Showing 276001 words to 279000 words out of 363274 words

Chapter 93 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2558


Hannun sa na jubar da jini haka ya daure ya ɗauki hiyana da hannu ɗaya ya nufi waje da ita yana faɗin "Aryan ka duba ɗakunan gidan nan ka nemo Khalid" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya fice daga gidan gaba ɗaya.
da sauri Shahram ya biyo bayan sa ya buɗe masa kofar motar
Bayan ya kwantar da hiyana sai ya shiga gidan gaba mazaunin driver Shahram na kokarin cewa bari na tuka motar bai kai ga buɗe baki ba kamar wata walkiya haka ya ga bgs ya ja motar da gudun gaske sun bar wajen.

Motar bgs na fita motar rundunar jibga jibgan sojoji har mota biyar suka shigo wajen. Kusan a tare jibga jibgan sojojin nan suka diro kasa daga saman motocin su da gudu suka nufi cikin gidan dai dai lokacin Aryan ya fito ɗauke da Khalid a kafaɗar sa.

Cikin ɗaya daga cikin motocin sojajin Aryan ya kwantar da Khalid ya shiga gefe ya zauna Shahram ya shiga mazaunin driver ya zauna tare da tada motar suka bar wajen da gudun gaske.

Kai tsaye gida bgs ya nufa da hiyana,tun bai kariso bakin katafaren gate ɗin gida ba ya fara horn,a guje security suka buɗe gate ɗin dan daga jin wanna horn ɗin sun san ba na lfy ba,da gudun gaske ya danno hanchin motar sa cikin gidan kai tsaye parking space ya nufa. yana kashe motar ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu,da hannu ɗaya ya ɗauki hiyana ya wuce da ita ɗakin duba marasa lafiyan su, bai damu da jinin dake zuba daga hannun sa ba ya fara ƙoƙarin cire mata bullet ɗin jikin ta burin sa kawai yaga ta fita daga haɗari yana aiki yana cije laɓɓa saboda raɗaɗin azabar da hannun sa ke masa.
Yayi nisa cikin aikin har ya kusa kammala mata dressing ɗin wajen Aryan ya shigo ɗauke da Khalid a kafaɗar sa

Saman gado ya kwantar da Khalid ya nufi bgs da sauri yana faɗin "dan Allah my blood kayi hakuri ka kwanta abaka taimakon gaggawa dan ba karamin blood ke zuba daga jikin kaba zafa ka iya faɗuwa" ko kallon inda Aryan yake bai yi ba aikin sa kawai yake hannu Aryan ya sa yana kokarin ansan alluran da bgs ke haɗawa a zafafe ya juyo ya kalli Aryan cikin tsawa yace "kana da hankali kuwa Aryan!? So kake ta mutu kenan!?" "No bgs ba wai ina son ta mutu bane pls try to understand me kana bukatar agajin gaggawa zan duba ku dukkan ku biyu amma yanzu dai kazo ka kwanta mu tsayar da jinin dake zuban nan kar wani abu ya same ka ba zan iya jurewa ba" "Aryan kamar yadda ba zaka iya jure wani abu ya same ni ba nima haka ba zan iya jure wani abu ya same taba a halin yanzu rayuwar ta tafimin tawa rayuwar muhimmanci abeg kaje ka kula da Khalid" yana kai karshen maganar ya juya yaci gaba da aikin da yake

Bandeji mai karfi Aryan ya ɗauko ya zo ya ɗaure hannun bgs ta sama da ta kasa iya karfin sa ya sanya ya matse wajen da aka harbi bgs ɗin har sai da bullet ɗin ya fito ya faɗi ƙasa ko kula shi bgs bai yiba,ɗinki wanjen da aka harbi hiyana yake bai ma jin me Aryan keyi hankalin sa yayi nisa.
Muryan Abba ne ya dawo da su cikin hayyacin su "Aryan Safras meke faruwa ne? Waziri yace min kun shigo da Khalid kamar baya numfashi" ya Kai karshen magana tare da shigowa ɗaki,shiru bgs yayi kamar bai ji me Abba yace ba juyawa Aryan yayi ya koma wajen Khalid ya fara bashi taimakon gaggawa yana bawa Abba lbr duk abun da ya faru daga farko har karshe har kashe dadyn jabir da sukayi.
Abba ya nuna ainihin rashin jin daɗin sa cike da tashin hankali yace "Safras dan Allah ka bari a dubaka tun da ka cire wa hiyana bullet ɗin jikin ta,jini fa kake zubarwa" shiru bgs yayi kamar bai san da mutane a ɗakin ba aikin gaban sa kawai yake. Ba yadda basu yi da bgs ba akan ya bari a dubashi shiko ya kafe ya tsare akan hiyana yace ba zai tashi daga kan taba har sai ya tabbatar ta samu damar cigaba da rayuwa,hakuri sukayi suka zuba masa ido suna binsu da addu'a akan Allah ya basu lfy

2h bgs ya shafe kan hiyana yana mata dressing wajen bayan ya kammala ya tsaya ya zuba ma kyakkyawar face nata da yarame yayi fari tas ido.
dishi dishi ya fara ganin kafin Aryan yayi wani yunkuri ya yanke jiki ya faɗi saboda jinin da ya zubar bai kai ga karisawa kasa ba Aryan yayi saurin tarosa ya rungume sa da kyar ya iya kwantar da shi a kan gado ya kwaso kayan aiki ya fara duba shi.

"Abba ina Ahmad da Yusuf!? Cewar Aryan,zama kusa da bgs Abba yayi cikin tashin hankali yake magana "kwana biyun nan duk bana ganin Ahmad ɗin nan ko ina yake zuwa oho masa shi kuma Yusuf yana fama da matar sa bata da koshin lfy" "subhanallah me ke damun ta?" "Ammin ku ta sanar da ni karuwa muka samu" chak Aryan ya tsaya da alluran da yake kokarin yiwa bgs cikin sauri ya juyo tare da sakin cool murmushi yana faɗin "Alhadulillah Alhadulillah ya Allah muna godiya Allah mai kyauta mai kari ya Allah ya sauke ta lfy amma babyn jidda tace zata riƙe mana mu zamu reni babyn awajen mu zata zauna" murmushi Abba yayi yana matuƙar jin daɗi yadda ƴaƴan sa suke kansu a haɗe suna matikar kaunar junan su ba banbanci ko kaɗan. Juyawa Aryan yayi ya cigaba da aikin da yake

Sai da ya tabbatar bgs Khalid hiyana duk sun fita daga haɗari sanna ya fito daga ɗakin tare da Abba suna tafiya suna hira kai tsaye part ɗin Ummi ya nufa "Aryan ba wanka zakaje kayi ba? ina kuma zaka tafi" "Abba ba zan iya zuwa ko ina ba har sai naje na duba lamrat na mata kyau ta mai girma sanna nayiwa Yusuf congrat" girgiza kai Abba yayi yana farinciki ya wuce part na shi, Aryan kuma ya shige part ɗin Ummi.

A hankali Zahra ta lallaɓo ta fito daga part ɗin bgs ta nufi ɗakin da su hiyana ke kwance dan taga lokacin da bgs ya shigo da hiyana ta window ɗakin ta.
Zubawa hiyana ido tayi tana hawaye kafin ta juya ta koma wajen yaya Khalid zama tayi kusa da shi tana shafa face nashi tana tofa masa addu'a,ta rame sosai saboda tunani da rashin barci da bata yi two days ba slowly ta kwanta a gefen sa ba jimawa barci ɓarawo yayi awon gaba da ita

Karfe 9 na dare bgs ya farka a hankali ya waro idon sa, kuka ya fara ji kasa kasa cikin sauri ya miƙe daune tare da zuro kafar sa kasa da kyar ya iya cewa "auta me ya same ki kike kuka Aryan meke faruwa!?" sai lokacin Zahra dake rungume da Aryan tana kuka ta juyo tare da sakin Aryan ta tafi da gudu ta faɗa jikin bgs.
Cikin kuka take faɗin "yaya Prince naji yaya Aryan yana faɗa wa Abba wai yaya Khalid ya rasu amma da na tambaye sa sai yace min wai aa bai rasuba kuma wlh naji lokacin da ya faɗa wa Abba banyi barci ba" waro ido waje bgs yayi da karfi yace "what!!? Slowly ya ɗago idon sa ya kalli Aryan tare da ɗaga masa gera ɗaya alamar tambaya girgiza masa kai Aryan yayi alamar tabbatar masa da zancen Zahra gaskiya ne yaya Khalid ya rasu,sakin Zahra yayi ya miƙe da kyar sai lokacin ya lura dasu Ammi dake wajen bai bi ta kan kowa ba ya nufi gadon da Khalid ke kwance fuskar sa tayi fari tas kamar babu jini kura masa ido bgs yayi yana kallon face nashi sosai
Juyowan da zai yi sai ganin Zahra yayi tana kokarin faɗuwa kasa,cikin zafin nama ya tarota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sumammiya, yana kokarin ɗaukan ta ya kai ta saman gado Aryan yayi saurin ansan ta dan bai san ta famawa bgs hannun sa.

Cikin karyewar zuciya Ammi tace "wai meke fatuwa ne? ga hannun ka da ciwo hiyana na kwance jikin ta duk bandeji Khalid kansa duk bandeji wai menene ya faru!?" Komawa saman gadon sa bgs yayi ya zauna cikin sanyin murya yace "Ammi haɗari muka haɗu da shi" dogon sakati su Ammi sukayi gaba ɗayan su har suna haɗe baki,Ummi ce tayi ta maza tace "ai na hakan ya faru?" "no Ummi ba wai haɗari da mota bafa kidnaping na Khalid da sister wasu sukayi ni kuma tsabar tashin hankalin da na shiga lokacin dana binciko location ɗin sai na tafi ni ka ɗai kuma ban ɗauki makami ba burina kawai na isa in da suke,ashe yan ta'addan suna riƙe da manyan makamai sai suka farmin Allah ya tsare Aryan ya kawo mana ɗauki" ya kai karshen magana tare da kwanciya saman gadon.

Addu'a sosai su Ummi suka musu akan Allah ya tsare daga sharrin duk wani abun halitta. shiru palon yayi kowa da abun da yake tunawa

Almost 1h sunyi shiru ba wanda ya sake magana.
Dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya a hankali ya fara salatai tare da ambato sunan Allah,a sukwane bgs ya miƙe ya nufesa yana kiran sunan sa,da sauri gaba ɗaya family sukayo kansa suna faɗin "Khalid!! Khalid" hannu bgs ya ɗaga musu alamar suyi shiru karsu ruɗar da shi. Shiru sukayi suka zuba masa ido
ya jima yana salati da ambato sunan Allah kafin daga bisani ya waro manya manyan idon sa yana bin ɗakin da kallo.
Kamar wadda akayi wa allura haka ya miƙe zubur yana faɗin "kar kuyiwa sister komai dan Allah ni ku kashe ni ku kyaleta ta tafi kuyi hakuri" dafa kafaɗar sa bgs yayi cikin nitsuwa yace "Khalid now your safe kayi shiru" kara waro ido waje Khalid yayi sai yanzu ya lura dasu Ammi
ɗaya bayan ɗaya ya fara binsu da kallo, Kan face bgs ya tsai da idon sa cikin dashewar murya yace "ina sister take?" da hannu bgs ya masa nuni da gadon da take kwance,yunkurawa yayi zai mike,yayi saurin komawa ya zauna sakamakon jirin da ya ji ta na neman kwashe sa, kasa kasa yace "yinwa nake ji over" tun bai karisa rufe baki ba Fahad ya juya ya nufi fridge ya ɗauko masa fresh milk mai sanyi ya dawo ya miƙa masa,ansa yayi yana kokarin buɗe wa bgs yayi saurin anshe wa yana faɗin "abu mai zafi sosai zaku bashi ba mai sanyi ba" bai kai ga karisa maganar ba Aunty mardiya ta fice da sauri.

Jim kaɗan ta shigo hannun ta ɗaya ɗauke da plate mai ɗauke da ferfesun kayan ciki sai tiririn hayaki yake ɗayan hannun nata kuma rike da cup mai ɗauke da haɗaɗɗiyar tea mai zafi, ta kawo ta mikawa bgs ansa yayi ya zauna gefen Khalid ɗin da kansa ya fara bashi a baki.
Sosai Khalid ya ci abincin sai da ya cinye tas ya shanye tea ɗin ma tas mikewa yayi ya kwanta yana faɗin "Alhamdulila Allah na godema da ka bani yan uwa masu kaunata" shiru ɗakin ya sake yi ba wanda ya sake magana

Sallama suka jiyo daga bakin kofar shigowa ɗakin a tare suka kai kallon su wajen yaya bello ne da hasana rike da hannun hajjo.

barka da zuwa Ammi ta musu,cikin fara'a suka amsa tare da karisa shigowa ɗakin

Ɗaya bayan ɗaya suka bi mutanen ɗaki suka gaida su kowa ya amsa musu ban da bgs,dan shi ko kallon inda suke bai yi ba
"Ammi ina mara lfy take? ita mukazo dubawa zamu shiga part naki wani soja yace kuna nan" cewar yaya bello,satar kallon Ummi Ammi tayi ta kasan ido dan bata son Ummi ta san da zancen Aunty farida,
Abba ne yayi saurin cewa "kuje part ɗin Ammi tana zuwa" yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin da sauri, Ammi tabi bayan sa
gaba ɗaya family suka bi bayan Ammi sai yan kame kame Ammi take bata son Ummi ta bita part nata saboda Aunty farida amma ba yadda zatayi dole ta hakura suka tafi tare gaba ɗaya

ɗakin ya rage daga hiyana dake kwance sai bgs da Khalid da Zahra dake sume Aryan ma yabi Ammi dan yaje ya duba jiddan sa.

A palo suka samu Aunty farida kwance kamar dai kullun zama sukayi saman sofa,kowa ya zauna saman sofar da yake so. Ba karamin mamaki Ammi ta shaba ganin Ummi taga Aunty farida kuma bata ɗaga hankalin ta ba

"Me ya faru Ammi? naga kin sunkuyar da kai kinyi shiru" cewar Ummi "kiyi hakuri Ummi wlh....bata kai karshen maganar ba Ummi ta dagatar da ita ta hanyar cewa "aa ba sai kin min wata bayani ba dani dake duk ɗaya ne awajen ƴaƴan mu duk abun da zan iya yiwa farida kema zaki mata kuma banji komai ba dan kin ɓoyemin bata da lfy ni daɗin hakan ma naji tun ranar da Aryan ya kawo farida gidan nan na sani. duk da rashin lfy nata ya dame ni amma ban nuna ba kasan cewar nasan kun ɓoyemin ne dan karna shiga damuwa yanzu ma na biyo kune dan inason sanin halin da take ciki" Ammi na kokarin yin magana yaya bello yayi saurin katse ta da cewa "subhanallah wanna ai asiri aka mata ya akayi hiyana bata sanar da ku ba? ko dai bata gani bane Ammi ya akayi baki gane ba? Wanna ai mugun asiri ma aka mata ba mai sauki ba" gaba ɗaya idon mutanen palon ya dawo kan yaya Bello mikewa yayi ya dawo kusa da Aunty farida yana kare mata kallo
cikin ruɗu Ammi tace "wlh Bello ni nadaɗe da watsar da duk wani abu na kauye yanzu ba abun da na sani game da gargajiya na manta komai shi ya sanya ban gane ba" "ina akwatin bappa da hiyana ta ɗauka? Dan kwanaki naje ɗaukar akwatin inna tace hiyana ta ɗauka ku kawo akwatin bazaa rasa makarin asirin nan a cikiba sanna daman ina son inyi magana da hiyana akan akwatin dan kafin bappa ya rasu ya bani wasiya akan idan su hiyana sun mallaki hankalin kansu na basu sakon dake cikin akwatin" shiru palon yayi duk sun zubawa Ammi ido suna jiran suji me zata ce "Bello hiyana ce ta ɗauki akwatin kamar yadda inna ta faɗa amma ban sa aina ta ajiye akwatin ba,ke diyana ko kin sani?" Shiru diyana dake zaune kusa da yaya Aryan ta ɗan yi kafin tace "eh Ammi kamar naga ta ajiye cikin jakar Qur'ani bappa da ta ɗauko jakar yana drawer sa kayan mu" tun diyana bata gama rufe baki ba Aunty mardiya ta miƙe ta nufi ɗakin nasu.

Jim kaɗan ta dawo ɗauke da jakar a hannunta, yaya Bello ta mikawa sannan ta zauna kusa da Aunty farida
Buɗe jakar yayi ya fito da akwatin yana karewa akwatin kallon "ina key ɗin akwatin yake?" Ya tambaya yana dawo da kallon sa kan Ammi "a haka mukaga akwatin babu key mun duba key ɗin a ɗakin bappan amma bamu gani ba" yaya bello na kokarin yin magana Aryan ya rigasa da cewa "ku fasa akwatin mana tun da ba key" murmushi kaɗan yaya Bello yayi kafin yace "ai akwatin bazata fasu ba koda kuwa bindiga zaka sa mata ni na san in da key ɗin ma yake sai dai nayi tunanin ko sun gani sun ɗauka ne ka ne yasa na tambaya" da sauri Ammi tace yauwa bello tun da ka sani ka ɗauko ka buɗe mana dan Allah mu samu feeda ta samu lfy" "aa Ammi kona ɗauko key ɗin ba zai buɗuba sai hiyana ce kawai zata iya buɗe wa dan bappa yace ita kaɗai ce zata iya buɗe akwatin duk kuma wanda yayi gigin kuskuran gwada buɗe wa tofa komai ya faru shi ya jawa kansa ko diyana ba zata iya buɗe wa ba sai hiyana bappa ya nunamin in da key ɗin yake da jimawa kuma ina da tabbacin yana wajen,yanzu dai sai yaushe hiyana zata farka?".
Gaba ɗaya jama'ar palon kallon su ya dawo kan Aryan suna jiran suji yaushe hiyana zata farka ta buɗe musu akwatin nan. "Aryan yaushe Hiyana zata farka?" Cewar Ammi dogon numfashi yaja tare da sauke ajiyar zuciya kafin yace "In Sha Allah muna sa ran gobe ma zata iya farkawa domin bullet ɗin bai shiga jikin ta sosai ba a baki baki ya tsaya bgs ya...bai kai karshen maganar ba yayi shiru yana ɗan satar kallon Ammi ta gefen ido "yayi me kuma? Ammi ta jefo masa tambaya,tana kare masa kallo
ɗan sosa kansa yayi kafin ya waske da cewa "yayi mata treatment mai kyau" shiru Ammi tayi tana tunanin "anya ba wani abun suka aikata ba dan dukka yaran nan basu saba karya ba idan suka yi kuma sai an gane yanzu dai Aryan karya yake ba haka yayi niyar faɗa ba akoi dai wani abu amma koma me zan binciwo wlh idan har yanzu yaron nan yana kallazawa hiyana sai ya rabu da ita ta auri wanda take so yake son ta kuma sai dai ya nemi wata uwar ba ni ba haba yaro ne baya jin magana idan baa aure ni zan auri Abban ku ne har na haife ka ne?".

Buɗe jakar da kyau yaya bello yayi ya fito da wata katuwar littfin tafsiri ya buɗe tsakiyar littfin ya ɗauko wani ɗan karami key mai shegen kwalli yana ɗaukan ido key ɗin mai design ɗin yatsun mutun karami mikawa Ammi key ɗin yayi yana faɗin "Ammi ki ajiye gobe da safe zamu zo idan hiyana ta farka sai ta buɗe mana akwatin ni kuma na haɗawa Aunty farida magani dan na san akoi magunguna sosai a ciki wani lokaci idan nazo nace wa bappa cikina na ciwo a cikin akwatin yake ciro magani ya bani" ansan key ɗin Ammi tayi tana mamaki tace "Amma gaskiya wanna key ɗin yana bani mamaki tun muna yara haka yake wanna kwalli har yanzu bai dai na ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login