Showing 339001 words to 342000 words out of 363274 words
hannun sa ya yage rigar jikin sa ya ɗaure hannun sa in da bullet ɗin da yaran Major suka har bi bindigar hannun sa ya ɗan taɓa shi. bayan ya ɗaure hannun na sa ne ya ɗago yana karewa gidan kallon kafin ya ɗaga ɗayan hannun sa ya taɓa Bluetooth dake manne a kunnen sa kasa kasa yace "Yusuf a hawa na nawa Aryan ya ke dan na kewaye kowani ɗaki dake a gidan da bom kafin na shigo ina son in tashe su gaba ɗaya" daga ɗayan ɓangaren Yusuf dake tsaye gaban desktop computers yace "Suna hawa na 2 ɗaki na uku Please bgs kayi sauri dan ba iska sosai a ɗakin numfashi Aryan na gab da dauke wa ga bom dake jikin sa saura 20mins ya tashi" daga murya Yusuf ya yi da karfi yace "Bgs ka matsa" a sukwane bgs ya bar wajen. Yana barin wajen suna harbo karamar nuclear ji kake dooom wajen ta ta shi ham dala bgs ya yi wa Allah sanna ya yi wugi da bin digar hannun sa dan bindigar ta cika kara kasa kasa yace "Yasuf mutane nawa ne a dakin su Aryan" "Babu kowa daga Aryan sai sojojin mu da suka rage" ya yi maganar kamar zai yi kuka da karfi bgs ya fara daddanna yar na'uran dake hannun sa ya ji kake dom dom boma bo man da ya sanya suna ta shi, ba shiri yaran Major da shi kan shi Major da manya manyan abokan har karlan sa da suke meeting wadda suka laɓe a ɗakin suka ɓuyan wa mutuwa suka fara fitowa da gudun gaske wasu ma kafin su fito bom ɗin ya tarwatse da su iya bancin rai yau ran bgs ya ɓaci a sukwane ya ciro gun dake kugun sa ya fara basu wuta da karfi Major yace "Shage na san sai kai idan ba kai ba ba wan da ya isa ya jiyo ko kamshin in da nake bare ya tunkaro ni" harbin sa a hannu bgs ya yi kafin ya mai da sai tin bindigar ya fara har bin wayan da ke saman bene suna kokarin harbin sa yana tsaye kamar jatumin sadaukin yaki yana basu wuta. Shi kuma Major ya tsugunna kasa yana ihun azaba na harbin sa da gun a hannu da bgs ya yi.
Bgs Ya shagala da harbin wayan da ke saman bene suna kokarin har bin sa bai ankara ba yaji an sa masa bindiga a kai ta bayan sa hannun sa ya ɗaga sama tare da sakin bindigar hannun sa yayi saranda a hankali ya juyo dan ya ga wanene mai karfin guiwar da zai sa masa bindiga kallon sama da kasa ya musu matasa ne masu jini a jiki su 6 suka sa masa bindiga a kai. Suna kokarin ɗana kunamar bindigar su harbe sa suka fara jin ruwan bullet daga ta sama da sauri bgs ya ansa bidigar ɗaya daga cikin su ya cigaba da basu wuta da sauri jibga jibgan sojojin Dubai suka fara dirowa cikin gidan daga saman jirgin su duk wanda ya diro sai ya cire parashoot na jikin sa ya yi wurgi da shi ya ɗaga bindigar sa ya fara sakin wuta haukacewa yaran Major suka yi suka fara gudun cetan ran su a fusache bgs yace "Yusuf me yasa ka nemi taimakon sojojin kasar nan?" "Kayi hakuri bgs dole ce tasa yanzu dai dan Allah Aryan biyu daga cikin sojojin ma Allah ya musu rayuwa kasan cewar na ce maka babu iska isasshen a ɗakin ga shi an ɗirka musu kayan maye suna bukatar iska please bgs safe my blood" da sauri bgs ya haura saman benen ya nufi ɗakin da su Aryan suke sojojin Dubai kuma suna ɓarin wuta a kasa. Ko da yaje ɗakin a rufe da kwaɗo an sanya sarka a fusace ya koma baya da karfi ya yi wa kofar taku ɗaya sai ga kofar a kasa, cikin fushi ya dan na kai cikin ɗakin sai da ya ɗan ja baya saboda yadda hodar ibilis ke tashi a ɗakin gashi ba iska Windows ɗin duk a rufe ba wata hanyar iska da sauri ya nufi Aryan dake kwance rai a hannun Allah yana numfashi sama sama kamar ba zai yi rai ba hannu yasa ya ɗaga sa ya zubawa rigar bom ɗin ido yana kallon time ɗin saura 7mins bom ɗin ya tashi kallon notirar dake jikin rigar ya yi ba ta yadda zai yi ya kwance su dawo da kallon sa kan face ɗin Aryan ya yi lokacin guda ya ji wani irin tashin hankali da ɓacin rai da bai taɓa ji ba ta ziyar ce sa a lokacin guda, yau ga Aryan na buƙatar taimako ba halin ya tai make sa ɗaga kai ya yi ya kalli sama ya daga murya yace "Ya Allah save my blood da kai ka ɗai muka dogara ba wanda ya isa ya mana abun da baka rubuta mana shi ba" yana cikin addu'a ya jiyo bom ɗin ta fara warning saura 4mins dai dai lokacin major Ishaq ya shigo ɗakin tare da sai ta bgs da bindiga yana faɗin "Ka sake sa ka fito ka tsaya ka zuba ido ka ga yadda zasu tashi da bom a gaban ka bayan sun mutu sai mu ɗora da yaki daga in da muka tsaya idan kuma ka ki to zan harbe ka ku mutu tare" a gigice bgs ya yi kukan kura tare da sakin Aryan ya miƙe ya shako wuyar major da hannu ɗaya Major na kokarin harbin sa da gun ɗin hannun sa bgs ya ɗaga sa da hannun ɗaya ya yi wurgi da shi wajen da karfi hakan ya yi sana diyar saman Major kasan cewar bayan sa ta bugu a karfen bene bgs yana kokarin bin mejor dan idon sa ya rufe sai jin ya yi bom ɗin ta kara sautin karar gudun ta tit tit tit da alamar zata ta shi a sukwane ya karisa wajen saura 2mins. Ganin saura minti biyu ya rasa Aryan har abada a rayuwar sa ne ya sa yayi shahada ya sanya bakin sa kan wayar da aka haɗa bom ɗin ya tsinka bakar wayar da aka haɗa bom ɗin still bom ɗin bai mutu ba saura 1mins da karfi ya sa bakin sa ya fara tsitsinke wayoyin bom ɗin Yusuf dake tsaye gaban desktop computers yana kallon su hawaye yake sosai gani yake kamar shike nan zai rasa bgs da Aryan ji yake tamkar zuchiyar sa zata buga cikin kiɗima yake cewa "Bgs kayi a hankali karka yi kuskure" idon bgs ya rufe bai tsaya duba wayar da ta dace ba kawai ko wanne waya tsinka wa yake da baki yana karanto kalmar shahada dan ya san yana kuskure kaɗan bom ɗin zata ta shi, sai tuna masa Yusuf yake yana hawaye yana faɗin "Dan Allah bgs ka nitsu karkayi kuskure" ganin Yusuf na neman rikita shi yasa ya sanya hannun sa ya cire Bluetooth ɗin kunnen nasa ya yi wurgi da ita gefe cikin fidda rai da rayuwa ya yi sa'ar tsinke wata yar karamar bakar waya dake kusa da madannin bom ɗin nan take bom ɗin ta tsaya cak dogon numfashi ya ja tare da rungume Aryan yana sauke ajiyar zuciya sai lokacin ya samu daman fitar da zafafan hawaye daga idon sa yana godiya ga Allah da ya bashi ikon cetan ɗan uwan sa a yau, ba zai taɓa manta wanna rana ba, shi kan shi Yusuf dake tsaye gaban desktop computers yana ganin su tsugunawa ya yi a wajen tare da yiwa Allah sujudur shukur yana sakin kuka mai tsuma rai yana jerowa Allah kirari da yabo. Jin zuciyar Aryan na bugawa da karfi karfi sauri sauri, yasa bgs dawowa hayyacin sa cikin sauri ya miƙe ya ɗauke sa cak a kafaɗar sa ya fito waje ganin Major Ishaq sume a bakin kofa ya sanya ya sauke Aryan a fusace ya ɗauki Major ya yi wurgi da shi kasan benen daga saman cikin kunan rai yace da jibga jibgan sojojin Dubai dake kasa suna barin wuta "Idan da sauran ran sa ku samin shi a girjin sojoji a kai min shi us" yana kai karshen maganar ya ɗauki Aryan cak ya sauko kasa kai tsaye waje ya nufa har ya kai bakin kofa ya juyo yace da sojojin "Ku fito da sauran sojojin dake da rai a wuce da su hospital kuyi sauri dan suna halin rayuwa ko mutuwa" yana kai karshen maganar ya fice kai tsaye in da jirgin yakin su ya sauka bayan ya sauke su ya nufa nan ya kwantar da Aryan a gidan baya ya tsaya yana jiran a fito da sauran sojojin, ya kara shiga tashin hankali lokacin daya ga kwata kwata sojoji 8 aka fito da su hakan yake nuna duk sauran sun mutu kara riƙiɗewa idon sa ya yi yayi ja sosai sai furzar da iska mai zafi yake daga bakin sa yana huci tsantsan ɓacin rai ne cike a ransa haka ya shiga jirgin bayan ansa sojojin jirgin ya ɗaga suka wuce cikin gari nan ya baro sojojin Dubai suka karisa yakin suka ɗauko Major dan bai mutu ba sai dai bayan sa ta karye tare da kafar sa ɗaya ta karye haka suka wuce da shi kamar zai mutu suka sa shi a jirgin sojoji kamar yadda bgs ya bukata aka wuce us da shi umarni Yusuf ya yi wa sojojin akan su tashi gaba ɗaya gidan da bom haka ko a kayayi ba tare da ɓata lokacin ba suka tashi gaba ɗaya gidan da bom sanna suka wuce suka bar wajen suka koma wajen aikin su suna masu murnan nasara da suka samu.
A ɓangaren bgs kuwa suna shiga hospital a ka anshe su hannu bibbiyu aka wuce dasu Aryan A&E Accident and emergency nan aka fara basu taimakon gaggawa da farko likitocin sun tsorata basu gane bgs ba kasan cewar duk jikin sa ya baci da jini fiskar sa duk jini ya masa penti sai daga baya da ya wanke face na shi sanna suka yarda suka ansa su Aryan bayan sun gane bgs ne yana tsaye a bakin A&E ɗin likitoci sai shiga da fita suke ya dafe kan sa yana tunanin.
Almost 1 hour san nan wani babban likita ya fito cikin harshen larabci ya fara yiwa bgs bayani kamar haka "Ranka ya daɗe kayi hakuri biyu daga cikin sojojin sun rasu saura shida sai ɗan uwan kan nan kuma yana cikin mawuyacin hali dan sun bashi kwayoyin da ya wuce misali mun yi iya na mu sai kuma ta Allah ku ta ya su da addu'a kawai" tsabar ɓacin rai bgs ya kasa magana wayar sa ya ciro ya shiga massage ya turawa Shahram massage akan ya shirya musu jirgin su, su wuce us dan gani yake kamar likitocin nan basu san aikin su da kyau ba. Ba tare da ɓata lokacin ya miƙe ya shige cikin A&E ɗin ya ɗauko Aryan dake kwance saman gadon rai a hannun Allah ya saɓa sa a kafaɗar sa jikin sa ba riga suka fito da dugu rundunar sojojin da gomnatin Dubai ta turo musu asibitin dan basu kariya suka yi saurin buɗe masa kofar ɗaya daga cikin motocin da suka zo da shi suna sara masa a gidan baya ya kwantar da Aryan sanna ya musu umarnin akan su fito masa da sauran sojojin. Da gudu sojoji 10 suka nufi ɗakin jim kaɗan suka fito ɗauke da sauran sojoji da suka saura da rai likitocin asibitin suna tsaye suna kallon su har suka tashi motocin su da gudun gaske suka bar hospital ɗin kai tsaye Airport suka wuce ko motsi Aryan ba ya yi alamar ya suma bgs ya ɗaura kan sa saman cin yar sa yana kallon face na shi yana jin zuciyar sa na masa zafi wai yau Aryan aka bawa kayan maye over har haka wa iyazubillah ji ya yi jikin sa ta fara tsuma tsikar jikin sa na tashi dan tsananin ɓacin rai. A haka suka isa Airport tun basu gama parking ba ya buɗe kofar motar tare da sauke kan Aryan daga saman cinyar sa ya kwantar da shi a kujerar motar ya fito waje da gudu Shahram ya iso wajen ya cire jaket na jikin sa ya sanyawa bgs kallon sa bgs ya yi yana kara jin kaunan Shahram a ran sa mutun mai amana da gaskiya gyra jaket ɗin ya yi tare da jan zip ɗin ya juyo zai ɗauki Aryan sai yaga tuni Shahram ya ɗauke sa wucewa ya yi ya shiga jirgin yaki da zasu tafi nan take sojojin Dubai da suka rako su suka ɗauko sauran sojojin suka sa su cikin jirgin suna musu fatan alkhari nan take jirgin ya ɗaga sai us.
Kano
A ɓangaren su Abba kuwa sun shirya shirin zuwa Sudan tsab Abba Ammi Ummi Hajjiya Fateema da Abba yace sai gobe sai kuma ya sake fasawa yace su tafi yau, shi kuma Haidar ya shirya tsab ya nufi saudiya dan ɗauko wa hajj Fateema mai aikin ta da kuma sakon da tace ya ɗauko mata a ɗakin ta sai murna yake zai haɗu da Fariza Abba ne ya kira Uncle Aliyu awaya akan yazo ya same su a Sudan dan su haɗu su taya Hajj Fateema neman afuwar iyayen ta to ya amsa da shi san nan suka wuce zuciyar Hajj Fateema sai bugawa yake haka suka bar Nigeria tare da sojoji 20 dan basu kariya duk abun da ke faruwa da Aryan basu da masani ya a kai.
A ɓangaren Diyana kuwa Khalid ya bata kulawa bayan tafiya bgs dan kafin bgs ya tafi sai da ya sanar da Khalid abun da ke faruwa sosai Khalid ya basu kulawa ita da Hiyana tun da Hiyana ta tashi daga barci karfe 8 na safe take ta fama da aikin kuka dan taji yaya Khalid na waya ta system ɗin bgs ta ji shi yana waya da yaya Yusuf, yaya Yusuf yana faɗa masa bgs da Aryan suna gaɓar mutuwa dan bom ɗin jikin Aryan ya ki ciruwa tun da taji haka ta gane bgs ya tafi yaki sosai take kuka tana musu addu'ar dawowa lafiya haka ta fito daga part nasu ta tawo ɗakin da Diyana ke kwance ta zauna a gefen gadon da Diyana ke kwance tana kuka tana kallon Diyana face nata ya yi haske sosai saboda wahala da kuma jinin da ta zubar Khalid ya yi iya kokarin sa wajen ganin ya rarrashe ta amma taki yin shiru shi duk tunanin sa Diyana take wa kuka bai kawo a ransa taji wayar da ya yi da Yusuf ba dan lokacin da Yusuf ya kira shi bata ɗakin sai dai ya manta yanzu fa ita Hiyana matar bgs ce ta iya dayawa daga cikin bincike da bgs ke yi yanzu Duk wani motsi da mutun zai yi a gidan tana iya sani hakan yasa da taji abun da Khalid da Yusuf suka faɗa sai ta ɗauko wayar ta, ta fara kutsawa cikin na bgs dan ta tabbatar da in da yake ganin location ɗin wayar bgs ɗin ya nuna mata Dubai ne yasa ta kara shiga tashi hankali sosai, yanzu ta kware wajen iya bincike da sauran kana nan abubuwa har ta fara taka matsayi mai dan girma game da abubuwan da bgs ke koya mata.
Ita kuwa Diyana ko motsi bata yi tana kwance kamar yarda bgs ya bar ta.
Duk wanna abun da ke faruwa Fahad Zahra Amrat Lamrat ba su sani ba suna part na su suna sharar barci bgs ya hana a faɗa musu saboda cikin dake jikin su, shi kuma Fahad ya san Aryan baya nan amma bai san abun dake faruwa na bgs ya bi bayan Aryan ba kuma bai san meke faruwa da Diyana ba.
3pm jirgin su ya sauka a us har lokacin Aryan baya ko motsi kamar ba rai a jikin sa bgs ya sha mamakin ganin dubban jibga jibgan sojojin sun cika Airport ɗin kallon Shahram ya yi alamar neman karin bayani kasa Shahram ya yi da kai kafin yace "Sorry sir daman na sanar a office ne" murmushi kaɗan bgs ya yi kafin ya miƙe ya ɗauki Aryan ya saɓa shi a kafadar sa suka fito wajen jirgin, mamaki ganin bgs ya yi murmushi ya hana Shahram motsawa daga in da yake dan bai taɓa ganin murmushi bgs ba, ko magana bai fi sau uku bgs ya taɓa yi masa ba tsawon lokacin da suke tare shi yasa yau daya ga murmushi sa mamaki ya hana shi motsi. Bgs na fita rundunar sojoji sukayo kan sa a sukwane suka ansa Aryan dake hannun sa suka sanya shi cikin ambulance sojojin da suka jeru layi kuma suka fara ɗaga hannu suna sarawa bgs wuce wa ya yi bai ko kalli in da suke ba ya nufi motar da aka tana da domin ɗaukan sa jibga jibgan sojoji biyar ne suka yo wajen sa har suna rige rigen buɗe masa kofar mota, gidan baya ya shiga ya zauna bayan sun buɗe masa motar sanna ya dubi ɗaya daga cikin sojan yace "Anwar ina mutumin da aka kawo?" Cikin sauri Anwar yace "Yana hospital na wajen aiki" a fusace bgs yace "Nace ku bashi wani kulawa ne? Mutumin da zan kashe ta hanyar horo maza ku cire duk wata kulawa ku ɗaure min shi kafar sa a sama kan sa a kasa sai na zo" murya na rawa Anwar ya amsa da"to sir" da gudu ya bar waje umarni bgs ya yiwa sojojin akan su fito da sauran sojojin da suka taho da su, su sasu a mota su wuce asibiti da wuri. Cikin sauri suka fito da sojojin daga jirgin suka sasu a motocin suka shiga sukawa motocin key da gudun gaske suka bar airport ɗin suka nufi hospital.
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
💋 Duk Karfin Izzata 💋
💋The talent troupe writer's 💋
By
Star Lady
Page