Showing 348001 words to 351000 words out of 363274 words
dan yana bala'i son yara kam sosai amma yau har da sa hannu zai ansa jariri lallai Allah mai iko. Ita kuwa Dr ganin bgs ba zai iya rike babyn bane yasa ta riƙe baby da kyau cikin harshen turanci tace "Kana baban baby kuma baka iya ɗaukan baby ba amma kuma ka iya bawa maman baby cikin babyn ai ko?" Toshe baki Aryan yayi saboda dariya da ta kubce masa, shi kuwa Khalid taya Dr murna yake a ransa yana faɗin "Lallai dr kin yi Sa'a idan da abaya ne ai ko kallon bgs ba zaki yi ba bare kice masa ya iya bawa mace ciki tab ai da a baya ne kika masa wan nan magana da yanzu kina gadon asibiti ko ana shirye shiryen jana'izar ki eyee lallai dr kin tsallake rijiya da baya" shi kuwa bgs dogon tsaki yaja tare da wucewa ya bar wajen ya nufi motar sa ya shiga, da sauri Aryan ya kariso wajen ya ansa baby duk da shima ba wani iya rikewa yayi ba sai da Dr ta gyara masa yana kokarin yin magana sai ga Shahram ya kariso wajen hannun sa riƙe da rafan bundir ɗin dala wadda akalla zai kai daya 50k ko sama da haka ya miƙa wa Aryan yana faɗin "Sir gashi in ji Oga bgs wai a bawa dr" murmushi Aryan ya yi har ransa yaji daɗi yadda bgs baya nuna musu bambanci duk da cewa yafi kaunar sa amma yana kokarin ya nunawa su Yusuf suma haka yake kaunar su da ya shiga damu ganin bgs baiwa dr kyauta ba dan yasan idan Diyana ce ta haihu sai yayi wa gaba ɗaya hospital nan kyau ta sai kuma gashi shima Yusuf da matar sa ta Haihu an ma dr kyau ta sosai Aryan yaji daɗi kuma ya kara jinjinawa adalcin da bgs ke kokarin gudanarwa a tsakanin su. "Dr zan iya shiga inga matata" cewar Yusuf girgiza kai dr tayi kafin tace "A'a ka ɗan jira tukun nan" zama saman kujera Aryan yayi rike da baby a hannun sa sai faman gyara masa rikon dr take da sauri Khalid ya matso ya ansa baby shi ya fisu iya riƙe babyn miƙewa Aryan ya yi ya miƙa wa dr kuɗin da bgs ya bata nan take ta fara washe baki tana zuba godiya key ɗin motar sa ya ciro daga aljihun sa ya miƙa wa Fahad dake tsaye yayi tagumi kamar mai tunani sai miƙa masa key Aryan yake amma hankalin Fahad baya wajen "Fahad me kake tunani?" Aryan ya tambaya yana kallon face nashi yar firgigit Fahad ya yi kafin yace "Yaya Aryan ba dole nayi tunani ba a na cewa Haihuwa na da hawala ashe faɗe a baki ma ba'a faɗan komai sai an ga wahalar a ido yanzu haka amri ma zata sha wan nan wahala? kai gaskiya mu daga baby ɗaya bazamu karaba wahalar nan tayi yawa kai" kallon Khalid Aryan ya yi abun ma dariya yaso basu wato daga baby ɗaya bazasu karaba to sanda zasu karama waya sani matsowa Yusuf ya yi kusa da shi tare da dafa kafaɗar sa yana faɗin "No Fahad ko wace mace da kalar yadda Haihuwa ke zuwa mata yanzu dai addu'a zaka mata Allah ya raba lafiya" miƙa masa key ɗin motar Aryan ya yi yana faɗin "Ka mata addu'a muma muna taya ku yanzu dai ɗauko min kuɗi a cikin mota bari na bawa dr gift" da kyar Fahad ya iya ansan key ɗin gaba ɗaya jikin sa a mace ya tsorata da ganin yadda Lamrat ta sha wahala kafin a shiga da ita labour room wan nan ma bai ga wahalar dake cikin labour room ɗin ba da kyar ya iya cewa "Nawa zan ɗauko maka yaya Aryan?" "Ko nawa ma ka ɗauko ka bawa dr" juyawa yayi ba tare da ya sake magana ba yana kokarin barin wajen Khalid yace "Ga nawa key ɗin nima ka ɗauko mata kuɗi a motar" dawowa ya yi ya ansa key ɗin Khalid san nan ya wuce yana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Bayan ta fiyar sa Khalid ya dubi Aryan yace "Kai Fahad fa da gaske ya tsorata da lamarin Haihuwa" girgiza kai Aryan yayi kafin yace "Ai ba Fahad kawai ba ni kai na na kara jinjinawa mata kullun a baki muke jin sunan Haihuwa to yanzu munga kaɗan daga ciki ba a banza Allah ya kira uwa sau uku kafin ya kira uba sau ɗaya ba yanzu ba yan dukka wan nan wahala ta nakuda Allah yasa ta Haihu lafiya kuma tazo ta kara ɗauka wa ta hawalar shayarwa reno tarbiya kuma duk abun da yaran nan zasu yi mara kyau ita za'a ɗaurawa laifi idan mai kyau ne kuma sai a ce mahaifin su dan rashin a dalci irin na ɗan adam Allah dai ya sakawa duk wata mace da ta Haihu ta gina kanta a kan koyar wan manzon musamman (SAW) alkhari da gidan aljannatul firdaus" jinjina kai Khalid ya yi yana faɗin "Gaskiya dai kam mata suna kokarin fatan mu muma muyi kokarin wajen yi musu adalci" Yusuf na kokarin yin magana Fahad ya dawo hannun sa rike da rafan dala kusan irin wadda bgs ya bawa dr sai dai wan nan bai kai na bgs yawa ba rafa uku ne a hannun sa, nashi rafa ɗaya na Aryan ɗaya na Khalid ɗaya haka ya miƙa wa dr ta ansa sai murna take tana washe baki kamar zata sume dan dadi dai dai lokacin Hiyana ta fito daga ɗakin da aka kwantar da Lamrat tana faɗin "Yaya Yusuf Lamrat na kiran ka" tun Hiyana bata gama rufe baki ba ya mike da sauri ya shiga ɗakin dawowa kusa da Aryan Hiyana tayi ta zauna tana lekan baby tana son ɗauka bata iya ba mamaki Aryan yake har yanzu ita dai Hiyana shiru ba ciki ba labari.
Suna zaune shiru wayar Aryan ya fara kara yana dubawa yaga Abba ne cikin sauri ya ɗaya tare da manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Hello Abba" daga ɗayan ɓangaren Abba yace "Aryan jirgin mu ya sauka yanzu kuna gida ne ko dai kuna asibitin" "Abba karka damu na faɗa wa sojojin in da zasu kawo ku ai" "To ya jikin Lamrat ɗin ta sauka ne?" Da murmushi Aryan yace "Eh Abba ta sauka yanzun nan mun samu soja" "Alhadulillah Alhadulillah Allah mungodema sai mun kariso" "to" kawai Aryan yace sanna ya katse kiran da murna Hiyana tace "Yaya Aryan dasu Ammi Abba yazo" "Da su kowa a kazo dan munce a nan za'ayi suna har su kawun ku Abdussalam suma zasu zo jibi dukka family zasu zo dan bgs yace ba zamu koma Nigeria yanzu ba a nan za'ayi komai" tsabar fariciki Hiyana bata san lokacin da ta tashi ta buga tsalle tana tafiba Allah sarki Diyana Zahra cikin su yayi nauyi Zahra haihuwa yau ko gobe itama Diyana cikin nata yanzu ya shiga wata na 8 sun yi nauyi shiyasa Aryan yace a barsu a gida itama matar Hisham tana fama da tura nata cikin Haihuwa yau ko gobe.
After 1 hour manya manyan motocin masu numfashi ne su kayi wa asibitin dirar mikiya kan kace me jiniya ta kewaye ko ina manya manyan jibga jibgan sojojin ne suka diro daga saman nasu motocin suka bubbuɗewa su Abba motocin su Fahad na tsaye awajen parking space ɗin hospital ɗin shi yayi wa su Abba jagora zuwa in da su Aryan suke da gudu Hiyana ta mike ta faɗa jikin Ammi tana dariya tana faɗin"Oyoyo Ammi na" Ammi tasha ruwan mamakin ganin Hiyana wayam babu ciki ita duk a tunanin ta zata ga Hiyana da katon ciki ɗan wata 5 ko 6 amma sai taga shiru ba Ammi kaɗai ba har da Abba da Ummi duk sun yi tunanin Hiyana na da ciki dan Abba ba abun da yake buri da ya wuce yaga ɗan bgs a duniya. Ɓoye mamakin su, sukayi suka rungumi Hiyana suna farinciki amma Ammi ta shiga waswasi sosai tunani take "to ko dai har yanzu da matsala tsakanin yaran nan ne ko basu dai dai ta kan su bane basa samun kwana waje guda" da wanna tunani suka shiga ɗakin da Lamrat ke ciki an mata alluran barci dan ta huta tana ta sharar barci Yusuf na zaune kusa da ita ga baby na kwance gefen ta wucewa Ammi tayi ta ɗauki baby tana faɗin "Masha Allah yaro mai kama da Auntyn sa Diyana wallahi kaman su ɗaya sak har ɗan bakin" da sauri ta matso tana rike da ɗan inna wadda Abba ya sanya masa suna Ayaam tace "Ai kuwa dai ɗan nan ba in da ya baro Diyana a kamanni da rana ɗaya suka haihu da sai ince anyi canji" sai murmushi jama'ar ɗakin suke musamman yaya Ahmad da ya kusa angwancewa gasu yaya Omar su hajjo anzo Us sai kalle kalle ake gaba ɗaya family sun zo saura mutanen sudan da Aunty farida da Aunty farida da Aunty salma su kuma sai gobe zasu zo mutanen sudan kuma sai jibi. Kallon Aryan Abba yayi yana faɗin "Aryan tun da komai yayi dai dai ka ansa sallama mu wuce gida zai fi ko?" Gyaɗa kai Aryan yayi yana faɗin "Eh Abba hakan yafi ku shirya komai bari nayi magana da likitocin" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya fice daga ɗakin. Tun ba'a basu sallama ba Yusuf ya ɗauki Lamrat kamar yar baby tana barci suka fice daga ɗakin su Abba suka bi bayan sa kai tsaye wajen motocin su suka nufa. Ko da Aryan ya dawo ɗakin ba kowa girgiza kai kawai yayi yabi bayan su nan ya samesu har sun shige motocin su suna jiran shi Ammi na rungume da baby shiga nashi motar shima yayi a tare sukawa motocin key suka bar hospital ɗin da gudun gaske.
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
[8/20, 9:49 PM] SAFIYYA: 💋Duk Karfin izzata 💋6
By
Star Lady
Page 63
.... Suna isa gida Yusuf ya ɗauki Lamrat zai wuce da ita part nasu Ammi tace "Sannu Yusuf" kasa ya yi da kai yana ɗan satar kallon Aryan wucewa Aryan yayi ya nufi part nasa a ransa yana faɗin "Ai in dai su Ammi ne ma kaɗan ka gani yanzu zasu ma gargajiya ni dai kam ba wanda zai rabani da matata wlh idan kuma suka ɗauke ta to zasu ga tsiya a ɗakin zan rinƙa kwana" da wan nan tunanin ya wuce part na shi nan ya isko Diyana na sana'ar wato barci bata da aiki sai barci toilet ya wuce dan yin wanka. Shi kuwa Yusuf haka ba dan yaso ba ya wuce part ɗin Aiman da lamrat dake ta faman barci saboda alluran da ta sha a Part ɗin Aiman su Ammi suka sauka kasan cewar bedroom uku ne a sama uku a kasa sai su Ammi suka ɗauki saman bene Ammi ɗaki ɗaya Ummi ɗaya Abba ɗaya kasan kuma suka barwa innar yaya bello dasu yaya Bello tare da su Aisha shi kuma Sadiq ya wuce bq dake ta baya.
Ita kam Hiyana gaba ɗaya tarewa tayi a ɗakin Ammi ga sabon baby san nan ga Ammi da gudu Zahra ta shigo ɗakin tana tura katon cikin ta Haihuwa yau ko gobe hayewa saman gadon tayi suka zubawa baby ido sai barcin sa yake daga ita har Hiyana ba wanda ya iya ɗaukan baby sai dai su zuba masa ido yana kwance suna kallon sa amrat Diyana basu san meke faruwa ba dan barci suke wucewa Ammi tayi ta nufi toilet dan wanka.
Sai misalin karfe 9 na dare Bgs ya dawo gidan kai tsaye part nasu ya wuce yayi wanka ya shirya cikin jallabiya fara tas ya gyara gashin kan sa sai fitinan kamshin perfume ke tashi a jikin sa kai tsaye part ɗin Aiman ya nufa yana shiga Khalid ya shigo ya biyo Zahra dan duk sun tattaru awajen Ammi sun makale a gado suna kallon sabon baby lamrat ma ta tashi gasu Diyana duk sun haɗu sai hira suke anyiwa baby wanka an gyara shi an sanya masa kayan sanyi yayi kyau sosai sai barci yake zubawa abun sa dukkan su ba wanda ya iya ɗukan baby sai dai su zuba masa ido kawai suna kallon sa.
Da sallama bgs da Khalid suka shigo Ammi na tsaye gaban table tana haɗawa Lamrat tea mikewa su Hiyana su kayi zaune a saman gadon sai satar kallon bgs Hiyana take dan tana ganin call nashi har sau uku taki ɗauka ko kallon in da take bai yi ba ya wuce kusa da Ammi ya zauna saman sofa dake ɗakin yana faɗin "Sannun ku da zuwa Ammi ya hanya?" da fara'a Ammi tace "Yauwa mun same ku lafiya?" "Lafiya lou mun samu karuwa" "Eh kun zama iyaye" shiru yayi dan bai san me zai sake cewa ba dan wanna mun samu karuwa da yace ma Aryan ne ya faɗa masa abun da ake cewa idan an haifi yaro kallon sa Ammi tayi kafin ta kawar da kallonta, ta fara magana cikin harshen fullanci "Oh kai dai wato har yanzu baka canza ba ko fatar alkhari da akewa wadda ta haihuma baka iya ba" hannun Ammi ya riko cike da girmamawa yace "My Ammi yanzu ban yi kokari ba?" "Aa bawani kokari da kayi ya kamata ka iya yiwa mutun fatan alkhari da sauran abubuwa makamantan haka" kasa Ammi tayi da murya kafin tace "Yanzu idan ka tashi kace wa lamrat Allah ya raya zata ji daɗi" matse hannun Ammi yayi cikin nashi yana faɗin "To my Ammi zanyi yadda kike so" "To Allah ya maka albarka" "Amin" ya amsa tare da sakin hannun Ammin ya zuba mata ido har ta karisa haɗa tea ɗin ta ɗauka ta nufi gadon da su Hiyana ke kai sun nitsu tsit suna kallon baby ita kuma Hiyana sai satar kallon bgs take.
Ko kallon in da take bai yi ba ya mike ya fita ya nufi ɗakin Abba da sallama ɗauke a bakin sa, kwance ya isko Abba saman gado gefen gadon ya zauna yana faɗin "Sannun ku da zuwa Abba ya hanya" mikewa zaune Abba yayi yana faɗin "Hanya Alhadulillah mun same ku lafiya?" "Lafiya lou Abba" shiru suka ɗan yi kafin Abba yace "Safras kana da matsala da matar kane?" Da sauri bgs ya ɗago kai ya kalli Abba da mamaki yace "Matsala kuma Abba ita tace maka muna da matsala?" Girgiza kai Abba yayi yana faɗin "Aa ni kwata kwata ma ban yi magana da ita ba kawai a nawa ganin ne kamar kuna da matsala" "A'a Abba babu wata matsala a tsakanin mu" shiru Abba ya ɗan yi kafin yace "To ina son kuje asibiti a duba min ku akan batun Haihuwa" sai yanzu bgs ya gane me matsalar da Abba ke son faɗa, shi kan shi hakan na damun sa sai dai ya ɓoye nashi damuwar ne dan ganin Hiyana na damuwa sosai akan batun Haihuwar sai shi ya ɓoye nashi dan ya kwantar mata da hankali "In Sha Allah Abba zamuje ni kai na ina son muje ɗin" murmushi Abba yayi wadda tun da yazo sai yanzu yayi dan ya shiga damuwa duk tunanin sa bgs da Hiyana basa zaman lafiya ne to yanzu tun da yaji suna zaman lafiya sai yaji sanyi a ransa.
Da haka suka yi sallama da bgs ya fito ya shiga wajen Ummi ya gaida ta lokacin Ayaam na barci bai ma lura da shi ba ya fito ya koma ɗakin Ammi nan ya samu duk su Diyana mazan su sunzo sun ɗauke su saura Lamrat Ammi Hiyana sai baby da aka haifa satar kallon Ammi yayi ta kasan ido kafin yace "Eshat tashi mu tafi" make masa kafaɗa tayi tana faɗin "A'a yaya Prince ni zan kwana da sabon baby da Ammi" kallon Ammi yayi da kyau cikin sauri Ammi ta kawar da kallon ta daga gare su ita kuwa Lamrat tuni ta ci abinci ta sake mai da barci abun ta tana huta gajiya. "Ammi sai da safe" ya faɗa tare da juyawa ya fice.
Yana fita Ammi ta dubi Hiyana tace "Humaira tashi ki bi mijin ki" shagwaɓe murya Hiyana tayi tana faɗin "Dan Allah Ammi ki barni a nan tun da ya hakura ya tafi" "waya ce miki hakura yayi ai wan nan cemin sai da safe da yayi sako ya bani dan haka tashi ki tafi karki mai dank uwar banza" turo baki Hiyana tayi ta sauko daga gadon ta nufi hanyar fita. Har ta kai bakin kofar fita sai kuma ta juyo da gudu ta dawo tayiwa baby kiss a kumatu san nan ta fice daga ɗakin ta nufi part nasu har cikin ranta Ammi ke tausayin Hiyana dan yadda take son baby gashi ita kuma har yanzu shiru Allah bai bata ba.
Lokacin da ta shigo yana kwance saman gado ya lumshe ido kamar mai barci sallama ta masa a cikin zuciya ya amsa wucewa tayi ta nufi toilet tayi wanka ta fito ta wuce dressing room ta shira cikin wasu shegun kayan barci riga zuwa cinya da yar pant ɗin sa ta gyara lallausan bakin gashin kan ta sanna ta fashe jikin ta da perfume mai bala'i kamshin ta dawo ɗakin tare da hayewa saman gadon idon sa alumshe sai shakan kamshin perfume na ta yake amma yaki buɗe ido kasa kasa tace "Kayi hakuri yaya Prince" shiru ya mata kamar bai san da mutun awajen ba faɗawa saman kirjin sa tayi tare da sakin kuka mai ɗan sauti. Jin ba kukan shagwaɓan take ba kukan gaske ne yasa ya waro idon sa a saman kyakkyawar face nata "Subhanallah Eshat me yayi zafi kuma na