Showing 3001 words to 6000 words out of 363274 words
Yusuf kuwa sanye yake chikin wandon jeans baki da t-shirt ash ya gyara gashin kan san nan kamar wani balarabe, Khalid na sanye chikin blue jeans da white t-shirt Ahmad ma na sanye chikin blue jeans da black t-shirt dukkan su sunyi kyau sosai "wae ina Aiman ne Hisham ya tambaya yana kallan Yusuf " guntun tsaki Yusuf yaja yana faɗin oh bari dai na kirasa awaya muji chiro wayar sa yayi daga aljihu yanufi waje yana kiran layin Aiman ɗin
Hotel
Aiman na chikin barchi yaji wayar sa na ringing wani dogon tsaki yaja, batare daya buɗe ido ba yasa hannu yana lalubar wayar da kyar ya isa ɗauko wayar dan har kiran ta kusa yan kewa da kyar ya iya ware idon sa dan barchin daya masa yawa picking call ɗin yayi yana faɗin wae dan Allah Yusuf me namaka ne da kake ta'kurawa rayuwata "Yusuf yace amma gaskiya Aiman baka kyauta ba dan Allah menene hakan wato ma barchi kaje kake koh to kazo mutafi ɗau'rin auren lokachi yayi chewar Yusuf, a fusache Aiman yace "bazan jeba yana yana kai karshen maganar batare daya jira amsar yusuf ba ya katse kiran yayi wurgi gefe da wayar ya chigaba da barchin sa
Yusuf kuwa Aiman na katse kiran ya juya jiki ba kwari ya koma chikin palon a zuchiyar sa yana faɗin wlh yau Aiman da nine yayan ka da sai nayi maganin ka, wan nan wani irin wulakanchine kan chine sae kace ba tare suka taso da Hisham ba a sanyaye ya shiga chikin palon, Hisham na ganin sa yace"Aiman ɗin yace bazai zo bako,shiru Yusuf yayi dan ban san amsar da zai bawa Hisham ba kunyar haɗa ido da Hisham ɗin yake ji, dafa kafaɗarsa Hisham yazo yayi yana faɗin karka damu yusuf nasan halin ku gaba ɗaya SO duk wani abun daya da suke gudun zuwa aure nawa nasa,ni ban ma taba tunani daman zaku so aure naba,kadai na damuwa ngd sosai da zuwan da kukayi, kasani DON da Aryan Bawai basu sona bane yasa suka ki zuwa jiya da daddare DON ya turomin 1m a matsayin gift haka Aryan ma 1m ya turamin to kaga bawai basa sona bane kawai sudai a nasu ganin dakuma tunanin su duk wan da ya raɓi mace to yaza mai rauni sukuma kasan basa san mauni sunfi san kullun su ji su zam zam,"murnushi kaɗan yusuf yayi zai yi magana Hisham yace "No badai yanzuba, yanzu kam muje lokachi yayi ana jiran mu, jerawa sukayi gaba ɗayan su suka fito harabar gidan,
su yusuf suka shiga motochin da suka zo dasu Hisham kuwa yashiga nashi motar,suka yiwa motochin key, security ya wangale masu gate da gudu suka danna hanchin motochin waje sosai suke gudu dan sunyi latti kai tsaye babban masallachin jummaa suka nufa a harabar masallachi sukayi parking dub bannin jamaa ne suka halak chi ɗaurin auren kama daga minister's governors members har shugaban kasa muhammadu buhari yazo ɗau rin auren dashi da Shugaban kasa mai jiran gado tinibu, misalin karfe 2 dai dai na rana dubbanni jama'a suka she'da ɗau rin auren Hisham Nasir alkali tare da matar sa ilham Abdussalam, ana gama ɗau rin aure Yusuf ya dawo chikin mota da sauri dan yaji jama'a nata faɗin ina yayan Abubakar saraki ma sunzo bikin, yana zaune chikin mota yana jin jama'a na ta neman family Abubakar saraki,amma yayi kamar bar ji ba, buɗe kofar motar da Yusuf ke chiki ango Hisham yayi yashiga ya zauna yana faɗin "yanzu Yusuf abun da kayi ka kyauta eh " ɗaure fuska Yusuf yayi yace to me kuma nayi "ka fini sanin me kayi ae ka dubi yan da jama'a ke naman ku kuzo kuyi hoto kowa Burin sa yayi hoto da family Abubakar saraki, amma ka watsa musu kasa a ido koh "kaga Hisham idan kagama dana ka jama'a mutafi dan ni yanzuma zan wuche kano, Hisham zaiyi magana Khalid ya buɗe kofar motar yashigo yana faɗin "Hisham me kuma ka zauna kake a nan baza kaje kutafi walimar bane "yanzu Khalid kuna nufin da gaske baza kuje walimar nawa ba Hisham yayi tambayar yana kallan fuskar Khalid, Khalid zai yi magana Yusuf ya riga shi da chewa "gaskiya ba zamuje ba ae nafaɗama iya ɗau rin aure kawai mukazo dan haka yanzu zamu wuche tun da angama abun daya kawo mu, shiru Hisham yayi yana tunani, ganin yanayin da Hisham ya shi gane yasa Khalid chewa, " No Hisham dole zamuje walimar taso muje ga jamaa na chan na jiran mu,jiki ba kwari Hisham ya fito daga motar Khalid na rike da hannun sa suka bar Yusuf a chikin motar,
Fito Yusuf yayi ya kira sojojin sa tare da basu umarnin akan su wuche Airport dashi, da sauri suka shiga mota suka wa motochin key suka bar masallachi sae tsaye Airport suka nufa, jirgin kasuwa Yusuf yabi yabar wa su Khalid jet ɗin Aryan a Airport ɗin tare da sojoji 2 ya tafa ya nar biyu su taho dasu Khalid,
Karfe 3:45 jirgin su ba yusuf ya sauka a malam Aminu Kano international Airport,bai sanar da kowa zu'wan nasa ba ba wan dayazo ɗaukan sa motar haya suka hau shida sojojin nasa suka nufi gd, a bakin gani gidan sarki mai motar ha'yan ya ajiye su sauƙa Yusuf yayi ya biya sa kuɗin sa yanufi chikin gd sojojin na biye dashi, ɓangaren sa yanufa natare daya shiga chikin gd ba a bakin ɗan karamin gate na shiga ban garen nasa sojojin suka tsaya shi kuma ya wuche chiki, wanka yayi a gur guje ya zura jallabiya ya kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba dashi
Aban garen su Khalid kuwa ansha walima duk chikin su Khalid ne kaɗai ya halak chi walimar karfe 4 dai dai a ka tashi taron, wajen holl ɗin Khalid yafito da sauri yana kiran layin Yusuf, wayar tayi ta ringing sai da ta kusa katsewa Yusuf ya ɗaga chikin muryan barchi yace,"hello "ina kake ne Yusuf lokachin tayi fa yayi "ina kano mana " kano kuma Khalid ya tambaya yana riƙe haɓa "wani dogon tsaki Yusuf yaja yana faɗin kaga Khalid dan Allah ka kyale ni wlh bar chi nake kata dani " to yanzu Yusuf mota kake so mubi zuwa kano ne kokuma me menene dazaka dafi kabar mu "oh my god nima Khalid bada jet na zaba jirgin kasuwa nabi jet ɗin na Airport na bar muku, yana gama faɗin hakan ba tare daya jira amsar Khalid ba ya katse kiran, bin wayar da kallo Khalid yayi yana faɗin ya Allah ka shirya min yaran bappa ba mutane ne sai kache wasu aljanu bazaka taba gane kan suba in sun juya ba mai iya juyo su, layin Aiman yafara kira again har ta katse Aiman bai ɗaga ba, tsaki Khalid yaja yasake kira, wayar nata ringing har ta kusa katsewa Aiman yayi picking, "ina kake Aiman Khalid ya tambaya a fusace, chikin muryan barchi Aiman yace " wai dan Allah menene naha bazaku bar mutun yayi bar chin sa ba "au barchi ma kake ke nan to wlh sai dai ka kwana a Abuja dan tafiya ta,zanyi, wani dogon tsaki Aiman yaja yana faɗin to a sauka lfy san nan ya katse kiran, Khalid kamar yayi wurgi da wayar dan haushi haka yasake hakura yafara neman layin Ahmad kira ɗaya Ahmad yayi picking " ina kake chewar Khalid "haba Khalid ni karamin yaro ne da zaka min irin wan nan tambayar, a fusace Khalid yace to wlh idan ba kazo Airport nan da 20 mnt ba tafiya ta zanyi na bar ku " to yaya Khalid a Allah ya sare hanya yana kai kar shen maganar ya katse kiran, a fusache Khalid ya juya yanufi motar su yana faɗin wlh ku kam idan mutun ya biye muku zaku kashe sa da bakin chiki, chikin mota yashiga driver ya ja motar da gudu suka nufi Airport, abun ma maki ko da yaje Airport ɗin zaune yasamu Aiman da Ahmad chikin jirgin suna jiran sa dan bakin chiki ko sannu bai che musu ba ya shiga jet ɗin shima ya zauna suma ko sannu basu che masa ba har jirgin su ya ɗaga
Karfe 6 na yamma dai dai jirgin su yayi landing a malam Aminu Kano international Airport kano basu wani ɓata lokachi ba suka fito shiri suka tsaya sai yanzu suka tuna basu sanar da zu wan su ba wan daya zo ɗaukan su wuche Aiman yayi ya fita Airport ɗin ya tari motar haya yashiga abunsa, ganin Aiman shiga motar haya ne yasa suma suka fito suka tari motochi biyu na haya suka hau suna nufi gd a bakin gate sukache da mai motan ya tsaya suka sauka,suka Biya shi suka nufi chikin gd,kowa ya nufi ɓangaren sa Khalid kuwa yanufi babban gate ɗin ya shiga chikin gd a dai dai bakin gate ɗin ya haɗu da Umar da haidar sosai suma suke kama da su yusuf ko ba'a faɗa ma ba kasan kannen sune "kai haidar ina yusuf Khalid ya tambaya yana kallan fiskar haidar "haidar yache nima ban sani ba yaya Khalid daman yaya yusuf na gidan nan na,juyo da kallan sa Khalid yayi kan Umar dake tsaye yana mur tuƙe fiska "kai Umar awani ban gare Aunty farida take,kara ɗaure fuska yayi yace "kai yaya Khalid dan Allah ka shiga chiki ka duba mana mu ka daina tambayar, mu tana gama faɗin haka yaja hannun Haidar suka nufi waje, baki buɗe Khalid ke kallan ikon Allah a zuchiyar sa yake faɗin, gaba ɗayan su ƴa'ƴan bappa halin su ɗaya ba yaran ba ba man yan ba, juyawa yayi shige chikin gida,
Wani katafaren Falo na Al'farma Khalid ya doka sallama,haɗuwar falon ya zarce tunanin me tunani yaji komai na furniture,wasu hadaddun Sofa set ne,Launin Milk colour,masu numfashi,a tsakiya kuma akwai Sofa tabls,daga gefen Hagu,Tv stand ne,baka jin sautin komai sai Sanyin A.c dake ratsa sassan jiki, yan matane 3 ke tsaye a tsakiyar palon suna goge goge da alama kuyangu ne,har kasa suka duƙa suka gaida Khalid fuska ba yabo ba fallasa ya amsa yana tambayar su "ina Ammi, "tana chikin ɗaki suka amsa masa, bai jira sun kai karshen maganar ba ya haura stair case ɗin,wani ɗan karamin haɗaɗɗen palo ne a saman mai ɗauke da sofa set 1 ash colour atsakiya kuma a kwai sofa table gefen dama kuwa wani makekiyar Tv awajen,palon ɗauke yake da ko'fofin betroom's 4 a chikin sa,babu kowa a palo sai sanyin A.c dake tashi bakin kofar betroom ɗin Khalid yanufa sallama yayi ya gyara tsayuwar sa yana jiran a masa izinin shigowa almost 7 mnt kafin a amsa masa sallamar tasa tare da izinin shigowa, tura kofar yayi ya shiga
Wata kyakkyawa mata che sosai, kamannin ta ɗaya da DON,fuskarta ɗauke da murmushi,a zaune take saman tulu irin na gidan sarauta,babbar macace A ƙalla tayi 45 years,irin hajiyoyin nan ne wanda naira ta zauna masu,jikinta na sanye da tsadadden cord lace,wanda akayi mata bubu gown dashi,duka hannayenta da wuyanta,Kayan adone na Zallar zinayi, karisawa chiki Khalid yayi ya zauna a kasa a gaban ta,chikin ladabi da girmama,yace "barka da hutawa Ammi,shafa kansa Ammi tayi yace "baba saukar yau she "yanzu nan muka zo Ammi "to zuwa babu sallama,ina sauran yan uwan naka, "prince da Aryan basu zo ba suna London "ni basu nake tambaya ba ina ruwa na dasu,murmushi Khalid yayi daman da gangan ya kawo wa Ammi zan chen DON "baba ba kache komai ba ko dai kai kaɗai kazo ne "aa Ammi ni da su Yusuf ne amma ae kin san halin su ni ko in da suke ma ban sani ba "to ka sanar da Salma kun zone "aa Ammi kamar yadda bamu sanar ɗa ku ba haka ba wan da muka faɗawa "to yaka mata ku sanar da ita dan kaga kuka ɗai gare ta ku rinka tau saya mata "to shike nan Ammi zanyi yadda kika che amma ina Aunty farida "inajin tana bangaren Ummi,mikewa yayi yana faɗin to Ammi bari na dubo ta, "ok kawai Ammi tace, yana kokarin fita daga ɗakin wata kyakkyawar budurwa tashigo wadda a shekaru bazata wuche 16 ba kyakkyawa che sosai duk kaman nin su ɗaya dasu DON da gudu tatafi ta faɗa kirjin Khalid tana faɗin "oyoyo yaya Khalid, rungume Khalid yayi shima yana faɗin "oyoyo Auta oyoyo, ina kika fito hakan nan sai kam shi kike " turo baki Zahra tayi tace daga wajen Aunty farida nake "ina take Aunty farida yayi maganar yana raba jikin sa da nata " tana ɓangaren Ummi "ok to muje ki rakani "aa yaya Khalid ni tun danaga ka nasan ba kai kaɗai kazo ba, nasan su yaya prince ma sun zo ni bazan fita ba ina tsoran su "murmushi Khalid yayi yana faɗin"kai Auta tsoran me kuma ai dani zamuje "Allah yaya Khalid shiyasa nafi son ka dan duk gidan nan kai kaɗai ne mai sona " aa Auta kowa na gidan nan na son ki "aa yaya Khalid badai kowa ba Aunty Maryam da yaya prince da yaya Aryan da yaya Aiman, "girgiza kai kawai Khalid yayi ya ja hannun ta suka nufi waje yana faɗin,Ammi mun tafi, Ammi dai murmushi kawai take tana binsu da ido..✍️
Pls more like comments and share
*DUK ƘARFIN IZZATA*
_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*
💖The talent troupe writer's 💖
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*Episode 2*
Khalid rike da hannu zahra suka fito daga part ɗin,Ammi suka nufi part ɗin Ummi suna tafiya suna hira kamar wasu friend, a dai dai kofar da zata sada su da part ɗin Ummi, su kayi karo da yusuf fiskar nan a daure kamar bai ma san menene dariyaba, nan take jikin zahra ya hau kerma, murya na rawa tache "inawuni yaya yusuf,bai bai amsa ba ya ra ɓa ta gefen su zai wuche, da sauri Khalid ya damki dam tsen hannun sa, juyowa Yusuf yayi yana kallan chikin idon Khalid ɗin "me kuma kake kallo na eh idan bazaka amsa gai suwar Zahra ba ni ba yayan ka bane dazaka raɓa gefe'na ka wuche " a kule Yusuf yace sorry ykk "ban sani ba Khalid ya faɗa yana sakin hannun Yusuf ɗin,aiko kamar jira yake Khalid yasake sa da sauri ya wuche ya barsu tsaye, dawo da kallan sa Khalid yayi kan Zahra dake tsaye kamar zatayi fitsari a wando saboda tsoro"menene Auta,chikin rawar murya Zahra tace,"yaya Khalid shiyasa fa nache maka kai da Aunty farida da Aunty mardiya ne kawai kuke sona sai Aunty salma, kana ganin yaya Yusuf ko gaisuwa ta bai amsa ba bare ma ya tambayeni ko ina lfy,ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kakalo murmushin dole Khalid yayi dan ko shi kansa Yusuf ya ɓata masa Rae "karki damu Auta muje mutafi hai ki rabu dasu tun da ni ina son ki kinji yayi maganar yana shafa kanta "to shike nan yaya Khalid muje, chiki suka nufa a kofar balon Ummi sukayi sallama kafin su shiga komai na chikin palon Ummi irin na Ammi ne har colour komai iri ɗaya
Wata kyakkyawar mata che zaune saman sofa mai zaman mutun 2 a gaban ta kuwa sofa table ne dake ɗauke da kwan dan fruit mai kyan gaske a hankali take gatsar Apple ɗin take hannun ta fara che itama tas kaman nin ta ɗaya da yusuf a kallan zata kai 36 years, da gudu Zahra ta tafi ta faɗa jikin ta tana faɗin Aunty "farida na dawo "kai Auta zaki balla ni ai, dari Zahra tayi tana faɗin to Aunty na tashi, karisa shigowa chikin palon Khalid yayi ya zauna saman sofa mai ma zaunin mutun 3 yana faɗin "Aunty babba barka da hutawa,murmushi Aunty farida tayi kafin tace ai kune manya yanzu na bar muku girman, da sauri Zahra ta miƙe zaune tana faɗin "Aunty farida harda ni, ki kabawa girman "eh Auta har dake mana,tsalle Zahra tayi, tana faɗin nima na zama babba yan zukam, murmushi kawai Khalid da Aunty farida keyi suna kallan irin farin chikin da kanwar tasu ke chiki
Wayar Aunty farida dake zaune kusa da Zahra yafara kara alamar shigowar kira,da sauri Zahra ta ɗau wayar tana faɗin ni zanyi picking call ɗin ni zanyi picking call ɗin," to Auta yimana chewar Aunty farida tayi maganar tana kokarin ajiye Apple dake hannun ta a chikin kwandan fruit ɗin, takawo wayar Zahra tayi dai dai sai tin fuskar ta zatayi picking call ɗin, a sukwane tamiƙawa Aunty farida wayar ta hannun ta har kema yake, ansar wayar Aunty farida tayi tana kallan Zahra da mamaKi, dariya Khalid yayi kafin yace Auta lfy irin wan nan riki chewa haka DON ko Aryan ne suka kira wayar ko, Zahra dai shiru tayi bata che komai ba, zai faman zazzare ido take
Picking call ɗin Aunty farida tayi takara wayar a kunen'ta "hello Aryan ykk, daga ɗayan ɓangaren Aryan yace lfy lau Aunty babba ykk "ina lfy y prince, bai bata amsa ba sai dai yace "kinyi magana da Abba ne "aa bamuyi ba lfy dai koh ta tambaya a ɗan ruɗe "eh to lfy kedai in kinyi waya dashi sai muyi magana " aa Aryan wlh ban yar daba za kasa nashiga tunani pls kafa ɗa min da wata matsala ne "aa Aunty farida babu komai ke dai ki kula mana da kanki kinji, bai jira amsar taba ya katse kiran, dagowa Aunty farida tayi tana kallan Zahra"Auta lfy kika nitsu haka "turo baki Zahra tayi tace ba komai, Khalid kuwa sai dariya yake musu dan yasan dalilin nisuwar Zahra, dawo da kallanta Aunty farida tayi tana faɗin lfy, bro kake kallan mu haka," lfy lau kawai ina mamakin irin son damuke miki ne, duk