Showing 294001 words to 297000 words out of 363274 words

Chapter 99 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2556

Aryan ina a a a" kasa cigaba yayi da magana sakamakon ciwon zuciya da ta kama shi lokaci guda dafe sai tin zuciyar sa yayi kafin Aryan ya farga sai ganin sa yayi ya sulale kasa yayi flat kamar gawa baya numfashi a ruɗe Aryan ya kira likitoci suka ɗauki sa,sanan yace a nuna masa ɗakin da hiyana ke kwance, ana nuna masa ba tare da ɓata lokacin ba ya shiga cikin ɗakin
Tana kwance flat tsabar tayi losing blood furkar ta tayi wani irin yellow kamar ba mutun ba karisowa gaban gadon da take kwance yayi ya zuba mata ido yana kallon ta duk taurin zuciya irin mashi sai da ya mata hawaye cikin kuka yake faɗi "sister ki yafe wa ɗan uwana ya Allah kasa bata riƙe ɗan uwana a ran taba wanna wace irin jarabawa ce innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya al...bai karshen maganar ba idon ya sauka akan gefen idon ta hawaye na gangarowa ta wajen yana bin kunnen ta cikin sauri ya ɗaura hannun sa saitin kirjin ta shiru kirjin nata baya bugawa kamar bata da rai da sauri ya zame hannun sa ya kamo tannun ta da karfi ya riƙe sosai yayi shiru kamar mai sauraren wani abu a sukwane ya sakin hannun nata kasan cewar yaji jijiyar hannun ta na harbawa sai dai duk wani jijiya na jikin ta ya tsaya har zuciyar ta ya tsaya da bugawa na ɗan lokaci mawuyacin abune ta tashi ɗiban kayan aikin asibitin yayi ya shiga aikin ceto yaruwar ta duk wani ilimi daya sani a duniyar nan a fannin likita sai da ya tattaro bai ma bi ta kan likitocin ba ya fara tikar aiki dan tana tsakanin mutuwa da rayuwa kai mawuyancin abune ma ta tashi tsaki yaja lokacin daya ga aikin ba zai yiwuba sai an kara mata jini dan jinin ta yayi kasa over cikin sauri ya ɗebi jinin sa ya gwada jinin nasa batayi dai dai da nataba da gudu ya fita ya nufi dakin da aka kwantar da bgs likitoci na kokarin ceto ran shi ya ture su ya ɗaure hannun bgs dake sume ya ɗebi jini gwajin farko yaga jinin su iri ɗaya da hiyana sai dai still jinin bgs akoi ragowar alluran nan da yayiwa kan sa da safe tsaki Aryan yaja kafin yace "da ki mutu gwara na sa miki jinin nashi ko da akoi tangarɗa ai mijin kine kuma yayan ki" yana kai karshen maganar ya koma ɗakin da bgs ke kwance ya fara ɗeban jinin sa mamaki lokacin keyi da basu san Aryan ba da sai suce ya samu taɓin hankali shiko ko kallon in da suke bai yi ba ya ɗebe jini ya fice abun sa dan yanzu rayuwar hiyana ce da muwarsa bai damu da jinin bgs bai dace asa mata ba shi dai tun da jinin iri ɗaya shi kenan ba dai zata tashi ba burin sa ya cika shima da alama ya fita hayyacin sa. Yana kokarin sa mata jinin sai kuma wani tunanin ya faɗo masa akan ya ɓoye hiyana ya kyale bgs akan ta mutu sai ta samu sauki ta dawo dai dai tunani ya fara yi to wace likita ce ta dace tabawa hiyana kulawa dan wanna case natan yasha gaban tunanin sa.
yayi tunanin duniyar nan ya kasa tunano likitar ɗa zai iya bari ta kula da hiyana.
Daga karshe dai ya saɓe ta a kafaɗar sa yayi waje da ita hannun sa rike da ledar jinin bgs ya nufi motar sa. Da gudun gaske yaja motar dai dai zai fita asibitin yayi karo da wata babban likita babbar mace ce dan akalla zata kai 58 years tsayuwa yayi ya mata bayani a gurguje da yake turawa basu da matsala ta wanna ɓangaren sai ta amince ta shiga motar ta bi sa abun dayasa ta kara yarda da shi dan tasan shi babban soja ne tana ganin su a News shi yasa ta aminta da shi tasan bazasu aikata wani abun da ba dai dai ba.
kai tsaye Airport ya wuce da su a jet nashi aka ɗauke su zuwa us dan bai san bgs yasan hiyana na raye duk da yasan yanzu bgs yayi nadama amma suna bukatar kawar masa da zafin zuciyar san nan.

Katafaren gidan Bgs dake us suka wuce duk wani abu da likitar zata bukata ya sai mata sanna ya zube musu kuɗi dayawa har ya fita sai ya kuma dawowa dan gani yake kamar zasu bukaci wani abun ATM card nashi ya ciro ya ajiye musu tare da faɗa wa likitan pin number sa sanna ya wuce nan take dr ta ɗorawa hiyana jinin bgs, shi kuma Aryan ya wuce ya koma uk.

Gaba ɗaya wayoyin sa ya kashe su dan idan Abba ya kira shi bashi da amsar da zai bawa Abba

Lokacin da ya koma uk kai tsaye ɗakin da bgs ke kwance ya wuce babu kowa a ɗakin bgs ne kaɗai ke kwance har yanzu baya numfashi da alamar bai farfaɗo a an daura masa karin ruwa juyawa yayi ya koma office na babban likita dan jinme ke damun ɗan uwan sa.

Zaune ya isko babban likita ba tare da bata lokaci ba cikin harshen turanci yace "dr meke damun dan uwana? gyara glass na face ɗin sa dr yayi ya fara yiwa Aryan bayani kamar haka "zuciyar ɗan uwan ka na gab da bugawa sakamakon zafi daya ɗauka sosai kuma da alama ya rasa wani abun da zuvyiyar sa ke so ko kuma kun hana shi wani abun da zuciyar tasa ke so munyi iya bakin kokarin mu dan ganin ya rayu yanzu sai dai mujira ta Allah kawai amma yana iya mutuwa ako wani lokaci haka kuma yana iya rayuwa ako wani lokaci mungama aikin mu sauran naku ku tayasa da addu'a" shiru Aryan yayi yana tunanin wanna wace irinyar jarabawa ce mai wuyar gaske mikewa yayi ya fito waje jiki ba kwari ya ciro wayar sa ya kunnata ya nan ya ci karo da miss call sun fi 70 daga gida kawai aunty Farida Abba kusan miss call 30 suka masa ba wanda bai kira layin sa a gida ba layin Aunty farida ya fara kira dan yasan ita kaɗai zata fahimce sa kuma ta taimaka masa.
Bugu ɗaya ya mata ta ɗauka a ruɗe babu ko sallama tace "Aryan lafiya ka kashe wayar ka? Ina kake? ina su Prince da hiyana? Ka gansu ne? Suna lafiya ko?da kyar ya iya cewa "Aunty farida pls calm down tun da kikaga na kiraki ai kome ke faruwa zami ji yanzu dai idan kina cikin mutane ki fito kije keɓabɓen waje zamuyi magana" "Aryan ka faɗa min meke faru ni kadai ce dan ina part ɗin Ummi ina ɗaki na nazo yin wanka ne" nan Aryan ya shiga bata labarin duk abun dake faruwa ba abun da ya rage mata cikin tsawa tace "hauka Safras yake yi ne zuciya haukace duk zuciyar sa wlh bai kai ko rabin Ammi ba amma tana iya sarrafa nata wlh ina da tabbacin idan su Ammi suka samu labari idan bata tsinewa prince ba to zata cireshi daga ƴaƴan ta wanna wani irin zalunci ne!!? "Aunty farida ki bar wanna maganar tun da yanzu shima yayi nadama kuma shima yana halin mutuwa ko rayuwa ya kamata mu sassauta masa yasamu sauki ta bangaren mu ko zamu samu ya farfaɗo thank God da sister bata rasu ba abun zai zo mana da sauki abun da nake so dake yanzu ki shirya ki je Airport ki zo kasar nan dan inason bgs ya samu farincikin na cewar mu bamu gujesa ba kinga ta haka zamu iya ceto ransa amma idan muka gujesa wlh Aunty farida mutuwa zai yi dan yana ɗaya daga cikin abun da yasa zuciyar sa ta kusa bugawa yana bala'i son mu yana tunanin kowa daga cikin mu yanzu zai gujesa gashi matar sa ta rasu shi yasa ya shiga tashin hankali har zuciyar sa ta kusa bugawa yanzu dai kinga na ɓoye sister kuma baza mu bayyana taba sai ta warke sumul ta dawo dai dai ta manta da duk wani ciwo zamu nemi abun da zamu faɗa wa su Abba shi kuma bgs zamu barshi akan sister ta rasu dan ya wahala sosai sai ya cire zafin zuciya gaba ɗaya a rayuwar sa sanna mu bayyanata" "na gamsu da maganar ka Aryan amma yanzu abubuwa biyu ne agaban mu na farko dole dadyn Junior yasan da maganar dan ya bani goyan bayan wajen sanar da su Abba na koma Maiduguri dan karsu neme ni abu na biyu shine kasan dai ko me zamu shiryawa su Abba akan su hiyana bazasu taɓa yarda ba zasu ce suna san yin magana da ita awaya" "no Aunty farida ki bar wanna zancen ki bari idan ta farfaɗo ni zan iya haɗa ta da su Abba awaya sister tana da hankali kuma tana jin magana ta bazata sanar da su komai ba" "anya Aryan hakan zai yiwu kuwa ya za'ayi shi Prince mu sanar da shi ta mutu kuma mu sanar da su Abba tana raye baka ganin zai iya zuwa yace zai nemi gafarar su Abba har ya samu labarin bata mutu ba?" "Aa Aunty farida kinsan burin su Abba ne daman su ɗauke ta su ɓoyeta har sai ya san darajar ta zanyi magana da Ammi zance mata sunyi haɗari ne sai na faɗa mata abun da ya faru a asibiti har naje na ɓoye sister kinga zasu tafinwa bgs akan ta mutu ke dai ki barmin komai a hannu na kinji?" "To shikenan gani nan zuwa bari na shirya sai na sanar da dadyn Junior sai na tawo airport ɗin sai munyi waya" to kawai yace sanna ya katse kiran

To nima anan na katse karatun sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu love u lodi lodi masu min comments Allah ya kare min ku Allah ya bar zumunci 🥰🥰
[8/1, 7:14 PM] SAFIYYA: 💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By
Star Lady



Page 47



Kamar kullun yau ma Abba ya tara ahalin sa da suka rage a gidan a palon sa suna tattaunawa akan matsalar hajj Fateema kallon Hajj fateema Abba yayi ya fara magana "munyi magana da malamai daban daban akan case naku shi Abu Abdurahman yanzu babu Aure tsakanin ku kwata kwata kuma kin haramta gare shi sa kamakon yana sane yayi Aure kan aure da gangan yayi sai batun ƴaƴan wata nafsi tace ƴaƴan subuhane wata kuma tace shegune amma nafsin da ta shagan tasu ta fi karfi dan haka ita zamu ɗauka a taikace dai ƴanzu ƴaƴa naki ne ki rike kayan ki ba ruwan sa da ƴaƴan,zaki iya yi masa sallama yanzu sallama kuma ta har abada sanna kiyiwa baban su hiyana takaba dan shine asalin mijin ki bai sake ki ba bayan takaba zaki iya yin wani Aure"salati gaba ɗaya jama'ar palon suka sa saboda ba wanda ya zaci hakan sosai Aunty mardiya tayiwa Ayaam da Ayana kuka yara bayin Allah basu san komai ba an mai da su shegu yanzu idan suka girma ya zasuyi da rayuwar su ya zasuji alokacin da suka samu labarin abun da baban su ya aikata kai son zuciya dai kwata kwata bai yi ba Allah wadaran mai son zuciya. Kuka Abu Abdurahman yake sosai kamar ƙaramin yaro cikin kuka yake faɗin "son zuciya bata yi ba na cuci su Ayaam na san bazasu taɓa yafe min ba idan suka girma jama'a zasuyi ta ce musu shegu kenan? innalillahi wa inna ilaihir rajiun na cuci kaina na ɓata zuri'a ta wanna yazama muku darasi gaba ɗayan ku mutanen dake palon nan karku biyewa sharrin zuciya karku bi san zuciya zakuyi nadama mara amfani wayyo Allah" kuka yake sosai hawaye sharshar haka su fariza suma kuka suke sosai dan har ga Allah suna son Hajj fateema har cikin ransu ta rike su da amana da zuciya ɗaya,bakin cikin da shagan ta ƴaƴan ta da Abu Abdurahman ya ja musu yasa Hajj fateema yanke jiki ta sume dan bazata iya jurewa ba shi kansa Abba daurewa yake Ayaam da Ayana sun bashi tausayi sosai "yanzu menene amfani son zuciya" cewar Ammi da sauri Aunty mardiya ta ɗauko ruwa zata zubawa Hajj fateema Fahad yayi saurin cewa "aa karku zuba mata ruwa ku kyale ta ta huta idan kuka zaba mata ruwa ta farka zuciyar ta zai iya bugawa ku kyale ta na yan mintoci ko 1h" dawo da kallon sa yayi kan Abu Abdurahman yaci gaba da cewa "Abu Abdurahman zaka iya kwashe ƴaƴan ka ku tafi dan karku karasa mana uwa idan ta farfaɗo,ban son ta farfaɗo ta sake ganin face naku" ya kai karshen maganar akule da sauri Yusuf yace "aa ai dole ya ansa hukunci kamar yadda addini ya faɗa domin abun da yayin nan dai dai take da wanda yayi zina da matar Aure" "good ka faɗi gaskiya Yusuf" cewar Khalid kallon Abba Ahmad yayi yace "wai ina Aunty farida ne?" "Tun jiya dadyn Junior ya kirata ta koma Maiduguri"Abba ya bashi amsa kuka sosai amrat lamrat Zahra suke saboda sumar da Ummin su tayi dan ita Amrat bata masan illar acewa mutun shege bama bata ma san akan me ake magana a palon ba ita dai kukan suman da Ummin ta tayi take gwara Zahra da lamrat sun fahimci akan me su Abba ke tattaunawa "Fahad ku ɗauki matan kun nan kuje ku rarrashe su akashe case nan shi kuma Abu Abdurahman ku turashi kotu karku ɗau doka kotu ta masa hukumci su Abdurahman kuma ku sasu a jirgi amai dasu gidan su tun da ba yara bane su zasu iya zama a gida ai, su kuma Ayaam da Ayana ku barmin su har ga Allah zan ruƙe su tamkar ƴaƴa na" cewar Abba da sauri Aunty mardiya tace "Abba dan girman Allah ku bani su ku tausaya min wlh Abba ji nake kamar zan mutu idan na tuna ni ban taɓa aihuwa ba wlh ina son su zan riƙe su na maka alkawari Abba zan rike su kamar ƴaƴan dana haifa" tana magana tana hawaye shi kan shi Abba yana tausaya mata domin rashin haihuwa babban ciwo ne amma a haka sai kaga wasu mata Allah ya basu suna kokarin zubar wa abun da kuɗi mulki isa izza bata sayan sa wasu na nema ido rufe wasu kuma Allah ya basu ko su zubar ko su haifi ɗan su jefar ko dai su haifa basu bashi kulawa yau da kuɗi na sayan aihu da mardiya da salma sun dade da sayan ƴaƴa jama'a muji tsoron Allah mu kula da ƴaƴan da Allah ya bamu amanace sai Allah ya tambayi duk wanda ya bawa ɗa ya ya kula da tarbiyan sa cin sa shan sa suturar sa amma sai asaki ƴaƴa suna abin da suka ga dama komai mutun zai yi ya rinƙa tuna mutuwa bayan mutuwa arinƙa tuna kwanciyar gabari sanna ga uwa uba gadar siraɗi hisabi ya Allah duk halin da zamu shiga Allah ka tausaya mana ka barmu da imani.

cikin dakiyar zuciya da Ammi tace "mardiya na baki na baki Ayaam da Ayana har abada na san fateema ko ta tashi bazata ce komai ba dan na isa da ita ki rike su da amana kuma ɗauke su daga gaban tama zai sa ta samu saukin ciwon dake zuciyar ta amma idan suna kusa da ita kullun zata rinƙa kallon fiskar baban su a tattare da su bazata dai na shiga ɓakin ciki da tashin hankali ba" har kasa Aunty mardiya ta tsugunna tana kuka tana zubawa Ammi godiya kawar da kai Ummi tayi da sau da dama tana yiwa Aunty mardiya kuka akan rashin aihuwa mikewa Ahmad yayi ya kira sojoji suka tafi da Abu Abdurahman sanna ya tasa su fariza a gaba suka nufi waje har ya kai bakin kofa ya juyo yace "Abba ina shi Abdurahman ɗin dan naga ai da shi suka zo" shiru palon ya yi suna tunanin ina yayi kuma karyaje ya ɓata fa kasar da ba nasu ba cikin kuka lamrat tace "ranar ina tsaye a window ɗaki naga yaya Prince yasa sojoji sun kama shi" kallon Fahad Abba yayi ba tare da yayi magana ba cikin sauri Fahad ya mike ya fice daga Palon mamaki Abba yake ko me Abdurahman yawa bgs da yasa sojoji suka kama shi oho lokacin guda kuma face ɗin Abba ya sauya tunawa da bgs da yayi nan take ɓacin rai ya bayyana akan face nashi.
da sallama Fahad ya dawo palon yana faɗin "yaya Ahmad kaje sojojin zasu sa maka Abdurahman ɗin a mota dan baya iya tafiya" waro ido waje Abba yayi kafin yace "baya iya tafiya me Safras ɗin yasa aka masa? Wai ma me ya haɗa su ne? Shi kam dai Safras sai ya godawa kowa halinsa yanzu har bakon ma bai bariba to me ya masa?"a nitse Fahad yace "Na duba fayel nashi yayi wa hiyana magana ne shiyasa yaya Prince yace a bashi hukunci mai tsanani dan danaje gadroom ɗin ma sunki bani shi wai yaya Prince yace a horashi ya horu sosai ta yadda ko kiran sunan sister akayi sai ya suma" dogon salati Ammi tasa tana tafa hannu ta rike haɓa da hannu ɗaya tace "yanzu dan yayiwa hiyana magana yasan akan me ya mata magana ne yasani ko tambayar ta kawai yayi kai amma wanna yaro dai Allah ya shirya" cikin shassheka Zahra tace "aa Ammi wlh ya iya son mata dan diyana ta bani labarin agidan Aunty farida ya taɓa zuwa zai taɓa ta ta maresa" sunkuyar da kai Fahad yayi a ransa yana faɗin "a lallai Aryan yayi nisa da yau Abdurahman ka sake komawa gadroom a karo na biyu harda yunkurin taɓa diyana Allah ya rufama asiri basu kusa ai da ka gane nan ba chan bane wlh ba dan Abba bama ai dana sa an mai da ka ɗan banza wlh larabawan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login