Showing 123001 words to 126000 words out of 363274 words

Chapter 42 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2604

chikine ko kuma, bazan samu ba"

"My diyana jeki ɗaki ki kwanta ba wani chikin da zaki samu ai shima Abdurahman ɗin yayan kine.
"To Aunty farida" tana kaiwa nan ta wuche ɗaki,

"Hajj farida wacece wan nan kuma? Hajj fateema ta tambaya tana nuna diyana dake tafiya ɗakin su da hannu,
"Kanwata ce Aunty farida ta bata amsa tana kokarin komawa ta zauna saman kujerar da ta tashi. "Gaskiya hajj farida naji kanwar nan taki ta kwanta min arai sosai jinake kamar ki bani ita, waro ido waje Aunty farida tayi chikin zuchiyar ta tana faɗin "tab lokachi yayi da zan hana kowani bakona ganin diyana, yarinya ne sai shigen farinjini kowa yace yana son ta ba maza ba ba matan ba kowa abashi ita kawai.

"Hajj Farida lfy? Tunanin me kike"?
"Ba komai hajj fateema" to ya maganar ya rinyar fa pls ku bani ita" "a'a hajj fateema wannan yarinya amana che awaje na wlh, ban isa inyi kyau ta da itaba, shiru hajj fateema tayi bata sake Magana ba

Yola

Zaune Inna take a tsakar dan ɗakin bukkan ta ga uban amai a gaban ta da ta tula, ta kasa ko mukewa,
Da kyar ta yunkura zata miƙe sai wani amai kuma ya kubche mata, nan fa tasake komawa ta zauna tana kwara amai, tun taba amai da daɗin rai har tafara fita hayyachin ta,
Tana amai ta baki tana zawayi ta kasa, sosai ta jajjaje ta ko ina sama da kasa gaba ɗaya yoyo yake, kwanchiya tayi cikin zawon nata tana nunfashi sama sama, kamar zata mutu gashi babu kowa bare ta sa ran za'a tai maka mata.

Wannan kenan tun da munzo munga ya inna take mu koma gidan Abba kuma

KANO

Da sallama ɗauke a bakinta hiyana ta shigo chikin ɗakin da yaya Ahmad ke kwnache dakin babu kowa, Allah sarki bawan Allah gaba ɗaya ya rame ya kare, baya iya chin komai sai dai ruwan da ake ta saka masa, yayi baki sosai kamar ba shiba

Karisawa bakin gadon dayake kwanche,hiyana tayi ta zauna a gefen sa kaɗan, cikin sanyin murya tace "yaya Ahmad ya jiki, tayi maganar tana kallon face nashi, shima ita yake kallo, kumshe mata ido yayi ya sake budewa

Zubur hiyana ta miƙe tana faɗin "yaya Ahmad daman kana jin me muke faɗe? Lumshe mata ido yayi san nan ya buɗe, komawa tayi a hankali kusa dashi ta zauna, shiru tayi na ɗan mintoci, tana tunani "da alama chiwon yaya Ahmad ɗin nan yayi kama dana shafun aljanu ko kuma sihiri, domin duk wata alama da suratul baƙara ta bayyana a matsayin shafin aljanu ko sihiri to ya bayyana a tare dashi, amma duk gidan nan ba wan da zaka faɗawa hakan ya ɗauki abun da mahimmanci, bari dai nayi nawa kokarin kawai mugani" juyo da blue eyes nata tayi kan face mashi,

A hankali ta fara motsa lallausan pink lips nata ta fara karanto suratul baƙara, domin rusatul bakara surache datake karya sihiri, duk girman sihiri zata karya shi, haka zalika surache mai ɗauke da maganin duk wata chuta da take duniyar nan, sai dai idan bakasan in da ayar warakar chutar ka takeba a chikin surar, matikar kana karanta suratul baƙara tofa aljanu ma ba zasu zo in da kake bama bare wani sihiri.

Tun hiyana na karatu a hankalin har tafara da ɗan karfi karfi, kamar daga sama taji wani tsawa, da murya mara daɗin ji, nan take iska mai karfi ta taso a iya ɗakin kawai kuma, hakan ne yakara tabbatar wa da hiyana chewar lallai chiwon yaya Ahmad, asirine ko kuma aljanu, duk da iskan da ya taso a ɗakin da tsawar da akayi mata hakan bai hanata chigaba da karatun ba, sai ma kara ɗaga murya da tayi duk da a tsorache take.

Kamar yadda take kara saukin voice nata wajen karatun haka iskan ma ke kara yawaita, matso da ɗan karamin bakin ta tayi dai dai sai tin kunnen yaya Ahmad ta chigaba da karatun da ɗan karfi,

Wani ƙara yaya Ahmad yayi da wata iriyar voice mara daɗin ji wadda yasa hiyana mikewa da gudu ta bar ɗakin, tana faɗin "na shiga uku na to wai daman me ya kaini gudu take sosai da sosai kamar zata tashi sama, tazo dai dai, wajen part ɗin yaya Aryan sukayi karo da Bgs, domin bata lura da mutun yana zuwaba kawai gudun cheton rai take, da karfi kanta ya bugu da kirjinsa tayi baya ta faɗi kasa, tana numfashi da kyar

Kafar sa ya ɗaga ya tsallake ta ya wuche ya shige part ɗin Aryan, ya barta zube a kasa

Da kyar hiyana ta iya mikewa tana jan kafa a hankali har ta shiga part ɗin Ammi.


Abangaren Bgs kuwa,

Awan nan karon ba ko sallama ya faɗa betroom ɗin Aryan,
Aryan na kwanche saman katafaren gadon sa ya rufe gaba ɗaya jikin sa da blanket har fuska, chikin ɓachin rai Bgs ya shigo ɗakin Amma yana ganin yanayin da Aryan ke chiki hakan yasa ya manta da wani bachin rai ma ya nufi gadon da sauri.

Yaya blanket ɗin yayi ya zubawa Aryan green eyes nashi, fiskar nan tasa tayi fayau ya kara haske sosai, jin an yaye masa blanket din ne yasa ya waro idon sa a hankali, ya sauke su kan face ɗin Bgs

"Subhanallah Aryan meke damun ka? Baka da lfy ne? Idon ka na chiwone?" Bgs ya jero masa tambaya a ruɗe.

Dafa kafaɗar Bgs Aryan yayi yana kokarin mikewa da sauri Bgs yasa hannu ya tai maka masa ya miƙe zaune.

"Aryan what is wrong with U?" "Nothing bro Nothing kawai barchine" shiru Bgs ya ɗan yi kafin yace "ok to ina kaje tun da safe nazo nan two time baka nan, bayan kuma nasan babu in da kake zuwa, na kira layin ka akashe, ina kaje?"
"Yola naje mana" Aryan ya bashi amsa yana kwaɓe fuska.

"What? Yola kuma to me kajeyi a chan?" "Wai dan Allah Bgs kai ɗan sanda ne da zaka sakani a gaba da tambayoyi, ko kuma ni yaron kane, pls my blood ka rabu dani ka rabu dani.

ikon Allah Bgs dai green eyes nashi ya zubawa ɗan bakin Aryan yana ganin yadda yake zuba masifar,
Ganin Bgs ya tsare sa da ido ne yasa ya ja tsaki ya juya ya zuro kafafun sa kasa yana kokarin sauka daga gadon.

"Kai ina zakaje kuma? "
Wayyo Allah Ni Aryan na shiga uku wai dan Allah Bgs baa neman ka a London ne? ya kamata ka koma wlh ka addabeni pls ka rabu dani.

Bgs daya ga abun na Aryan yana neman ya wuche gona da irin sai ya ɗaure fuska sosai chikin tsawa da bada umarni yace

!!"Ina zakaje Aryan" Aryan ya gane me Bgs ke nufi wato zai nuna masa chewa ya fishi a shekaru kuma ya fishi awajen aiki dan sama yake dashi.

a kule yace "to ai nan ba wajen aiki bane gida ne, wai dan Allah Bgs bazaka barni naji da abun dake damuna ba so kake kasa zuchiya ta ta tarwatse ne? Ko so kake na mutu ka huta ko? So kake ka bugamin kwakwalwa tane? Pls my Oga ka kyale ni haka"

Tunani Bgs ya shigayi "tabbas ina bukatan in san menene matslan ɗan uwana domin bai taɓa mayar min da magana haka ba, kome zan masa kuwa, jikin sa yayi mugun sanyi a hankali ya zuro kafarsa kasa ya
Sauko daga gadon ya tako zuwa in da Aryan ke tsaye.

Hannu biyu ya ɗora saman kafadar Aryan chikin sanyin murya ya fara magana "ban san meke damun kaba Aryan kuma bazan sake tambayar ka meke damun kan ɗin ba, domin nasan kai ma baka sani ba idan kasani to bazaka ɓoyemin ba, amma tabbas kana da damuwa kadage da addu'a nima zan tayaka sosai, har Allah ya kawo maka sauki, amma yanzu dai ka faɗamin ina zakaje?

Rungume Bgs Aryan yayi yana faɗin "wajen Ammi zanje, daman tun da na dawo nake san zuwa wajen ta amma ɓachin rai ya hanani zuwa kuma bana soma naje wajen ta ina cikin bachin rai, dan kar zuchiya da sheɗan su zugani nayi ba dai dai ba, shiyasa kaga na kwnata ina jiran zuchiyata tayi sanyi"

Hannu ɗaya Bgs yasa yana ɗan bubbuga bayan Aryan ɗin kaman yaro yana faɗin "ok kaje ni kuma daman wajen Abba zanje ya kirani, yana son gani na, sai mun haɗu anjima" yana gaama fadin hakan ya saki Aryan ɗin ya juya ya nufi waje, bayansa Aryan ma yabi kusan tare suka fito, Bgs ya nufi fada Aryan kuma ya nufi part ɗin Ammi


Da sallama ya shiga betroom ɗin Ammi, kamar kullun tana zaune a bakin gadonta tana karatun qur'ani mai girma, karisa shigowa chikin ɗakin yayi dan yau bai tsaya jiran sai an bashi izinin bama,

sama throw pillow, manya manyan dake tsakiyar ɗakin ya zauna, shiru yayi yana sauraron karatun qur'ani suratul ma'ida, da Ammi ke rerawa

sai da ta kai aya sai nan ta rufe qur'ani ta ajiye a saman drawar gefen gadon, ta dawo da kallonta kan face nashi, chikin ni tsuwa tace "Aryan lfy dai ko?
Dogon numfashi yaja kafin yace "Ammi pls tell me ina kika kai yarinyar nan?

Aryan na faɗa maka ai na mai data gidan babanta. "No Ammi bata chan ai naje Yolan da safe wlh bata Chan

Wani dukan uku uku Ammi taji kirjin ta yayi tunani ta shigayi, "gaskiya dole naje nasamu mai martaba, lallai na yarda Son da Aryan kewa diyana ba son wasa bane, har yola yaje saboda ita, tab a lallai dole azo abashi matar sa wlh, dan ni nariga na bashi ita duniya da lahira.

Ganin ammi tayi shirune yasa Aryan yace "Ammi pls ni na san ke mai Son muche baki son bachin ranmu dan Allah ki faɗamin inda take

"Aryan ban isa in faɗa maka in da diyana takeba kaje ka tambayi Abban ka kaji nima Umarnin sa nakebi, a sukwane Aryan ya miƙe yana faɗin "au daman Abba ne ya yasa aka ɓoyeta wlh yau sai ya fitomin da ita yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin chikin bachin rai.

Kai tsaye fada ya nufa, yazo dai dai zai shiga fada sai ya tuno Abba na tare da Bgs dan haka sai ya juya kawai ya koma part nashi

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)





More comments an like pls
*💫STAR LADY💫*34

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣4️⃣*


Misalin karfe 5:30 na yanmma Abba na zaune a fada yayi shiru kamar mai tunanin, da sallama dauke abakin sa Aryan ya shigo ranshi a ɓache fuskar nan tasa kamar bata san menen dariya ba, daku yake irin na jaruman maza, saman kujerar dake kusa da Abba yaje ya zauna, sai wani fitar da iska mai zafi yake daga bakinsa.

"Aryan lfy naga ran ka aɓachin haka"
"Abba pls ka dawo da yarinyar nan gidan" murmushi gefen fuska Abba yaɗan saki a chikin zuchiya yana faɗin "kafara zuwa hannu kenan ae daga kai har sauran sai nayi maganin ku chikin ruwan sanyi zan dafaku.

"Abba pls magana nake makafa wai ina ka kai tane? "Wace yarinya kuma Aryan? " Abba yarinyar dake kai mini coffee ɗin nan mana, daure fuska Abba yayi sosai kafin yace "au daman akoi wata yarinya dake kai maka coffee ne a gidan nan ban sani ba" a sukwane Aryan ya ɗago ash eyes nashi yana kallo Abba,
Ƙara ɗaure fuska sosai Abba yayi
"Eh mana Abba yarinyar da Ammi ta ɗauko su daga Yola" "to ae Aryan su huɗu ne wane daga chikin su kenan? Dafe kai Aryan yayi dan shi kwata kwata bayason kiran sunan diyana gashi kuma Abba yana neman ya kuresa.

"Abba wan nan mai bin babban, ni ban san sunan taba, ba karamin daɗi Abba yaji ba ganin yadda Aryan ke girmama sunan diyana har bai son kiran sunan, hakan ya kara tabbatar masa bakaramin so Aryan kewa diyana ba, dan haka sai yace
"Au diyana kake nufi? Da sauri Aryan yace "eh Abba ita nake nufi.

"To me yasa kakeson adawo da ita kuma? bayan kai ne da bakin ka kace baka son ganinta"

"Nifa Abba banche bana son ganin taba" "to naji ba kache ba amma yanzu me yasa ka keson adawo da ita? "Abba ina son adawomin da itane tazo ta chigaba da kawomin coffee dan tafi kowa iya haɗa coffee a gidan nan"
Nan take Abba yaji ransa ya ɓache, bakaramin haushi Aryan ya bashiba, wato dai bazai che yana son taba kuma har yanzu dai bai san darajar taba, tunda kallon mai kawo masa coffee yake mata wlh zanyi maganin shi kuwa"

chike da ɓachin rai yace "ai ba ita kaɗai bace daga yauwa duk gidan nan ba wanda zai sake kai maka coffee sai dai masu aiki domin nache Ammin ku ta ɗauko min sune dan suzo su huta ba wai suzo suyiwa wani ko wata aiki ba, kuma bazan dawo da itaba tabar gidan nan kenan, a chan zan mata Aure, na huta itama ta huta"

Da karfi Aryan yace "No Abba no ka daina irin wadan nan maganganun wlh kanasawa naji zuchiyata kamar zata buga zan iya mutuwa Abba banason jin su" da mamaki Abba ke kallon Aryan, yasan chewa duk chikin ƴaƴan shi ba wanda ya kai Bgs Aryan Fahad kishi, suna da bala'e kishi sosai kuma da kishin nasu zaiyi amfani yayi maganin su.

"Abba dan Allah ka dawo da ita" "Aryan Allah bazan dawo da itaba sai ka faɗamin akan wani dalili kakeson ta dawo?
"Abba na faɗa maka ai coffee zata rinƙa kawomin" mikewa Abba yayi chikin fushi yace "to kai ba left kanal ganaral na sojoji bane sai ka nemo in da take ai da kanka, yana gama faɗin hakan ya nufi hanyar fita faga fadan ma gaba ɗaya
Kwafa Aryan yayi yana faɗin "ai kuwa zan nemota Abba zakasha mamaki, chike da kwarin guiwa da yadda da kansa ya mike shima ya fice daga fadan.

Washe gari da safe misalin karfe 5:30, hiyana che tafito daga part na Ammi sai sauri take kamar zata tashi sama, tana tafiya tana yan waige waige, kamar mara gaskiya, kai tsaye ɗakin da Yaya Ahmad ke kwanche ta nufa,
A hankali ta tura kofar ta shiga hannunta rike da roban ruwan faro,

kamar dai kullun kwanche yake idon sa biyu yana kallon sama, ga hawaye nan bushe a fuskar sa, ta gefen kunne Allah sarki bawan Allah da alama kuka yasha.

Kusa da shi hiyana taje ta zauna tare da fadin "yaya Ahmad ya jiki?" dawo da kallon sa yayi kanta ya lumshe mata ido ya buɗe alamar da sauki.

"Yaya Ahmad zaka iya shan ruwan adduar nan wlh jiya kwata kwata ban yi barchiba kwana nayi ina maka addu'a, tayi maganar tana nuna masa roban ruwan faro dake hannun ta, ɗaga mata ido sama yayi alamar a'a ita kuma, hiyana bata fahimtar ba, kasan chewar iya lunshe ido kawai tasan yanayi, chiki sauri ta ɓuɗe robar ruwan sauri sauri take dan bata son kowa ya ganta kuma tasan su Bgs suna dawowa masallaci zasu zo duba shi dan suga ya ya kwana, ita kuma tana son ta bashi ruwan addu'ar kafin ta tafi school.

Tsiyaya ruwan tayi a marfin gorar, san nan tasa ɗayan hannun ta ta ɗan buɗe bakin nasa ta zuba masa, ruwan zuba wa bakin nashi ido tayi tana gabin yadda ruwan ke dawowa alamar ba zai iya haɗiyewa ba, wani iri taji sai taji gaba ɗaya jikin ta yayi mugun sanyi, Allah kawai take roko da yasa yaya Ahmad ya haɗiye ruwan nan koda kaɗanne.
Tana chiki wan nan yanayin ne tajiyo diran motochin su yaya prince alamar sun dawo daga masallaci, kuma tasan kai tsaye ɗakin zasu zo
A sukwane ta ɗauki gorar ruwan ta nufi waje, tsabar sauri har tana kokarin faɗuwa.

Allah dai ya rufa mata asiri babu wanda ya ganta a chikin su, har ta shige part ɗin Ammi


Maiduguri

Diyana riƙe da hannu junior suka fito harabar gidan, nan suka sami Aunty farida da dadyn junior zaune chikin mota suna jiran su, da sauri suka karisa wajen motar suka buɗe gidan baya suka shiga, dady'n junior da kanshi yayi driving nasu a nitse yake tuƙi
Da sauri baba mai gadi ya wangale musu katafaren gate ɗin gidan, a hankali dady'n junior ya dan na hanchin motar waje,

tuki yake suna yar hirarsu da Aunty farida, chikin ƙanƙanin lokachi suka isa school nasu junior, batare da bata lokachi ba dady'n junior ya fito daga mota ya barsu Aunty farida a gurguje yaje yayi wa diyana komai na registration da sauransu san nan ya dawo yace "diyana da junior su biyo sa,yana gama faɗin hakan ya juya ya fara tafiya, da sauri suka fito diyana ta rike hannun junior sukabi bayan sa ya rage Aunty farida che kaɗan a motar, office ɗin HM na school ɗin suka shiga, anan ya miƙa masa amanar diyana ya juya ya tafi

Hm


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login