Showing 9001 words to 12000 words out of 363274 words
wani irin kai ne dake ba "share kwallan fiskar ta diyana tayi tana faɗin yanzu hiyana haka zamu chigaba da rayuwa ni gaskiya bazan iya jure wa ba, yazamuyi mu ɗebo ruwa da kofi kuma a che mu chika abuba dake gida da ruwa har dana dabbobi nidai bazan iyaba "to duk bake kika jaba da zaki che bazaki iyaba kin nafa sane da kyar bappa yasamu yaje chikin birni ya sawo mana buket ɗin nan, yanzu gashi kinsa buba ya fasa bappa kuma ba takawa yake ba yanzu bare ya sawo mana wani ai dole ma mu ɗebo ruwa da kofin tun da dai kin san inna in tayi magana ba wan da ya isa yasa ta chanza, shiru diyana tayi bata sake chewa komai ba harsuka kai bakin rafin suka ɗebo ruwa a kofin suka juyo suka kama hanyar gd
More comments an share
*DUK ƘARFIN IZZATA*
_💖Story And Written💖_
⬇️
*Mrs BMB*
💫New team 💫
⬇️
💖The talent troupe writer's 💖
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*Episode 3*
Kwan che DON yake chikin ɗan karamin pool nashi dake wajen sha'katawar sa na chikin ɗaki kwan che yake chikin ruwan gaba ɗaya jikin sa na chiki iya kansa kawai yabari a waje idon sa a lunshe kamar mai barchi, Aryan dake zaune saman ɗaya daga chikin kujerun wajen, yace "DON da alama fa maganar Yusuf zai zama gaskiya, batare daya buɗe ido ba yace "haba Aryan kayi magana da Yusuf ɗin ne "aa bamuyi ba amma dai da alama zan chen nashi zai iya zama gaskiya "hmm da kuwa sun gama dani sun kashe idan haka ne "to yanzu wani mataki zaka dauka Aryan ya tambaya yana kallan face ɗin shi, sai lokachin ya buɗe green eyes nashi ya sauke su akan Aryan, yayi da Aryan ɗin ma shi yake kallo " Slowly ya furta banyi tunani a kai ba amma anjima zanyi magana da aunty farida Jinjina kai Aryan yayi yana faɗin "why baza kayiwa, Ammi maganar ba "hmmmm kai ma dai Aryan da wani magana kake,kafasan halin Ammi ni ko kallo ma ban ishetaba bare tasa baki a lamari na, shiru Aryan ya ɗanyi kafin yace "bari nizan gwada, yimata magana, guntun tsaki DON yaja yana faɗin "dama ka kyaleta dan ba sauraran mu zatayi ba nasani "eh to hakane kam amma dai yakamata tasa baki, mikewa yayi yana kokarin fita daga chikin pool ɗin,wayarsa dake ɗaki tafara kara, daukan towel dake jere awajen yayi yana goge jikin sa, yana faɗin "nifa inaganin kai tsaye zan yiwa Abba magana dan gaskiya a yadda nakeji yanzun nan bazan iyaba "to kana ganin hakan shine mafita " kwarai kuwa, yayi maganar yana kokarin shiga ɗaki "
Katafaren gadon sa yanufa yasa hannu ya ɗauki wayar, dake kan gadon kafin ya ɗauki wayar kiran ta katse,dubawa yayi dan yaga waya kirasa ganin Khalid ne,yasa yabi kira ringing ɗaya Khalid yayi picking, sa wayar a H-free DON yayi ya ajiye saman mirrow, yana gyara lallausan haɗaɗɗen gashin kansa sai kyalli gashin ke yi kwanche har bayan sa,
daga ɗayan ɓangaren Khalid yace 'wai yanzu DON da gaske bakuyi kewar mu ba ko?,ko neme mu bakuyi ba, guntun tsaki DON yaja yana faɗin abun da ka ƙira ka tambaya ke nan, "kwarai kuwa shi nakira na tambaya "DON zai sake magana, Aryan yasa hannu ya ɗauki wayar yana faɗin " dan Allah ku zauna a naija pls kar ku dawo dan da kuka tafi rayuwar tafi daɗi ma,dariya Khalid yayi kafin yache hakan ya tabbatar min da kunyi kewar mu ke nan, tun da kache mu zauna a naija hakan na nufin muyi sauri mudawo ke nan tsaki Aryan yaja kana ya jefar da wayar a kan gado ya juya yanufi hanyar fita ɗakin yana faɗin in kagama shiri kakirani awaya san nan ya fiche daga dakin, DON kuwa yana jin Khalid nata magana achikin wayar amma yayi banza, har yagama gyara gashin sa yatara ya ɗaure a baya san nan ya shafa mai mai kamshi da tsada ya fesa Dubai perfume mai kamshi sosai yanufi dressing room almost 30mnt san nan yafito, sanye chikin black jeans da blue t-shirt kayan sun kara bayyanar da Asalin kyan sa chi'kakkiyar surar sa irin na jaruman maza yakara bayyana, faffaɗar kirjin san nan a tsaye dam dam ga dam'tsen hannun sannan kamar zasu fashe a chike suke sosai laɓɓansan yayi ret sosai kamar yasa jan baki, sake fisa turare yayi a jikin sa yasa booth baki akafara sa sai wata dan ƙareriyar agogon daimon mai matikar kyau da tsada ya daura a hannun sa ba karamin kyau yayiba tamkar shiyayi kansa, a hankali ya tako kamar bai san taka kasan yanufi gaban, katafaren gadon sa hannu yasa ya ɗauki wayar sa yana bin screen ɗin da kallo a hankali ya buɗe baki kamar bayasan magana yace Khalid wai har yanzu baka gama surutun naka bane "a fusache Khalid yace gaskiya DON kai dan rai'nin hankaline "oh baka gama surutun ba kenan to pls in kagama ka katse kiran dan zan fitane,rai a ɓache khalid yake faɗin "zaka sanine wlh zamu haɗune, DON dai bai sake chewa komai ba, Khalid dayaji shiru sai ya katse kiran girgiza kai DON yayi yana faɗin na sani bani da masoya kamar ku nima kuma ina kaunar ku
dau kan wayar sa yayi a nitse yanufi waje yana ko karin kiran layin Aryan kirayayi har takatase Aryan bai ɗagaba, waje gaba ɗaya yanufa, a dai dai baƙin kofar babban palo sukayi karo da Aiman da Ahmad, ko kallan inda suke bai yiba yabi gefen su zai wuche "wato DON bakayi murna da dawowar mu bakoh? chewar Ahmad
Aiman kuwa wuche warsa yayi shima ko kallan DON ɗin bai yiba ya haura stair ɗin tsakiya yanufi ɗakin'sa DON kuwa chigaba yayi da tafiyarsa batare daya tankawa Ahmad ba, sai daya kai tsakar gidan batare daya juyoba yafara magana to daman wayache kudawo "rai a bache Ahmad yace ae daman badan kai muka dawoba dan kuwa inda dan kai nema wlh ko kallan kasar nan bazamuyi ba, DON dai bai sake chewa komaiba hasalima tsayuwa yaje yayi a bakin katafaren pool nasu na tsakar gidan, tsayuwa yayi ya juyawa chikin gd baya ya zura hannu a aljihu
Rai a ɓache Ahmad ya juya ya nufi chikin gida a tsakiyar babban palo yachikaro da Aryan shima yana sanye da black jeans da white t-shirt yana daure da agogon daimon irin na DON, ya tara gashin kansa waje ɗaya ya ɗaure yazuba jelar abaya kamar wata mace ga gashin da tsawo, har bayan sa yayi kyau sosai kamar shiyayi kansa, ko kallon in da Ahmad yake bai yiba ya wuce yanufi waje, a kule Ahmad yafara magana "kudai bakuji daɗin halinkuba mutane ne kamar wasu aljannu yanzu haka kafin mu iso sai danayi tayiwa Aiman faɗa amma ko kallona bai yiba haba dan Allah yakamata ku chanza hali, Aryan dai wuchewar'sa waje yayi batare da yace komai ba, haurawa san benen Ahmad yayi yana surutai
Waje Aryan ya nufa kai tsaye inda DON ke tsaye yanufa irin tsayuwar da DON yayi shima yayi ya zura hannu a aljihu suna fiskantar babban gate ɗin gd, gaba ɗayan su fiska kaman an aiko musu da sakon mutuwa, Almost 30mnt suna tsaye a haka babu wanda yache da ɗan uwan sa kala kuma ko motsi basuyiba a tsayuwar tasu
jim kaɗan saiga Aiman yafito shima ya shirya chikin blue jeans da t-shirt ash yayi kyau sosai kuwa duk kansu agogon hannun su iri daya ne, gefen Aryan yazo ya tsaya
juyawa DON yayi yafara tafiya ta ɓan garen dama, ganin DON yajuya yafa tafi yasa Aryan juyawa shima yabi bangaren hagu,Aiman kuma ya miƙi hanyar tsakiya yanufi bakin gate
wani gate dake chikin gidan ta ban garen daman DON yashiga, wasu haɗadɗun motochi ne masu tsadar gaske awajen da alama nanne parking space na gd zubawa motochin ido yayi na ɗan wasu mnt, wasu jibga jibgan sojoji ne suka nufo inda yake tsayen a kalla zasu kai 10, kusa dashi suka ja suka tsaya hannu suka ɗaga suna sara masa, jinjina kai kawai yayi,batare dayayi magana ba kana yasa hannu ya musu nuni da motar da zai hau wata dan karekiyar motache kirar Marcedes Benz, black colour, wani matashin sojane mai jini jiki kato mai ji da karfi fari tas yanufi motar da DON yanuna ya shiga yawa motar key har,inda DON ke tsaye ya jawo mota, wani bakin soja kato dashi kak karfan gaske yazo da sauri ya buɗe wa DON kofar motar
takawa yake sannu a hankali yashiga motar ya zauna, sara masa sojan yayi san nan ya rufe kofar motar, sojan yaja motar da ma tsakai chin gudu suka fita ta ɗayan gate ɗin
A gaban Aryan da Aiman motar DON tayi parking, sauƙe glass din motar DON yayi, yasa hannu ya karbi bindigar da Aryan ke mika masa juyawa Aryan yayi yanufi nashi motar
Aiman kuwa yana tsaye,suma kuma suna tsaye basu tada motochin nasu ba Almost 5 mnt suna tsaye shiru a nitse DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aiman calmly yafara magana "kai inbazaka shiga bane muyi tafiyar mu, tsaki Aiman yaja yana faɗin "au ashe dai bazaku iya tafiya ku barni ba, na zachi nima wulakanchi zakumin DON dai bai sake magana ba sai ma mai da glass ɗin motar yayi ya rufe Aiman kuwa sai da ya sake tsai dasu for Almost 5mnt tukun nan yabude motar DON yashiga, ko kallan in dayake DON bai yiba yayiwa Abdol umarnin akan suwuche a nitse Abdol ya taɗa motar da matsakai chin gudu suka nufi gate, tun basu karisa security suka wangale musu katafaren gate ɗin a jere suka dan na hanchin motochin nasu waje, motar DON ne a gaba sai na Aryan ke bi masa sai wasu motochi 3 chike da sojoji, shinfi ɗadɗiyar titi suka miƙa
kira ne yashigo wayar DON saida wayar takusa katsewa yachirota daga aljihu, Yusuf shine sunan daya bayyana a kan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi ya kara a kunnensa yana faɗin hello daga ɗayan ɓangaren Yusuf yace "bro ykk "a hankali ya furta normal kai fa "Yusuf yace nima normal, inaganin gobe zan shigo abun dayasa ban shigo yau ba kaga Abba yana da zama damu, Aiman da Ahmad sun gudu sunki jiran meeting ɗin , SO kaga bai kamata nima naki tsayawa ba jinjina kai DON yayi yana faɗin "eh hakane amma kayi amfani da lokachin ka dan lokachi bata jira sai dai ajirata "kai DON tun munayara kake yawan faɗa mana haka inshaa allah zamuyi amfani da lokachin mu, " good kawai yace san nan ya katse wayar
Aiman dake zaune Age'fensane yace akoi matsala fa DON " batare da ya kalla inda Aiman yakeba yafara magana matsala batada wajen zama a family Abubakar saraki, tsaki Aiman yaja kafin yace "ta kanka kuwa zatama fara "koh? DON ya tambaya yana kokarin mai da wayar sa aljihu Aiman dan haushi bai ma sake maganaba
Yola Nigeria
Da kyar da kyar suke tafiya suna rike da kofi a hannun su kamar bazasu kai lbr ba tun safe yaran nan suke debo ruwa da cups amma har yanzu karfe 6 na yamma basu gama ba subhanallah
da kyar diyana ta bude baki tafara magana hiyana bazan iya chigaba da ɗeban ruwan nan ba wlh yinwa nakeji numfashi na zai iya ɗaukewa "ki kara hakuri diyana Allah natare kinji, kiyi addua kawai adun halin dakika tsinchi kanki kuma ki kasan che mai godewa Allah sai Allah yakawo miki sauki "alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah Allah ngd, Allah mai kyauta mai kari ya ubangiji kadube mu da idon Rahma Allah ka kawo mana sauki "
ameen ameen diyana haka zaki rinkayi a kowanihali kika tsinchi kanki, diyana batare da ta sake magana ba tanemi waje kasan wata bishiya ta zauna, a'razane hiyana ke faɗin "aa diyana kitashi dan Allah mutafi inbahakaba kinfasan inna "wlh hiyana sai dai yau inna takashe ni, haba da wani kafa kikesan intafi nagaji nagaji yinwa nakeji ko ran dunan dake chikin gidan nan fa bamugama chikawaba barema har musa na dabbobi ta karisa maganar kamar zatayi kuka, hiyana zatayi magana sai sukaji magana ta bayan su da sauri suka juya gaba ɗayan su har suna haɗa baki wajen chewa "inawuni yaya bello "lfy me kukeyi anan da man'gariban nan " ruwa muke ɗiba wa inna diyana tabashi amsa, "to ya kamata kutashi kutafi gida tunda kunga man'gariba ta kawo kai ga dajin nan da machizai, ina ruwan naku in taya ku ɗauka zuwa chikin gari, hiyana ta nuna masa kofin dake hannun ta tache gashi nan "to yau kuma da kofi kuka koma debo ruwan ne ina boket na ɗiban ruwan naku, da sauri diyana tace buba ne ya fasa mana boket, inna kuma tache mukoma debowa da kofi, girgiza kai bello yayi yana faɗin kuchigaba da hakuri kuna addua inshaa Allah, Allah zai kawo muku mafita amma dai yanzu kutashi kutafi gida
"da kyar diyana tamike daga zaman datayi yaya bello yayi gaba su kabi bayan sa tafiya suke kamar babu jini ajikin s,Juyowa bello yayi yana faɗin "ga gyada ku karba kuchi yanzu na chiro a gona yayi maganar yana mika musu ledar gyaɗan dake hannun sa chikin ladabi hiyana ta ansan musu gyadar tana faɗin mun gode murmushi kawai bello yamata batare daya amsaba ya juya ya chigaba da tafiya,suma suka chigaba da tafiya da kyar da kyar har suka fito chikin gari, bello ya nufi gidan sukuma suka tsaya a kasar bishiya mangoron kofar gidan nasu, suka fara chin gyaɗar da yaya bello yabasu
kinsan me hiyana naso ache gyadar nan dafaffache "au yanzu diyana hakanma baki godewa Allah ba karki manta fa tun safe fa ba abun da mukachi, kuma babu wanda ya tausaya mana yabamu wani abu dan kin'samu yanzu yaya bello yabamu gyada shine zaki waniche da dafaffache koh, to kije kidafaɗin, in bazaki iyachi hakaba sai kibari dan bawanda yamiki dole "aa hiyana abun ae bafaɗa bane kawai daga faɗin ra'ayi na "wan nan ba ra'ayi bane diyana rashin godiyar Allah ne kawai, kuma kullun ina faɗa miki kirinka godewa Allah a duk yadda kika samu kanki "to kiyi hakuri hiyana nayi kuskure alhadulillah Allah nagodema dakaba mu abun da za mu sa abakin mu "to kokefa yanzu naji magana "la hiyana kingafa kamar lamrat che ke zuwa diyana tafaɗa tana ɗan murmushi " da sauri hiyana ta juyo tana kallan inda diyana ke nunawa "itache wlh mujirata ta karaso sai mushiga gd tare koh
Gyara tsayuwar su sukayi har lamrat ta kariso, sanye take da kayan fulani farache tas itama mai dogon hanchi kamannin'ta ɗaya da hiyana sai dai idon su ba iri ɗaya bane idon lamrat baki ne idon hiyana kuma blue ne lamrat bazata wuce 13 years ba " lamrat kindawo chikin harchen fullanchi diyana tayi maganar " lamrat tace eh Aunty diyana nadawo "Allah yasa kin sayar da nonon chewar hiyana "eh aunty hiyana nasayar dukka "murmushi diyana tayi tana faɗin alhamdulillah nagodewa Allah dayasa kika sayar yanzu kinga inna bazata bugekiba " nifa aunty diyana duk dukar da inna takemin bai dameni'ba nidai kawai bansan naga tana bugun ku,in nika'ɗai zata yita bugu bazan damuba "to aimuma hakanne bamusan inna ta bugeki ya'fimana tabuge'ni nida diyana tabar ku ke da amrat "hmmm hiyana yakamata mushiga gd kunji anfara kirar sallar mangariba koh chewar diyana " hiyana tace gaskiya kam mutafi tayi maganar tana mikawa lamrat ledar gyadar dake hannunta "aa Aunty hiyana nasan tun safe baku chi komai'ba, ni kuma kinga bintu tabani abinchi awajen talla kuchi kawai " hannu hiyana tasa aledar ta debo gyadar ta mikawa lamrat tana faɗin abinchi daban gyada ma daban " lamrat tasa hannu ta amsa gyadar kana tayi godiya haka suka jera har chikin gida
da sallama suka shiga innar tasu na tsakar gida tana zaune ga amrat zaune a gefen ta, tana tuka mata tuwo, wuchewa kichin hiyana da diyana sukayi dan juye ruwan dasuka ɗebo lamrat kuma tazo ta sugunna a gaban inna ta chiro kudi tamika mata
inna ta karba ta irga kudin san nan tace "yau Allah ya rufa miki asiri kitashi kije ki daukoh wanke wanke kimani,murya na rawa lamrat ta fara magana "inna dan Allah kibari nayi sallah dan wlh ko a'zahar da la'asar banyiba ga kuma mangarib.. bata karasa maganarba ta'farajin saukar duka, da karfi tafara ihu tana faɗin dan Allah inna kiyi hakuri, da gudu diyana da hiyana suka fito daga kichin ɗin sukayo wajen inna suka duka kasa suka kama kafarta suna faɗin inna dan Allah ki kyale ta mu ki dakemu a madadin ta dan Allah inna kiyi hakuri, kafa inna tasa ta shuresu ta ɗau koh itachen a chikin wuta a murhun da amrat ke tuka tuwo tafara bugun su dashi, suna ihu kamar ran su zai fita, amrat na tuƙa tuwo tana kuka, haɗesu inna tayi tamusu duka mai isar duk ta gun bura musu jiki, zama tayi a saman dutse tsakar gidan tana mai da numfashi, "ke diyana ke da hiyana kutashi kutafi ɗiban ruwan ku wlh tun ban tashi na ɓaɓɓala ku ba chikin tsawa inna tayi maganar ke kuma lamrat kitashi ki kama aikin dana saki, ba kun che bakuji ba to wlh zan gyara muku