Showing 102001 words to 105000 words out of 363274 words
Fahad su kayi suka bi bayan Abba haidar da Umar suka rufa musu baya
a hankali Aryan ya mai da Ahmad ya kwantar, san nan ya shafa kansa yace "Allah ya baka lfy my bro, abun mamaki gani Aryan yayi Ahmad ya lumshe ido a hankali ya buɗe alamar ya ji daɗin addu'ar da Aryan ya masa
.... A sukwane Aryan yace "Ahmad daman kana jin mu, lumsha ido Ahmad ya sake yi san nan ya buɗe alamar eh ina jin ku, a ruɗe Aryan ya zauna gefen sa ya riko hannun sa yana faɗin zaka iya buɗe bakin ka juya ido Ahmad yayi alamar a'a, "ok to shike nan bama sai ka buɗe baki ba tun da kana jin duk abun da nake faɗe, idan eh haka ne sai ka lumshe min ido idan kuma ba haka bane ka ɗaga min ido sama kaji,? Lumsha ido Ahmad yayi ya buɗe alamar yaji "akoi in da yake maka chiwo ne a jikin ka? ɗaga ido sama Ahmad yayi alamr aa "zaka chi abin chi? nan ma ɗaga ido sama yayi alamar a'a bazai chiba, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin kunchin Aryan, wai yau Ahmad ne ke magana da ido kai duniya abun tsoro, ɗaga ido sama Ahmad yayi alamar Aryan yayi shiru ya dai na kwalla, fika kai Aryan yayi kan goshin Ahmad ya chigaba da kwallar sa, hawayen sa na zuba kan fiskar Ahmad,
Sai da Aryan yayi kukan sa mai isar sa sannan ya ɗago yana bin Ahmad da kallo,
...hawaye kwanche a chikin idon Ahmad ɗin ga wasu na bin gefe gefen idon sa alamar dai shima kukan yake, girgiza kai Aryan ya shiga yi yana faɗin "No bro No bai kamata kayi kuka ba kaga baka da lfy lunshe ido Ahmad yayi alamar yaji, hannu Aryan yasa ya goge masa hawayen, san nan ya miƙe ya koma saman sofa daƙe chikin ɗakin ya zauna yana kallan Ahmad, shiru sukayi dukkan su har bar chi ya ɗauki Ahmad, ganin yayi barchi ne yasa Aryan mikewa ya fiche daga ɗakin daman ya zauna ne dan bai san ya bar Ahmad shi kaɗai.
Misalin karfe 9 na dare zaune Aryan yake a bakin katafaren gadon sa yana latsa waya, sanye yake chikin kayan barchi riga da dogon wando Sky Blue masu kyau da tsada, yayi nisa chikin abun da yake a wayar tasa, yaji wani fitinannen kamshin perfume ta kai mai karo a hanchi kan ya ɗago kai, sai yaji tafiya kwas,kwas,kwas, ai bai ma san san da ya saki wani cool murmushi ba tun bata karisa shigowa ɗaƙin ba,
ba ko sallama diyana ta shigo hannun ta ɗaya rike da cup mai ɗauke da coffee, ɗayan hannun nata kuma rike da jakar da ya bata amatsayin tsaraba, from head to toe yake kallan ta,
Sanye take chikin wata dan ƙareriyar lace Blue colour da ratsin fari, ɗinkin riga da sket kayan sun zauna a jikin ta sosai, yau ba ta yi make up sosai ba iya powder ta shafa sai man baki, tayi kyau kamar ita tayi kanta, ga ɗaurin dan ɗaurin ɗan kwali ture kaga tsiya da ta yi, yau kam ta rufe kan nata, gawani high heel fari da tasa a kafar ta sai wani fitinannen kamshin turaren humra dake tashi a jikin ta zubawa, a hankali take takawa tana wani rausaya ta kariso chikin ɗakin
.....gaban shi tazo ta duka har lokachin bai dai na kallan ta ba, yama kasa ɗauke idon sa daga kanta "ina wuni yaya Aryan, wani dogon numfashi ya ja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya, kasa amsa gaisuwar nata ma yayi, jin bai amsa ba yasa ta ɗago kai a hankali, karaf blue eyes nata ya sauka chikin ash eyes nashi da sauri tayi kasa da kanta,
"yaya Aryan dan Allah ka ansa mana wlh chinyata na min zafi kayan sun matseni sosai ta karisa maganar kamar zatayi kuka, slowly yasa hannun ya ansa cup ɗin ita kuma ta miƙe, tana faɗin yaya Aryan ga jakar ka buɗe min ta karisa maganar tare da miƙa masa jakar, batare da ya ansa ba yasa ɗayan hannun sa ya mata nuni da kan drawar gefen gadon alamar ta zauna, ba musu ta zauna ta ajiye jakar a kasa a gefenta
"Bana hanaki kwalliya da daddare ba, yayi maganar yana ɗaure fuska turo dan karamin bakin nan nata tayi a shagwaɓe tace "to ai Aunty farida che tache nayi kwalliya nazo na kawo maka coffee, shiru yayi bai sake magana ba ya ɗago da cup ɗin sai tin ɗan bakin nasa ya fara sha coffee ɗin yana kallan ta, juyo da kallanta itama tayi kan sa, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke idon ta kasan chewar yana kallon ta
"yaya Aryan me yasa kayi kuka kuma meyasa naga ka rame, a'sukwane ya chire cup ɗin daga bakin sa ya kara waro manya manyan ashe eyes nashi yana kallan ta, batare da ta kallesa ba ta chigaba da magana "ko ɗazun fa da yaya Ahmad ya fara rashin lfy kowa a palon yayi kuka har da ni, nima nayi amma kai da wan nan mai kama da hiyana da kuma Abba ba kuyi kuka ba to yanzu kuma.....ba shiri ta ja birki bata karisa maganar ba saka makon hannun da Aryan yasa ya rufe mata baki, ɗago ido tayi tana kallansa zaro mata manya manyan ashe eyes nashi yayi ya ɗaure fuska sosai da kakkausar murya yafara magana
Waya koya miki kallon maza? zaro blue eyes nata tayi sosai har sai da Aryan ya zame hannun sa daga bakin ta ba shiri, dan ganin idon nata yayi data zarosu waje kamar ta kara musu haske ne har wani kyalli suke, zuba wa kwayar idon ta ash eyes nashi yayi sosai yana kallan su abun ma mamaki ya bashi, ganin haka yasa diyana ta turo ɗan karamin bakin nan nata tafara magana "ni bana kallan maza ni ba maza bama har mata dukka bana kallon su.
a fusache Aryan ya miƙe, ganin ya miƙe yasa itama ta miƙe da sauri "Ke ni zaki chewa baki kallon maza, baya baya ta fara jaa tana girgiza kai chikin tsoro, binta yafara yi har suka kure bango matse ta yayi sosai da jikin bangon, a tsorache tace "Allah yaya Aryan ni bana kallon kowa ma "baki kallon kowa ya akayi ki kasan gaba ɗaya mutanen dake palo lokachin da Ahmad ya faɗi sunyi kuka? ya akayi ki ka san nayi kuka? Ya akayi ki ka san na rame? "Allah yaya Aryan Saboda kana da mahimmanci ne awaje na shiyasa na sani kuma ai kaga kullun ina kawo maka coffee, kuma ai idan nazo kullun ina kallon ka sau ɗaya, shiru yayi har chikin ranshi ya ji daɗin amsar da ta bashi na chewa yana da mahimmanci awajen ta, "me yasa nake da ma himmanchi awajen ki? yayi maganar yana ƙara matsowa kusa da ita sosai "ai saboda yanzu ka dai na yimin tsawa kuma kana sona baka buguna ka kawo min tsara ba kuma ranar kache nayi kyau, tunani ya shiga yi sosai anya yarinyar nan mutun che kuwa yar karama da ita sai ƙwaƙwalwa yanzu duk waɗan nan abubuwan bata manta da suba ko wama ya faɗa mata ma'anar mahimmanci oho, ganin yayi shiru ne yasa tace "yaya Aryan Allah ni bana kallon kowa pls kayi hakuri kaji, "ok promise me that ba zaki rinƙa kallon kowa ba, da sauri ta ɗago a dai dai goshin ta bakin sa ya sauƙa saboda yayi kusa da ita sosai, wani irin shock yaji daga tsakiyar kansa har izuwa tafin kafar sa da sauri ya ɗan ja da baya, ita kam ko ajikinta bata ma san yayi kissed na goshin ta ba ..
....Yaya Aryan Allah nama alkawarin ba zan kalli kowa ba, batare da yayi magana ba ya wuche ya koma bakin katafaren gadon sa ya zauna, san nan yace "dawo ki zauna muyi magan, a hankali ta tako izuwa kan drawer da ta tashi ta zauna "kin san me nake so dake "aa tafaɗa tana girgiza kai "daga yai idan munje chin abinchi a palo kai bama palo ba ko ina ne, kar na sake jin kinyi magana da kowa,sai dai idan an tambaye ki abu, kuma idan an tambaye iya abun da aka tambaya iya shi zaki amsa karki kuskura ki ɗaura wani abu kinji, to kawai tace, ɗaukan coffee nashi da ya ajiye yayi ya chigaba da sha
"yaya Aryan ayya bani wayar ka na buga game, batare da yayi magana ba ya ɗauki wayar ya chire pin ɗin ya miƙa mata, ansa tayi tafara latse latse "ayya yaya Aryan to ai ni banga game ɗin ba "shiga play store ki ɗauko dan ni kam bani da game, da murna a fiskar ta tace to
Aryan a tunanin sa diyana batasan kan waya ba shiyasa ma bai damu ba ya miƙa mata wayar
"Laaaa yaya Aryan daman hoton mun nan yana nan, a sukwane Aryan ya ɗago ya ansa wayar yana kallon screen ɗin "ke ya akayi ki ka ga hoton nan? yayi maganar yana mai do da idon sa kan face nata, shiru ta danyi kafin tace "kawai naga an rubuta KGA ne a jikin App ɗin shine na shiga "to ai akoi pin awajen ya akayi ki kasan pin ɗin?, "nima fa wlh ban sani ba kawai ni dai hannuna ya daddanna wayar ne shine naga ya buɗe, kara waro ido waje yayi a zuchiyar'sa yana tunani yanzu *kam zargin na ya fara tabbata koda diyana mutun che to tabbas tana da aljanu a kai* "yaya Aryan ka bani wayar mana na ɗauko game ɗin, pita chikin App ɗin yayi ya chanza pin ɗin san nan ya mika mata wayar
Game har uku ta ɗauko daga play store, super killer mario subway, subway ta shiga ta fara bugawa, tani nisa chikin buga game ɗin da take, sai taji an fisge wayar da sauri ta bi hannun sa zata kwache wayar dan ita tama manta a dakin yaya Aryan take ita duk tunanin ta tana ɗaki kuma Zahra che ta fisge wayar, tafiya tayi gaba ɗaya ta faɗa kan faffaɗar kirjinsa, dukkan su suka zube kan gadon, kallon face nata sosai Aryan ke yi ita kuma ta runtse ido tana mai da numfashi
wani irin bakon yanayi Aryan yaji gaba ɗaya jikin sa ya mutu, har wani sanyi yake ji kamar mai zazzaɓi, da kyar ya iya juyawa da ita a kan kirjinsa, ya mai da ta kan gadon ya mata runfa da faffadar kirjinsa yana kallon face ɗin ta, sosai taƙara runtse ido tana jiran taji saukar mari, chikin wata iriyar kasa lalliyar murya yace "ke me yasa kika faɗomin jiki? Lips nata sai kerma yake tace "wlh yaya Aryan na manta ne na ɗauka Zahra che ta anshe wayar shiyasa na bi hannun... Bai bari ta karisa maganar ba ya rufe mata baki da hannun
sa sauko da kansa yayi ya haɗe goshin su waje guda han chin su na gogan na juna, yayi shiru yana mai da numfashi.
...ko motsin kirki ya kasa saboda wata kasala da ta saukan masa lokachi guda almost 10mnt suna kwanche haka sai da yaji diyana na kokarin suma ne ya ɗago kai da sauri yana kallon ta, da kyar take numfashi saboda danneta da yayi wan nan ma iya rabin jikin sa ne kawai a kanta, da kyar ya iya miƙewa ya koma gefe ya jingina da jikin kayin gadon ya ɗaga kai sama ya lumshe ido, ita kam diyana ta kasa mikewa dan har lokachin numfashi ta bai dawo dai dai ba
Sauko da kai yayi Slowly ya ware idon sa a kanta tana kwnache tana kallan sama chikin da shewar murya yace "tashi ki kawo jakar naki na buɗe miki ki tafi ɗaki dare yayi, da kyar ta iya mikewa itama ta ɗauko jakar ta miƙa masa ansa yayi yana faɗin "to jeki dressing room na kije wajen ajiye agogo zaki ga wani ɗan karamin a kwati awajen na gold ki ɗauko ki kawo min, a hankali ta nufi dressing room ɗin
After some mnt
Ta fito rike da wani ɗan karamin a kwati mai kyau sai ɗaukan ido yake tazo ta mika masa, ansa yana faɗin "to zauna yayi maganar yana nuna mata gefen sa a bakin gadon, zama tayi tana kallan yatsun kafar ta, buɗe ɗan karamin akwatin yayi ya chiro wasu key guda biyu, ya ajiye ɗaya a gefensa yasa ɗayan kuma ya buɗe jakar
"ɗago to ki kalli abun da ke chikin jakar da kika damu abuɗe maki, ya karisa maganar yana kallan face ɗinta, da sauri ta juyo, idon ta na sauka kan jakar ta mike zubur tasa hannu a baki tana faɗin yaya Aryan.....✍️✍️
💖The Talent Troupe Writer's 💖
1 Duk Karfin Izzata
2 Gidan Aunty
3 Jini Ɗaya
4 Sarki Sameer
5 Kafita Zakka
Kar kubari abaku lbr love Story's
More comments like an share
💖The Talent Troupe Writer's 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*Episode 2️⃣8️⃣*
.....da sauri takoma kusa da shi ta zauna "yaya Aryan yanzu wan nan kayan dukka nawane har da kayan make up ɗin, gyaɗa mata kai kawai yayi batare da yayi magana ba, hannu tasa tafara watsa kayan "yaya Aryan to ai baka buɗe ɗayan gefen jakar ba, tayi maganar tana nuna masa ɗayan zip ɗin da ke kulle "zan buɗe miki shi amma ba yanzu ba kuma karki sake chewa na buɗe maki, irin kayan su Zahra ki kache ki ke so to gashi nan shi kuma ɗayan gefen idan lokachi yayi da kai na zan buɗe maki, kinji ko? gyaɗa masa kai kawai tayi alamar taji "ok to kwashe kayan kije ɗaki kinga dare yayi kuma karki kuskura ki bawa wani jakar nan kije ki ɓoyeta, in lokachi yayi zan ansa sai na buɗe maki, "to yaya Aryan dan allah ka dan faɗamin menene a chiki, ɗago ido yayi yana kallanta yayin da itama shi take kallo, ji yayi harshen sa ba zai iya yimata musu ba, "sako ne a chiki ya faɗa yana mai do da kallan'sa kan jakar "to dan Allah yaya Aryan ni ka buɗe min mana in gani, ta karisa maganar kamar zata yi kuka, "oh my god ke dai wan nan yarinya to shike nan tun da hakan ki ke so, rufe idon ki..
...da murna tasa hannu ta rufe idon ta, tana ta murnushi, ɗaukan ɗayan key ɗin da ya ajiye a gefen sa yayi, yasa ya buɗe jakar, ɗago ido yayi dan yaga shin da gaske ne ta tufe idon ko dai tana kallon sa, dan yasan halin ta
ganin ta rufe idon ta da gaske ne yasa yayi saurin buɗe jakar ya chire wani kana Box da akayi selling nasu guda 2 ya ɓoye ta bayan sa, san nan ya ɗago ya zuba mata ash eyes na shin nan Sosai yake kallan face nata, ta rufe ido sai murnushi take
Sauko da idon sa yayi kan wuyar ta, a zuchiyarsa yana faɗin, wan nan yarinya akoi dogon wuya ga wuyar nata a chike, ba ƙaramin kyau wuyar nata ya masa ba jiyake kamar ya sa hannu ya shafa ko zai rage raɗaɗin da zuchiyar sa ke masa a duk lokachin da yake kallon ta, sosai ya kura wa wuyar nata ido, ita kam diyana bata ma san meke faruwa ba sai murmushi take tana jiran yace ta buɗe ido,
slowly ya sauko da manya manyan ashe eyes nasan nan zuwa kan kirjinta, kara waro idon nashi waje yayi yana kallon kirjin nata sosai, chikin zuchiyar sa yana faɗin, i think yarinyar nan ba zata wuche 15 years ba to ya akayi take da manya manya boobs haka, kodai ta wuche hakan ne "ke shekarar ki nawa, batare da ta buɗe ido ba tace "na kusa chika 16 shiru yaɗan yi still dai kallonta yake
"Yaya Aryan nayi kyau ne yasa kake tambaya ta shekaru na, ai bai san lokachin da murmushi ta kub che mana ba, ita dai bata da wata matsala burinta kawai ache tayi kyau, "yaya Aryan to ba kache komai ba "eh mana my sister kinyi kyau sosai da sosai kuwa kuma ai ke daman kyakkyawa che tun asali, wani haɗadɗen murmushi ta saki,
Manuniyar yatsan hannun sa, yasa chikin ramin da dimple nata ya lotsa saboda murmushi da take yana faɗin "nafi son wan nan a gaba ɗaya face naki, "laaaa yaya Aryan to zan baka kyauta, murnushin gefen fuska ya ɗan saki kafin yace "ok to ngd
"yaya Aryan in buɗe ido na? "Eh buɗe, da sauri ta waro idon ta a kan face nashi wani cool murmushi ya sarkar mata wadda shi kan shi bai san yayi ba "yaya Aryan ka buɗe jakar tayi maganar tana mai do da kallon ta kan jakar "eh na buɗe gashi nan da sauri tasa hannu ta fitar da wani ɗan ƙaramin Box mai shagen kyau gwaldin colour sai kyalli yake
Yaya Aryan taya ake buɗe wan nan Box ɗin?, ansan Box ɗin yayi daga hannunta ya buɗe mata san nan ya mika mata, wani dagareren abun hannun gold ne a chiki mai matikar kyau da tsada an masa kwalliya da duwasu farare masu kyalli ajikin sai ɗaukan ido yake, anyi rubutu da larabchi a jikin "yaya Aryan me aka rubuta a nan tayi maganar tana nuna masa rubutun Arabic ɗin, kallan rubutun yayi, kafin yace "sunanki ne ajiki, shiru ta ɗanyi kafin ta sake chewa
"laaaa yaya Aryan daman kasan