Showing 336001 words to 339000 words out of 363274 words

Chapter 113 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2621

duk wanda ya yi hakan kuwa ba zai taɓa gama wa da duniya lafiya ba koba alokacin ba sai Allah ya hukun tashi ya ansawa iyayen hakkin su Ammi na gama nata faɗan Ummi da Innar Bello suka ansa sosai suma suka wa Hajj Fateema faɗa mai ratsa zuciya hakan yasa ta kara girmama girman iyaye jiki ba kwari ta mike ta fice ta nufi part ɗin Ammi tana shiga ta haye gado tana mai dana sanin abun da ta aikata a Rayuwar ta a gefe guda kuma tana mai kara jin kaunar bappa da tsanar Inna Habiba da ta kashe sa da kyar barci ya iya ɗaukan ta.

Us

Bgs na shiga ɗakin nasu na duba marasa lafiya ya kwantar da Diyana saman gado cikin sauri ya yage rigar dake jikin ta runtse idon ya yi lokacin da idon sa ya yi arba da glass ɗin da ta yanke ta a marar ta sosai, ga glass ɗin a ciki kato bai fita ba kayan aiki ya ɗauko allura kashe zafi ya ɗauko ya mata a wajen sanna ya fara ƙoƙarin cire glass ɗin Hiyana na tsaye tana kuka sosai kamar ranta zai fita kasa kasa yace "My Eshat ki yi shiru mana dan wanne ɗaya zan ji ki sassauta min ta bangaren ki, ki dai na kukan nan karki sa zuciya ta ta fashe kin san yadda na ke ji idan ki na kuka kuwa? Ji nake kamar zuciya ta zata fashe tana min zafi da raɗaɗi" da gudu ta kariso wajen ta faɗa saman bayan sa tana kuka kasa kasa cigaba da aikin sa ya yi yana mai tausayawa Diyana dan glass ɗin ta kusa wuce wa in da ba'a zato abu kaɗan ya hana ya buɗe cikin nata sakamakon danne sa da tayi tana murkusoso duk tasa glass ɗin ya yi ta kara nitsawa cikin nata, sosai ta bashi tausayi duk da ya mata alluran kashe zafi bata dai na hawaye ba. A nutse ya mata aiki dan ceto ranta ya yi Sa'a komai ya tafi yadda ya dace bayan ya ciro glass ɗin ya mata ɗin kin wajen ya sanya mata plaster awajen sanna ya gwada ta dan ya ga cikin jikin ta na nan ne ko ya fita gwajin farko ya kalla cikin na nan godiya ya yi ga Allah sanna ya mata alluran barci dan ta huta yana gamawa ya duba time a agogon dake manne a bangon ɗakin 5:20 cikin sauri ya juyo tare da rungumar Hiyana dake kwance a bayan sa yana faɗin "My Eshat ki godewa Allah ko mai ya tafi dai dai yadda muke so yanzu muje muyi sallar asuba lokacin ya tafi rungume sa tayi tana shassheka cire safar hannun sa ya yi ya a jiye ya ɗauke ta cak suka fice daga ɗakin.
suna shiga bedroom na su wayar sa dake saman bedside drawer ta fara kara cikin sauri ya sauke ta dan dole ya saurari duk wata kiran da zata shigo wayar sa a yanzu saboda samun information akan su Aryan. Ya nufi wajen wayar ya ɗauko tare da duba wanene ke kiran sa da asuba ganin sunan blood Yusuf yasa ya yi saurin ɗaukan kiran tare da man na wayar a kunnen sa. Jim kaɗan ya ciro wayar daga kunnen sa ya nufi hanyar fita yana faɗin "Eshat ki yi Sallah we need your prayer" kafin ta yi wani magana ma ya fice daga ɗakin jiki ba kwari ta wuce toilet ta ɗauro alwala ta gaba tar da Sallah nan kar dadduma barci ya ɗauke ta kasan cewar bata samu barci jiya da daddare ba tana sallame Sallah ta baje awajen daman sallar ma tana yi tana gyangyaɗin barci.

Bari muleko Aryan mu gani me yake ciki wata kila kafin mu dawo Diyana ta farka

Dubai

A hankali suke ta kawa kamar wasu ɓarayi haka suka kutsa cikin saharar nan. Sun yi tafiya mai ni san gaske har sun dai na jiyo kam shin motocin su Aryan yana musu jagora yana duba location ɗin da yan ta'addan suke a yar karamar naura dake hannun sa. Sosai bugun zuciyar sa ta karu jikin sa ya fara basa gida ba lafiya ba dan ya saba zuwa yaki ba yaune farau ba bare yace saboda yaki ne yasa gaban sa ke faɗuwa ba hakan ya sa ya ciro wayar sa ya dakata da tafiyar da suke tare da miƙa wa ɗaya daga cikin sojojin sa na'uran hannun sa, suka ansa suka ci gaba da tafiya. Shi kuma ya tsaya tare da kunna hasken screen na wayar sa layin bgs ya laluɓo ya fara kira. Sau uku yana kira bgs bai ɗaga ba wani muguwar faɗuwar gaba yaji gaban sa ta yi ras cikin sauri ya kira layin Diyana ita ma sau uku yana kira bata ɗaga ba ya kira layin Hiyana ita ma bata ɗaga ba sosai ya shiga tashin hankali idon sa ya rufe baya ganin number da yake kira cikin ki ɗima ya kira layin Fahad lokacin Fahad na Sallah bai ɗaga ba, yana kokarin sake kiran wani layin ya ji yo karar har bin bindiga cikin sauri ya mai da wayar aljihun sa ya bi bayan sojojin nasu nan yayi arba da suna musayar wuta da criminals ɗin komawa gefe ya yi ya ciro wayar dan ya cigaba da neman layin su bgs dan hankali sa yaki kwanciya duk layin wanda ya kira baya ɗagawa dan lokacin duk suna Sallah suna taya sa da addu'a shi kuma bgs da Hiyana suna kokarin ceto ran Diyana lokacin wayoyin su na bedroom na su.

Aryan ya shiga damuwa ya fita hayyacin sa sosai sai kashe musu sojoji criminals ɗin suke shi bai ma sani ba hankalin sa na kan wayar sa burin sa kawai yaji yan uwan sa na lafiya gaba ɗaya tawagar farko da ya zo da su an kashe su har tawaga ta biyu suka zo suka wuce sa suka shiga wajen bai sani ba yana latsa wayar sa.
lokacin da ya farga ya dawo cikin hayyacin sa an kashe musu sojoji da dama a firgice ya duba time 7 am dai dai lokacin a zafafe ya yi wurgi da wayar tasa ya ɗana bindigar sa ya kutsa cikin wajen ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin an kashe musu sojojin rundunar farko da yazo da su duk an kashe su suma runduna ta biyu da suka shigo daga baya saura kaɗan an kashe dayawa daga cikin su wani zuciya tace masa ya danna kararrawar neman agaji ko bgs zai iya kawo masu ɗauki ko a tura musu wasu sojojin daga nan kasar wata zuciya kuma tace masa aa idan ka danna na uran ma zaka ɗaga wa yan uwa ka hankali ne a banza dan ko ka danna ba lallai sojojin su iso baa a kashe ku ba gwara kawai ka kyale yan uwan ka kayi shahada. Ya yi nisa cikin tunani sai jin ya yi an san ya masa bindiga a kai sa duk wanna bata dame sa ba burin sa kawai yaji meke faruwa a gida da gaba ɗayan su suka ki ɗaukan wayar sa ya san dai ba lafiya ba ɗaya daga cikin criminal ɗin ne ya dake sa a kafa sai da ya faɗi kan guiwowin sa anshe bindigar hannun sa suka yi ɗaya daga cikin su ya buga masa gindin bindigar a goshi nan take jini ta wanke masa fuska duk wanna abun da suke masa baya jin su hankalin sa na gida yana tunanin meke faruwa.

Tattara sojojin 20 ɗin da suka rage da rai criminals ɗin suka yi suka haɗa da Aryan suka wuce da su cikin wani ɗaki mai girman gaske. Nan suka fara dukan su sosai criminal ɗin suna da yawa sosai da sosai sun fi sojojin da aka turo yawa.
suna cikin dukan su ogan su gaɓa ɗaya ya shigo ɗakin yana faɗin "Yau ɗaya daga cikin burika na akan Safras zai cika ku kashe min dukkan sauran sojojin nan bana bukatar su shi kuma Aryan ku bashi kayan maye sosai, ku ɗura masa hodar ibilis sosai ta yadda sai ya kasa ganin komai ku ɗauke sa ku kai sa kan babban titi ku sake sa mota ta taka shi ya mutu ku dauki video sa a yayin da yake tangal tangal a titi ku turawa wancan ban zan dan uwan nasa sanna ku baza video a duniya kusa kurɓatatcen soja ya sha kayan maye ya hau titi mota ta takasa ku ɓata masa suna kunga idan video ta fita dole za ayi stoping na ɗan uwan sa daga wajen aiki ni kuma burina ya gama cika" jin muryan mutumin yasa Aryan ya ɗago kai da sauri yana kallon sa mamaki ya hana shi magana gani yake kamar mafarki yake hannu yasa ya goge idon sa dan ya tabbatar wan da yake gani da gaske ne ko dai mafar ki yake a hankali ya furta "major Ishaq" yana cikin mamaki ya jiyo ɗaya daga cikin criminal ɗin yana faɗin "oga mai zai hana mu basu kayan maye dukkan su kafin mu kashe su kaga zasu tafi lahira cikin jin daɗi" murmushi mugun ta wanda Aryan ya kira da major Ishaq ya yi yana faɗin "Shawara mai kyau ku basu dukkan su amma shi Aryan sosai zaku bashi wadda zai goge masa komai na kan sa san nan ku tabbatar kun masa dukan mutuwa kafin ku fitar da shi" yana kai karshen maganar ya fice daga wajen cikin sauri yaran Major Ishaq suka fara aikin su na ɗirka wa sojojin kayan maye sosai suka danne Aryan suka fara ɗura masa kayan maye suna shaƙa masa hodar ibilis nan take idon sa ta fara sauya kamanni izuwa ja zuciyar sa na masa zafi shi da yake yaki yake hana shan kayan maye yake kama masu sayar wa ya kashe shugabannin Companys ɗin sa suke haɗa kayan maye yau shi ake bawa kayan maye da kan sa, idan ya tuna hakan zuchiyar sa kuna take masa ji yake kamar ran sa zai fita saboda ɓacin rai su kuwa sun danne sa mutun biyar suka danne sa uku kuma sun dage sai ɗura masa hodar suke tun yana iya gane wani abun har ya dai na ya fara ganin duniya na juyawa ya fara ganin sama na kokarin faɗo masa a kai sai da suka ɗura masa hodar sosai ya fita hayyacin sa ya dai na gane komai sanna suka fara dukan su.
Ba karamin duka suka musu ba dan gaba ɗaya sojojin da suka rage basa wani mumfashi sosai, shi kuwa Aryan kwata kwata baya duniyar mutane dan na shi wahalar ma ta daban ne ɗaure su suka yi irin ɗaurin da akewa goro suna kokarin fita da Aryan ogan nasu ya shigo ya dube su yace "Na canza shawara ku ɗaura wa Aryan bom a jiki ku sai ta bom ɗin 40mins sai ku ɗauke sa ku fita da shi kuje ku sake sa a kan hanya ya ɗan yi tangal tangal ku masa video dan mu samu na ɓata musu suna mu samu a tsaida ɗan uwan sa daga wajen aiki san nan ku dawo min da shi ku rufe sa a ɗakin nan bom ɗin ya tashi da su su mutu gaba ɗaya na huta dan gwara min shi ya tashe su da bom su mutu a rufe babin su idan ba haka na yi ba bgs zai gane na san halin sa da kaifin ƙwaƙwalwa idan muka harbi sojojin nan da bindiga mun tona wa kan mu asiri wallahi ko ta hanyar bullet dake jikin su bgs zai nemo mu dan zai nemi Company da muke sayan kaya ya bincika sai ya gane amma kun ga idan muka kona su da bom ba zai samu wani makama ko kaɗan ba, ba zai samu damar yin wata bincike ba bare har ya iya gane wa kuyi sauri ku sanya masa rigar bom wadda ake ɗaure wa da notir wadda mutun kafin ya kwance sai ya ɗauki 1h hakan zai sa koda wani ya kawo musu ɗauki shi Aryan dole ya mutu dan rigar bom ɗin ba zata fita ba kafin su fitar bom ɗin ta tashi sanna idan kun dawo da shi ku tabbatar kun ɗaure sa da sarka kuma kar ku manta kuyi shirme sai kun sa masa rigar bom ɗin sanna zaku sai ta time ɗin bom ɗin" yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin cikin sauri ɗaya daga cikin yaran Major Ishaq ɗin ya fita. Jim kaɗan ya shigo hannun sa ɗauke da rigar bom basu ɓata lokaci ba wajen sawa Aryan rigar bom ɗin sanna suka sai ta time ɗin sauran sojojin sai juyi suke a tsakiyar ɗakin kansu na buga musu shi Aryan ma ba'a magana dan kamar ya suma baya wani motsi haka suka ɗaga shi jikin sa a sake suka kama kafar sa suka fara jan sa a kasa suka nufi hanyar fita.

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

.


💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By
Star Lady


Page 59


***Rike kafar sa suka yi suka fara jan sa a kasa suka nufi hanyar fita.
Wani gigitatchiyar kara suka ji wadda ta firgita musu kwakwalwan su wani irin gigicewa suka yi dan ba su taɓa jin irin wanna kara ba suna tashin bom a waje da ban da ban amma basu taɓa jin kara mai karfin wanna ba kunnen su ya toshe na wancan gadi saboda karar da suka ji yo. A kiɗi me major Ishaq ya shigo ɗakin suna tsaye a tsakiyar ɗakin sun kasa ko da motsawa cikin kiɗi ma yace "kai wan nan karar me haka?" da kyar ɗaya daga cikin su ya iya cewa "Oga muma bamu sani ba" a fusace Major yace "To ba zaku je ku duba ba, ko ni kuke so naje na dubo ne? Meeting muke karku ɓata mana shiri kuje ku duba menene da wuri in ma wani abun ne ku dakatar da shi da wuri" cikin sauri suka saki kafar Aryan suka nufi waje ba shiri suka ja birki sakamakon gigitatchiyar kara da suka sake ji wadda yasa har ginin ɗakin da suke ciki ya girgiza kamar zai rushe a sukwane suka toshe kunnuwan su dan karar ta gigita su shi kan shi Major toshe kunnen sa ya yi ya sunkuyar da kan sa kasa kamar mai jiran abu ya faɗo masa.
Jin karar ya ɗan lafa ne yasa Major ya yi kokarin fita daga ɗakin dan ya koma wajen meeting na su. A dai dai bakin kofa ya sake jiyo karar mai karfin gaske wadda ta fi na baya dan awan nan karon sai da ginin ɗakin ya fara rugujewa kan kace me gidan ya gauraye da karar har bin bindigu da karfi Major yace "Safras daman nasan wanna karan ba karar komai bace face karar tashin bom ɗin kwararrun sojoji ne daman na san sai ya zo sai dai ban kawo da wuri haka zai zo ba maza ku yi gaggawar ɗaure Aryan da sarka ku rufe Windows na dakin sanna ku rufe kofar kusa kwaɗo ta yadda bom ɗin zai ta shi da su su mutu a gaban sa ba yadda zai yi ya cece su yau zan ga hawayen Brigadier general Safras" ya kai karshen maganar tare da sakin dariya ya juya da sauri ya fita daga cikin ɗakin yana faɗin "Kuyi sauri ku fito ku shirya cetan ranku dan idan hasa she na gaskiya ne Safras ne da kan sa yazo ina da tabbacin mawuyacin abu ne ɗaya daga cikin ku ya yi rai da... Bai kai karshen maganar ba yaji diran mutun a kan kwano dai dai sai tin in da yake da gudu ya bar wajen ya shige ɗakin meeting na su.
Da karfi bgs ya diro a tsakiyar gidan daga kan kwanon tare da cire parashoot dake jikin sa ya yi wurgi da shi gefe ya mike tsaye fuskar nan tasa kamar bai taɓa sanin menene dariya ba a rayuwar sa sai huci yake jijiyoyin kan san nan duk sun mike jikin sa har tsuma yake tsabar shiga tashin hankali duk wani gashin jikin sa sun miƙe sai zufa dake keto ma sa daga kan sa yana furzar da iska mak bala'i zafi daga bakin sa kallon face na shi kaɗai ya isa ya sa mai karamin zuciya, zuciyar sa ta buga ya mutu idan kana da dakakkiyar zuciya kayi Arba da shi a wan nan ya na yi tofa zaka iya sumewa saboda tsoro.
Da gudu yaran Major 6 suka kewaye sa tare da sanya masa bindiga a kai a fusace ya sa hannu ya damko wuyar ɗaya daga cikin su ya ɗan yi baya nan take suka fara masa ruwan bullet sai ta musu wan da ya kama ya yi suka rinƙa har bin sa da bindiga cikin zafin nama ya anshi bindigar hannun wadda ya kama yaran Major suka har ba cikin, cikin da bara ya shammace su ya ciro ɗan karamin bom daga kugun sa tare da buɗe marfin ta ya jefa musu da gudu ya saki wadda ya kama ya bar wajen kan yaran Major suyi yunkurin barin wajen bom ya tashi da su nan take suka tar watse suka yi kaca kaca bgs na kokarin ɗana kuna mar bindigar ƴaran Major wasu suka fara fitowa daga ɗakuna daban daban daga cikin gidan bai farga ba sai ji yayi sun harbi bindigar hannun sa ta tarwatse kafin ya ɗago kai sun yi yun kurin har bin sa a sukwane ya kaucewa bullet ɗin ta su duba agogon hannun sa ya yi yana duba time da ta ragewa bom ɗin jikin Aryan da karfin ya furta "Oh shit" ya faɗi hakan tare da sai ta wani ɗan karamin na ura dake hannun sa kan kace me in da yaran Major ke tsaye ta tarwatse bom mai karfin gaske ta tashi ji kake booom tsaki yaja tare da tufar da yawu ya sanya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login