Showing 120001 words to 123000 words out of 363274 words

Chapter 41 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2537

ka haɗawa coffee ba Ni ba Ni kataɓa ganina inashan coffee ne? Kaje ka ajiye a saman table ɗin, bari mu sauko, juyawa Fahad yayi ya maida plate ɗin saman table sannan ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1, yanan jiransu
Miƙewa Abba yayi yana faɗin sai kun fito fada sannan ya nufi hanyar fita, Aryan ne kawai ya amsa wa Abba da to

A tare suka sauko daga gadon suka nufi Fahad dake zaune saman sofa yana latsa waya.

A saman sofa mai zaman mutun 3 suka zauna da sauri Fahad ya miƙe ya ɗauko cup mai ɗauke da coffee ya miƙawa Aryan, sannan ya ɗauko cup mai ɗauke da hot milk ya miƙawa Bgs shi kuma ya ɗauki black tea ɗin sa ya koma ya zauna, shiru sukayi

A hankali Bgs ke ɗan korɓan hot milk ɗin haka zalika Fahad yana latsa waya yana ɗan kurban Black tea, Aryan kuwa ya riƙe cup ɗin ya kasa kai wa bakin sa yayi shiru kamar mai tunani

"Aryan me kake tunani? Meke damunka? Bgs ya jefo masa tambaya, ajiyar zuchiya ya sauƙe kafin yace "babu komai my blood bana jin sha coffee ɗin ne bakina ba ɗan ɗano

ajiye cup ɗin hannun sa Bgs yayi sannan ya juyo da kyau yana kallon Aryan "Aryan wai nikam yaushe kadawo ragon namiji ne? Waro manya manyan ashe eyes nashi waje Aryan yayi a sukwane ya juyo da kyau shima yana kallon Bgs, da mamaki "rago ya mai mai ta kalmar chike da jin haushin dan gantashi da kalmar da Bgs yayi, nan take kuma yaji wani karsashi yazo masa, ji yayi duk wata damuwa ta gudu domin ba abun da ya tsana arayuwa iri amasa kallon ya gaza ko kuma yana da rauni ko dai ache masa rago.
Ganin yayi shirune yasa Bgs yace "me ya sauya kane Aryan? da alama fa yanzu kafara zama... da sauri Aryan ya sa hannu ya rufe masa baki bai bari ya karisa maganar ba domi ba zai iya jin taba, zuba masa green eyes nashi kawai Bgs yayi yana kallon face ɗin sa

A hankali Aryan ya zame hannun'sa daga bakin Bgs san nan ya ɗauki cup ɗin coffee sa ya fara sha, juyawa Bgs ma yayi ya ɗauki hot milk nashi ya chigaba da kurɓa a hankali, shiru sukayi ba wanda ya sake magana

YOLA

da sallama Inna habiba ta shiga gidan su buba, da kyar take iya jan kafarta, har ta karisa tsakar gida, inna yaya Bello da innar buba suna zaune saman tabarma guda, inna yaya Bello tana shafawa innar buba magani a kafarta daya kumbura sosai yayi wani green kamar ya ruɓe,

Saman ta barman Inna habiba taje ta zauna "sannun ki da zuwa habiba Chewar Innan yaya Bello, wani harara inna ta wurgawa inna yaya Bello, tana faɗin "to ai ba wajenki na zoba munafuka sai ki tashi ki bamu waje, ajiye robar maganin hannun ta innar yaya Bello tayi tana kokarin miƙewa,

Da sauri innar buba ta riƙe hannun ta tana faɗin "aa innar bello dalla kiyi zaman ki, ki rabu da habiba, bata da hankali ne, waro ido waje inna tayi chikin tsawa tace "ke larai ni zaki chewa bani da hankali eh, au yanzu da wannan munafukar kika haɗa kai,kenan? "habiba ki daina zagin min yar uwa wlh idan ba haka ba zamusa yaranmu su miki duka tsiya,

Wani dariya Inna tayi har da shewa kafin tace yanzu ne kika san dachewa ita yar uwarki che ko? to wlh idan baki dawo chikin hankalin ki ba Allah sai na tona asirin duk abu da kika aikata wa yaron ta Bello, dariya Innar buba tayi kafin tace
"Ki tona mana, dan Allah habiba ki tona ni bani da wata damuwa idan kin tona saboda nasan bello da innar sa, zuchiyar su ba irin na dabbobi bane wlh duk kauyen nan babu mutanen kirki kamarsu ki duba duk kuntatawa rayuwansu da nayi hakan bai hanasu taimako na lokachin dana shiga halin mutuwa ko rayuwaba, alhamdulillah kuma ni nasamu na roki gafarar su kuma sun ya femin, ke ma wlh idan dai baki tuba ba to karshen ki ba zaiyi kyau ba, ko da yake ko kin tubama dole sai kin karɓi azaba da hukunchi, domin Allah baya yafe hakkin wani bawan, sai dai idan bawan shiya yafe maki da kansa, to kuma aina zaki ga bappa ki roƙi gafarar sa ina zakiga su hiyana da mahaifiyar su, duk babu wlh habiba kekam kinshiga uku

A fusache inna ta miƙe ta ɗaga hannu zata zabgawa innar buba mari, chikin tsawa Bello dake tsaye a bayan su tun ɗazun yace "wlh kina marin ta sai na shemeki da sandar nan, a tsorache inna ta juyo da sauri dan tasan Bello akoi shi da zuchiya sosai kuma idan yace zaiyi abu tofa zai yi ne "zo ki fita mana a gida Bello ya faɗa yana nuna mata hanyar fita da hannun sa, ba musu ta kama hanya fita tana jan kafa a hankali hankali har ta fice daga gidan

Karisawa yaya Bello yayi wajen su inna ya zauna gefen innarsa yana faɗin "innar buba kinsha maganin ki kuwa? "eh bello nasha ni dai ba abun da zanche muku sai dai in muku fatan alkhairin kuna da kyakkyawar zuchiya
"Ki daina faɗin haka Inna ai duk abun da muka miki yiwa kaine kuma ai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa chewa idan kana tare da mutun yana aikata abun da ba dai dai ba to karka kyamachesa karka gujesa ko da ka masa wa'azi bai jiba karka damu ka jashi a jiki kana masa alkhairin a hankali kana nuna masa abun da ya keyi ba mai kyau bane sannan kana binsa da addu'a, sai kiga Allah ya shirya shi ya chanza hali ya dai na, ba wai idan kaga mutun yana abun da bai dache ba sai kaje ka zauna kana zaginsa kana tsine masa a chikin mutane ba, yanzu ba gashi da muka jaki ajiki bamu je wajen kowa mun zage kiba bamuyi gulmar ki da kowa ba bagashi Allah da ikonsa ya shirya mana ke ba, kin gane gaskiya

Ajiyar zuchiya Innar buba ta sauke kafin tace "hakane Bello zancheka gaskiyane to Allah dai yasa itama habiba ta gane Allah ɗaya ne, a tare innar yaya Bello da yaya Bello suka haɗa baki wajen chewa Amin,
Miƙewa innar yaya Bello tayi tana faɗin bari naje na ɗora mana girkin safe dan yau naga kamar hasana batajin daɗi,
miƙewa yaya Bello ma yayi ya nufi ɗakin sa dan ya duba jikin matar tashi, suka bar innar buba ita kaɗai,

Maiduguri

Da gudu junior ya fito daga ɗakin su diyana na biye dashi a baya tana faɗin "wlh idan na kama ka zakayi bayani da harchen larabchi, kai tsaye ɗakin Aunty farida suka nufa,

Aunty farida na kwamche saman katafaren gadon tana shararan barchinta chikin kwanchiyar hankali, kamar daga sama taji diran mutane a kanta, a sukwane ta farka ta miƙe zaune, ganin Aunty farida ta miƙe zaune ne yasa junior ya faɗa jikin ta yana faɗin "na ɓuya ai, dafe kai Aunty farida tayi tace "my diyana zonan ki zauna, ba musu diyana ta zauna kusa da ita ta zuba mata ido

"My diyana kina jina, gyaɗa mata kai diyana tayi alamar eh chigaba da magana Aunty farida tayi, "my diyana yanzu fa kin girma bai kamata kina wasan guje guje ba kinji ko? Gyaɗa mata kai diyana tayi alamar taji, "good yanzu dai kutashi kuje palo ku fara breakfast ina zuwa, bari nayi wanka "Aunty farida yaushe zaki mai dani gida? Diyana ta tambaya
"My diyana ki saurareni da kyau kiji me zan faɗa miki, gida ba yanzu zaki koma ba, anjima dady'n junior zai dauke ki kuje yamiki registration a school nasu junior, ki fara zuwa school kinaji na ko? Turo baki diyana tayi kamar zatayi kuka tace "Aunty farida nikam ina son komawa gida Allah, ina son ganin yaya Aryan dasu Ammi,

"My Diyana yaya Aryan fa ya koma London, dan haka ki daina tunanin sa gida kuma zamuje nan da wata 3 kinji yanzu dai kuje Aunty jummai ta zuba muku abinchi kuyi breakfast ina zuwa,

Jiki ba kwari diyana ta miƙe ta riko hannu junior suka fito daga ɗakin, ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke kafin tace "gaskiya ina da aiki babba kafin na sauya ki my diyana, dan ba abun da kika sani sai shirme da wasa
A hankali ta zuro kafar ta kasa sannan ta miƙe ta nufi toilet


KANO

Misalin karfe 3:10 dankareriyar family ka dake ɗauko su hiyana daga school che ta kutso kai ta chika katafaren gate ɗin gidan, kai tsaye parking space driver ya nufa, tun bai gama gashe motar ba hiyana ta buɗe kofar ta fito da sauri ta nufi part ɗin Ammi,
Da sallama ta shigo palon betroom ɗin Ammi ta wuche kai tsaye, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga

Ammi na zaune a bakin gadon ta, tana riƙe da littafin addu'oe, gaban ta hiyaba tazo ta tsugunna ta sunkuyar da kai kasa
da wanna zazzakar kuma sanyayyar muryan nata tace "barka da rana Ammi,

"Hiyana lfy bakije kin chire uniform ba eh? Ammi ta tambaya tana ɗago haɓar hiyana da hannun ta, "Ammi daman nazo in roke ki ne dan Allah ni ki mai dani kauye sai ki dawo da diyana nan, kinji ni zan iya jure duk wata wahala, kuma zan iya hakuri da halin inna da buba, na san diyana bazata iya hakuri ba kome buba ya mata zata che zata rama kuma wlh Ammi dukan mutu buba yake mata tsoro nakeji kar su kasheta shiya gara ni ki kai ni chan sai ki dawo da diyana nan.

tsabar tausayi Ammi batasan lokachin da kwalla ya chika mata ido ba har yana kokarin zubowa, gaskiya hiyana mutunche, wadda samun irinta a duniyar yanzu akoi wahala ya Allah kasa ta zama matar ɗaya daga chikin ƴaƴana

"Ki kwantar da hankalin hiyana kinji, diyana bata kauye, tana chan wajen wata kawata hajj fatima dake zaune a saudia, ammafa karki faɗawa kowa kinji ko an tambaye ki, kiche tana kauye

ɗago blue eyes nata tayi ta ɗan saki murmushi har sai da dimple nata ya bayya, tace "to Ammi bazan faɗaba "yauwa my hiyana koke fa kinga yadda kika kara kyau da kikayi murmushi nan kuwa? To yanzu dai ki tashi kije ki chire uniform kiyi wanka kuzo kuchi abinchi, karki kara saka wata damuwa a ranki, "to kawai hiyana tace sanna ta mike da murnar ta har sauri take tanufi kofar fita

Tana tura kofar zata fita shi kuma yana shigowa karo sukayi kanta ya bugi faffaɗar kirjinsa nan kasan chewar ya fita tsawo sosai, waro blue eyes nata tayi nan take tafara ganin jiri, baya baya tayi tana kokarin faɗuwa..



💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)





More comments an like pls


*💫STAR LADY💫*33

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣3️⃣*


.......Baya baya tayi ya yanke jiki ta faɗi kasa saboda tsorata da tayi, shiko ko ajikinsa juyawa ma yayi zai koma in da ya fito dan ji yayi ya fasa shiga ɗakin,

"Idan ka kara taku ɗaya wlh in ranka yayi dubu sai na ɓata maka, chewar Ammi tayi maganar chike da jin haushi abin da Bgs ɗin yayi,

Chak ya tsaya bai tafiba kuma bai juyoba, chikin faɗa Ammi ta fara magana
"Ai wlh ko baka tausaya wa yarinyar nan dan maraichin taba zaka tausaya mata dan wahalar da tasha arayuwa kanaji fa, agaban ka lokachin da bata da lfy Aiman ya dubata, kaji ji da kunnen ka Maryam ta bugi yarinyar nan sosai a kai shiyasa idan ta tsorata take suma Amma duk da haka bazaka dai na tsoratata ba sai ka kasheta ka huta ko? wai ma me yarinyar nan ta maka ne?

A sukwane ya juyo dan jin yadda Ammi ke magana, chikin faɗa a hankali ya tako ya dawo chikin ɗaki hannu ɗaya ya sa ya ɗauki hiyana ya saɓata ta a kafaɗarsa yanufi gadon Ammi da ita, sai wani kwaɓe fuska yake kamar ya ɗauki kashi, a chikin zuchiyar sa yana faɗin "Allah Ammi kema bazaki kara ganina a part naki ba bare ki rinƙa haɗani da waɗan nan abubuwa kamar aljanun,

Sauko da hiyana yayi da nufin yayi wurgi da ita kan gadon sai kuma yaɗan sachi kallon Ammi yaga dai, still shi ta ke kallo dan haka sai ya kwantar da ita a hankali, a sukwane ya juya sai sauri yake ya fice daga ɗakin.

Girgiza kai kawai Ammi tayi kafin tace " Allah ya baki lfy hiyana amma gaskiya maryam ta chucheki wlh, saukin abun ma ɗaya tun da naji Aiman yace zaki iya warkewa amma sai a hankali, wani karin abun haushin kuma wai inkin suman kar azuba miki ruwa abarki sai san da kika farfaɗo da kanki, Allah sarki baiwar Allah ko abinchi baki chiba, Allah dai ya baki lfy shine kawai addu'ar da zamu Miki.

Maiduguri

Aunty farida diyana junior suna zaune a katafaren babban palon kasa, diyana sarkin kwalli tasha kwalliya sosai, ta sanya wani dankareren shadda, brown colour an masa aiki da milk colour zare, ɗinki dogowar riga, ba karamin zama kayan yayi ajikin taba, ta ɗaura ɗankwali ɗaurin ture kagatsi ya, tana zaune saman sofa,ta tasa laptop ɗin junior a gaba tana buga game,
Kamar daga sama sukaji diran motochi gidan, da sauri diyana ta kawar da laptop ɗin gefe tana faɗin "Allah yasa yaya Aryan ne, dasu hiyana, mamaki ne ya kama Aunty farida yanzu duk irin maganar dana gayawa yarinyar nan ashe baima shiga kunnen taɓa, oh ni farida gaskiya sai nayi da gaske dan naga alamar, kafin nasa ta daina zanchen Aryan to za'a sha wahala, tayi nisa chikin tunanin, sai taji sallama, da sauri ta ɗago ido, sai kuma ta mike tsaye da fara'a tana faɗin

"Oyoyo oyoyo hajjaya Fateema, mutanen saudiya saukar yaushe, Hajj fateema kyakkyawar macece ajin farko fara tas, ga dogon hanchi har baka, kai daga ganita kasan naira ta zauna gata irin wayayyun matan nan ne,

Ɗaukan laptop ɗin junior diyana tayi sanan ta kama hannun sa suka nufi waje tana faɗin "junior mu tafi garden koh? tun da bakin sunzo zasu dame mu.

Suna fitowa harabar gidan, blue eyes nata ya sauka kan wani hadaɗen balaraben guy, zaune yake saman bayan ɗaya daga chikin motocin da suka zo dashi, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya ga wasu jibga jibgan bodyguard guda 4 a kusa dashi suna tsaye,
kyakkyawa ne guy ɗin shima, amma dai bai kai yaya Aryan kyau ba Chewar diyana.

Tunda diyana tafito ya tsareta da manya manyan fararen idon nan nashi, sosai yake kallonta, itakam ko ajikinta kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta, ta chigaba da tafiya, har suka iso in da yake zaune, zasu wuche kenan, chikin harchen larabchi yace

"Aslm yammata min ti ɗaya dan Allah" diyana zatayi magana, sai ta tuna abun da yaya Aryan yace mata idan tayiwa wani namijin magana to zata samu chiki, da sauri ta ja hannu junior suka wuche har suna haɗawa da gudu, suka shige chikin garden ɗin.

A hankali guy ɗin ya diro kasa daga saman bayan motan, yabi bayansu, bodyguard nashi zasu bishi ya ɗaga musu hannu alamar su tsaya,
Tsayuwa sukayi a wajen moton tasa shi kuma yabi bayan su diyana

Ko daya shiga garden ɗin zaune ya same su, diyana nata buga game a laptop, junior kuma yana zaune gefenta yana ta mata surutu,

"Yammata namiki magana ɗazun baki amsa ba kodai bakyajin larabchi ne? Banza diyana tayi dashi kamar bata san da tsayuwar mutun awajen ba.

Chanza harche yayi zuwa harchen turanchi, yace "pls kiyimin magana nasan ai kina jin English kam, idan ma ba kyajin larabchi" nan ma shiru diyana tayi batayi magana ba, "yammata pls ki faɗamin sunan ki, Ni dai sunana, Abdurrahman" shiru diyana tayi kamar bata awajen.

Hannu Abdurrahman yasa ya ɗan taɓa kafaɗarta yana faɗin "nasan kina jina kawai jamin aji k... Bai karisa maganar ba yaji saukan mari a kumatun sa, kafin ya farga diyana ta damko hannun junior sun kwasa a guje sukabar wajen sai chikin gida.

.........dafe kunchinsa Abdurrahman yayi yana faɗin "in ban da soyayya kamar ni yau Abdurahman Abdurrahim, mace zata mara, kash amma soyayya baki min adalchiba, baki kyau tamin ba amma ba damuwa bari dai nayi kokari na samu soyayyar ta zan rama marin daga baya" jiki ba kwari ya juya ya koma wajen motar'su.

Aɓan garen diyana kuwa, aguje ta shigo palo sai numfashi sama sama take da sauri Aunty Farida ta miƙe ta nufota tana faɗin
"My diyana lfy? me ya faru ki kayi guduwa haka?

"Aunty farida yaya Aryan yace min idan namiji ya min magana na amsa ko ya taɓani zan samu chiki, shine wanchna Abdurrahman din kuma yazo ya taɓani, shine fa na mareshi, na gudu dan Allah Aunty farida ki kiramin yaya Arya bari na tambayeshi da wanchan Abdurrahman ya taɓani zan samu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login