Showing 327001 words to 330000 words out of 363274 words

Chapter 110 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2602

da Eshat kuma Duk wani training da bgs ke ba ta, ta fanni motsa jiki yanzu ta iya ita da kan ta ma tana yi ba sai ya taya ta ba yanzu har rige rige take da shi idan suna gudu ko press up ta samu karfi dai dai yadda yake so a yau suka shirya za ta fara koyan har bi da bindiga da ko yan faɗan hannu ta yi kyau abun ta sai kara freash take sai dai ta ɗan rage ƙiba saboda motsa jiki da take.

Misalin karfe 4 na yamma suna zaune a wajen motsa jiki shi da ita dukkan su suna sanye cikin guntun wando na sojoji iri ɗaya da t-shirt na sojoji yar karama mara nauyi ba karamin kyau kayan sojojin suka mata ba dukkan su ba su ɗaure gashin kan su ba sun bar shi a watse har baya, ya kara kyau sosai shi ma hankalin sa a kwance yana zaune saman sofa yana kokarin haɗa mata bindigar wasa ta fara da shi,ita kuma tana tsaye tana faman sanya hand gloves da ya bata. wayar sa dake saman table dake kusa da ita ya fara ringing, cikin sauri ta sanya hannu ta ɗauko ta miƙa masa kallon mai kiran yayi kafin ya ansa wayar cikin sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Barka da yamma Ammi" daga ɗayan ɓangaren Ammi tace "ɗazun da muka yi waya na so sanar da kai sai na man ta" "menene Ammi" yayi maganar tare da ciro wayar daga kunnen sa ya sanya ta a hand-free ya a jiye a gefen sa ya ci gaba da haɗa bindigar da ya ke "Daman akan wanna mata da ta kashe mahaifin su Hiyana ne daman nace a barta ka mata hukunci sai Yusuf yace ba zai yiwu a mata hukunci ba har sai ta haife cikin dake jikin ta shi yasa nace a ajiye ta sai ta haihu in sanar da kai ka mata hukuncin da ya dace to ta haihu da hai huwar nata ma sati biyu ke nan ya ka mata kazo ka mata hukuncin da ya dace dan ta cutar da su Hiyana sosai ta haukata musu mahaifiyar su ta kashe musu mahaifi ta kuntatawa rayuwar su sosai ga laifin zina da shirka dukka" yana kokarin yin magana ya jiyo sautin kukan Hiyana daga bayan sa a sukwane ya juyo yana kallon ta ta kifa kai da guiwa tana kuka ajiye bindigar hannun sa yayi ya ɗauki wayar ya cireta a hand-free ya mai da kunnen sa ya fara magana "Ammi zan sa a mata hukuncin da ya dace zamu yi waya an jima da daddare" "to Allah ya kai mu daren amma gaskiya ina son ka hukunta ta da kan ka" "Amin Ammi ke dai zamuyi waya an jima" "to" kawai Ammi tace sannan ya katse kiran tare da a jiye wayar ya nufi wajen da Hiyana ke zaune ya zaune kusa da ita tare da sanya hannu ya ɗago ta cak ya ɗaura ta saman cin yar sa yana faɗin "Me ya faru my Eshat?" Cikin kuka tace "Yaya Prince daman Inna ce ta kashe bappa na innalillahi wa inna ilaihir rajiun wallahi ba zan taɓa yafe mata ba ta cutar da mu a rayuwar mu, yaya Prince dan girman Allah ka mata hukunci mai tsananin gaske gaji?" rungume ta yayi sosai a jikin sa yana ɗan bubbuga bayan ta a lamar rarrashi kasa yayi da murya da sigar rarrashi ya fara magana "Da ban yi niyar hukunta ta da kai na ba amma saboda ke zan yi hakan ki dage ki gama koyan har bi da bindiga next month sai muje Nigeria na mata hukuncin da kai na kin ji? Amma duk da haka zan sa a tsare ta prison a rinƙa bata horo mai tsanani kafin na zo" kara shigewa jikin sa tayi tana kuka ƙasa ƙasa hannu ya sa ya ɗago habar ta yana kallon kyakkyawar face nata "My Eshat ya isa haka kukan nan kin ji ko zan hukunta ta dai dai da abun da ta mana, please kiyi shiru wanna kuka da kike tamkar kina caka min mashi ne a zuciya please ki yi shiru" ya kai karshen maganar tare da sanya kyakkyawar hannun sa yana goge mata hawaye shiru ta yi ta dai na kukan cikin raunaniyar murya tace "Yaya Prince ka san me?" Girgiza mata kai ya yi a lamar a'a ba tare da ya yi magana ba "Yaya Prince ni ma ina son in samu ciki kaga su Diyana fa dukkan su sun samu ciki har ma nasu cikin ya girma" dogon numfashi ya ja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya Hiyana ta taɓo masa in da ya ke masa ciwo "My Eshat ni kai na bani da wata buri da ya wuce in gan ki da ciki kin haifa mana yara dozen abun na damu na amma koma me na san Allah ne bai kawo ba" shiru ta ɗan yi kafin tace "Ya Allah ya bamu masu Albarka" manna mata kiss yayi a gefe kumatu yana faɗin "Good haka ake san bawa ya ka sance mai tawakkali kar ki rin ƙa addu'ar Allah ya baki Aihuwa ki rinƙa addu'ar Allah ya baki zuri'a ɗayyiban kin ji In Sha Allah muma mun kusa samun na mu ƴa'ƴan" tana kokarin yin magana Aryan da Yusuf suka iso wajen bakin su ɗauke da sallama cikin sauri ta mike daga jikin sa tana ɓoye fuska dan karsu Aryan su ga tayi kuka cikin girmamawa tace "Ina wuni yaya Aryan" da fara'a ya amsa da lafiya lou sister" "Yaya Yusuf ina wuni" da fara'a shi ma ya amsa da "Lafiya lou" juyawa tayi ta na kokarin barin wajen Aryan ya yi saurin cewa "A'a sister zo ki yi zaman ki sallama kawai zamu yi da shi" koma wa ta yi ta zauna ku sa da bgs ta ɗan sunkuyar da kai ƙasa. Hannu Aryan ya miƙa wa bgs yana faɗin "to zan tafi amma ban sanar da jidda akan zan ta fi ba dan inna faɗa mata ba zamu kwashe lafiya ba, na baku amanar ta ban san me zai kasan ce ba kila na dawo da rai ko akasin haka to idan ban dawo da rai ba idan ta haifi ɗa Namiji kasa masa sunan ka idan kuma mace ce ka tambayi jidda ta sa mata suna" kunyar kiran sunan Aunty Amarya yake saboda bai san ta da abun da ya wuce miƙa masa hannu bgs ya yi suka gaisa yana faɗin "Idan mace ce sunan Aunty Amarya In Sha Allah lafiya lou zaka dawo da kan ka zaka raɗawa ƴa'ƴan ka suna" ya kai karshen maganar tare da mikewa suka rungumi juna ya na yi wa Yusuf a lama da hannu akan ya zo cikin sauri Yusuf ya kari so suka rungumi juna su ukun kukan Hiyana ya dawo da su hayyacin su cikin sauri suka raba jikinsu, su ka juyo suna kallon ta "Eshat lafiya meke faruwa" bgs ya tambaya ya na koma wa kusa da ita ya zauna cikin kuka tace "Yaya Aryan ina zaka je? Me ya sa ka ke magana idan baka da wo ba asawa yaron Diyana sunan yaya Prince?" Kallon bgs Aryan ya yi a ya yin da shi ma bgs ɗin shi yake kallo "sister nasan kina da fahimtar zaki fahimce ni zanje kama wanna mutumin da ya taɓa kama ku ke da Khalid ne mun samu address na su suna da yawa sosai yana da yara a kasa she da ban da ban, mun samu labarin zasu yi taron karshen shekara da suke ko wani karshen shekara a Dubai wanna ita ce ka ɗai daman da muke da shi na kama su gaba ɗayan su dan ko wani shekara a kasa da ban da ban suke taron kin ga idan bamu yi zafin naman kama su wanna shekarar ba ba lallai wata shakara mu san kasan da zasu yi taron ba zan jagoranci tawaga biyu ne muje bgs yana wani aikin shi ya sa ba zai ja goran ce mu ba ki kula min da jidda In Allah ya yarda ba zamu wuce kwana biyu ba" ya kai karshen maganar tare da juyawa cikin sauri ya bar wajen shi kan shi bgs dannewa yake har cikin ran sa yake jin zafin tafiyar Aryan ji yake kamar zasu rabu ke nan.
A yau dai bgs bai samu daman fara koya mata harbi da bindigar ba saboda tafiyar Aryan duk ya kashe masa jiki ya rasa meke masa daɗi da kyar ya iya ɗaukan ta saboda kasala suka wuce cikin gida Yusuf ya wuce ɗakin binchiken su dan ya fara aikin sa ita kan ta Hiyana jikin ta ya mutu mu samma idan ta tuna Diyana ta tuna maganar Aryan in da yake cewa idan ban dawo ba ka sawa ɗana sunan ka da kuma in da yake cewa zamu je kama yan ta'adda sau da dama tana ɓoyewa tayi wa Diyana da Aryan kuka Diyana kuwa tana ɗaki tana sharan barci saboda alluran da Aryan ya mata ba dan haka ba ba za ta taɓa barin sa ya tafi ba shi yasa ya mata alluran barci Yusuf Khalid Fahad duk basa cikin jin daɗi yau dukkan su tunanin Aryan suke gaba ɗaya samarin Abba har da su Abba da Hiyana yau basu yi barci ba Sallah suka kwana yi suna yiwa Aryan addu'a mu samman Ammi da Aunty farida dan Yusuf ya kira kowa a gida ya faɗa musu ba karamin aiki Aryan ya tafi ba yana bukatar addu'a ya zama dole a faɗa wa kowa a gida dan su taya shi da addu'a bgs da kan sa ya kai Hiyana ɗakin su Diyana akan ta taya ta kwana dan yana zargin alluran zai iya sakin ta cikin dare kar ta tashi ta fara kuka dan ya san halin ta Diyana na barci Hiyana na Sallah tana kuka tana ta yi wa Aryan addu'ar samun na sara da dawowa lafiya haka sauran ma kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare tun farkon dare har karshen ta suna kan dadduma Abba da Ammi sun shiga damuwa sosai Aunty maryam itama tana Sallah tana kuka ta rokon Allah ya dawo mata da ɗan uwan ta lafiya daga shi sai Omar suka rage mata.

Hasashen bgs ya tabbata domin kuwa karfe ukun dare Diyana ta farka da zazzaɓi mai zafi da kyar ta iya waro idonta ta mike zaune saman gadon tana kallon ɗakin kamar bakuwa can ta hango Hiyana a kan dadduma kara waro ido tayi tana kallon Hiyana tana mamakin me ya kawo Hiyana ɗakin su da daddaren, a hankali ta zuro kafafun ta kasan gadon ta mike ta nufi in da Hiyana take dai dai wajen glass table dake tsakiyar ɗakin jiri mai karfi ya kwashe ta ta faɗi saman table ɗin ta buge cikin ta ji kake tass table ɗin ya tarwatse azababben ihu ta saki tare da dafe cikin ta tana juyi awajen a sukwane Hiyana ta juyo tare da mikewa da gudu ta kariso wajen ta a razane ta koma baya ganin jinin dake bin kafar Diyana kara itama Hiyanar ta saki a guje ta fita ɗakin ta koma bedroom nasu babu ko sallama ta faɗa cikin ɗakin bgs na zaune saman dadduma yana rike da al Qur'ani mai girma jin motsin mutun ya sa ya ɗago kai waro ido waje ya yi yana kallon ta murya na rawa tace "Yaya Prince Diyana ta ji ciwo jini na zuba sosai" tun bata kai karshen maganar ba ya ajiye al Qur'ani dake hannun sa ya mike ya nufi waje yana fita ta bi bayan sa da gudu.
Diyana na in da Hiyana ta bar ta tana kuka ta dafe ciki tana juyi a wajen duk ta ɓata wajen da jini kallo ɗaya bgs ya mata ya dafe kai yana karanto sunan Allah a ran sa cikin sauri ya ɗauke ta cak ya fito da ita ya wuce ɗakin su na duba marasa lafiya sai kuka take ta kan kame sa saboda azaban ciwon da cikin ta ke mata da gudu Hiyana tabi bayan su ita ma sai kuka take.

A ɓangaren Aryan kuwa lokacin yana can Dubai yana shirin yaki yana kokarin jera bullet a kugun sa bayan ya gama ya ɗauki kana nan bindiga huɗu ya sanya biyu a cikin sa ta gefe da gefa, biyun kuma ya sanya a gefen takalmin sa ta ciki haka ɗai yake jin gaban sa na faɗuwa zuciyar sa na tsinke wa sunan Allah yake ta ambata a ransa a zuciyar sa yana tunanin ko dan saboda yaki da zai je ne ya sa zuciyar sa ke tsinke wa kwata kwata bai taɓa kawo wa ransa matsala daga gida ba yayi shirin sa tsab ya fito wajen rundunar jibga jibgan sojojin su da zasu tafi tare da su bugun gaban nasa sai kara tsananta yake dannewa yayi ya umarci horarrun sojojin sa akan su raba kan su gida biyu wayan da za su fara shi ga wajen da kuma wayan da zasu yi shiga ta biyu sanna ya rufe da cewa kowa da ya kunna tracker jikin sa saboda tsaro dan mutumin da zasu je kamawa yana da mutane sosai sanna suna da manya manyan maka mai a hannun su.
Bayan sun gama shiri Aryan ya jagoranci rundunar farko suka yi gaba, sau ran suka biyo su a baya ɗan ne sa ne sa da su cikin sahara suka kutsa hancin motocin su tun daga baki bakin shiga saharan suka kashe motocin su suka fito suka fara tafiya da kafa Aryan ya ɗana kuna mar bindigar sa yayi gaba suka rufa masa baya tafiya suke suna lallaɓawa kamar wasu ɓarayi awani wajen ma sai su tsugunna sun yi tafiya a tsugunne

To masu karatu sai mun haɗu Monday idan mai dukka ya kai much kauna🥰💔🔐

💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By
Star Lady


Page 57



KANO NIGERIA


Misalin karfe 9 na safe gaba ɗaya family Abba da suka rage a gida Abba ya haɗa su a palo suna tattaunawa ciki har da su yaya bello da innar sa ka san cewar da aka kama su inna habiba sai ya ɗauko innar sa ya tawo da ita kusa da shi, cikin Hasana matar sa ya girma sosai Haihuwa yau ko gobe sai fama take ga cikin nata ya yi girma sosai ya yi kasa. Cikin nitsuwa Abba ya fara magana "Ba sai na faɗa muku ba kun san halin da Aryan ya ke ciki ina fatan kuna taya shi da addu'a? Sai magana ta gaba rana ita yau zan ajiye mulki in bawa Uncle na ku Aliyu magana ta uku akan maganar auren Ahmed da Hajara ina son Bello ka sanar musu zamu zo neman Auren ta bayan naɗin sarautan Aliyu sanna ka faɗa musu da munzo za'a ɗaura Auren a ranar dan ban son ɓata lokaci zamu zo da duk wani abu da za'a buƙata sai magana ta karshe a kan maganar Omar da Haidar Omar na sanya Yusuf ya sanya sojojin sa su tattaro min duk wani bayani akan ita Zainab dan ina son a haɗa Auren su rana ɗaya da na Ahmad sai shi kuma Haidar ya sanar da ni yana son yar wajen ki Fateema wayan nan yara da ku ka zo da su ya ma sunan ta Haidar?" Cikin sauri Haidar yace "Fariza" murmushi Hajj Fateema tayi dan tasan Fariza yarinyar bata da matsala cikin tsokana tace "eyee Haidar ba kunya ko? Har da saurin faɗe to shike nan daman ina da sako Saudiya dan ina son a ɗauko min Hindu mai aiki na ina jin daɗin zama da ita tana da kirki sosai dama kuma kai zan aika dan akoi abubuwa da zaka ɗauki min sai aje da goron tambaya dama a ka idar family su kakan su ke bada Aure muna da kyakkyawan fahimtar tsakanin mu mutumin yana kauna ta sosai da sosai na san zai bawa Haidar Auren Fariza In Sha Allah" "Allah yasa" Abba ya amsa da shi sai murmushi Haidar yake daga shi har Omar yau dukkan su bakin su yaki rufuwa sai murna suke cigaba da magana Abba ya yi "Fateema sai magana a kan ki ina son sanin ina yan uwan ki suke ke yar ina ce?" Lokacin guda face ɗin Hajj Fateema ya sauya cikin raunin murya tace "Haidar Omar Su Aisha ku bamu waje" ba musu suka mike cikin sauri suka fice har da su yaya Bello dukkan su suka fice palon ya rage daga Abba Ammi Ummi Innar yaya Bello wadda Hajj Fateema ta hana ta tafiya sai ita Hajj Fateema kallon Abba tayi cike da damuwa ta fara magana "Ni dai yar sarkin sudan ce na taso cikin gata da jin daɗi kasan cewar lokacin ni kaɗai ce mace kafin daga baya a haifi kanwata yan biyu ina da yan uwa maza biyu yan biyu Abdurahman da Abdussalam sai ni sai yan uwana yan biyu da Khalil da khalisat mu biyar iya yen mu suka haifa to ni mutun ce mai san shiga cikin daji in yi wasa ko in yi ta kewaye cikin gonaki. Akoi wata rana alokacin ba zan wuce 14 years ba na shiga cikin daji sai kuma nayi Sa'a ranar dogarawan Abban mu basu biyo ni ba kasan cewar na musu wayo dan ban son suna bina na fison na shiga daji ni kaɗai. Ina cikin tafiya ta ina ratsa cikin bishiyoyi da masara da shuke shuke ina yar waƙata tun daga nesa na hango wani dogon bafulatani mai kiwo yana tsaye jikin wata bishiya yana rike da sandar kiwon sa ga shanayen sa daga ɗan nesa da shi suna kiwo naji tsoron ganin sa sosai saboda kyan sa yana da kyau sosai kamar wani aljani gashi ɗan siriri da shi jikin sa mai kyau yana da dogon hanci mai tsini har baka da manya manyan idon masu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login