Showing 183001 words to 186000 words out of 363274 words

Chapter 62 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

3205

shigayi shin yauma naje na gyara masa ɗaki ne ko dai na kyalesa kar yazo yamin hukunchin irin na jiya.

Da wannan tunanin ta koma betroom nashi, gadon ta nufa ta chire bet shirt ɗin ta nufi waje ajiye kayan datti ta ajiye ta dawo ta shiga dressing room ta ɗauko wani dankareren bet shirt fari tas mai bala'i kyau da tsada ga laushi kai ka che audigane, sauri sauri ta shinfiɗa gadon ta sauko ta nufi toilet ta wanke masa fes ta gyara ko ina a chikin ɗakin, ta sanya turare mai bala'i kamshi, shiru ta tsaya tana mai da numfashi tunani take in koma palo in zauna ne ko dai in zauna a nan kar kuma na zauna a nan ya dawo ya fara faɗa, dan shi bazaka taɓa gane menene idan ka masa dai dai da kuma ba dai dai ba, yanzu na samu ya fara ansan abu daga hannu na bai kamata nayi masa wani laifin da zai sa ya dai na hakan ba, jiki ba kyari ta fito palo ta zauna saman sofa, tayi shiru tana tunanin chan ta tuno ashe tana da waya, mikewa tayi chikin sauri ta ɗauko wayar a chikin akwatin ta, ta kunna babu charji, mikewa tayi ta sanya wayar a chaji ta dawo ta zauna.

Karfe 6 Bgs ya shigo palon yana waya betroom nashi ya nufa har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo kallo ɗaya ya mata ya kauda kai tare da chere wayar daga kannun sa, daga in da yake tsaye ya sai ta ta da wayar alamar tazo ta ansa, chikin sauri ta miƙe ta garisa gaban sa ta sugunna ta ansa watar juyawa yayi ya shige chikin betroom ɗin.

Manna wayar tayi a kunnen ta, chikin sanyi da girmamawa duk da batasan wanene ba tace "Assalamu alaikum ina kwana" daga ɗayan ɓangaren Ammi tace "lfy hiyana Ykk y gida? Chike da farin chiki da zumuɗi tace "Ammi ina lfy ya gida yasu Abba wlh ina kewar ku dukkan ku" "sunanan lfy muma muna kewar ki" "ayya Ammi ki sa a dawo dani gida kinji na gaji da nan banason kasan nan ko kaɗan" jin abun da hiyana tace ba karamin ɗagawa Ammi hankali tayi ba hakan ya tabbatar mata da Bgs baya kula da hiyana idan yana kula da ita bazata yi wan nan furuchin ba, wani irin bakin chikine ya tokarewa Ammi makoshi awan nan karo gaskiya bazata kyale Bgs ba ya isa haka "Ammi ya naji kin yi shiru ko dai kin kashe wayar ne? Muryan hiyana ta katse mata tunani da sauri tace "aa ban kashe ba, kina jina hiyana yanzu zan sanya yayan naki ya sai miki waya yau ɗin nan anjima sai muyi magana da wayar ki yanzu kam ki bashi wayar sa" Ammi ai jiya yaya Khalid ya sai mana waya dukkan mu nawa babu charji ne yanzu nasa a charji idan yayi charji zan ansa number ki ko wajen Aunty Zahra ne sai na kiraki" mamaki ne ya kama Ammi lallai ba karamin abu Bgs kewa hiyana ba tun da gashi shine mijin ta amma batace zata ansa number na awajen Shi ba sai dai wajen Zahra yarinya kwata kwata bata so ayi mata zanchen sa, amma bari na ɗan tambaye ta "Hiyana ina yayan ki? "Yana ɗakin sa Ammi" "to naga lokachin tafiyar su wajen aiki ya kusa kije ki tayashi shiryawa mana zamuyi waya anjima" "kai Ammi! Shiryawa kuma kinason ya....sai kuma ta yanke maganar tace "to Ammi bari naje" hmmmm kawai Ammi tace dan ta rasa me zata che da Hiyana, chikin karyewar zuchiya tace "to hiyana ki je ki kai masa wayar In Sha Allah daga yau kasar zata fara yimiki daɗi kinji? "To kawai hiyana tace tare da mikewa ba tare da ta katse kiran ba ta nufi betroom nashi

da sallama a bakin ta ta shiga yana tsaye gaban mirrow yana shafa mai, gaban sa dazo ta tsugunna chikin sanyin murya tace "yaya prince ina kwana ga wayar" shiru yayi bai ansa mata gaisuwar ba kuma bai ansa wayar ba, aikin gaban sa kawai yake, Almost 10mins tana sugunne shi kuma ya gama shafa mai yana gyara gashin, chike da tsoro tace "yaya prince dan Allah ka ansa wayar mana wlh ji nake kamar zan faɗi kai na na chiwo sosai" shiru kamar baya wajen duk wannan abun da suke Ammi na jin su dan bata katse kirar ba, sai da ya gama abun da yake san nan ya ansa wayar ya wuche dressing room dan shirin zuwa wajen aiki, sauri sauri Hiyana ta miƙe ta fito ta nufi kitchen already jourfree ya gama shirya breakfast na bgs ɗauka tayi ta nufi betroom nashi.

Tana shigowa dai dai lokacin ya fito daga dressing room ya shirya chikin haɗaɗɗadiyar suit ash colour, da alama wani meeting zai je ba ƙarin kyau kayan suka masa ba, sun kara fito masa da ainahin suran jikin sa, kyawun sa ya kara bayyana sosai, ya ɗaure lallausan bakin gashin kan nan nashi, sai wani haske da ya kara, fiskar nan tashi a ɗaure take sosai kamar wadda akayiwa wani abun, dan yanzu da yake tsaye gaban mirrow fiskar a ɗan sake, daga shigan sa dressing room ya fito fiskar sa ta sauya sosai, ɗamtsen hannun san nan kullun kamar kara hurasu ake sai kara chika suke kamar zasu fasa hannun rigar,
sosai hiyana ke satar kallon sa ta kasan ido tana addu'ar Allah ya dai dai ta tsakanin su, kwata kwata bata son ya fahimci tana son shi shiyasa bata taɓa yarda tayi gigin kallon face nashi kai tsaye sai dai ta rinƙa satar kallon sa ta sanya wa ranta ko mutuwa zatayi da son sa bazata taɓa bari ya fahimci tana son nasa ba.

Saman table ta ajiye masa abincin, ta tsaya awajen tana jiran shi yazo tayi sarving na shi

Sake feshe jikin sa yayi da perfume nashi mai bala'i kamshi da daɗi sannan ya nufi saman sofa ya zauna, chikin sauri ta fara haɗa masa tea ta miƙe masa, sai da ya ɗauki tsawon 2mins kafin ya ansa cup ɗin, a hankali ya kai cup ɗin sai tin dan karamin bukin sa ya fara sha tea ɗin, kasa kasa hiyana ke satar kallon yadda yake shan tea ɗin kamar bai san sha, zuba masa chips tayi a plate tare da soyayyun kaji, ta dora saman table ɗin ta matso masa da table ɗin, komawa gefe tayi ta zauna tana jiran ya kammala ta kwashe kayan.

Muryan sane ya daki gogon kunnen ta yana faɗin "kije ki ɗauki magani a drawar chan ki sha guda biyu bayan kinchi abinchi, san nan idan kika sake magana ta da Ammi kin san sauran" murya na rawa tace "kayi hakuri yaya prince bazan sake ba" shiru yayi bai sake magana ba yachi gaba da shan tea ɗin sa mikewa tayi ta nufi drawer ta ɗauko maganin ta fice daga ɗakin ta nufi kitchen

abinci kaɗan ta zuba a plate ta dawo palo ta zauna, a nitse ta chi abin chin ta ta sha ruwa sannan ta sha maganin tana kokarin mikewa ta nufi ɗakin, shi kuma yana fitowa, kasa kasa chikin tsoro tace "adawo lfy Allah ya tsare" a'sukwane ya juyo ya kalleta nan take taji numfashi ta ya tsaya duk wani jini dake gudu a jikin ta sai da ya tsaya chak addu'a ta shigayi Allah yasa ba laifi tayi ba faɗin hakan da tayi, juyawa yayi ya chigaba da tafiya ba tare da yayi Magana ba bin bayan sa tayi da kallo har ya fice, yana fita ta sauke nauyin ajiyar zuchiya tare da miƙewa ra nufi betroom ɗin

Kwashe kayan abin chin tayi ta maida kitchen ta dawo ta kara kyara ɗakin ta shiga toilet na shi tayi wanka a gurguje ta fito ɗaure da towel nashi wadda yazo mata har kasan guiwa, fitowa tayi ta nufi betroom nasu Fahad, sallama tayi a bakin kofar, Amrat na daga chiki ta amsa tare da faɗin "Aunty Hiyana ki shigo mana yaya Fahad baya nan" "aa Amrat ni bazan shigo ba ki kawomin hijabi idan akoi a chikin kayan ki" "Aunty hiyana hijabin ɗan karamin ne fa bai wuchi ya tsaya zuwa kirjin ki ba" "eh kawomin" bata karisa rufe baki ba amrat ta fito rike da wani haɗaɗɗen dan karamin hijabi mai stone a jiki, pink colour ta mika mata, chikin sauri hiyana ta ansa ta sanya a jikin ta ta juya batare da ta kara Magana ba sauko palon kasa tayi, ta nufi part na su Zahra.

dai dai zata shiga part ɗin Zahra na fitowa karo suka kusayi baya hiyana tayi tana hararan Zahra "lfy kike harara ta Aunty hiyana? Zahra ta tambaya tana guntse dariya dan tasan batun hijabi ne ya kawo hiyana "yanzu Aunty menen hakan dan Allah ki bani hijabi idan kina da shi wlh yau da blanket ɗin yaya prince na rufa nayi sallah" "dan Allah Aunty Hiyana da gaske kike yi yau da blanket na yaya prince kikayi Sallah" hararan wasa hiyana ta wurga mata kafin tace "eh mana" dukawa kasa Zahra tayi tayi sujudur shukur tana ɗagowa ta rungumi hiyana tana faɗin "Alhadulillah Alhamdulliah ya Allah na godema da ka nunamin wannan rana ya Allah ka dauwamar min da yar uwata chikin farinchiki ya Allah kasa yaya prince ya so ta sosai" "ke Aunty Zahra waya che miki sona yake, baya nan fa na ɗauki blanket na shin kema ai kin san da yana nan ban isa ba" "Aunty Hiyana ke dai karki damu jiya kwana nayi ina sallah ina miki addu'a Allah ya juyo da hankali yaya prince gareki" "hmmmm ko kuma kwana kikayi kina zubawa yaya Khalid iya shege ba" "kai Aunty hiyana to duk ma ba wan nan ba yaya khalid ne yace daman naje na sanar dake ki shirya zamuje yanzu nan ya mana registration zamu koma school" "da farinchiki Hiyana tace "kai Alhadulillah Alhamdulliah daman na gaji da zaman gidan nan, yanzu dai Aunty Zahra dan girman Allah ki bani hijabin ki da kika sanya da zamu zo nan kina ga fa ko hijabin sallah bani da shi" "kimin alkawarin iya sallah zaki rinƙayi da shi kawai" "Aunty Zahra na miki alkawari iya sallah kawai zan rinƙa yi sai kuma idan zan fito palon kasa ya miki? "Eh ya min kije ki shirya zan kawo miki hijabin yanzu" to kawai hiyana tace ta juya ta koma part nasu Zahra kuma ta koma ɗaki


8pm dai dai Khalid ya ɗauki su hiyana suka tafi registration yaje ya musu sannan suka wuche wajen sayyaya saya musu duk wani abun da zasu bukata na makaranta yayi sai karfe 1pm dai dai suka dawo gida kowa ya wuche part nashi.

Hiyana na shiga part nasu kai tsaye wajen da ta ajiye trolley kayan ta ta nufa dan ta sanya kayan school nata a chiki, da mamaki take bin wajen da kallo, gani babu trolley ɗin awajen lallaɓawa tayi ta leka betroom ɗin ta tagani ko yaya prince yasa an kai su chan, gani tai basa chiki, juyowa tayi ta nufi betroom nashi, da mamaki take kallon yadda jourfree ya shirya mata trolley ɗin ta a chikin ɗakin tunani take to waye yace jourfree ya kawo mata kayan ta nan kar yaya prince yazo ya hukun tata yayi tunanin ko ita ta kawo su ɗakin, jiki ba kwari ta nufi trolley, zuge zip ɗin babban tayi ta zuba kayan makarantar nata a ciki, ta miƙe ta wuche toile

sauri sauri tayi wanka ta fito gaban mirro taje ta tsaya chike da tsoro ta fara shafa man shafawar sa tanayi tana tunanin karfa yaji kamshin man shi ajikin na ya hukun tani, hannu ta kai zata ɗauki perfume nashi sai kuma ta fasa ta juya taje ta ɗauko wasu sheɗanun riga da wando kwata kwata rigar babu hannu, ita kuwa wando crazy che duk an tsastsaga ta a dai dai chinyoyin, sosai kayan suka matse ta, chinyoyin ta kamar zasu fashe, ɗaure gashin kanta tayi ta ɗauki hijabin Zahra ta sanya, ta fito ta nufi kitchen, already abin chin Bgs na shirye ɗauka kawai tayi ta koma part nasu, saman table da ta saba ajiye masa a nan ta ajiye ta kara gyara masa ɗakin ta nufi wajen turaren ɗaki dake gere chikin wani box glass mai ɗan girma wani haɗaɗɗen turare ta zaɓo mai bala'i kam shi ga daɗi, gaba ɗaya lungu da sakon dake chikin ɗakin sai da tabi ta feshe air freshener nan ta kara gudun Ac ta fito ta zauna a Palo, ta ɗauko wayar ta, ta kunna ta shiga massage dan ta duba massage ɗin da yaya Khalid yace ta duba, tana kokarin fara karan tawa sai taji takun sa alamar yana shigowa da sauri ta ajiye wayar, ta nitsu ta kame jikin ta waje guda

Kasa kasa yayi sallma kafin ya shigo, kafin ta buɗe baki ta gai da shima har ya shige betroom nashi, chikin sauri ta gyara hijabin jikin ta, ta miƙe tabi bayan sa, zaune saman sofa ta same sa ya jingina kai a jikin sofan yana kallon sama, gaban shi tazo ta tsugunna chike da tsoro ta fara chire masa ta kalmin kafar sa tana faɗin "sannu da dawuwa yaya prince ina wuni" chikin sanyin murya tayi maganar shiru yayi kamar ba da shi tayi maganar ba, bata damu ba dan bai amsa mata gaisuwa ba idan da sabo ta saba, zame masa safar kafan sa tayi, zubawa kafan sa blue eyes nata tayi ba Karami kyau yatsun kafar sa ke mata ba, ba abun da ya faɗo mata a rai sai marin da ta sha ranan akan taɓa kafar sa da dayi tuna hakan ne yasa tayi saurin kawar da idonta gefe tare da mikewa ta ɗauki ta kalman da safan ta mai dasu wajen da ya dace

Gaban shi ta dawo ta sugunna ta ɗauko goran ruwan faro mai sanyi daga chikin try abin chin da ta kawo masa, dauko glass cup tayi ta balle bakin roban ruwan ta zuba a chikin glass cup ɗin, ta ɗago ido tana satar kallon sa chikin sanyin murya tace "yaya prince ga ruwa" sai lokachin ya ɗago daga jinginan da yayi a jikin sofan, ba tare da kalli in da take ba yasa hannun ya ansa cup ɗin, a hankali ya kai cup ɗin sai tin dan karamin bakin sa ya fara shan ruwan, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke wadda yasa shi ɗan kallon in da take chikin sauri ta fara kokarin zuba masa abin chi, hannun ya ɗaga mata kasa kasa ya furta "no need am ok" yana kai karshen maganar ya miƙe, da sauri ta miƙe itama ta dan duka ta anshi cup ɗin hannun sa, wuchewa yayi ya nufi toilet ita kuma ta kwashe kayan abin chin tayi waje dasu, sai murna take yau yaya prince ya bari ta chire masa ta kalma lallai yau ba zata manta da wannan rana ba, Allah dai yayiwa Ammi albarka daman ta faɗa mata daga yau yaya prince zai sauya mata to kuma gashi nan zan chen Ammi ya fara tabbata, kitchen ta mayar da kayan abin chin ta dawo palo ta haye doguwar kujera ta kwanta tare da jan hijabin jikin ta ta rufe har kafanta, ta lumshe ido kamar mai barchi.


Maiduguri Nigeria

Da matsanan chin gudu sosai motar su Aryan ta shararo akan mikakkiyar hanyar da zata sadasu da titin gidan Aunty farida, dai dai zasu shiga kwanan da zata sadasu da hanyar gidan Aunty farida, lokachin motan Ahzan ya danno kai, a sukwane ya taka birki, da da sauri motochin su Aryan ma suka taka birki wani wawan birki Shahram yaja wadda yasa Aryan dake zaune a gidan baya kan shi ta bugu da kujerar gaba na motar saura kaɗan motar sojojin dake gaban ya bugi motar Ahzan, chike da bachin rai Aryan yace "wani irin birki ne wannan Shahram? Murya na rawa Shahram yace "sorry sir bamusan mota na zuwa a gaban mu bane Shiyasa Allah ma ya tsare" shiru Aryan yayi bai sake magana ba ya dukar da kan sa dake matsanan chin sara masa, zuchiyar sa na bugawa da sauri sauri ji yake gaban sa na faduwa sai mai mai ta innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil a chikin zuchiyar sa

A ɓangaren Ahzan kuwa chike da jin haushi ya kama marfin motar zai fita Hanan dake zaune a gidan baya kusa da Ummi tace "yaya Ahzan karka fita dan Allah kana ganin wayan nan manya manyan Sojojin daga ganin fiskar su basu da imani" "haba hanan sufa suka so buge ni, ko ina mukaje sune masu laifi dan baa shiga kwana da irin wannan gudun da suka shigo yanzu da mun samu haɗari fa? Dole doka tayi Aiki a kansu duk da suke sojoji ai sun karya doka su kaya, juyawa yayi yana kokarin buɗe kofar motar sai ji yayi ana buga glass ɗin motar, fasa buɗe motar yayi ya sauke glass ɗin, da sauri ya runtse ido yasa hannu yana goge idon na shi dan ya tabbatar wa kan sa ba mafarki yake ba kuma ba karya idon sa ke gane masaba, wani jabgegen sojane tsaye awajen fiskar sa babu annuri chikin tsawa da karfin murya sojan yace "kai ka jaye mana motar kan nan ka bamu hanya!! Nan take jikin Ahzan ya fara rawa hannun sa sai kerma yake da kyar ya iya tada motar da gudu ya bar wajen, komawa chikin mota sojan yayi suka tayar suka bar wajen da gudun gaske.


UMMI

"Aunty hanan ji nake kirjina na bugawa da karfi zuchiya ta sai tsinkewa take kamar wani abu zai faru dani, Ahzan dake zaune a mazaunin driver yana tuki ya ɗan kalleta ta chikin mirrow motar yace "haba Ummi kawai kin tsoratane saboda haɗarin da muka kusa yi, ba wani abu da zai faru dake ki chigaba da faɗin hasbunalluhu wani mal wakil kinji? Gyaɗa masa kai Ummi tayi alama to, suka chigaba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login