Ahmad
Wani dogon tsaki Hajj sadiya ta kuma ja kafin tace "amma hajj Hajara bansan baki da wayau ba sai yau wlh ki na tunanin idan da uwar su che ta samu damar da ki ka samu a kan ƴaƴan ki, zata raga musu ne? wlh bazata ragawa kowa ba, ke kowa da kika gani aduniyar nan kanshi kawai ya sani wlh sai dai in bai samu dama bane sai ya rinƙa nuna chewa shi na Allah ne, da zarar ya samu dama to a nan zaki gane asalin mugun halinsa, ki tsaya ke dai kiche kinajin tausayin su kina ji kina gani, Aisha zata mamaye komai na gidan in bakiyi Sa'a bama wlh sarki na mutuwa yar wanke wanke Aisha zaki zama, dan haka zaɓi yarage gareki.

Dogon numfashi Aunty amarya taja tare da sauƙe ajiyar zuchiya kafin tafara magana "eh hajj sadiya kina da gaskiya wlh,dan yanzu ma mai martaba yafi jin maganar Aisha fiye da na kowa a duniyar nan, da Zarar Aisha tace ga abun da takeso wlh zakiga jikin sa har rawa yake wajen biya mata bukatun ta, kin dai san halinsa idan yayi magana baya chanzawa to wlh Aisha tana sa shi ya sauya magana.

"Yauwa hajj Hajara kin gane abun da nakeson ki gane kenan yanzu dai bari mugana dasu diyana sai mu koma kan farida muna gamawa da ita sai muyi maganin Aisha itama, wani murmushi Aunty amarya tasaki kafin tafara magana "yauwa kawata shiyasa nake son ki ai, amma yanzu ya zamuyi da maganar zulaihat? tunda kinga ita ya kamata Safras ya aura
"Eh karki damu yanzu zulaihat ɗin ma bata nan wlh wai tabi saurayin ta party a Dubai, zasu dawo nan da tsakiyar wata mai shiga, inaga abun da za'ayi, idan ta dawo kasar sai ta dawo wajenki da zama har musamu shi Safras ɗin ya fara Son ta ni kuma zanyi nawa kokarin wajen malamai na dan naga an chusa masa Son ta sosai

"Haba hajj sadiya ya za'ayi ki barta tabi saurayi, yanzu tana zuwa yawon nan ne kuma kike tunanin Safras zai sota to wlh tun wuri ki hanata in ba haka ba tofa duk in da zaki shiga Safras dai ba zai sota tana yawon banza ba "Karki damu hajj Hajara idan ta dawo ai shike nan zata dawo wajen kine da zama, gashi kinga gidan ku ba'a fita sai masu zuwa school, suma kai su ake, a dawo dasu, kinga ba halinta fita taje yawon ko ?

"Eh hakane kam to shike nan sai munyi waya zan turomiki 500k ki karawa malamai ɗin naki amin aiki masu kyau da zafi, "to kawai hajj sadiya tace daga haka sukayi sallama, Aunty amarya ta ajiye wayar sama drawer gefen gadonta ta karisa hayewa gadon gaba ɗaya ta kwanta, ta lunshe ido


Aryan

Zaune yake a bakin katafaren gadon sa sanye da kayan barchi riga da dogon wando masu laushi farare tas,yan shara shara marasa nauyi, ya dukar da kan sa kasa, gaba ɗaya gashin kan nan nashi a hargitse ya kwanto masa har kan fuska, ya zuba uban ta gumi, sai wani irn huchi yake kamar wadda aka batawa rai wayar sa dake kan gadon ya ɗauko ya kunna hasken screen ɗin, ya duba time 10:30pm chire password na wayar yayi ya shiga chikin contact nashi, yayi dealling num ɗin Zahra, wayar tana ta ringing har ta kusa katsewa san nan Zahra ta ɗaga.
Chikin muryan barchi tace "hello yaya Aryan, ina wuni
Bai amsa mata gaisuwar sai yace "ki chewa yarinyar nan ta kawomin coffee
"Yaya Aryan ai bata nan, "what? Bata nan ina kuma taje a daren nan? yayi maganar chikin tsawa
"Ammi ta mai da ta kauye, zubur ya miƙe yana faɗin "what? kauye kuma to da izinin wa za'a fita da ita gidan nan, nache a kai min ita wani waje ne?
Ita dai Zahra tsoro ne ya kamata jin yadda yaya Aryan ke magana chikin tsawa, muryar ta har rawa yake tace, "kayi hakuri yaya Aryan,

a fusache ya nufi kofar fita batare da ya sake che da zahra komai ba, kuma bai katse kiran ba,dan yama manta waya yake, idon sa ya rufe,
har ya kai bakin ƙofa zai fita sai kuma ya dakata ya ɗago wayar sa dake hannunsa, ya katse kiran Zahra san nan ya duba time 10:38 " dare yayi bai kamata naje part na Ammi yanzu ba,
Chike da ɓachin rai ya juya ya koma kan katafaren gadon sa ya kwmata ya lumshe ido kamar mai barchi, Almost 5mnt

Sai kuma ya miƙe zubur ya zauna chikin tsawa yace "kauye kuma aa ina hakan ba zai yuwuba wlh, wai shin nama bada izinin ta fita gidan nan ne? wlh duk ma wanda ya fita da ita daga gidan nan sai na hukun tashi, akan wani dalili?

Zuro kafarsa kasa yayi kafin ya miƙe gaba ɗaya yanufi hanya fita yana faɗin "wlh Ammi dole na tasheki a daren nan, dan in ji ina kika kai yarinyar nan ba zan iya hakuri gari ya waye ba,
Taku yake irin na jaraman maza ji kake dif dif dif idan yana taka kasa, sauri yake sosai kamar zai tashi sama,

Da sallama ya shigo babban palon Ammi na kasa, chikin sauri ya haye sama, kai tsaye betroom na Ammi ya nufa, a bakin kofa ya tsaya tare da ɗan buga kofar yana faɗin Assalamu alaikum.

Ammi dake kwanche kan katafaren gadon jin muryan Aryan yasa ta miƙe zaune da mamaki a face nata, ta amsa masa sallamar

San nan ta sauko daga gadon ta nufi drawer kayan ta ta ɗauko hijabi ta sanya a jikinta, ta dawo bakin gadon ta ta zauna tana faɗin "shigo mana Aryan.

A hankali ya turo kofar ya shigo, tsayuwa yayi a bakin kofar ya ɗan jingina da jikin kofar, yana kallon Ammi dan ya kasa ko magana saboda azaban raɗaɗin da zuchiyar sa ke masa

"Aryan lfy baka yi barchi ba? Da kyar ya iya buɗe baki ya fara magana "Ammi pls tell me ina kika kai yarinyar nan
Ɗaure fuska sosai Ammi tayi kafin tace "kauyen su mana na mai data
"Kauye kuma Ammi to akan me? Akan wani dalili? Kuma taya zaki mai data kauye ba tare da izinina ba, tirkashi Ammi dai baki ta sake tana ganin ikon Allah, ganin Ammi tayi shiru bata bashi Amsa ba yasa yace "wai ma tayaya zaki ɗauke ta bada izinina ba? Kuma wani driver nema ya fita da ita daga gidan nan wlh yau sai ya karɓi hukunchi, in a serious matter yayi maganar,
"Kaga Aryan wlh ka fita min a ɗaki bansan iya shege fa, kai da kanka kazo nan da safe kache baka son ganin yarinyar nan a gidan nan yanzu kuma na mai data gidan baban ta san nan kache, ya za'ayi a mai data ba da izinin ka ba to sannu,nache sannu,

Waro ash eyes nashi yayi waje sosai kafin yace " Ammi yaushe nache bana son ganin ta kuma, ni fa aa inaga dai mantuwa ki kayi Ammi,

cheke da jin haushi Ammi tace
"Karya dai zakache na maka ba mantuwa ba, girgiza kai ya shigayi yana faɗin "nashiga uku karya kuma Ammi aa wlh ban haka Ni nake nufiba kawai abunne yake bani mamaki da ki kache, Ni nache bana son ganinta.

"To idan ka gama mamakin naka sai katafi ɗaki ka kwanta ai dan dare yayi,

shiru yayi kamar mai tunani almost 10 mnt yana tsaye ya kasa koda motsi,
sosai ya bawa Ammi tausayi dan bata taɓa ganin Aryan a irin wan nan yanayi ba sausauta murya tayi tace "Aryan kaje ka kwanta kaji dare yayi, ɗan firgigit yayi alamar tunani yaƙe, ɗago ash eyes nashi yayi ya sauƙe su kan Ammi, bakaramin tsorata Ammi tayiba ganin yadda idon sa suka sauya sukayi jaaa sosai, ya kasa magana ma a hankali ya juya ya fice daga ɗakin

Dafe kai Ammi tayi tana faɗin "wai duk wannan abun na menene mai yasa mai martaba zai wa yaran nan haka ni ai tunani na burin shi kenan yaga sun fara son mace har ya samu ya musu aure to Amma me yasa yanzu kuma zai wa Aryan haka, ni gaskiya bazan iya ganin Aryan a chikin irin wan nan halinba dole musan abunyi, yau kawai da bai ganta ba jibi yadda ya dawo, hmm

jiki ba kwari ta chire hijabin jikin ta ta mai da drawer san nan ta dawo ta kashe wutar ɗakin ta haye gadonta ta takwanta

Aryan kuwa saboda bakin chiki da ɓachin rai dakyar ya iya kai kanshi ɗaki, dan gaba ɗaya idon sa sun rufe baya gani, addu'a kawai yake Allah ya gaimu gobe, yayi wa garin Yola diran asuba yana shiga ɗaki ya haye katafaren gadon sa ya kwanta, sai juyi yake ya kasa barchi
sai ya lumshe ido kamar mai barchi idan ya tuna diyana na kauye kuma wata kilama yanzu tana tare da wanchan wawan Bello sai ya sake ware manya manyan ashe eyes nashi, da suka sauya yanzu suka koma jaaa sosai saboda tsananin kishi da ɓachin rai,

Da kyar ya iya laluɓo wayar sa ya kunna hasken screen ɗin, ya shiga Kga App yayi playing na hoto nan diyana ya fara binsu ɗaya bayan ɗaya yana kallo, nan take murnushin ta bayyana a kan kyakkyawar fuskar sa, abu ɗaya kawai yake tunawa kuma yake jin sautin a kunnensa wan nan zazzakar muryar tata idan tana faɗin Yaya Aryan, wow gaskiya yau nayi missed sexy voice naki sis, sosai yake ta kallon hotunan yana murnushin har ya kai kan video da ya musu shekaran jiya da zai saka mata sarƙa,

playing na video yayi ya fara kallo yana murnushin, zuba mata ido yayi sosai yana kallon yadda ta zura hannu a riga tana kokarin chiro sarkan, bai ankaraba kawai sai yaka boobs nasa a waje daman shekaran jiya ya kawar da kansa bai san taya ta fitar da sarkan ba, ashe wayar sa ta ɗau komai, a sukwane ya chire video ya fita daga App ɗin san nan ya kashe wayar ma gaba ɗaya, ya ajiyeta a saman drawer gefen gadon, shiru yayi kamar mai tunani har barchi ɓarawo ta ɗauke sa batare da ya saniba.

Maiduguri

Aunty farida che kwamche kan katafaren gadonta ta tada kai da chikin yar dadyn junior, suna yar hirarsu yana shafa kyakkyawa kuma lallausan bakin gashin kanta
My farida magana mai muhimmanci nake son muyi dake fa amma kinzauna kinata zubamin shagoɓa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login