Showing 291001 words to 294000 words out of 363274 words
aiki bgs ya kama wasu sun yiwa hiyana fyaɗe tun da sun saba kawo musu makaman ciyar wannan patient ɗin sai dai awan nan karon patient ɗin nan tasha bambam da kuwace patient da suke kawowa wanna an mata mai kan kankat case nata ya wuci tunanin su
Cikin zafin rai bgs ya damko wuyar likitan dake masa bayani ya shaƙesa sosai cikin tsawa yace "karya ne bata mutuba ku dubamin matata ta tashi ko kuma ku za ku mutu yanzu nan" kasancewar duk likitocin dake asibitin sun san bgs da Aryan da Yusuf sai ɗaya daga cikin su yayi gaggawar kiran Aryan awaya dan kar bgs ya kashe musu likita Aryan yasha ruwan mamaki lokacin da ya samu kiran likita ashe bgs na uk thank God shima Aryan ɗin bai jima da shigowa kasar ba dan yana tunanin bgs na nan sai dai ya neme sa wajaje daban daban bai same sa ba har yana shirin barin kasar ya dawo gida Nigeria.
ba yadda ba'ayi da bgs ba yaki sakin wuyar likitan nan likita har ya fara fita hayyacin sa
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
[7/31, 9:04 PM] SAFIYYA: 💋 Duk Karfin Izzata 💋
💋The talent troupe writer's 💋
By
Star Lady
Page 46
Ba karamin ɓacin rai Abba ya shiga ba sai dannan sa Hajj fateema da Aunty farida suke shiko Aryan tun jiya da ya tafi shiru shiru ko kiran su awaya bai yi ba. "Abba dan Allah ka dai na sawa kanka ɓacin rai haka bamu son ganin ka cikin damuwa, yanzu dai muyi hakuri mujira mugani zasu dawo ko da haka sun sallame mu"cewar Hajj fateema a kule Abba yace "ni ba ɗaukan ta da yayi suka tafi bane ya ɓata rai abun da ya batan rai shine yau rana ta farko na zana layi wani daga cikin ƴaƴana ya tsallaka kuma a cikin ƴaƴan nawa ma wadda nafi kauna fiye da komai shi ya tsallaka layin da na zana abun yamin ciwo sosai sannan kuma ina son sanin ko suna lafiya dan duniyar yanzun nan kana tare da yan uwan ka lafiya kana ɗan bada baya sai kaji wani abu ya faru to gaskiya ina son sanin wani hali suke ciki ai na suke dan wlh tun jiya zuciya ta ke bugawa ina jin ajikina kamar wani abu ya faru dan a banza haka Safras ba zai kashe duk wata layin da za'a same sa ba" shiru hajj Fateema ta ɗan yi dan ita kan ta idan ta tuna hiyana sai gaban ta ya faɗi ajikin ta tana jin ba lafiya ba dannewa kawai take saboda dalilai biyu na farko hiyana ce yar farin ta na biyu kuma karta tada hankali ta karawa su Abba tashin hankali ban da haka ita kanta cikin damuwa da tashin hankali take kirjin ta sai dukan uku uku yake.
Har karfe 1 na rana Abba na tare da su Aunty farida yau ko fada bai je ba dan ɓacin rai a ɓangaren Ammi ma hakan take ta shiga damuwa sosai
karfe 1:30 bayan sunyi sallar azahar Abba ya haɗa family sa gaba ɗaya a palon sa banda Hajj fateema kasan cewar ita bata samu yin Sallah akan lokaci ba tana ɗakin Ammi tana sallar azahar.
Kallon Khalid Abba yayi yana kokarin yin magana Hajj fateema ta shigo bakin ta ɗauke da sallama tare da wani kyakkyawar balarabe dogo fari tas mai bakin saje yana rike da hannun kyawawan yara biyu farare tas masu kama da shi ga wasu kyawawan yammata kan su ɗaya su uku suna biye da su abaya kallo ɗaya zaka musu ka gane raina ta zauna musu. Da fara'a Abba ya tarbe su har gaban Abba Abu Abdurahman yaje ya duka ya bawa Abba hanu suka gaisa sauran yan matan da yazo da su kuwa sai kallon banza sukewa su Aunty mardiya suna kwaɓe fuska dan basu san kowa awajen ba.
lokacin da idon babban cikin su ya sauka kan Fahad dake zaune yana latsawa waya ba karamin girgiza tayi ba dan atunanin ta bgs ne ihu ta fasa tana ja da baya tana faɗin "Oum Ayaam see this man here" a tare gaba ɗaya mutanen palon suka zuya suna kallon in da take nunawa ganin Fahad ne yasa Hajj fateema tayi murmushi taje ta rungumota tana faɗin "Fariza calm down this is not Safras" shiru Fariza tayi sai lokacin ta lura ba bgs bane dan bgs yafi Fahad murɗaɗen jiki da kuma tsawo da cika,amma duk da haka fariza a tsorace take taki sakin jikin ta shi kanshi Abu Abdurahman ya girgiza lokacin da ya gane nan ne gidan su Safras cikin harshen turanci yace "dan girman Allah ku nunamin wacece mahaifiyar jarumin na mijin nan gaskiya Safras duniya ne duk in da ake neman namiji Safras ya kai ina son inga wadda tayi sa'ar haifan wanna ɗaya tamkar da dubun" kallon Ammi Aunty farida tayi kafin tace "ga mahaifiyar sa nan" a sukwane Abu Abdurahman ya kai kallon sa kan Ammi "eh tabbas mahaifiyar sa ce ga kamanni nan wow gaskiya madam ke mai Sa'a ce ina tayaki murnan samun wanna babban kyau da Allah ya miki na ɗa Safras zakin duniya" Abu Abdurahman ya washe baki sai dariya yake yana yabon bgs bai ma san yau gaba ɗaya Abba da Ammi hau shin bgs suke ji ji suke kamar su shakosa dan saushi cikin sauri Abba ya canza topic ɗin hirar cewa "Abu Abdurahman muna son ka sanar damu in da ka samu Hajj fateema har ka Aure ta" Abba yayi sauri canza topic ɗin hirar ne dan bayason Abu Abdurahman ya cigaba da musu zancen bgs abun na ɓata masa rai.
Gyara zama Abu Abdurahman yayi cikin harshen turanci ya fara magana "a jidda na haɗu da ita a lokacin tana ciwon hauka naje wani meeting ina fitowa bayan sallar mangariba na sameta wasu samari suna tsokanar ta kallo ɗaya na mata Allah ya jarrabe ni da son ta nasha fama kafin na samu ta yarda na ɗauke ta a motata alokacin matata ma haifiyar su Fariza ta rasu ta barni da ƴara huɗu kana yan uwana sunyi sunyi nayi Aure naki dan ina kaunar mahaifiyar su Fariza amma kallo ɗaya nayiwa fateema naji duk duniya ba wanda nake so sama da ita,ban san kowa na taba ban san ita yar ina bace ni dai kawai na ganta a ciwon hauka, ina ɗaukan ta gidana na wuce da ita tsawon shakara biyu ina mata magani malamai da dama na kira sun zo sun dubata duk wani malami dana kira maganar ɗaya suke min shine asiri aka mata da farko naki yarda dan ni ba irin mutanen nan bane masu yarda da tsuɓɓace tsuɓɓace daga karshe dai na hakura na yarda na fara nema mata maganin makarin asiri, abu na farko daya fara ɗaga min hankali shine lokacin data fara samun sauki sai na fahimci tana da ƴaƴa awata kasar dan mafi yawancin lokaci zakaji tana faɗin "wayyo ƴarana Aisha ta" ni kuma ina bala'i son ta bazan iya rabuwa da itaba dan haka sai nayi kokarin mantar da ita rayuwar ta na baya amma ina abun yaki yuwa domin kamar yadda take kara samun sauki haka take kara zancen ƴaƴan ta bazan iya jure rabuwa da ita ba bani da wani zaɓi da ya rage min nasa amata haɗin asirin da zata manta komai da kowa na rayuwan ta na baya haka ko akayi ta samu sauki ta warke sumul amma bata iya tuna komai na rayuwar ta na baya,duk wanna shakara biyu da fateema ta kwashe a gidana yan uwana basu sani ba daga karshe na koyawa fateema sona sosai sanadiyyar kawo fateema gidana da nayi ne yasa na kwashe su Abdurahman na kai su Madina karatu kuma na hana su dawowa hutu dan karsu zo suga fateema su ɓata min shiri shiyasa na kai su gidan babban yayana Madina sai da na tabbatar fateema tana sona na gama shirya komai da kaina nayi mata hayan iyaye na tura yan uwana gidan suka nema min Auren ta ban bata lokaci ba dan kar asiri na ya tonu nayi gaggawar auren ta dan ko sati biyu ban bari an cika da nema min auren ta ba aka ɗaura Auren ranar ji nayi tamkar an sani a aljannan alokacin fateema tana da karancin shekaru dan bazata wuci 23 years ba hakan yasa na sata nakaranta tana da ƙwaƙwalwa sosai nan take komai ya buɗe mata ta fara karatu gadan gadan na ɗauko mata mai mata lesson a gida lokaci da su Fariza suka dawo daga madina fateema ta rungume su sosai kamar ƴaƴan data haifan hakan yasa na gane ita ba yar kasar makka bace dan matan larabawa yan uwana basu yarda su rike ƴaƴan mijin su hakan yasa na ji tsoron karayin aure abaya lokacin da maman su fariza ta rasu dan kar yarana su sha wahala naji daɗi kuma na kara son fateema ninkin yadda nake son ta da saboda rike min su fariza da tayi da zuciya ɗaya ji nake kamar na mai data cikina ko zan huta saboda so da kauna rayuwar mu tayi daɗi sosai,muna cikin farin ciki da anna shuwa,sai da muka shafe shekara 7 da fateema bata samu aihuwa ba sai a shekara na 8 ta samu ciki nayi murna sosai kuma har lokacin ban ji labarin mai neman fateema ba,da lokacin aihu yayi kasar turai na fita da ita taje ta aihu a can nan Allah ya bamu twins Ayaam da Ayana" ya kai karshen maganar yana nuna kyawawan yaran dake jikin Aunty farida "wanna shine takaitacen labarin tsakani na da fateema" salati Abba ya sa kafin yace "kasan tana da Aure amma saboda son zuciya ka ɓoye ka Aure ta kan Aure innalillahi wa inna ilaihir rajiun duniya ina zaki damu ya Allah ka raba mu da sharrin zuciya wanna zuciya wanna zuciya itake gefe dayawan mutane wuta ya ilahi ya lillahi ya Allah ka sassauta mana zuciyar mu zuciya bata da amfani ko kaɗan wanna case na kun sai mun dangana da manyan malamai dan muji ya matsayin Ayaam da Ayana shin halastattun ƴaƴa ne ko dai suna cikin ƴaƴan shubuha ko dai kai tsaye shegune laila ha illallahu Muhammadar Rasulullah sallahu alaihi Wasallama ka chuchi wayan nan yaran subhanallah ni gaba ɗaya kun ɗaure mun kai" tun da Abu Abdurahman ya fara bayani Hajj fateema ke hawaye yanzu daman Abu Abdurahman cutar ta yayi ita ta ɗauke sa a matsayin masoyi shi ya kara sa ta manta da iyayen ta mijin ta da ƴaƴan ta lallai ɗan Adam baa gane shi ta shigar sa a ido idan kaga abu Abdurahman kaga cikakken musulmi duk in da ake neman cikakken musulmi Abu Abdurahman ya bayyana a face nashi ashe zuciyar sa ba ta musulunci bace tabbas bai kamata mutun ya yarda da mutun ta fannin shigar kamala da siffar kamala ba wlh gwara mai shigar banza ansan dai daman shigar banza yake amma mutun yayi shigar musulunci ya cuceka kai amma Abu Abdurahman ya cutar da addini musulunci tir da shi. Da kyar su Aunty farida suka shawo kan ta tayi shiru suka lallaɓata suka wuce part din Ammi da ita
dukar da kai Abu Abdurahman yayi yana faɗin "karki gujeni fateema ina kaunar ki idan kika barni mutuwa zanyi wlh innalillahi nayi nadamar yin hakan" kallon su Fahad Abba yayi yace "ku kai shi ɗakin baki zuwa gobe zan kira malam sai muji me matsayar Auren su da ƴaƴan su tun da shi baban su hiyana ma Allah ya masa rasu ina ganin abun zai zo da sauki" yana kai karshen maganar ya mike ya fice ya nufi fada.
Karfe 4 na yamma Ammi ce zaune a bakin gadon Abba Abba na tsaye ya jingina da jikin gadon suna tattaunawa "Aisha munyi kuskure munyi kuskure babba" "wani kuskure kuma mukayi ranka ya daɗe?" "Aisha duk abun da su Safras ke aika tawa yanzu mune sula mu muka ja" "mu kuma ranka ya daɗe ban gane mu muka ja ba" dogon numfashi Abba yaja tare da sauke ajiyar zuciya kafin yace "A'isha mu godewa Allah dayasa har yanzu ƴaƴan mu basu fi karfin mu ba suna jin maganar mu wlh na jinjina musu Aisha idan baki manta ba tun yaran nan basu wuce shekara 9 a duniya ba muka ɗauke su muka maisu kasar turai a tunanin mu gata muke musu Aisha ba gata bane da kan mu muka lalata yaran mu wlh Allah ma yana son mu da rahma da yasa har yanzu suke jin maganar mu Allah na son mu da yasa basu sauka daga tarbiya irin na hausa fulani ba alhadulillah ƴaƴana basu taɓa zina ba basu taɓa shan giyaba basu taɓa sata ba munyi Sa'a ta nan ɓangaren amma idan kika duba ɗabiun Safras ya banban ta da ɗabiar hausa fulani ni kuma ban taɓa damuwa da hakan ba ina ganin ya girma zai iya yiwa kan sa faɗa sai yau na gane kuskuren yin hakan Safras idan yayi zuciya ba mai iya tinkarar sa ko mu da muka haifesa Safras bashi da kunya ko kaɗan in fact Safras bashi da cikakkiyar imani duk na san da hakan a tunani na idan na masa Aure zai iya sauyawa sai kuma na ga akasin hakan ni yanzu damuwa ta karyaje yayiwa yar mutane wani mugunta dan zai iya kashe ta ba damuwan sa bane tun da ya iya jefata cikin ruwa kuma ya iya sa bindiga ya harbeta bayan nan ya bata wahala kala kala Aisha ina na damar tura ƴaran nan kasar turawa da wuri dana bari sai sun girma sun mallaki hankalin kansu" ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka "kayi hakuri ranka ya daɗe In Sha Allah babu abun da zai faru" jinjina kai yayi kafin yace "Allah yasa" tare da zama kusa da ita sukayi shiru kowa da abun da yake tunani
A ɓangaren su bgs kuwa
Ba yadda likitocin nan basu yi ba akan bgs ya sake musu likitan su amma yayi, numfashi likita na gab da ɗauke wa Aryan ya iso cikin zafin nama yasa hannu ya ɓanɓaro hannun bgs daga wuyar likita nan take likita ya faɗi kasa sumamme, a fusace bgs ya juyo ya damki wuyar Aryan,ganin Aryan ne yasa ya zame hannun sa kallon tsab Aryan ya masa cikin sauri yace "bgs lafiya meke faruwa? Meke damun ka? Me ya kawo jini jikin ka? Accident kayi ne? Ina sister? Me yasa kake cikin rafin rai haka? Kamin magana dan girman Allah ina sister?" "Ta mutu ta mutu Aryan ni da kai na na kashe ta ni da kai na na kashe ta Aryan nayi nadamar zuwata duniya nayi k....bai kai karshen maganar ba Aryan ya ɗauke sa da wata wawan gigitatchiyar mari cikin tsawa da zafin ran da bai taɓa shigaba yace "ka kashe ta kake faɗa min!!? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Safras yanzu menene amfanin zuciya dan ina tabbacin cikin zuciya ka kashe ta kana cikin hayyacin ka bazaka kashe taba ka cuce mu bgs ka cuci su Ammi yanzu ina gawar nata yake?" Sulalewa wa bgs yayi ya zube kasa ya kifa kansa a kasa idon sa sunyi ja kamar jini jikin sa har ɓari yake tsabar tashin hankali da ɓacin rai da kyar ya iya faɗin "Aryan ka kashe ni kayiwa Allah ka kasheni na bi matata wlh ba zan iya rayuwa ba tare da Eshat ba son ta ya mamaye dukkan jinin jiki na na cutar da ita ta mutu da bakin ciki na bazan yafe wa kai na ba zuciya ta cuceni zuciya bata da wani amfani a rayuwa sai dai ya kai ka ya baro ka idan ka biyewa zuciya to tabbas zakayi dana sani mara amfani kamar dai ni ɗin nan innalillahi wa inna ilaihir rajiun Aryan ka kashe ni bazan iya kashe kai na ba zanubin zai min yawa nayi dana sanin zuwata duniya na kara mai mai tawa yau zuciya tasa nayi dana sanin zuwata duniya Aryan mari yayi kaɗan a hukuncin daya dace kamin yayi kaɗan ku bani hukuncin dai dai da wanda yayi fyaɗe kuma yayi kisan kai ka hukun tani kamar yadda kake hukun ta criminal ɗin da suka yi wa yarinya fyaɗe kuma suka kashe ta domin abun danayi kenan nima" lokacin guda Aryan yaji mugun tausayin bgs ta rufesa da ya zuciya sosai amma ganin halin da bgs ya shiga yasa ya ɗan sauko dan ko amafarki bai taba tunanin bgs zai shiga wanna yanayi saboda mace ba, dukawa yayi ya dafa kafadar bgs ɗin kasa kasa yace "ina gawar sister yake? Kuma me ya hadaku har ka kashe ta?" Cikin tashin hankali ya fara bawa Aryan labarin duk abun da ya faru tsakanin su "innalillahi wa inna ilaihir haba bgs meyasa zakayi wa kanka allura haka why why? Kafi kowa sanin illar alluran nan sanna kasan a addinan ce ma haramun ne kai da kake yakar Company masu buga ire iren alluran nan kai da kake yaki akan masu fitar da shi kake kama masu amfani da shi why? Yau zakayi wa kan ka meyasa baka kirani ni naje nayiwa criminal ɗin hukun ciba duk da nasan cewa nima yanzu bazan iya hukun ta mutun kamar da ba ni yanzu ko kuna ma bazan iya sawa criminal a jiki kamar da ba amma tun da babban criminal ne zan san ya zanyi yanzu gashi ka ɓata komai mawuyacin abu ne Abba Ammi hajj Fateema kai kowa dake gida mawuyacin abune su yafe maka wlh ni nasan har Yusuf sai ya guje ka akan sister" "Aryan zuciya ta zafi take min Aryan zuciya ta cuceni ta gama dani bani da abun cewa karka ɓoyewa kowa abun dana aika ta ka faɗa wa kowa a gida ta yadda zasu nunamin tsana har na samu zuciyata ta buga na mutu Aryan ina son matata ba zan iya rayuwa babu ita ba tazama bugun numfashi na ina kaunar ta