Showing 69001 words to 72000 words out of 363274 words
daga ɗayan ɓangaren Aryan yace,"hello my lovely Aunty " ba itabace yaya Aryan ni che ina wuni " lfy lau y jikin naki " nasamu sauki hiyana che kawai tarage bata samu sauki'ba " subhanallah me ke damunta ina nurse naku " nurse ta koma jiya wai zataje tayi shirye shirye sallah " to meke damun hiyanar " chiwon kai da jiri " ok jibi zamu dawo ae sai na dubata amma duk da haka zansa a kawo mata magani " to bari na kaiwa Aunty farida wayar " daman kinsan zaki kai mata wayar'ne kikayi picking call ɗin " eh ae nayine daman dan na gaisheka tun da mun daɗe bamuyi magana'ba " to ae kece kika manta dani shiyasa " dariya diyana ta ɗanyi kafin tace, ni ban manta da kaiba dan bani da waya'ne Allah dana kiraka " wani ajiyar zuchiya ya sauke"to amma kina kewata kuwa " eh mana ina kewar'ku dukkan'ku " ok to shike nan ki ajiye wayar kawai anjima idan Aunty farida tazo ta kirani dan naji Abba na nemana " to kawai tace tare da chire wayar a kunnen'ta ta mayar kan gadan ta ajiye,"takoma gaban mirro tachigaba da kwalliyar'ta
YOLA
Inna na ɗaki kwanche a kan yar gadon chiyawar'ta taji sallama daga kofar gd mikewa tayi daga kwanchiyar datake tana amsa sallamar,"ɗaukar mayafinta tayi tanufi waje " ganin bello ne ke sallamar yasa inna ta ɗaure fuska sosai tafara magana to yau kuma dame kazo funafiki " ina wuni inna " daban wuniba zaka ganni'ne " to Allah yabaki hakuri daman naga gobe sallane shine nache bari na sauke hakkin ma kwabtaka na kawo miki wan nan,"yayi maganar tare da ajiye wa inna gaji guda uku a gaban'ta, batare daya jira amsar'taba yayi wuce warsa gidan'su " da mamaki inna ke kallansa har yashiga gida, duƙawa tayi ta ɗauki kajin tayi chikin gida," a tsakar gida ta ajiyesu san nan ta ɗaukoh wuƙa tayanke igiyar da aka haɗesu aka ɗaure, ta samu wani igiya ta ɗauresu ɗai ɗai ta kaisu kichin tafito takoma ɗaki ta kwanta," tana kwanchiya babu jimawa buba yashigo gidan da sallama yana ɗingisa kafa da sanda " tana daga chikin ɗaki ta amsa masa san nan tace yashigo " shiga ɗakin yayi hannunsa riƙe da buhu " lfy buba ina zakaje da buhun nan " bappa'ne yace na kawo miki, shin kaface wai kiyi girkin sallah " da murna inna tamike zaune wayyo Allah kacewa bappa ngd sosai Allah yaƙara arziƙi " amin yafaɗa tare da ajiye mata buhun ya juya yafita " buɗe buhun tayi taga shin kaface mai kyau da murna ta tura buhun bayan kyaure ta ɓuye
KANO
Misalin karfe 7 na dare, sun haɗu a palon Abba suna buɗa baki " kai my diyana sarkin san kwalliya chewar Aunty farida tayi magabar tana ɗan jan kumatun,diyanar " ae kwalliyar dazanyi gobema sai yafi wan nan kyau " Allah ko ae haka akesan mace takasan'ce mai tsabta da kwalliya " Zahra tace Aunty farida ae muma munayi " eh kunayi amma my diyana tafikuyi sosai, kuma kuƙara dagewa " to shike nan zamu rinƙayi sosai " ok to kuchi abinchin'ku dawuri muje mu kwanta dan kunga gobe sallah zamu tashi da wuri " har suna haɗa baki wajen chewa toh " shiru kakejin palon babu mai magana sai paran spoon kawai zakaji " sallama sukaji anyi a bakin kofar palon " amsa sallamar Aunty farida tayi san nan taba da izinin shigowa " ɗaya daga chikin security bakin gate ne,har ƙatsa ya duƙa ya gaida Aunty farida " ta amsa tare da tambayar'sa ko lfy " eh lfy wani likitane yakawo saƙon nan wai inji oga yace abawa hiyana " ok to ajiye a saman table ɗin gaban kan nan " mikewa yayi ya ajiye sakon san nan yanufi waje
Bayan sun gama chin abinchine suka mike zasu tafi ɗaki, Aunty farida tasa hannu ta ɗauki sakon tana faɗin muje ɗaki kisha maganin hiyana " toh kawai hiyana tace, san nan suka nufi waje " sai da Aunty farida ta tabbatar hiyana tasha magani san nan takama hannun diyana da amrat suka nufi,dakinta, a gurguje sukayi wanke sukayi sallar issha suka kwanta asuba tagari
Tunda sukayi sallar asuba yau basu mai da barchiba " diyana tun karfe 7 take gaban mirro ta goga wan nan ta fenta wan nan ba karya tayi kyau sosai tamkar zataje gasar sarauniyar kyau " da sallama Aunty farida tashigo ɗakin tana waya da Aryan, wow my diyana kin ganki kuwa kamar wata sarauniya " dariya diyana tayi tana faɗin ngd Aunty farida " dawa kike magana kuma Aryan ya tambaya " hmm nina mantama muna waya wlh, kyan my diyana ne ya rikitani " shiru ya ɗanyi kamar mai tunani chan kuma sai yace to ɗauke'ta hoto ki turomin naga kyan daya rikitakin " ae kuwa kai ma idan kagani sai ka rikiche " to shike nan turomin ɗin dai kekam " ok tace tare da chire wayar daga kunnen'ta ta katse kiran" tadubi diyana tace to tashi kisa kaya namiki hoto " yauwa Aunty farida Allah yamiki albarka daman inasan inje in anshi wayar Aunty Zahra nazo nayi hotan, tayi maganar tana kokarin mikewa..✍️
More comments pls
💖The Talent Troupe Writer's 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*Episode 19*
Lafayar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗauko, Aunty farida da kanta ta ɗaura mata baƙaramin kyau tayiba ga kitso guda biyu a gaban goshita, kamar wata amarya ga lallenta ja da baki " wow my diyana kin haɗu iya haɗuwa yanzu muje wajen flowers ɗin garɗing muyi hotan koh zaifi kyau " to Aunty farida amma sai na ɗaukoh takalmi a ɗakin Ammi " ina takallamar dana kawo muku " aa shikam sai gobe zansa yanzu high heel nakeso " murmushi Aunty farida tayi tare da jan hannunta tana faɗin to muje " fitowa palon sukayi nan suka isko su Zahra suma sun sha kwalliya sosai sai dai su dukkansu hijabi suka'sa dan zuwa sallar idi " Aunty farida ina zakuje Zahra ta tambaya " hoto zamuje muyi a garding, ko zakuyine kuma " aa nikam banso chewar Zahra " to kufa tayi maganar tana nuna su lamrat "har suna haɗa baki wajen chewa aa bamusu " da kyar hiyana tamike dan sarawar da kanta ke mata tana faɗin Aunty farida muje kimana tare ni kam ina so " riko hannunta Aunty farida tayi dan yadda taga yanayinta kamar zata faɗi da kyarma take tafiya" a harabar gidan suka tsaya san nan Aunty farida tace my diyana kije ki ɗauko ta kalmar naki kinji, kiyi saurifa dan kinga hiyana bazata iya tsayuwa sosaiba " da sauri diyana ta juya tanufi bangaren Ammi " Shahram na ganin'su yazo wajen da sauri ya gaida Aunty farida san nan ya tambayeta ko fita zasuyi'ne ya kaisu " aa tace masa " juyawa yayi yakoma bakin gate " suna tsaye har diyana ta dawo kwas, kwas, kwas, take tafiya, a nitse take zuba takunta da yanga " daga nesa Aunty farida tafara ɗaukarta video sai faɗin wow take, sai da ta iso kusa dasu tukun nan Aunty farida ta tsai da video, suka nufi chikin garding ɗin " hotona sosai, tamusu a tare san nan tawa diyana ita kaɗai kala kala, bayan sun gamane suka nufi chikin gd Aunty farida na faɗin to my diyana sai kije ki ɗaukoh hijabinki muje masallachi koh " to diyana tace tare da wucewa ɓangaren Ammi " Aunty farida da hiyana kuma suka nufi ɓangaren Ummi
SAUDIA
Tsaye yake a gaban mirrow ɗaure da towel a kugunsa da alama wanka yafito, yana shafa mayukan'sa masu kanshi da tsada' bayan ya gamane ya gyara gashin kansa ya sake feshe jikinsa da turare mai kanshi da tsada, trolley'sa ya jawo ya buɗe ya ɗaukoh farar jallabiya, ya juya a jikinsa yayi kyau kamar balarabe,tsayuwa yayi a gaban mirrow yana kallan kansa, wayarsa dake kan gado tayi kara alamar kira yashigo, a hankali yake takawa kamar yana tsoran taka kasar ya isa gaban gadan,hannu yasa ya ɗauki wayar my blood ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, da sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen'sa " hello " daga ɗayan ɓangaren DON yace jirginmu zai sauka 9:30 dai dai "ok by the i will be they " thanks ya faɗa tare da katse kiran' Aryan zai ajiye wayar ke nan yaji tasake kara alamar shigowar sako, ganin my lovely Aunty yasa ya buɗe sakon,
da sauri ya zauna a bakin gado tare ta kara waro ash eyes nashi a kan'wayar,Sosai yake kallan wayar kamar zai chinye, wow dole Aunty farida ki ruɗe irin wan nan kyau haka,yarinya kamar wata aljana, yayi maganar yana manna wayar a kirjinsa, jinake kamar jibi yamin nisa jinake tamkar ranakun tsawo suke karawa, kusan 10 mnt yana zaune yana surutai, san nan a hankali ya miƙe yanufi hanyar fita,wayar na manne a kirjin'sa
Kai tsaye ɗakin khalid ya nufa nan yasami Yusuf ma a chan dukkan'su sun shirya chikin fararen jallabiya bakaramin kyau sukayiba " muje koh lokachin sallama yakusa ae chewar Aryan" Khalid yace wai Aryan ina DON ne tun shekaran jiya nake tambayar'ka kakemin wani kauce kauce koh " nafaɗama'ka Khalid yana nan kawai yaje chikin madina ne " lallai Aryan to karyan ma bai dace da kaiba, baka sabayi'ba shiyasa ma dakayi yanzu, karyan bata zauna ba " dogon tsaki Aryan yaja tare da faɗin inkun gama kusameni a masallachi nayi gaba tun da naga baku da niyar tafi, yana gama faɗin hakan yayi waje " kallan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido Khalid yayi"muje koh " hmmmm kasan'me Khalid wlh DON baya kasar nan wani lokachi sai Aryan yarinƙa magana kamar ba tare muka tasoba ina da tabbachin DON yana London zai wani chemana yana madina shi ko karyan ma bai iyaba " kaga Yusuf kafita maganar Aryan da DON kazo mutafi masallachi kar murasa sallah, yakai karshen maganar yana nufar hanyar fita " mikewa Yusuf yayi yabi bayan'sa " suna fita waje suka samu gaba ɗaya family sun haɗu amma banda Aryan " Khalid ina Aryan da Prince Ummi ta tambaya tana kallan fuskarsa " sunyi gaba Ummi " to muma ae sai muje koh dan kar lokachi yakure " tare suka jera dayake masallachi kusane da masaukin'su " suna isa suka rabu su Ammi sukayi ɓangaren mata su Abba kuma sukayi ɓangaren maza
Nigeria
Zaune suke a palon Ummi diyana yau baƙi ya buɗu ta tasa fruits a gaba sai chi take " hiyana na rike da littafin addu'oe tana karatu " lamrat na game a waya Zahra " amrat na kallo a wayar Aunty farida " Zahra kuwa ta kwanta ta tada kai da chinyar Aunty farida sai hira suke kamar saannin juna " da sallama Aunty Maryam ta shigo palon " Aunty farida ta amsa mata fuska ba yabo ba fallasa " zama tayi a saman sofa mai zaman mutun 1 tare da faɗin, ina wuni Aunty farida anyi sallah lfy " lfu lau ykk "lfy Alhadulillah ta faɗi hakan tana mikewa " inakuma zakije kitsaya muci abinchin rana tare mana tun da lokachin yayi chewar Aunty farida " aa bana buƙata a inda,na fitoma akoi abinchi dama dai kawai nabi dokar gd nanne nazo na gaisheki kuma namiki barka da sallah a matsayinki ta babba, SO no need na tsaya yin wani abun, tana gama faɗin hakan tayi waje " Allah ya shiryaki Maryam Allah yasa ki gane.. bata garisa maganar'ba sukaji diran manya manya motochi a gd " da fara'a Aunty farida ke faɗin oyoyo Aunty salma oyoyo Aunty mardiya" tun Aunty farida bata karisa magarba Zahra tamike a guje tayi waje, mikewa Aunty farida ma tayi tabi bayan Zahra suka bar su diyana a ɗakin " hiyana ta dubisu diyana" kukam bazakuje kumusu oyoyo bane " ni kam bazanjeba dan bansan'suba kilama halinsu irin na Aunty Maryam ne chewar diyana" lamrat da amrat ma sukache muma bazanjeba " baki hiyana ta taɓe tana kallansu zata yi magana sai gasu Aunty farida sun shigo" Aunty farida rike da hannun Aunty Salma "Aunty mardiya rike da hannun Zahra da wani baby boy mai kyau dashi mai kama da yaya khalid,saman sofa suka zauna " da sauri hiyana tafara ɗaga musu gaisuwa" wow Aunty farida wayan nan ƴa'ƴan larabawan fa kodai sune ƴaƴa Abba da ya faɗamin yasamu wasu ƴaƴa daga Allah Chewar Aunty salma " eh wlh salma sune " kai gaskiya bari Abba yadawo ya taimaka yabani wanchan da wan nan tayi maganar tana nuna hiyana da diyana " tab ae kuwa wayan nan yaran nan gani nan bari, inji Abba dan tun farkon zuwar'su nida mardiya mun roka ya hanamu " aa ae ni nace masa zanyi wlh har sai yabani " to Allah yaba da sa'a chewar Aunty farida " ameen Aunty salma ta amsa tare ta chewa ya su nanku ɗaya bayan ɗaya suka faɗa mata su nansu sai wow nice name kawai take faɗi " kutashi kuje kuyi wanka kuzo muchi abinchi " a tare Aunty mardiya da Aunty salma suka mike suka nufi dakinsu " inakuma zakuje Aunty farida ta jefo musu tambaya " ɗakinmu mana " wani ɗakin ae sai dai kuje ɓangaren Ammi dan kuwa ɗakinku yazama ɗakin Yan mata'na har sai randa Ammi ta dawo zasu barmuku ɗakin sukoma nasu " to ae danan da chan duk ɗayane badamuwa chewar Aunty mardiya tayi maganar tare da juyawa tanufi hanyar fita, bin bayanta Aunty salma ma tayi " Auta ki kiramin masu aiki suzo ku shirya mana abinchi ina zuwa mikewa tayi tanufi ɗakinta " Zahra kuma tasa hannu ta anshi wayar ta a hannun lamrat, tafara kiran layin binta, bugu binya ta ɗaya Zahra tabata umarni tazo ta shirya abinchi tana gama faɗin hakan ta katse kuran tamikawa lamrat wayar
SAUDIA
abinchi sukechi chikin nitsuwa shiru palon babu mai magana " Abba me zai hana mutafi gobene dole sai jibine, Chewar Aryan "a sukwane DON ya ɗago yana kallan'sa, shi ko ajikinsa saima latsa wayar'sa yake " meyasa kakesan mutafi gobe Aryan kodai ƙasa mai tsarkinne bakaso chewar Abba " aa Abba bawai bansan kasan bane wlh nagajine inasan inkoma gida " Khalid ya ɗago ya sachi kallan Yusuf sai murmushi suke " Aiman kuma ya kalli Khalid san nan yajuya ya kalli Yusuf yana girgiza kai a zuchiyar'sa yana faɗin muna fukai asirinku yakusa tonuwa ae idanma wani abu kuke shiryawa ɗan uwana to kanku zai dawo " Ahmad kam abinchin'sa kawai yake chi hankalin'sa kwan'che " haidar ya matso kusa da Umar yafara masa magana katsa katsa anya yaya Aryan lafiyar'sa kuwa "umar ya ɗago kai zaiyi magana karaf idon'sa ya sauka chikin na Fahad dake gurga musu mugun kallo " to shike nan Aryan tun da haka kakeso kukira'su farida ku faɗamusu gobe zamu dawo chewar Abba yayi maganar tare da mikewa yanufi hanyar ɗakin'sa " mikewa Ammi da Ummi sukayi sukabi bayan'sa "Aunty amarya kuma tamike tanufi nata ɗakin " kallan Umar da haidar DON yayi yana faɗin me kukejira ae tun bai kai karshen maganar'ba suka mike suka nufi waje, dawo da green eyes nashi yayi kan Fahad, tun baiyi magana'ba Fahad yamiƙe shima yayi waje " green eyes nashi ya jubawa Aryan sosai yake kallansa" Aryan nasane da kallan da DON ke masa amma yaki ɗago kai dan bai da amsar tambayar da DON ɗin zai masa " bazan sake tambayar meke damunka ba dan nalura kaima bakasan meke damun nakaba binchike mai kyau zanyi kawai a kan hakan " sai loakchin Aryan ya ɗago yana faɗin da ka taimakamin bro dan koba komai zaka daina tunanin chewa ina ɓoyemaka wani abu " ajiyar zuchiya ya sauke san nan yamiƙe yana faɗin to sai kuje kushirya ae tunda komawa gobe yakamamu gashi yanzu kusan karfe 4, da ɗai ɗai suka miƙe suka bar palan
Yola Nigeria
Inna tachi wankan ta tasa wata atampha da bappan, bubu ɗinka mata mayafi ta ɗauka tayi waje, kai tsaye gidan'su buba tanufa, da sallama tashiga gaba ɗayan'su suna tsakar gd " inna sannu da zuwa chewar buba" yauwa buba ya kafar taka " naji sauki ae yanzukam ina ɗab iya takawa batare da sandaba " to alhamdulillah Bappa ina wuni" bappa dattijon arjiki halinsa iri ɗaya da bello mutumin kirki yace lfy habiba anyi sallah lfy " lfy lau bappa inna larai mushiga daga chiki koh" inawuni inna chewar bello " yamutse fuska inna tayi kafin ta amsa da lfy, san nan tawuce ɗaki da sauri dan karma wani ya gaisheta, bello ma albarkachin bappa yana nanne shiyasa ta amsa gaisuwar" miƙewa innar buba tayi tabi bayan inna, innar bello dai dake zaune kan tabarma ta taɓe baki tai tana kallansu har suka shige ɗaki a zuchiyar'ta tana faɗin Allah ya kare mutun daga sharrinku dan kuwa wayan nan idan suka haɗu ko sheɗan suransu yake "
Lfy inna chewar innar buba" lfy ba lau'ba kinga anyi sallah yau yakamata gobe mukoma wajen malam koh dan asamu ayi aikin nan dawuri " aa to mezai hana muje yanzu chewar innar buba " to me zakice wa bappan buba idan zamu fita " aa ae yanzu zai fita dakin ɗan tsaya kaɗan'ma bazaki samesa'ba yanzu dai mujira fitar'sa " to shike nan bari naje gd na ɗaukoh kuɗin nadawo,bata jira amsar innar buba ba tayi waje " da sauri sauri ta shiga gd ɗakinta tanufa tana shiga ta ɗaga yar katifar chiyawar'ta ta ɗauki kuɗin ta kirga sauran 5k ,ta juya tanufi waje, a dab da bakin kofa tayi karo da bappan buba zai fita, matsa masa tai tana faɗin Allah ya kiyaye