Showing 354001 words to 357000 words out of 363274 words

Chapter 119 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2548

su manya manyan idon sa yana kare musu kallo har cikin ransa yake jin kaunar yaran nan. Yana tsaye har suka gama gyara baby's suka sanya musu kayan sanyi masu bala'i kyau baby's sun yi kyau sosai, cikin sauri ya ansa baby ɗaya yana kallon sa kyakkyawa da shi sosai, kaman sa ɗaya da Aryan ɗin kamar an tsaga kara har kalar idon sa ash ga idon nasa manya manyan hancin nan kamar karas dogo mai tsini sai dai ɗan bakin sa kuwa sak na Diyana ne ba abun da ya saba girgiza kai Aryan yayi a ransa yana faɗin "Allah yasa kaman ta tsaya a iya fatar bakin ban da surutun dake cikin bakin" sai kallon baby yake yana zancen zuci har aka gama shirya ɗayan baby Dr ta ɗauka ta kalli Aryan ɗin tana faɗin "let's go sir" yana kokarin juyawa muryan Diyana ta katse su cikin tsiwa idon ta a rufe ta fara magana "Kuje ina munafuka ina ruwan ki da mijina? ku daman turawan nan haka kuke shiyasa fa ni bana muku dariya wlh ki ajiye min baby na ki fita a ɗakin nan tun ban tashi ba munafuka dan kin ga yaya Aryan kykkyawa zaki wani kashe murya ki manne masa kina wani rungume min da baby dan munafurci ki wani ce kuje, to kuje gidan uwar wa?" Ta kai karshen maganar tare da waro manya manyan blue eyes nata da suka sauya zuwa ja dai dai lokacin ɗayan Dr tazo zata mata alluran barci dan ta samu barci ta huta gajiya, kallon rai nin wayo tawa Dr kafin ta nuna mata hanya da hannun tana faɗin "Get out" juyowa Dr tayi ta kalli Aryan dake tsaye yayi mutuwar tsaye yana mamakin Diyana wai ba yanzu ta gama cewa bata son shi ba, har kan sa ya ɗau zafi wajen tunanin ta yadda zai shawo kan ta ta sake yarda da shi sai gashi ko 10mins ba'ayi ba ta fara kishin sa kuma, harcikin ran sa yaji daɗi sosai ya dubi Dr cikin harshen turanci yace "Ku kyalemin ita karku mata alluran tun da bata so duk wani abun da bata ku kyalemin ita kar ku mata tun da anyi babban ta haihu lafiya" zuba masa ido Diyana tayi tana kallon sa cike da so da kauna mai da alluran Dr tayi ita kuma ɗayan dr dake rike da baby kasan cewar bata ji me Diyana ta faɗa ba tun da bajin hausa suke ba sai ta dubi Aryan tace "Oga Please let's go now" satar kallon Diyana yayi kafin yace da Dr "No go and keep the baby" mamaki ya kama Dr tana kokarin yin magana Diyana ta rigata "Yaya Aryan me kake ce mata wallahi idan Dr bata ajiye min baby na sun fita a ɗakin nan sun dai na kallon kaba zan tashi in kwakwale musu ido" dawowa yayi kusa da ita ya kwatar da baby san nan ya ansa na hannun Dr kafin yace su fita su basu waje dan bai dan duk wani abun da zai ɓatawa Diyana rai haka ba dan sun soba suka gyara Diyanar suka fice daga ɗakin. Suna fita ta dube shi tace "Yaya Aryan Haihuwa akoi wahala" kakalo murmushi dole yayi dan yanzu ya dai na mamaki, ya dawo gefen ta ya zauna tare da manna mata kiss a goshi kafin yace "Sorry my jidda Allah ya miki albarka" riko hannun sa tayi tana faɗin "Yaya Aryan dawaye baby na yake kama? please ba zan iya tashi ba ɗan miko min shi in gani" a ran sa yace "Oh Allah kamar ba yanzu ta gama cewa bata son baby's ɗin ba har na fara tunanin yadda zan shawo kan ta ta yarda ta ansa baby's ɗin sai kuma gashi da kan ta ta ansa to masha Allah, Allah nagodema" a fili kuma sai yace mata "Ai baby biyu muka samu ba ɗaya ba" murmushi tayi sosai har dimple nata ya lotsa kafin tace "Yauwa Alhadulillah yanzu sunan yaya Aiman zaka sawa ɗayan ko ni yaya Aryan ka nuna min su mana ina son su sosai wallahi" cikin sauri ya ɗago mata ɗaya wadda ya fara faɗowa duniya dan dr ɗin sun sa masa shaidar shi ya fara faɗowa duniya a hannu suka ɗaura masa wani ɗan kyalle ja. Shafa kumatun baby tayi kafin tace "Yaya Aryan kamin wayo da kai babyn yayi kama" murmushi yayi yana kokarin yin magana su Abba suka shigo mikewa yayi da sauri ya taro su Abba yana murmushi ya miƙa musu baby har rige rige su Ammi da Hiyana suke wajen ansan baby ita kuwa Aunty farida wucewa tayi ta ɗauki ɗayan baby dake kwance tana murmushi bakin ta yaki rufuwa. Kan kace me family sun cika ɗakin sai murna suke duk wanda kaga face nashi zakaga tsantsan farinciki da annashuwa.

.....ganin bgs bai shigo ba ne yasa Aryan ya ansa baby ɗaya ya fice daga ɗakin. Can ya hango bgs tsaye ya harɗe hannu a kirji ya dukar da kan sa kasa da alama wani tunani yake da fara'a Aryan ya karisa wajen hannun sa rike da first born baby ɗin. Jin motsin alamar tafiya yasa bgs ɗago kai ganin Aryan ne yasa ya saki hannayen sa tare da sakin murmushi ya kariso ya tari Aryan ɗin yana faɗin "Alhadulillah Alhadulillah" hannu yasa ya yana son ansan baby bai iya ba murmushi Aryan yayi yana faɗin "Ba sai ka ɗauka ba tun da baka iya ba gashi ma takwarar ka ne" girgiza kai bgs yayi kafin yace "No dole na ɗauki takwara ta" ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya ansa baby ya juyawa baby kai yafi ɗaga ta wajen kafofin yaron haka suka zauna saman kujerun dake wajen, . Sosai bgs ya kurawa baby ido na tsawon mintoci kafin ya ɗago ya kalli Aryan yace "Aryan yaron nan yayi kama da kai over ba abun da ya raba ku har hancin da kalar ido, har cikin rai na nake jin kaunar babyn nana sosai ina ganin kamar kai ne wallahi" Aryan dai baki ya ki rufuwa sai murmushi yake yace "In Sha Allah ita ma sister ta kusa samu" nan take face ɗin bgs ya sauya cikin karyewar zuciya yace "Aryan kullun sai Eshat ta ɓuye min tayi kuka ban san ya zan yi ba ban son ganin ta cikin damuwa, ku taya ni da addu'a ni kai na ji nake kamar zan yi kukan idan tana yi bata son ɗaga min hankali hakan yasa take ɓuya tayi kukan ta sai dai bata san ina ganin ta ba ina shiga damuwa sosai idan naga tana kuka gashi dukkan mu lafiyar mu kalau ba wata matsala" dafa shi Aryan yayi yana faɗin "Muna taya ka addu'a In Sha Allah nan ba da jimawa ba zata samu ciki kaji?" shiru bgs yayi bai sake magana ba shiru shima Aryan ɗin yayi kowa da abun da yake tunani. A wan nan yana yin su Abba suka fito suka same su kallo ɗaya Abba ya musu ya fahimci meke faruwa da man kuma tun da yaga Aryan ya fita da baby yasan haka zata iya faruwa "Aryan idan har Diyana lafiyar ta lou ita da baby's ɗin dukka to ya kamata mu wuce gida ko?" Cewar Abba Aryan na kokarin yin magana bgs ya riga shi da cewa "Abba baby's naji ka ce kenan ba baby ɗaya ta haifa ba?" "Eh twins ta haifa" Abba ya bashi amsa cool murmushi ya saki kafin yace "Mafarkin Eshat ita har yan huɗu ma take mafarki kullun bata da wani magana sai yaya prince nayi mafarkin na haifi twins ko triplet kullun aiki ɗaya" tuna abun da ya faru a labour room Aryan yayi ya girgiza kai yana faɗin "Ya Allah dan tsarkin mulkin ka Allah ka bawa sister baby's masu Albarka yan uku ko yan huɗu Allah ka sauwaka mata nakuda" Amin Abba ya amsa da shi dai dai lokacin idon sa ya sauka kan yadda bgs ya rike baby cikin sauri yasa hannu ya ansa baby dan bgs ya lankwasa masa wuya, ansan babyn Abba yayi ba tare da yayi magana ba ya wuce ɗakin su Diyana. A tare bgs da Aryan suka miƙe suka nufi office na Dr dan suji zasu iya wucewa gida.

After some minutes suka fito Aryan ya shiga labour room ɗin shi kuma bgs ya wuce wajen motocin su. Jim kaɗan Aryan ya fito ɗauke da Diyana a kafaɗar sa ya wuce wajen motocin su gaba ɗaya family suka biyo bayan sa sai mita Diyana ke masa ita ya sauke ta, ta ɗauki babys nata kar Hiyana taje ta buge mata su a shirmenta shiko Aryan banza yayi da ita yayi kamar bai ji taba ya wuce da ita cikin motar su ya sanya ta gidan gaba ya shiga yayiwa motar key yana kokarin barin Hospital ɗin. Ganin zasu tafi ba tare da baby's ɗin ta bane yasa ta fasa masa ihu tana faɗin "Ni yaya Aryan ka tsaya na ansa baby's ɗin na kana gani fa Hiyana aka bawa ɗaya ta rike ko iya rikewa bata yi ba kar taje ta jefar min da baby dan Allah ka tsaya na ansa ni bana son Hiyana ta rike min" a fusace ya juyo zai wanka mata mari sai kuma ya dakata ganin yadda ta waro ido tana kallon sa rai a matukar ɓace yace "Wallahil azim ba yanzu ba ko gaba idan kika kuskura ki kayi wa sister magana akan baby's nan ko karta ɗauka miki ko wani abu makamancin haka Allah kinji na rantse miki sai na miki dukan mutuwa kikace baki da hankali ko? ke ko halin da take ciki na rashin samun Haihuwa bai ci ki tausaya mata ki bata baby ɗaya ba Allah ba zan yi kaffara ba ki kuskura ki yiwa sister wata magana akan yaran nan zakiga yadda zanyi da ke ko kashe su zata yi ki kau da kan ki ni ban ma taɓa tunanin rashin hankalin ki ya kai har haka ba Diyana yar uwar ki na jini tana son ku fiye da yadda take son ran ta amma har ki iya buɗe baki dan yanzu kin samu yara ki ce karta gefar miki da baby kin manta lokacin da ta riƙe ki ke da kan ki kenan? kin manta lokacin da take kuka take haukacewa akan ku ko?" shiru Diyana tayi tana mamaki tare sa danasani "yau yaya Aryan ne ya kira sunana da bakin sa lallai na tabbaka babban kuskure" tayi nisa chikin zancen zucin da take bata ma san lokacin da ya kunna mota ya bar asibin ba.

Suna isa gida ya fito ya ɗauke ta cak ya nufi bedroom ɗin Ammi da ita. Yana shiga ya direta saman gado ba tare da ya kalle ta ba ya fice daga ɗakin ransa a matukar ɓace shiru tayi tana tunanin me ya dace tayi masa dan ya sauko bata taɓa ganin sa cikin irin ɓacin ran nan ba. A haka su Hiyana suka iso suka same ta ba tare da sun lura da halin da take ciki ba da fara'a Hiyana ta haye gadon hannun ta rike da baby tana faɗin "Diyana kina ganin saboda babyn ki yau na koyi rike yara fa kai amma fa babyn nan yayi kama da yaya Aryan sosai da sosai idan kika ganshi ma zaki ce yaya Aryan ne kike gani" kakalo murmushi dole Diyana tayi tare da riko hannun Hiyana ta fara hawaye tana faɗin "Kiyi hakuri Hiyana" waro ido waje Hiyana tayi kafin tace "Diyana menene kuma abun kuka? Ke da zaki yi murna Allah ya baki yara har biyu lokaci guda" rungumeta Diyana tayi tana hawaye cikin sauri Hiyana ta tureta tana faɗin "Ke ni ban son shirme kin danne min baby akan me zaki wani rungume ni bayan kin san ina riƙe da baby so kike ki danne min hancin yaro ko? Dan kinga hancin sa yafi naki tsini ko? To baki isa ba ko me zaki yi yaya Aryan dai ya fiki kyau" goge hawayen face nata diyana tayi tare da kakalo murmushi tace "Kiyi hakuri Hiyana daɗi ne yasa na rubgume ki" gyara zama Hiyana tayi tace "Ina su Aunty Zahra naga ban gansu a ɗakin ba" "Ina jin suna ɗakin Innar yaya Bello nima da na shigo ban gansu ba" Hiyana zata sake magana Ammi ta shigo tana faɗin "Ke Diyana tashi muje bayi agasa miki jiki a miki wanka kizo ki bawa baby nono suna jin yinwa" ba musu Diyana ta sauko daga gadon dan taga yadda aka yiwa su Zahra, ita kuma Hiyana sai murmushi take tana kankame da baby sai kallon face ɗin babyn take ji take kamar ta mai da shi cikin ta saboda so.

Bayan an yiwa Diyana da baby's wanka Ammi da kan ta tazo ta ɗauki baby ɗaya ta ɗaurawa Diyana akan cinyar ta akan ta bashi nono kallon su Aunty farida tayi taji kunya gaba ɗaya family Abba kowa na ɗakin ban da mazan da kuma familyn Abbo su basa nan amma su Aunty farida duk suna nan kunya taji ta kasa fito da nono kikewa Aunty farida tayi tazo ta fitar mata da nonon ta sawa baby a baki kamar jira Baby yake ya kama nono ya fara sha nan take Diyana ta fara hawaye tana son yin kuka da karfi amma batason tayi abun da zata sake ɓatawa yaya Aryan rai duk da baya ɗakin ta san suna da camera zai ganta. Hakan yasa ta daure ta jure tana hawaye har baby ya sha ya koshi Aunty farida ta anshe sa Hiyana ta miƙa mata na hannun ta shima Aunty farida ta sa masa nono a baki ya fara sha sosai Diyana ke kuka har shima ya koshi san nan Hiyana ta anshe sa Aunty mardiya ta kawo mata firfesun kayan ciki mai romo romo da tea mai kauri ta ansa ta fara ci.

Misalin karfe 9 na dare gaba ɗaya family kowa ya koma ma kwancin sa ɗakin ya rage Diyana Hiyana Ammi sai baby's Zahra na ɗakin Ummi ita kuma Lamrat ta koma ɗakin Innar Bello. Da sallama yaya Aryan ya shigo ɗakin still har lokacin ran sa a ɓace ciki ciki ya gaida Ammi da fara'a Ammi ta ansa san nan ta fice palo ta basu waje sai murmushi Hiyana ke yi ta gaida shi ganin fara'ar dake face ɗin Hiyana yasa ya ɗan saki fuskar sa kaɗan ya amsa mata gaisuwar nata cikin sauri ta mike ta ɗauki baby ɗaya tana faɗin "Yaya Aryan bari naje wajen yaya Prince na kai masa baby ya kara gani" samun waje yayi gefen gadon ya zauna yana faɗin "To sister ko ince maman baby sai kin dawo" dariya tayi ta nufi hanyar fita tana faɗin "Amma yaya Aryan wallahi naji daɗi da kace min maman baby na gode" ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin.
Hiyana na fita yasa hannun ya ɗauki ɗayan baby yana kallon sa a hankali ya furta "Little Safras" ganin tun da ya shigo ɗakin bai kalli in da take bane yasa ta matso ta kwanto da kan ta a saman bayan sa tare da sakin kuka tana faɗin "Kayi hakuri yaya Aryan nasan nayi kuskure amma na tuba bazan kara ba" shiru ya ɗan yi kafin yace "Shike nan" kara kankame sa tayi yana kuka, a hankali ya kwantar da baby daga ɗan gefen su ya juyo ya rungumeta yana ɗan bubbuga bayan ta yana faɗin "Sarkin rigima ba, to yanzu me abun kuka kuma?" Kara shigewa jikin sa tayi tana faɗin "Dole nayi kuka mana yauce rana ta farko dana taɓa ɓata maka rai har ka kira sunana abun da baka taɓa yi ba" shafa kan ta yayi kafin yace "Dole rai na ya ɓaci my jidda bakiga halin da sister take ciki bane kuma duk ɓacin rai da tashin hankali da sister zata shiga ki sani ɗan uwana ma zai shiga idan ɗan uwana yana cikin damuwa ko ruwa bazan iya sha ba yau da ɗan adam na bada Haihuwa ko kuma akoi wata hanya da ɗan adam zai samowa ɗan adam ɗan uwan sa Haihuwa wallahi da na samowa sister koda hakan zai zama shine abun da zan yi ta karshe a rayuwa ta kenan" "Hakane yaya Aryan nayi kuskure kayi hakuri kaji?" Jan dogon hanchin ta yayi yana murnushin ba tare da ya sake magana ba shiru sukayi dukkan su ba wanda ya sake magana.

A ɓangaren Hiyana kuwa tana fita bedroom nasu ta wuce sai murna take. Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga bedroom ɗin bgs na kwance saman gado yana sanye da kayan barci riga da wando a jikin sa idom sa a lumshe kamar mai barci. Jin sallamar ta yasa ya ɗago kai tare da waro manya manyan idon sa waje da sauri ta haye saman gadon tana murmushi tana faɗin "Yaya Prince tashi ka kalli babyn yaya Aryan wan nan shi ne second born fa Diyana tace min babban shi ne takwarar ka wan nan kuma takwarar yaya Aiman" miƙewa yayi zaune yasa hannu ya shafi face ɗin babyn kafin ya mai da hannun sa kan nata face ɗin a hankali yake shafa kumatun ta cike da so da kauna yace "Ina kaunar ki my Eshat" kara karfin murmushin nata tayi kafin ta manna masa kiss a kumatu tace "Yaya Prince nima ina kaunar ka sosai" zai yi magana baby ya fara ƙoƙarin yin kuka kallon sa tayi yayi da shima ita yake kallo "Je ki kai shi wajen maman shi ya sha nono sai ki dawo ki bawa yaya Prince na shi" "Kai yaya Prince ka bari na kwana a can mana gobe zan zo da asuba na baka kaji?" Lumshe ido sa yayi a hankali ya sake buɗe su cike da sha'awar ta yace "To shike nan in dai hakan zai saki farinciki to ki kwana da babyn kinji? Sai da safe" ya kai karshen maganar tare da manna mata kiss a saman lallausan lips nata, dirowa tayi daga gadon dan babyn yana son yin kuka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login