Showing 117001 words to 120000 words out of 363274 words

Chapter 40 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2584



Aunty farida tace "Kai baby Allah kana da neman rigima to yanzu kafaɗi maganar mana ina jinka ae,
"Watoma nine nake da rigima ko? "Eh mana Allah my baby kafini iya rigima,
Kwafa dady'n junior yayi yana faɗin zamu haɗune yanzu dai magana mai muhimmanci nake son muyi bari mugama maganar zakiyi bayani "to shike nan na ji yanzu dai faɗamin me ka ke so muyi magana a kai
"Yauwa my farida to bani hankalin ki nan, nitsuwa Aunty farida tayi ta zuba masa ido tana kallonsa

"Wan nan yarinyar da kika zo da ita wlh ta shiga raina sosai dan Allah idan ba damuwa ki faɗawa Abba, ya taimaka ya bawa Auta bakura Auren ta,

zubur Aunty farida ta miƙe zaune,tana kallon face ɗin shi taga dai da gaske yake "aa my farida lfy kika miƙe haka ko dai yarinyar matar Aure che? To ai ko matar Aure chema bai kamata kiyi irin wan nan miƙewarba,
"Dady'n junior diyana fa Abba ya riga da ya mata miji wlh, dan da zamu taho har mun shiga mota zamu tafi, Abba yasake bina har chikin motar yamin kashedin kada na kuskura na bar diyana ta kula wani namijin, domin ya mata miji a ɗaya daga chikin kanne na Amma bansan wanene daga chikin su ba, dan Abba'n bai faɗamin wanene ya bawa diyanar ba

Dogon numfashi dady'n junior yaja kafin yace "to shike nan, nima dai kafin na tambaya nayi tunanin hakan domin abun da mamaki ache yarinya kyakkyawa kamar wannan tafito daga gidan ku, dake chike da zaratan samarin nan, ache ba'a mata miji a chikin su ba abun, abun dubawa ne,
Aunty farida zatayi magana sai sukaji alamar motsi a palon kasa, kallon dady'n junior tayi shima ita yake kallo, a tare suka sauko daga gadon da sauri suka nufi waje

Suna saukowa palon kasa turus suka tsaya, suna kallonta da mamaki, Aunty farida tace "my diyana me kikeyi a nan ? Meyasa kika fito daga ɗakin? Shiru diyana bata basu amsa ba tana zaune saman sofa tana kallon kasa ta buga uban tagumi,
juyowa Aunty farida tayi ta kalli dady'n junior, shima ita yake kallo, sake dawo da kallonta tayi kan diyana dake zaune ko motsi batayi, a hankali Aunty farida ta taka zuwa kusa da diyana tasa hannu ta ɗan taɓata tare da kiran sunan ta a hankali,
Firgigit diyana tayi tare da miƙewa, zuba mata ido Aunty farida tayi kafin tace "my diyana lfy kike zaune a nan? Tunanin me kikeyi haka kuma?
Tsuke fuska diyana tayi ta turo baki ta fara magana

"Aunty farida wlh na kasa barchine, kuma ina jin ajikina kamar yaya Aryan bai da lfy san nan kuma Allah idan na rufe idona sai in rinƙa ganin yaya Aryan yana faɗin, bakin ki kawomin coffee ba yau to munɓata, Allah Aunty farida ina son ganin yaya Aryan, kewar shi nake

Tirkashi turus Aunty farida tayi tama rasa me zatachewa Diyana, domin iya gaskiya diyana tafaɗa dan bata karya, amma bansan meyasa Abba zai yankewa yaran nan irin wan nan ɗanyen hukunchin ba gashi diyana ta kasa barchi, kuma ina da tabbachin shima Aryan ɗin yana chikin damuwa.

ganin Aunty farida tayi shiru alamar ta tafi duniyar tunani ne yasa dady'n junior ya dubi diyana yace
"jeki ɗaki ki kwanta ko da safe da kaina zan kai ki wajen yaya Aryan kuma ki daina tunanin ko bai da lfy, lafiyan sa kalau sharrin sheɗan ne yasa kike ganin kamar bai da lfy, kije kiyi addu'a ki kwanta kinji, to kawai diyana tace san nan ta nufi ɗakin ta,

Hannun Aunty farida dady'n junior ya kama suka nufi stair ɗin suka koma ɗaki,
"My farida wai meke faruwane?, ko dai Aryan shine mijin da Abba yayi wa diyana
"Dady'n junior wlh nima abun yafara ɗauremin kai, nan dai Aunty farida ta shiga bashi lbr duk wani abun da ta sani dan gane da yaya Aryan da diyana, ta karisa maganar dai dai lokachin da suƙe hawa kan gadon su,

"Kinsan me my farida, batare daya jira amsar taba ya chigaba da chewe "Abba yana da gaskiya domin kinga dukkan kannen namu basu taɓa soyayya ba hasalima basu ɗauki mace da daraja ba, ganin ta suke kamar abun banza, wlh a irin wan nan yanayin da suke chiki idan aka ɗauki mace aka basu to ta shiga uku domin basusan darajar taba zasu wahalar da ita sosai, yanzu dai ki dubi yadda Aryan ke masifar son yarinyar nan batare da yasan Son nata yake ba amma duk dahaka daga ɗan magana dasu Umar sukayi, ya fusata har yaje ya samu Ammi ido da ido yace bayason ganin diyana kinga a nan ma rashin sanin darajar mace ya bayyana karara, a tare dashi, wlh gwara da Abba ya masa hakan, kuma ku barshi sai ya gasu sosai sai yasan mace fa halittace mai daraja wadda kowani ɗa namiji ke son kasan chewa da ita, ku kyalesa sai ya furata da bakin sa chewar yana Son ta, in ba hakaba ko an musu aure ran da su Umar suka sake mai maita abun da sukayi shima sake mai maita abun da yayi zai yi. da katawa yayi da maganar yana mai da numfashi,

"Kana da gaskiya dady'n junior wlh rashin sanin darajar macece har yasa Aryan ya iya tinkarar Ammi ya faɗa mata hakan, to amma abun tausayin a nan shine ita diyana yanzu dai da kunnen ka kaji halin da take chiki, tana son Aryan sosai Amma itama batasan chewa Son nashi takeba, saboda kaga ita yarinya che kuma gashi ba wani ilimin ke gareta ba ita ko kallon film batayi sai dai buga game kawai, ta iya

"Hakane my farida dolene diyana ta zama abun tausayi amma ke zaki jata a jiki domin ki rinƙa rage mata, kewar nashi kada ki bari ta rinƙa zama ita kaɗan, gobe idan Allah ya kaimu zan saya mata sabuwar waya mai kyau sai kisa Sim naki a chiki, ki mata download game's dayawa, idan kin gama ki chire Sim ɗin, san nan kema kiyi taka tsantsan da wayar ki dan kinsan gaba ɗaya kannen ki basa iya yin wuni ɗaya batare da sun kira ki ba, kada ki kuskura ki sakawa diyana Sim card a wayar ta, domin a yadda kika bani lbr na fahimci yariyar akoi kwakwalwa sosai, dan haka sai kinyi taka tsantsan da ita sosai

"To shike nan dady'n junior zanyi duk yadda kace Saboda nima ina kaunar diyana sosai kamar yadda nake kaunar Aryan, bazan so taje gidan mijin da bai san darajar ta ba, zanyi iya bakin kokarina wajen ganin, na bata kulawa na chanza mata abubuwa da dama

"Good my farida hakan yayi to yanzu dai mu kwanta muyi barchi kinga dare yayi ma karisa maganar gobe idan Allah ya kaimu,

atare suka kwanta ta shige chikin kirjin sa ta lafe shi kuma yana shafa bayan ta har barchi ya ɗauke su.

Kano

Tun misalin karfe 6 su hiyana suka gama shirin zuwa school, yaya Khalid kawai suke jira yazo ya ɗauke su.

sai misalin karfe 7:30 yaya Khalid yazo ya tasa su a gaba suka fito harabar gidan suka nufi parking space, yau da kanshi ya tuƙa su a family car,

Gudu yake shararawa da motar sosai akan shin fiɗaɗɗiyar hanyar school nasun, chikin kan kanin lokaci suka isa makarantar,kai tsaye parking space na ya nufa yana kashe motar, ya fito a gurguje ya yana faɗin "kufito ku tafi class dan kun kusa makara, yana gama faɗin hakan ya nufi office na HM na makarantar, domin naje ya biya musu kuɗin makaranra.

Abangaren su hiyana kuwa yaya Khalid na tafiya suma ko wace ta kama hanyar class nasu, amma kallo ɗaya zaka yiwa hiyana kasan tana cikin matsanan chiyar damuwa ga blue eyes natan nan duk sun kunbura da alama tasha kuka, dan dai ita ba mai yawan kallon mutane bane kullun kanta na kasa shiyasa mutun ba zai gane kunburin da idon nata sukayiba, tazo dai dai zata shiga class nasu, taji daga bayan ta an che "ke zonan chikin tsiwa, da sauri ta juyo, ganin....✍️✍️

More comments an share
*💫STAR LADY💫*32

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣2️⃣*

Da sauri ta juyo ganin jabir ne yasa ta ƙara ɗaure fuska sosai, ta sunkuyar da kanta kasa, "my hiyana me ya same ki kikayi kuka? Chewar jabir Ya yi maganar yana matsowa kusa da ita, ɗan ja da baya kaɗan tayi kasa kasa tace "ina kwana, batare da ya amsa gaisuwar nata ba ya sake mai mai ta mata tambayar daya mata da farko "me yasa meki ki kayi kuka? waya taɓamin ke?

Chikin sanyin murya tace "ni ba wanda ya taɓani kawai nayi kuka ne saboda an mai da kanwata garinmu,
"Eyya to sorry kinji kije class idan an tashi break kizo muyi hira dan ina missing naki sosai, ko dai ke baki missing na ne? Ya karisa maganar yana ɗan dukar da kai yana leka fuskan ta dayake ta sunkuyar da kan kasa, shiru tayi bata sake che masa komai ba, ganin bata da niyar magana ne yasa yace "to kije class ɗin idan antashi sai kizo na kawo miki tsaraba
Bata jira ya karisa maganar shiba ta shige class nasu da sauri, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya juya ya nufi nasu class ɗin

Sosai Bgs yake sauri kamar zai tashi sama taku yake irin na sadaukin yaki, yazo dai dai zai shiga ɓangaren Aryan, yajiyo muryan Abba daga bayan sa yana faɗin "jirani mushiga tare, batare da ya juyoba ya tsaya har Abba ya kariso, wajen a tare suka jera zuwa chikin part ɗin,

"Menene ya hana Aryan zuwa sallar asuba Abba ya tambaya yayi maganar dai dai lokachin da zasu haura stair case ɗin chikin palon Aryan,

"Abba wlh nima ban saniba abun da nazo tambayar sa kenan, shiru Abba yayi bai sake chewa komai ba, har suka karisa betroom ɗin, da sallama suka shiga a tare

Kwanche yake saman katafaren gadon sa,yana sharara barchin, da mamaki Abba ya juyo ya kalli Bgs wadda shima Abba yake kallo..

....Karisawa bakin gadon sukayi a tare zama Abba yayi a gefen gadon shi kuma Bgs ya haye saman gadon ya ɗan jayye bargon da Aryan ya lulluɓu, zuba masa ido Bgs yayi sosai kamar mai karantar wani abu a kan face nashi

"Abba da alama ɗan uwana bai yi barchi jiya da daddare ba koda kuma yayi to kaɗan ne, ka duba time fa yanzu Almost 8:5am amma yana barchi ko sallar asuba bai yiba, anya Aryan yana da lfy kuwa? Dogon numfashi Abba yaja kafin yace "kila akoi abun da ya tsare sa ya hana shi barchi da wurine.

Guntun tsaki Bgs yaja sannan yasa hannu yana ɗan bubbuga hannun Aryan,
"Aa Safras ka barshi mana yayi barchin sa chewar Abba "aa Abba ya tashi dai kofa sallar asuba bai yiba ya tashi idan yayi Sallah sai ya koma barchin, shiru Abba yayi bai sake Magana ba, bubbuga Aryan Bgs yake yana kiran sunan sa "my blood, my blood

Da kyar Aryan ya iya waro ash eyes nashi nan, sun chanza sunyi jaa saboda barchi chikin muryan barchi yace "Bgs lfy? Ɗaure fuska Bgs yayi kafin yace "zaka tashi kaje kayi sallar asuba ne ko dai sai na maka 1bloo 7 die,

Wani sallar asuban kuma? I Already nayi sallar ton asuba ɗin, yayi maganar yana kokarin miƙewa zaune, da kyar ya iya miƙewa zaune, da sauri yasa hannu ya dafe kansa dan ji yake kamar kan nashi zata faɗi kasa ga wani azaban chiwo da take masa, sai sara masa kan keyi kamar zai fashe,

Ganin Aryan ya dafe kai ne yasa Bgs saurin kai hannunsa saman goshin Aryan ɗin yana faɗin "my blood lfy? Menne? Kai ɗinne ke maka chiwo? Karisa hayewa gadon Abba ma yayi ya sa hannun'sa ya riko kan Aryan yana faɗin

"Aryan meke damun kane? ɗago jajayen idon sa yayi yana binsu da kallo ganin yadda suka ruɗene yasa ya ɗan kakalo murmushi gefen fuska, da kyar ya iya motsa lallausan red lips nashi ya furta "bb komai, a tare Bgs da Abba suka chire hannun su daga saman goshin nasa,

Aryan me yasa baka je masallaci da asuba ba? Chewar Abba yayi maganar yana sauƙa daga gadon, "Abba makara nayi wlh, lokachin da natashi already an gama Sallah "me yasamu wayar ka? na kiraka da asuba ai a kashe, Bgs ya tambaya yana kallon face nashi,
"Eh Ni na kashe wayar jiya da daddare, to akan idan nazo barchi zan kunna sai na manta

Shiru Bgs ya ɗan yi kafin ya chiro wayar sa daga aljihu wandon sa, ya kunna hasken screen ɗin ya chire password ya shiga contact nashi, layin Fahad ya fara kira ringing ɗaya Fahad ya ɗaga

"Hello big bro, ina kwana, "lfy Fahad, baki buɗe Abba da yaya Aryan ke kallon Bgs tunani Abba yake wai daman Bgs ya iya amsa gaisuwa tab lallai Fahad yarone mai Sa'a ya chire tuta a gidan nan, kaiii

Yaya Aryan ma tunani yake anya na taɓajin Bgs yana amsa gaisuwar wani ko wata kuwa? Yayi iya tunanin sa duk bai tunano in da Bgs ya taɓa ansa gaisuwa ba kwata kwata, ko awajen Aiki yaran mu zasu gaishe sa sai dai ya ɗaga musu hannu ko kuma ya musu alamar yaji da ido, ashe daman yasan yadda ake amsa gaisuwar kenan? Lallai yaya prince sai dai nace Allah ya shirya min kai.

"Fahad ka kawomin coffee mai zafi ka haɗo da hot milk, ina ɗakin Aryan yana gama faɗin hakan ya katse kiran.

..dawo da green eyes nashi yayi kan Aryan dake zaune ya zuba masa nashi Ash eyes ɗin shima yana kallon sa
"Aryan lfy kake kallo na haka? Kawar da kallon sa gefe Aryan yayi zai yi magana sai Abba ya rigashi da chewa "ba dole ya kalleka ba daman ka iya amsa gaisuwa? Dawo da kallon sa Bgs yayi kan face ɗin Abba yace "na iya Abba "au ka iya shine idan aka gaida ka baka amsawa "wlh Abba bawai da gangan nake kin amsawa ba, kawai ni ban son magana ne Allah harchena nauyi ya kemin idan zanyi magana

"Ba shakka Safras nima shaida ne ba tun yanzu ba haka aka haifeka baka son yawan magana amma dai karinƙa daurewa kana Amsa gaisuwar yan uwan ka, shiru yayi bai sake chiwa komai ba

A hankali Aryan ya zuro kafar sa kasa kafin ya sauko daga gadon, jiki ba kwari ya miƙe ya nufi toilet, wani irin jirine ta kwashesa batare da ya shirya ba kawai sai dai yajisa a faffadar kirjin Bgs, kara waro ash eyes nashi waje yayi, yana kallon face ɗin Bgs yayin da shima Bgs ɗin shi yake kallo

"Aryan baka da lfy ne? Abba ya tambaya yana karasowa wajen su, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi yace "aa Abba lfy na kalau kawai kai nane ke ɗan min chiwo sai jiri da nake gani, ɗan duƙawa Bgs yayi batare da yayi Magana ba ya saɓi Aryan a kafadar sa ya nufi toilet ɗin dashi,

komawa gefen gadon Abba yayi ya zauna yana tunani " lallai Aryan ai ka makara ita soyayya baa nuna mata jaruntar, ai san da zaka kawo kanka ma ba wan da ya sani, Ni kuma inshaa Allah sai na koyamaka sanin darajar mace sai kasan chewa mace halittace mai daraja Abba yayi nisa chikin tunanin sa, bai maga shigowar Fahad ba sai dai yaga mutun yana ƙoƙarin hawa gado yana faɗin
"Abba ina kwana, murnushi Abba ya sakarwa Fahad kafin yace "lfy ka tashi lfy, fuskar nan a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, da kaga Fahad ba sai an faɗa maka chewa kanin Bgs bane, zaka gane domin komai nasu iri ɗaya, kaman nin su ɗaya irin yadda Bgs ke haɗe fuska haka shima Fahad ke yi, rashin son maganar su ma irin ɗaya komai dai na Fahad sak na Bgs, dan yanzu ma da Abba yace katashi lfy Fahad, bai amsa ba sai ma kara ɗaure fuska da yayi ya zaro wayarsa yana latsawa, Abba kam ko ajikinsa dan gaba ɗaya ƴa'ƴan sa ba wanda bai san halin su ba,
Hannun su riƙe chikin na juna Bgs da Aryan suka fito daga toilet ɗin, da alama brush Aryan yayi, saman gadon suka haye, Bgs yace "Fahad ina coffee ɗin, Fahad ba tare da yayi magana ba ya sauko daga gadon ya nufi table ɗin tsakiyar ɗakin ya ɗauko kwakkyawar plate mai ɗauke da haɗaɗɗun cups guda 5 kowani cup an rufeshi da ɗan karamin plate mai kyau, bakin gadon ya dawo ya tsaya yana faɗin "gashi nan, ɗago green eyes nashi Bgs yayi yana kallon Fahad, da mamaki yace
"Fahad coffee da hot milk kawai nace ka kawomin ya naga cups har guda biyar?

"Eh to ai naji kache kana ɗakin yaya Aryan ne shiyasa na haɗo muku kai da shi ni kuma na haɗawa kai na black tea dan nima na taya ku sha, kaga cups 2 naka 2 na yaya Aryan, ɗaya'n nan kuma nawa, girgiza kai Bgs yayi yana faɗin "to ai daman Aryan nace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login