Showing 219001 words to 222000 words out of 363274 words
ta chikin glass har suka tada motocin su suka fice daga shopping ɗin waro ido waje tayi tana kallon su har suka kurewa ganin ta hawaye ne ya fara gangarowa a kan kuncin ta nan take tafara na damar dama bata biyewa zuchiyar taba da ta bishi sun tafi ta hakura da sayayyar yanzu ya zatayi tayiwa mijin ta laifi yayi magana ta ki bin maganar sa wai menene ya shiga kanta wayyo Allah" chikin kuka ta sanya hannu a aljihun jallabiyar jikin ta ta chiro wayar ta ta kira layin yaya Khalid bugu ɗaya ya ɗaga chikin kuka ta sanar da shi abun da yake faruwa dariya Khalid yayi kafin yace "kiyi sauri fitowa daga wajen ki ɓuya ta inda ba wan da zai ganki ganinan zuwa dan ina da tabbacin zai aiko a ɗauke ki amma bari muyi wasa da hankalin sa kaɗan" haka ko akayi chikin sauri ta fito daga wajen kamar yadda Khalid ya umarce ta ta boye ta bayan wani hospital dake kusa da wajen, bata fi 10mins da tsayuwa a wajen ba sai ga motar yaya Khalid,kiranta yayi awaya akan ta fito su tafi da sauri ta fito har tana haɗawa da gudu ta shiga motar Khalid suka bar wajen suna tafi ba jimawa sai ga Abdol ya dawo shi kaɗai a chikin mota yazo ɗaukan ta chikin shopping ɗin ya shiga batanan tambayar mutanen wajen yayi suka sanar da shi ta fita tun ɗazun juyawa yayi ya koma wajen motar sa ya ɗauko waya ya fara kiran layin Bgs sau biyu yana kira Bgs bai ɗaga ba sai a na uku ne ya ɗaga murya har rawa yake Abdol yace "sir madam fa bata wajen ta fita ta tafi" daga tsayan ɓangaren Bgs ya ja tsaki kafin yace "to ina ruwa na ka dawo ka chigaba da aikin gaban ka" yana gama magana ya katse kiran,shiru Abdol yayi yana tunanin hali irin na ogan sa wani lokaci abun ma mamaki yake bashi mutun ne kamar ba mutun ba bazaka gane me yake so me baya so ba yanzu fa shi yache nazo na ɗauko yarinyar nan amma danache bata nan ya nuna halin ko in kula bayan kuma kallo ɗaya zaka masa kasan ya ɗauki yarinyar da mahimmanci kai Allah dai ya shiryamin oga na amma gaskiya zan so ganin ya wanna wasan nasu zai kare shida sister nan tasa Allah ya sama kar a ganta har dare muga ya zaiyi dolene ma yaje neman ta ko dan iyayen su, da wanna tunani Abdol ya shiga motar sa ya bar wajen
to masu karatu mu koma Nigeria muga me sukeyi kafin mudawo kila yaya Khalid ya dawo mana da hiyanar mu
Kano
Zaune take saman sofa a palon habibin ta tana buga game da wayar sa ta sha kwalliya sosai jikin ta na sanye da dogiwar riga abaya pink color kanta babu ɗan kwali ta saki gashi har gadon baya tana taunar chewing gum tayi nisa chikin game da take bugawa kamar daga sama aka fisge wayar daga hannun ta a zafafe ta ɗago kai ganin yaya Aryan ne ya sanya ta turo ɗan karamin bakin ta tana faɗin "kai yaya Aryan me haka ne dan Allah" hararar wasa ya wurga mata kafin yace "wai ke baki da Aiki sai buga game to ki tashi kije ki ɗauki Kur'ani ki fara karatu zanje na duba wata criminal ina dawowa ba jimawa" miƙewa tayi tsaye chikin jin haushi tace "daman kana da wata budurwace zakache kana sona? Kallon ta yake da mamaki ya mai mai ta kalmar nata "budurwa" "eh mana budurwa ba yanzu kache zakaje ka duba ta ba to idan ma bata da lfy ne Allah ya sa ta mutu" dariya abun ma yaso bashi wai yar karamar yarinya da kishi to ko me takewa kishi yanzu oho ita da bata san menene Auren bama tukun nan,ganin yayi shiru ne ya san ta fasa ihu tana faɗin "to ni wlh babu in da zakaje sai dai muje tare kuma wlh in dai mukaje sai na kashe ta" Aryan dai yau yaga ikon Allah yama rasa mai zaiche shi da zaije hukunta zulaihat me ya haɗa shi da budurwa wani tunanine ya faɗo masa shin ko dai diyana bata san ma'anar criminal bane tuna hakan ya sanya yayi kasa da murya yace "my jidda nifa mai laifi zanje hukun tawa ni da nake dake ina ruwa na da wata ko kin taɓa kallona ina magana da wata mace ne, ina chewa wayata awajen ki take zama kin taɓa kallon hoto ko number mace? Idan ba su Aunty farida ba" jin haka ya sanya tayi shiru ta sa hannu ta rufe fuska ita adole taji kunya murmushi ya saki tare da chire hannun da ta rufe fuska da shi yana faɗin "my jidda sarkin rigima wato har yanzu baki dai na ba ko? Faɗowa jikin sa tayi tana dariya "ni dai ban taɓa kallon mutun mai kuka da dariya lokacin guda ba sai ke my jidda kuka baya miki wuya kamar yadda dariya ma bata miki wuya" ɗan karamin bakin ta ta kafa a sai yin kirjin sa ta gabza masa chizo har sai da yace "wash my jidda to laifin me kuma nayi? da akamin hukunci haka"chikin shagwaɓa tace "Allah yaya Aryan ka chika neman magana to ni gaskiya ko ina ma zakaje sai dai mutafi tare dan naji kace wadda zakaje hukun tawa macece kar ina zaune a gida kai kuma kaje daga hukunci ku fara soyayya" rungumeta yayi sosai yana shafa lallausan gashin kan ta yace "my jidda nifa ke kaɗai kin ishe ni bana son ƙari ki kwantar da hankalin" ɗago kan ta tayi daga kirjin sa tana kallon face nashi tace "yaya Aryan to yanzu dai ka askemin gashin nan dan wlh yana damuna" juyawa yayi ya kamo hannun ta ta baya ya haurar da ita bayan sa ya goyata ya nufi hanyar fita yana faɗin "muje ki rakani wajen mota kuma idan kika kuskura kika taɓa min wanna kyakkyawar bakin gashin nawa sai na miki hukunci gaba ɗaya jikin ki wanna kyakkyawar gashin naki yafi komai burgeni" "kai yaya Aryan Allah ni kuma ban son gashi ni gaskiya askewa zanyi" tayi maganar dai dai lokacin da suka fito harabar gidan "to shikenan kina aske gashin naki ni kuma zan Aure mace mai gashi domin ni inason mace mai gashi sosai" hannu ta sanya da karfi ta za gashin kansa har sai da yace "wash haba my jidda" yayi maganar tare da sauke ta ɗaure fusaka tayi sosai tana faɗin "yanzu duk dogon gashin kan nan naka bai ishe kaba sai....ba ta karisa magana ba tayi shiru tare da juyawa ta bashi baya, murmushi yayi kafin yace "oh my goodness my jidda wai fushi kikayi kenan? to shikenan yanzu dai muje ki rakani wajen mota idan na dawo sai na rarrasheki sauri nake yanzu" make kafaɗa tayi tana faɗin "aa ni ba zan je ba na fasa rakiyar kayi tafiyar ka" juyawa yayi ya nufi parking space yana faɗin "Allah ya sa na haɗu da wata baby kyakkyawa a hanya nayi wuff da ita" jin abun da yace ya sanya ta juyo da gudu tayi tsalle ta haye saman bayan sa tana dariya,buɗe baki yayi zai yi magana wayar sa ta fara ringing,chikin sauri ya fito da wayar daga aljihun sa dan ya san call ɗin Bgs kawai yake expecting chikin sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunne yana faɗin "hello my blood" daga ɗayan ɓangaren Bgs yace "ba sai kaje ba na sa an saki yarinyar" "What!!! Aryan ya furta azafafe tare da sauke diyana kasa daga bayan sa ya jingina da jikin motar sa "akan me zaka sanya a sake ta!? "Akoi dalili idan na gama da case ɗin zakaji" yana kai karshen maganar ya katse kiran juyowa Aryan yayi yana kallon diyana, gaba ɗaya yama manta bata da ɗankwali a kanta, "my jidda jeki ɗauko hijabi kizo mu tafi" "to" kawai tace ta wuce ta koma part nasu,binta yayi da kallo har ta shige ajiyar zuchiya ya sauƙe tare da ɗaga kai yana kallon sama jim kaɗan ta fito sanye da hijabi ɗan karami zuwa kirji,kallon ɗaya ya mata ya kawar da kansa tun bata kariso ba ya shiga motar gidan gaba mazaunin driver shiga ɗayan gefen tayi tana faɗin "yaya Aryan daman ka iya tuka motane? Yau kenan bazaka tafi da wayanchan masu mummunar fuskan ba" girgiza kai kawai yayi ya tada motar yaja suka nufi gate dan ya lura idan ya biyewa diyana sai su kwana a nan, a bakin gate na gidan ya tsai da mota tare da sauke glass ɗin motar ya dubi Shahram yace "ni kaɗai nake son fita kuma ba lallai mu dawo yau ba" yana kai karshen maganar ya ja motar da gudu suka fice daga gidan
Gudu yake shararawa sosai kamar zasu tashi sama chikin kankanin lokaci suka fita garin kano dai dai kafin su isa kwanan ɗan gora dake hanyar Zaria a wani ɗan karamin daji kusa da checkpoint na sojoji ya tsai da motar sa kusa da wata itacen mango dake fuskantar checkpoint ɗin, juyowa yayi yana kallon ta sai fakan kumbure kumbure kumatu take, murnushi ya ɗan yi kafin yace "my jidda sarkin shagwaɓa to yanzu kuma me nayi?ake fushi da ni" kara turu ɗan karamin bakin ta tayi tana wasa da ɗan yatsan hannun ta bata che da shi komai ba, jawota yayi ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa ya fara shafa bayan ta yana ɗan bubbuga ta a hankali kamar yar baby "my jidda wai me nayi ne? Kasa kasa tace "ba kai ne ka rinƙa gudu sosai da motar ba da yanzu mum mutu fa? ni fa bana son na mutu ban sa kayan sojoji na riƙe bindiga kamin hoto ba" ɗago habar ta yayi suna kallon juna kafin yace "In Sha Allah babu abun da zai faru ba zaki mutu ba har sai kin haifa min baby's dozin uku,dariya tayi sosai ta sanya hannu ta tana wasa da jikin rigar sa tace "yaya Aryan dozin uku fa kace kowani dozin guda goma sha biyu ne fa,tab ai ni ko baby uku ba zan haifa ba baby's biyu nake so ɗaya takwarar Ammi ɗaya takwarar Abba shike nan sun ishe ni" haɗe fuskokin su yayi chikin tsananin kaunar ta ya fara magana "gaskiya my jidda ina son baby's dayawa kuma ni bana son mata dayawa mace ɗaya ta ishe ni dan haka ki shirya ansan baby's koda 12 ne kin ji? Ɗago ido tayi suna kallon chikin idon juna yayin ta shi kuma yake goggoga mata karan hanchin sa a saman nata yana shafa ta da hannu ɗaya "Yaya Aryan...bai bari ta yi maganar da take son yi ba ya haɗe bakin su waje guda waro ido tayi waje tana kallon sa ɗayan hannu sa ya sanya ya rufe mata ido chikin dabara ya kwantar da kujerar motar da suke kai kwanchiya yayi da ita a jikin sa bakin su manne da na juna zuro ɗayan hannun sa yayi ta saman rigar ta tare da kara matse ta a jikin sa sosai wani daddaɗar ajiyar zuchiya ya sauke lokacin da hannun sa ya sauka saman lallausan tula tulan breast nata chikin sauri diyana ta kwache bakin ta daga nashi tana kokarin miƙewa daga jikin sa ya sake jawota a kule tace "yaya Aryan ni ka sake ni akan me zaka taɓa min nono?" mamaki ne ya kamashi ji yadda ta kira sunan su ko ajikin ta wanna dole ya mai data makaran ta da islamiya dan ba abun da ta sani jawo ta yayi ta faɗa jikin sa ya kankanme ta da kyau ya fara yi mata raɗa a kunne "my jidda wanna fa kayanane pls karki hana ni wasa da su namiki alkawari iya wasa kawai zanyi da su ko ganin su ba zan yi ba" shiru ta masa kamar bata ji me yace ba ta fara kuka kasa kasa,ba tare da ya lura da kukan nata ba ya fara kokarin zuge mata zip ɗin gaban rigar ta ji yayi ana knocking na glass ɗin motar ba tare da ya miƙe ba ya sanya hannun sa ya sauƙe glass na motar kasa, kamar daga sama yaji anja kofar motar da karfi an buɗe ana faɗin "fito munafiki ka sato yar mutane zaka mata fyaɗe ko? daman tun da naga kayi parking na motar ka a nan na fara zargin motar irin wanna shirgegiyar motar awan nan dajin dole ayi zargin ta ashe ashe zargina gaskiya ne maza ka fito yau taka ta kare!!" ɗan ɗago kan sa yayi yana kallon masu maganar wasu sojoji ne su uku a tsaye suna riƙe da gun tsaki yaja tare da mai da kansa ya kwantar dan gaba ɗaya jikin sa a mace kokarin miƙewa diyana take dan ta tsorata ganin sojojin nan jikin ta har kerma yake kara sautin kukan nata tayi sosai, hannun ta ya kama ya sake jawota jikin sa
chikin tsawa ɗaya daga cikin sojojin yace "lallai wanan ka chika marakunya bar gani ka fito daga babban gida kana yawo da wanna shirgegiyar motar yau zaka gane kuren ka ko uban ka bai isa ya fidda kai ba yau!!" shi dai Aryan ko kallon in da suke bai sake yi ba gashi yama kasa tashi gaba ɗaya jikin sa a mace, damkar kafar sa ɗayan sojan yayi yana jansa yana faɗin "ka fito daga chikin motar nan munafiki yau asirin ka ya tonu zaka gane kuren ka, ganin sojan nan ya damki kafar yaya Aryan yana jan sa ne ya sanya diyana ta fasa ihu tare da kara kankame Aryan ɗin ta
waro idon sa waje yayi tare da yunkurawa zai miƙe zaune jan kafar sa da sojan chan ya riƙe yayi yana kokarin zama tafiya sojan yayi luuuu ya buga kansa da jikin stearin motar da kyar sojan ya ja kan sa ya fitar ya tsaya a gefe tsaki Aryan yaja tare da mayar da diyana saman nata kujerar ya zaunar da ita chikin dashewar murya ya bawa diyana umarni akan ta zauna a mota karta fito, kafafunsa ya zuro waje kafin ya fito gaba ɗaya chike da jin haushi ɓata masa farincikin sa da sojojin nan sukayi ya ɗauke babban su da wani gigitatchiyar mari wadda sai da sanya shi tangal tangal kamar zai faɗi lokacin guda yaji duniya ta tsaya masa chak gaba ɗaya kunnen sa ta dai na jin sautin komai marin Aryan fa ba wasa ba, a zafafe sauran sojoji biyun suka ɗaga gun suka sai ta Aryan da shi suna faɗin "kneel down"
To masu karatu sai mun haɗu ranar Monday idan mai dukka ya kai mu ku bini bashin 2 page love u all
💋Duk Karfin Izzata 💋
💖The Talent Troupe Writer's 💖
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Book 2
Page 24
.... Kallon su Aryan ya fara yi daga sama har kasa kafin ya mai da kallon sa ga sauran sojojin checkpoint ɗin dake nufo su,tsaki yaja tare da komawa ya zauna saman kujerar motar chikin sanyin murya yace "my jidda ya isa kukan nan wai da me kike so ɗaya na jine da wayan nan da suka ɓatamin rai ne ko kuma da kukan ki?" Rage sautin kukan nata tayi chikin shesshekar ta fara magana "yaya Aryan mu koma gida ni tsoro nake ji ban san wajen nan ko kaɗan" yana kokarin yin magana wayanchan sojojin suka iso wajen babban chikin su ya sanya hannu ya damki kwalar rigar Aryan yana faɗin "wuce muje" ɗago kai Aryan yayi yana kallon sojan kafin ya mai da kallon sa saman wuyar rigar sa a razane sojan ya saki wuyar riga chikin tashin hankali ya duka gasa yana faɗin "innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Lefternal general Aryan" ba shiri sauran sojojin ma suka zube kasa dan sun san sunan Aryan fuskar sa ce dai basu taɓa gani ba tsaki Aryan yaja kafin yace "kuna kan dai dai ai bakuyi laifi ba in da nine na kama mutun zai yiwa yarinya fyaɗe to da yanzu maganar jana'izar sa ake ku tashi ku koma bakin Aikin ku amma ina son ku sani wanan matatace ba sato ta nayi ba" miƙewa sukayi chikin rawar murya babban su ya ɗan leko kai yana faɗin "sannu madan" hannu Aryan ya ɗaga musu chikin sauri yana faɗin "ba ta bukatar sannun ku ku wuce bakin Aikin ku kawai nace" jikin su har kerma yake suka wuce suka bar wajen
dawo da lallon sa yayi kan diyana "my jidda am sorry na wahalar da ke ko? Haka kawai yau naji ina son in tukaki a mota da kai na muyi tafiya mai nisa muna tafiya muna hutawa a hanya, Abuja nake son muje zaki iya jure tafiyar ne ko kuma in kira waya akawo helicopter mu karisa da shi?fa ɗowa tayi jikin sa tana kuka kasa kasa mai do da kafar sa chikin motar yayi tare da ɗaka kugerar motar ta dawo dai dai ya jawo kofar motar ya rufe ya tada motar,ganin ya kunna motar ya sanya ta ta tashi daga jikin sa tana kokarin komawa wajen zaman ta ta zauna da kyau "me yasa kika tashi? Ya tambaya dai dai lokacin da ya juya kan motar suka bar wajen wayar sa ya ɗauko ya fara kiran layin Bgs,wayar na ta ringing Bgs bai ɗaga ba sai da wayar ta kusa yanke wa sanna ya ɗauka manna wayar Aryan yayi a kunnen sa yana faɗin
"menene next? Daga ɗayan ɓangaren Bgs yace "kaje zuwa idan ka isa in da ya dace zan sanar da kai" yana kai karshen maganar ya katse kiran,ta chikin mirrow motar ya kalleta ta kwantar da kanta a jikin kujerar mota tana kallon hanya da glass na gaban mota,gudu yake shararawa sosai kamar zasu tashi sama lokacin kan kani suka isa
tsakanin zaria da kaduna