Showing 21001 words to 24000 words out of 363274 words

Chapter 8 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2525

"daga yau sai yau duk wanda ya sake,idan iyayen mu suna magana a tsakanin'su yasa baki kunsan me zai biyo baya ina ruwan ku da faɗan su
Shiru sukayi bawanda yache kala
DON yachi gaba dace wa "last warning nake muku idan kuka bari nasake kama'ku da irin wan nan dabiar bama sai nayi magana ba, kai Haidar da kai da Umar kuje wajen kwallo bayan nan kufara frog jump ina zuwa ya kai karshen maganar yana kallansu Haidar da Umar ɗin

mikewa sukayi suka fita jiki ba kwari suna fitowa Umar ya dubi hadar yafara magana "mun shiga uku wlh, yau zamu gane kuren'mu wayyo sheidan baka mana adalchi ba daga dawowar big bro muzai fara yiwa hukunchi ke nan wayyo Allah,
Chikin nar kewar murya Haidar yache "waima daman meyakai'mu shiga fadar matane yanzu gashi zamu karbi hukunchi,wlh ni nasan yau sai munkasa mikewa da kafafun'mu
Haka'dai sukayi ta surutai suna tafiya har suka isa wajen kwallan dukawa sukayi suka fara frog jump ɗin.


Miƙewa Yusuf Aiman Ahmad sukayi suka musu sai da safe suka fito nuka kowa yanufi part nashi ɗakin yarage daga DON Aryan Khalid Fahad, shiru suka zauna kowa na latse latse a wayar sa almost 10mnt Khalid ma yamiƙe ya musu sai da safe yayi waje, Khalid na fita Aryan ya ajiye wayarsa ya dawo da kallon sa da kuma hankalin sa kan DON yafara magana "zanje nayi magan da Aunty amarya batare da DON ya ɗago ba yace "a kan me fa "akan abun daya faru dazun a palo mana kasan komai kaji komai da kunnen ka,kasan wayafara taɗa rikichin to yakamata mu dakatar da abun tun bai yi nisa ba sai lokachin DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aryan ɗin kafin yache "a'a ka kyaleta to idan ma kaje me zakache mata itafa ta haifemu bamu muka haifetaba dan haka kabar abun zamu'san abunyi a kai "a'a DON duk da ita ta haife mu amma ai idan tana kuskure addini ya halakta mana mu mata gyara,amma tun da kache in bari to shike nan zanjira matakin dazaka ɗauka
DON bai sake magana ba shiru suka zauna na dan lokachi kafin Aryan yamike ya musu sai dasafe yanufi waje
juyowa DON yayi yana kalli Fahad dake kwanche yana latsa waya "kai wai a nan zaka kwana ne, da sauri Fahad yace "a'a yanzu zan tafi ya kai karshe maganar yana miƙewa, "sai da safe yache da DON batare daya jira amsar DON ba ya sauko yanufi waje


Karfe 11 nadare

Sau kowa yake a nitse yana sanye da kayan barchi dogon wando da riga mai dogon hannu yan shara shara marasa nauyi white colour jikinsa sai kamshi yake, ya tara gashin kansa ya ɗaure a baya sosai kayan suka fito masa da surarsa na chikakke kuma jarumin namiji mai ji da lfy da karfi,taku yake irin na jaruman maza masu jini ajiki, kofar baya ya buɗe ya fito waje kai tsaye wajen kwallo yanufa

Frog jump yasamu sukeyi da kyar da kyar suƙe iya ɗaga kafa duk sun galabai ta sama sama suke numfashi sun jiƙe sharkaf da zufa
da kak'kausar murya yache "kutashi ku tafi ɗaki a gala bai che Umar yace "sorry bro wlh bazan iya miƙewa ba da kyar Haidar ya iya buɗe baki shima yace "wlh yaya prince nima bazan iya tashiba
Chikin tsawa DON yafara magana "zaku kwana a nan ke nan, zaku tashi kutafi ɗakine ko sai nayi kwallo daku ai tun bai kai karshen maganar ba suka tattara sauran karfinsu gaba daya suka miƙe, har jiri suke gani rungume juna sukayi suna ɗungisa kafa da kyar da kyar suka nufi hanyar part nasu, shi kuma DON ya juya ya koma ta in da ya fito


jimeta yola


Jama'a ne zaune a kofar gidan su diyana suna karɓan kai suwar rasuwar bappa chikin gida kuma matane zaune suna yan koke koken su, hiyana diyana Amrat lamrat kuma suna zaune a kusa da rafe kasan wani bishiyar mangoro suna kuka, duk fuskar su ta kunbura kuka suke sosai kamar ransu zai fita chikin kuka da dashewar murya diyana ke faɗin "shike nan bappa ya mutu ya bar mu munshiga uku ina zamusa ranmu wayyo allah "da kyar hiyana ta iya buɗe baki muryan ta duk ya dashe saboda kukan data sha tafara magana "a'a diyana ki daina chewa munshiga uku gaskiya bamu shiga uku ba tun da mun rike Allah inshaa Allah, Allah bazai kyalemu muchigaba da wulakantaba chikin shessheka lamrat tace "eh hakane Aunty hiyana addua kawai bappa ke bukata, duk kansu suka haɗa baki su kache Allah yajikansa da rahma
Diyana tache "hmmm jiya fa Bappa yarasu amma baza abar'mu mu dan huta ba muji da rasuwar bappa ba inna tace, dan Allah yanzu muji da wanne muji da rasuwar Bappa ne ko kuma muji da ɗebo ruwa
Mikewa hiyana tayi tana faɗin "kutashi ma mukarasa ɗeban ruwan nan kar inna ta buge'mu da kyar suka mike suka nufi rafin suna rike da cups a hannunsu
Sun ɗebo ruwan zasu wuche ke nan sai sukaji muryan yaya bello na kiran'su daga chikin gona, chikin gonar suka nufa, a zaune a inda yasaba zama suka same sa ga tulu sababbi guda 4 a gabansa
A gaban sa suka duka suka gaidashi ya amsa chikin faraa san nan yamusu taziyar mutuwar bappa tare da adduar Allah ya jikansa suka amsa da ameen, kana yache ku ɗauki tulu nan nan dasu zaku rinka deban ruwa dan ku nasaya, duk da kukan rasuwar bappa dasuke hakan bai hana'su yin murna da ganin tulun ba ɗauka sukayi suna murna sai godiya suke masa suka fito gonar suka nufi rafi, ruwa suka ɗeba a sabon tulun su sai murna suke,suka nufi hanyar gida

One day later

yau Bappa yachika kwana uku da rasuwa, jama'a sun watse babu kowa a kofar gidan kowa kama kansa


diyana hiyana da lamrat sunbar amra a gida tana tikar aiki duk kansu suna dauke da tulun da yaya bello yasa musu suka nufi rafi suna tafiya suna yar hirarsu
Diyana tache "wai ya akayi inna batayi magana akan tulun nan bane Girgiza kak hiyana tayi tana faɗin "hmmm ai bata lura bane inda ta lura ai da saita tambayi waya bamu ko kuma ma ta fasasu
Lamrat tache "to yanzu idan inna ta tambayi waya bamu tulun me zamu'che mata,dogon tsaki diyana taja kafin tace "sai muche muma ba mu san mutumin daya bamu'ba,yaga muna ɗeban ruwa da kofine sai yabamu "yauwa diyana gaskiya kin kawo shawara daman sai tunani nake idan inna ta tambaye mu me zamu'che chewar hiyana,tayi maganar dai dai lokachin da suka iso bakin rafin ruwa suka debo,a tulun suka juya suka nufi hanyar gd,

"hiyana wai yan zu haka zaki Auri buba diyana ta tambaya, buɗe baki hiyana tayi zatayi magana sai taji an ture tukun dake kanta ta baya ya faɗi ya tar watse, asukwa'ne buba tagani tsaye yana mur mushin mugunta diyana naganin buba ta kwasa a guje tayi hanyar gida, gudu take iya karfinta har ta iso dai dai zata shiga ke nan tayi tun tube da dutsen kofar gidan ta faɗi kasa tulun ya faɗi kasa ya tar watse, wani kukan bakin chiki ta sake kuka take kamar ranta zai fita
a wan nan yanayi Hiyana da lamrat suka zo suka sameta tai maka mata Hiyana tai tamike tsaye ga goshin ta sai jini yake, dukkanbsu sai hawaye suke haka suka shiga gida

inna dake zaune a tsakar gd tache ina ruwan, kuma tun dazun na zauna a nan nake jiranku zan dora ruwan shayi
Chikin shesshekar kuka lamrat tace "wlh inna buba'ne ya kifar da ruwan
Da sauri inna tamike tana faɗin buba na zakuwa sharriko ai nama buba ya ganku bare ya kifar da ruwan to wlh yau zaku yabawa aya zakin'ta, suna tsaye awajen suna matsar kwalla, har inna tashiga ɗaki ta daukoh wasu manya manya bulalin bishiyar dalbejiya

Ta nufosu gadan gadan baji ba gani tafara sauke musu zabga zabgan bulalun nan ajiki babu ko imani bare tausayi, ihu suƙe hiyana da diyana suka haɗu suka kare lamrat, duka inna ta musu sosai sai da ta kutun suna iya kuka har kukan nasu ya daina fita sosai, sai da ta bugesu iya san ranta san nan ta kyalesu tana faɗin kutashi tun kafin na rufe ido na buɗe ku ɗauki kofi ku tafi ku ɗebo min ruwa,yanzun nan kugama kuzo ku jemin tallah tana kai karshen maganar ta nufi ɗakin ta, da kyar suka mike suka nufi Kichin suka ɗauki cups suka fice daga gidan, Amrat dake duƙe a wajen wanke wanke tana wanke kayan inna sai kuka take kamar ranta zai fita ba abun da take tunawa sai mahaifiyar su a zuchiyar ta take faɗin yanzu da umman mu bata rasu'ba da tana nan inna bazata musu haka ba wayyo Allah ka jikan umma da bappa haka dai Amrat wunin ranan ta wuni tana kuka su diyana kuwa suna jidan ruwa da kofi ga yinwa ga nisan rafi ga zafin rasuwar Bappa.


Misalin karfe 11 nadare zaune suke a dakin'su dukkan'su ba wan da yayi barchi saboda yinwar dasuke ji ta hanasu barchi diyana che ta dubi hiyana tafara Magana "hiyana yaufa tun safe jinin nan yasake dawowa na chanza zani har nagaji duk kayana sun kare jinin kuma bai daina fitowaba
A ɗan tsorache Hiyana tache "bari na lallaɓa naje na tambayo innar yaya bello sai muji kodai akoi wani abun da zakisha sai ya daina zuwa a razane lamrat tace "Aunty diyana wani jini kuma, diyana zatayi magana hiyana ta rigata da chewa ina ruwan'ki dake ake magana ne, shiru lamrat tayi taba sake magana ba
Amrat dai takasa magana jimamin mutuwar bappa har yanzu bai saketa ba, dan kuwa duk tafisu shakuwa da Bappa su basu yawan zama dashi sosai saboda aikin ɗeban ruwa da tallah, wani lokachima sai sufi kwana uku basu samu damar ganin saba saboda balai inna,shiya ita amrat tafisu shiga damu dan kuwa ita kullum tana gida idan tagama wa inna aikin gida sai tatafi ɗakin bappa, ta kwanta ajikinsa suyita hira.

Mikewa hiyana tai tana faɗin, bari dai na lallaba naje wajen innar yaya bello dan nasan itama batayi barchiba,tana kai karshen maganar ta fiche daga ɗakin, lallaɓawa take kamar wata ɓarau'niya ta fiche daga gd tana fita ta kwasa da gudu dan tsoro dare yayi ga duhu, sai data shiga gidan su yaya bello san nan ta ta tsaya tafara tafiya a hankali hankali dan kar wani yaji ya ganta ya faɗawa inna

Da sallah ta shiga ɗakin innar yaya bello sai wani sanɗa take innar bello na zaune a tsakiyar ɗaki ta tasa dakkere a gaba tana chi ganin Hiyana yasa tamike tana tambayar ta "lfy hiyana me yafito dake chikin daren nan "lfy inna daman nazo tambayar ki wani abune "to menen faɗi, hiyana tasanar da ita komai abun da yafaru da diyana har fyaden da buba yaso yayi mata san nan taɗora da chewa kuma inna jinin fa kwana binyu da suka wuche ya dai na zuba sai yau kuma ya dawo
Shiru inna ta ɗanyi kafin tace "kai buba Allah dai yashirya mana shi batun jini kuma al'adane bari nabaki pant da tsunmma guda 2 kibata tasa summa daya yanzu dasafe sai tachire ta wanke ta shaya, sai ta dauki dayan tasa, ba'a ajiye summar jinin kinaji na da an chire za'a awanke, to wakai hiyana tace, inna tanufi kwallar kayan sawar'ta ta buɗe ta dauko pant da tsunmma guda biyu ta mikawa Hiyana, amsa tayi tana fadin "to inna tayaya zatasa, inna tasake amsar summar tasa a chikin pant ɗin ta nuna mata yadda zatasa, san nan ta miƙa mata, Hiyana ta ansa tana faɗin mungoɗe inna,tanufi hanyar fita har takai bakin kofa sai kuma ta juyo tache inna "menene al'ada kuma
Inna tache "idan mace ta girmane yake zuwa mata kuma alokachin da mace tafara al'ada to karta yarda wani namiji ya sake tabata idan kuma tabari ya taɓata tofa zata samu chiki
Zaro ido waje hiyana tai jin an ambachi su nan chiki murya har rawa yake tache inna to meyasa ni banyi al'adan ba kuma ai niche babba, dafe kai inna tayi tana faɗin "kai hiyana sarkin tambaya to ai kowa da irin halittarsa ne shiyasa wata zakiga shekara 13 take farawa wata kuma sai takai shekara 16 to kowa da irin tasa halittar "to inna kullun yake zuwane dan naga na diyana fa yanzu kusan sati 1 ke nan kuma diyana tache kwana biyu dasuka wuche ya daina zuwa yau ne kuma yasake dawowa, shiru inna ta ɗanyi kafin tace "ina gani diyana na da sanyi'ne shiyasa al adan ke mata rikichi, yanzu dai dare yayi kije gd inkin samu lokachi idan azzalumar innan kun nan bata nan sai kizo in baki maganin sanyi kibawa diyana, yanzu kinga dare yayi kuma ban haɗa maganin bama tukun nan Hiyana tache "to inna mungoɗe sai da safe ta nufi waje tana fitowa kofar gdsu yaya bello, da gudu tayi gidan su chikin duhu dan dare yayi tana tsoro
In da ta barsu diyana a nan tadawo ta samesu zama tayi gefen Amrat tafara yiwa diyana bayanin da inna tamata
Diyana kam tunda akafara bayani take sauraro anazuwa wajen da akache intabari namiji yataɓata to zata samu chiki a tsorache tache
Hiyana yanzu ko yaya bello tab nashiga uku na wlh yanzu ke nan zan samu chiki tun da kunga ko jiyama na kama hannun yaya bello,wayyo Bappa na dan Allah meyasa katafi kabar mu yanzu ni ya zanyi da raina ni diyana da chiki
Girgiza kai hiyana take tana faɗin "ki dai na kuka diyana kinji kibari dasafe sai muje mu tambayi inna muji kina da chikin ne ko babu, da kyar hiyana tasamu diyana tayi shiru, san nan to koyawa diyana yadda zata yi amfani da tsumma da pant ɗin kamar dai yadda innar yaya bello ta koya mata, mikewa diyana tayi hiyana ta taimaka mata tasa pant ɗin san nan tasa tsunmar, suka kwanta shiri babu wan da yasake magana da haka har barchi ya ɗauke su



3 days later

Zaune take a tsakar gida ita kadai diyana ta tafi tallah amrat tatafi wanki kayan inna a rafi lamrat kuma tana debo ruwa ita kuwa inna ta bartane tamata girki
Shigowa gidan inna tayi babu koh sallama tache "ke hiyana ko ki shirya ko karki shirya gobe za'a ɗaura auren ki da buba
Hiyana dai bata che da inna ko mai ba amma a chikin zuchiyarta tana tunanin yadda zata gudun wa Auren, wunin ranar kuka hiyana ta wuni yi dan yau rasuwar bappa ya dawo mata sabo fill tasha kuka har blue eyes nata suka kumbura suka kankan che.

Da daddare bayan su diyana sun dawone suna zaune a dakinsu kamar yadda suka saba
Hiyana ta dubi su diyana tafara magana "lokachi yayi da zamu bar gidan nan
A tsorache diyana tace "to muje ina muda bamu san kowaba bamusan ko inaba "ko bamu san ko inaba yazama dole mu bar gidan nan, dan gaskiya bazan Auri buba ba wlh na tsanesa bansan ganinsa mugune, gaskiya bazan tsaya a ɗaura mana Aure ba hiyana ta karisa maganar kamar zatayi kuka "to yanzu idan mun bar gidan nan ina zamuje diyana ta tambaya fiskarta chike da damuwa "kidai na damuwa diyana, zanyi tunani a kai dole na nemo mama inda zamuje chewar hiyana da sauri lamrat tace "to ko zamu nemo addan (yaya) bappa ne ba yataɓa faɗa mana yana da adda ba (yaya)
Hiyana tache "to ai na zamuganta kenifa baruwana da kowa, yauwa birni zamu tafi muje munemi aiki har musamu kudi
Taɓe baki diyana tayi tana faɗin to yanzu muda bamu san hanyar birni ba ta ina zamu tafi, karfa mu bar gidan nan muje mu haɗu da masu yan kan kai suyan ke mana kai, da sauri Amrat tace "wlh bappa yataɓa faɗamin akoi masu yan kan kai a birni, kara zaro ido lamrat tayi, tana faɗin "tab nikam ba zanje ba wlh gara na zauna a nan ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kallon hiyana diyana tayi tace "to yanzu ya zamuyi Shiru hiyana ta ɗan yi kafin tace ke dai karki damu zansan yazamuyi, yanzu kan mu kwanta muyi barchi, da safe in munje ɗeban sai mukarasa maganar a rafi, har suna haɗa baji wajen chewa to

Suna kokarin kwanchiya kenan sukaga inna ta faɗo musu ɗakin kafin su ankara tafara sauƙe musu bulalun hannun ta ajiki, bugun su taƙe tana faɗin "buba ne bakiso ko to wlh koki mutu ko kiyi rai sai kin auri buba daga yau ba mai sake fita a gidan nan a chikin ku rufe ku zanyi a dakin nan ke hiyana gobe za'a kai ki gidan buba kukuma sauran yin'wache zata kashe'ku a chikin dakin nan dan kulle'ku zanyi ba inda zaku sake zuwa
Kuka suke sosai sun manne da juna diyana da hiyana sun haɗu sun karewa lamrat da Amrat ajikin su kawai bulalan ke sauka, inna kuwa bugun su take baji ba gani da iya karfinta,sai da ta farfasa musu jiki tukun nan ta kyalesu ta fiche daga ɗakin, kankame juna sukayi suna kuka a haka barchi ya ɗauke su


Kano ta dabo

Ammi na zaune a gefen katafaren gadan Abba shi kuma Abba yana kwanche a nitse da sanyayyiyar murya tace "ranka yadaɗe inasan muyi magana, mikewa Abba yayi daga kwanchiyar da yake ya zauna yana fiskantar ta "ina jinki Aishstu na manene yayi maganar yana kallan chikin idon ta, kasa da kai Ammi tayi chikin ladabi da girmamawa ta fara magana " daman inasan zuwa Yola ne wlh kwana biyun nan,bana jin daɗi ina ganin kamar akoi damuwa ina yawan mafarkin Ahmadu kasan shi ya ragemin kuma gashi na yaddashi, abun yana yawan damuna sosai, inajin a jikina kamar Ahmadu na chikin damuwa,tunaninsa har tafara yimin yawa, dogon numfashi Abba yaja kafin yace "ba'damuwa Aisha ae kin jima baki jeba kusan shekara 7 ke nanfa gaskiya yakamata kije, ki shirya sai kuje da su Safras su rakaki
"da murna Ammi ta juyo ta rungumi Abba tana faɗin ilove U ilove U
rungumeta sosai Abba ma yayi yana faɗin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login