Showing 333001 words to 336000 words out of 363274 words

Chapter 112 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2606

san yana jin yinwa kawai ya ki ci ne saboda yana ganin kamar abincin da yake kawo min bazata isa muci da shi ba" na kai karshen maganar tare da kara sunkuyar da kai na kasa dan tun da na fara magana ya zuba min manya manyan idon sa yana kallo na kallon sa Inna mutuniyar kirki ta yi kafin tace "To ka dai ji dawo ka zauna kuci abinci" ba musu ya juyo ya dawo ya zauna ɗan ne sa da ni Inna mutuniyar kirki da kan ta ta zuba mana ɗumamen tuwon jan masara da miyar zogale yaji man shanu sai kamshi yake zubawa kowa da kwanon sa ta zuba mana ta miƙa min kafin ta miƙa masa na sa sanna ta mike ta fita ta bamu waje. Inna na fita na kalle sa nace "Hamma me kace wa Inna a kai na?" Ba tare da ya kalle ni ba yace "Nace mata tsintar ki na yi ban san kowa naki ba kema kin ce baki san kowa ba na tambaye ki kin kasa gane komai na faɗa mata a Cameroon na tsince ki idan har na faɗa mata daga in da ki ke zata ce sai na mai da ki ni kuma gaskiya ba... Bai karisa maganar ba ya yi shiru tare da ɗaukan pai pai ya tare hasken fitillar ta dai na haska masa fuska yana son fara cin abinci amma ba zai iya ci ina kallon sa ba, shi ya sa ya tare fuskar sa "Hamma ni ba zan iya cin abincin nan ban yi wan ka ba" shiru ya ɗan yi kafin ya miƙe ya ɗauki pai pai ya rufe abincin sa ya ɗauki fitillar ya nufi waje yana faɗin "muke na nuna miki bayi" cikin sauri na mike dan na san halin sa baya son jira wallahi baban su Hiyana ta wani gefen halin sa sak irin na Safras dan bai son yawan magana ga shi da zafin zuciya bai son ɓata lokacin akan abu baya kallon mutane ba ruwan sa da kowa harkan gaban sa kawai yake ɗan zaman da nayi da shi na karan ce sa sosai shi yasa da Ammi tace Safras ɗan tane sai na dai na kallon laifin sa dan na san in da ya gado halin ban ban cin su shi Safras abun ya karun masa ne saboda horon sojojin da ya samu yana kashe criminal da sauran su shine ya kara masa zafin zuciya amma ban da haka ba in da ya baro baban su Hiyana. Gaba ya yi na bi bayan sa a bakin bayin (toilet) ya tsaya ba tare da ya yi magana ba idan da sabo na saba da halin sa na rashin magana a ɗan zaman da muka yi da shi cikin tsoro na sa hannu na ansa fitillar hannun sa na shige bayin ina faɗin "Dan Allah Hamma ka jira ni a nan kar ka tafi" shiru ya yi bai yi magana ba ya ɗan matsa gefe kaɗan ya tsaya ya juya ya bawa bayin (toilet) baya yana jira na cikin sauri na yi wanka tare da mai da kayan da na cire na fito yana tsaye fitillar da suke makalawa a tsakar gida tana haska shi cikin sanyin murya nace "Hamma na gama" wucewa ya yi ya nufi wani ɗakin bukka ba tare da ya yi magana ba ko ya juyo ya kalle ni. ina tsaye awajen cikin tsoro jim kaɗan ya fito hannun sa riƙe da kaya dai dai kofar ɗakin da aka bani ya tsaya kasa kasa yace "muje" da sauri na kariso wajen sa yana shiga ɗakin na bi bayan sa saman yar gadon da aka bani ya ajiye min kaya ya juya ya nufi waje yana faɗin "Idan kin sa kayan ki kirani ina waje" yana kai karshen maganar ya fice ɗaukan kayan na yi ina kallon su kayan fulani ne kala biyu sai wani dogon riga na atamfa na yi mamakin ai na ya samu kayan nan kusan dai dai da jiki na duk da ranar na zo gidan ban ga alamar akoi yarinya dai dai ni a gidan ba ita kuma Inna mu ta fini da tsawo da jiki kayan ta ba za su min ba wanna da ya kawo min kuma dai dai da ni da kaɗan rigan ya fi tsawo na sai daga baya na gane kayan Ammi ne bayan na tambayi Inna take faɗa mi kayan babban ƴar tace ta yi Aure a birni, bayan na gama shirya wa cikin dogon riga na leƙa waje yana tsaye ya bawa ɗakin baya zuba masa ido na yi na yan mintoci ina kallon yadda lallausan bakin gashin kan sa ke kwance a bayan wuyar sa sai kyalli da sheki yake yana tsaye fitillar tsakar gida na haska shi sosai na kare wa kyakkyawar surar sa kallo ta baya na shagala da kallon sa ba tare da ya juyo ba yace "Idan kin gama kare min kallon zan iya wuce wa" waro ido na yi ina son gane ta ina ya san ina kallon sa ina cikin tunani sai ji nayi ya kyasta min yatsun sa a face na yar firgigit na yi kafin na yi magana ma ya wuce ciki ya zauna ya fara cin abincin sa cikin sauri nima na dawo na zauna wajen nawa abincin na buɗe na fara ci zazzakar voice na sa ne ya daki dodon kunnen yana faɗin "Ki yi hakuri da irin abincin mu na san baki saba cin irin wanna ba nama da shinkafa ki ke ci" murmushi na yi ina faɗin "Hamma ai wan nan Abincin ma ya fi na mu daɗi" shiru ya yi bai sake magana ba har muka gama cin abincin ya mike ya mufi waje yana faɗin "Ki yi barci dare ya yi a huta gajiya" bai jira amsa ta ba ya fice da sauri kwashe kwanikan na yi na ajiye su ta bayan kofa na haye gado na kwanta saboda gajiya ba jimawa barci ya ɗauke ni.

Kun dai ji yadda Hajj Fateema ta haɗu da Bappan su Hiyana ko? to mu haɗe daku dan jin wanna irin labarin soyayyar ta su

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu





💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋



By
Star Lady


Page 58


A ranar nayi barci mai daɗi sosai ban farka ba har karfe 9 na safe na farka a hankali ya buɗe ido tare da mikewa zaune ina kallon ɗakin Inna bai war Allah ta kawo min abinci ta a jiye min mikewa nayi ya fito waje inna na zaune a tsakar gida tana gyara ganyen miya kusa da ita naje na tsuguna cikin jin kunya nace "Ina kwana Inna" da fara'a ta ɗago tana kallo na kafin ta amsa min da "Lafiya ya gaji yar hanya" "Lafiya" na amsa mata da shi ina son tambayar ta ina Hamma amma ina jin kunya shiru na yi Inna kamar ta shiga zuciya ta sai tace min "Hamman ki ya fita yaje zaga gari yace idan kin ta shi ki yi wanka ki shirya ki je ki same sa a wajen gona zai yi magana da ke" cikin zumuɗi nace "Ni inna na koshi da abincin ina ne gonar ta sa in je can" murmushi inna ta yi kafin tace "Aa Hamma ki yace sai kin ci abinci kin yi wanka" "To inna zanje na yi wanka sai na ɗauki abincin muje muci tare da shi" ganin na damu ina son ganin sa yasa Inna tace mini "je ki yi wanka ki ɗauki abinci kije ki same sa" da sauri na mike ina kokarin ɗaukan bokitin da na gani a tsakar gida Inna tace min "Hamman ki ya kai miki ruwa tun ɗazun yana bayi ki ɗebo na zafi a kitchen ki surka" sosai naji daɗi har rai na na ji na kara kaunar su suna da kir ki da karrama ɗan Adam suna son bako godiya na mata sanna na wuce kitchen na ɗobo ruwan zafi a kwarya na je bayi na surka ruwan na yi wanka a gurguje na fito na wuce ɗakin da ya kasan ce mallaki na a yanzu kayan fulani da ya kawo min jiya shi na ɗauko na sanya farin na mai da blue ɗin na ajiye ina da gashi mai tsawo na gyara kai na nayi tsab tsab ban san ina da kyau ba sai da na sanya kayan fulani nayi kyau sosai sai dai na kasa fita da kayan kasan cewar rigar zuwa cibiya ne bai rufe min cibiya ta ba kwance ɗan kwalin nayi na ɗaga rigar sama na ɗaura ɗan kwalin daga kirjina na sake shi yana da girma ya rufin cibiya ta na sake rigar, na yi kyau sosai na ɗauki abincin na fito waje Inna na zaune in da take nazo har gaban ta na tsugunna nace "Inna ina ne gonar" miƙewa ta yi tana faɗin muje "ta bayan ɗaki na muka bi sai yaba kyau na da kyan da kayan suka min take gidan su Bello muka shiga nan Inna ta kira Bello lokacin yana yaro sosai akan ya min jagora zuwa gonan Bappan su Hiyana tsabar zumuɗi na son ganin Bappan su Hiyana ko gaishe da su Innar Bello ban yi ba Inna tace da Innar Bello Bello yazo ya rakani gonar Ahmadu. Haka ko akayi sai zumuɗi na ke nayi wa Inna sallama sai albarka take samin har muka tafi. munyi tafiya mai ɗan nisa kafin mu iso gonar tasa tun daga nesa na hango sa yana zaune kasar bishiyar mangoro su uku da shi da wasu da ban san su ba a lokacin cike da farin ciki na karisa wajen tare da yi musu sallama mutanen dake zaune da shi ne suka amsa sallamar shi kuwa zuba min manya manyan idon sa ya yi yana kallona ba tare da ya yi magana ba har katsa na tsugunna na gai da su da fara'a abokan na sa suka amsa suna tambayar sa wace ce ni shi kuwa kallo na yake bai amsa gaisuwar ba banji daɗi ba da bai amsa gaisuwa ta ba ya dan sosa min rai cikin zolaya abokin sa yace "Wai Ahmadu Aure ka yi ne a can da ka je?" Shiru ya yi bai tan ka ba ɗayan abokin na sa ma ya sake tambayar sa ko Aure ya yi ne kasa kasa yace "Eh Aure na yi" jin abun da yace ya sa na manta da ɓacin rai da nake ciki na kin amsa gaisuwa ta da ya yi cike da murna abokan sa suka min barka da zuwa sanna suka mike suka bamu waje shi ma Bello ya juya ya koma gida kallo na ya yi da kyau kafin yace "Kin yi kyau sosai kayan fulani sun miki kyau kiyi hakuri akan abun da na faɗa wa su habu na cewa ke mata tace na faɗa musu haka ne dan ban son su takura miki idan suka san baki da Aure zasu yi ta damun ki suce suna son ki ni kuma ba zan so hakan ba ba zanso kiji wani rashin daɗi a kauyen mu ba" ina kokarin zama a kasa ya yi saurin ce min "Zo ko zauna a nan" ya yi maganar yana nuna min in da su Habu suka ta shi ba musu na zauna awajen tare da ajiye kwanon abinci da na zo da shi "Baki ci abinci ba ko?" Gyaɗa masa kai na yi alamar eh matso min da abincin ya yi yana faɗin "To buɗe ki ci" make masa kafaɗa na yi ina faɗin "Sai dai mu ci tare dan na san kai ma baka ci ba" haka ba dan yaso ba muka fara cin abinci tare naji matikar daɗi sosai. Wunin ranar dai tare muka wuni da shi muka yi ta hira ina jin kara kaunar sa a rai na.
Wasa wasa har na yi sati a kauyen su ba bana tunanin komawa gida bana tunanin ya yan uwana bana tunani komai sai Bappan su Hiyana a wanna yan kwana ki magana ta fito a kauye wai ni matar sa ce sai magana ake an dami Innar da magana hakan yasa ranar da na cika kwana goma da daddare ina zaune a ɗaki na ya shigo shi da Innar mu kusa da ni Inna ta zauna shi kuma ya zauna ne sa da mu cikin girma da nuna girma innar ta fara magana tare da dafa kafaɗa ta "Ummi kasan cewar haka Inna take kirana Ummi "Ummi kin na jin abun da yan kauyen nan suke faɗe ko? Wasu suna cewa Ahmadu ya sato ki ne wasu kuma suna cewa ke matar sa ce bana son hayani da tashin hankali gashi mu bamu san kowa na ki ba bare mu mai da ki garin ku, wanna abun yana damu na sosai na tambayi shi Ahmadu ya ce min a cikin daji ya gan ki ba zaki iya tuna ina yan uwan ki ba?" Ta ƙasar ido na saci kallon sa ya yin da shi ma ni yake kallo kashe min ido ɗaya ya yi ban san lokacin da na waro ido ina kallon sa ba cool murmushi ya saki yana ɓuye fuska nima murmushi na saki gaba ɗaya na manta a gaban inna muke ashe duk abun da muke Inna na kallon mu ganin mun shagala da kallon juna yasa Inna ta mike ta nufi hanyar fita tana faɗin "Ahmadu gobe ka sayi goro ka kaiwa liman bayan sallar azahar sai a ɗaura muku Aure" ta kai karshen maganar tare da fice wa daga ɗakin kunya naji kamar zan nitse kasa shi kan sa ya ji kunya amma sai ya danne ya dube ni yace "Ina son in ji me abun da ki ke buƙata in mai da ki garin ku ne? Ko kaya dan ni ba zan iya yin miki rashin a dalci ba ba zan aure ki ba tare da ki na so na ba ko makamancin haka kina da yancin ki yanke wa kan ki hukunci" "Hamma kana so na ko baka sona? A hankali ya ɗago ido yana kallo na a wan nan karon ban sunkuyar da kai ba nima na zuba masa ido ina jiran amsar sa cikin sanyin murya yace "Me ya sa ki ke tambaya? Ina son ki mana" "A'a Hamma ba irin wan nan son ba fa so irin na Aure ina nufin zaka iya Aure na" "Ina son ki tun ranar da na fara ganin ki amma sai dai...bai karshen maganar ba na tari mumfashi sa da faɗin "Amma me yanzu ba lokacin wani amma bane kaji me Inna tace gobe ka sai goro ka kaiwa liman idan an ɗaura Aure zan so ka fara yi min albirushir da kan ka" ina kai karshen maganar na mike na fice daga ɗakin na barshi zaune a wajen. Haka washe gari aka ɗaura mana Aure yan kauye sun yi ta surutu suna gulma Innar Bello itace mutun ta farko da ta fara jana a jikin ta bata ɗaukan gulman mutane haka mukayi ta rayuwa har inna ta rasu Allah ya bamu haihuwar ƴaƴa uku kafin Ammi tazo Hiyana Diyana Lamrat bayan na Haife sune Ammi tazo sau ɗaya kuma a gurguje tazo ta tafi hakan yasa ban samu daman zama da ita mun yi hira ba ko lokacin da tazo rasuwar Inna naso zama muyi hira da ita amma ban samu dama ba sauran labari akan su Hiyana kun san shi kunji daga bakin su Bello A ta kai ce wanna shine dalilin rabuwa na da iyaye na tun lokacin dana bar gida ban sake komawa ba har yanzu dana ke muku magana wanna shi ne labarin abun da ya faru" ta kai karshen maganar tana kuka sosai hawaye shara shara a firkar ta kallon Abba Ammi tayi kafin tace "A'a lallai Fateema kice ke ki ka ɓata komai ko in ce ku kuka ɓata komai dake da Ahmadu duk yaranta na damun ku an faɗa muku a na yiwa iyaye wanna wautan ne alhakin iyayen ki ne yasa Allah ya jarabce ku da Habiba iyaye sun wuce wasa dole ki koma ki nemi gafarar su idan ba haka ba wallahi musifa ma yanzu ki ka fara shiga bak....bata kai karshen maganar ba Abba ya ɗaga mata hannu yana girgiza mata kai alamar ta yi shiru shiru ta yi cikin nitsuwa Abba ya fara magana "Fateema kun yi kuskure ba'a yiwa iyaye hakan hakkin su ba zai barki ba dan ina da tabbacin har yanzu suna cikin tashin hankali suna tunanin ki ki faɗa min ya ki ka ji lokacin da ki ka fahimci ba tare da ƴaƴan ki, ki ka yi rayuwa ba? Cikin kuka tace "Naji ba daɗi naji zafi da kunan rai wadda har yanzu ma nake ji" "Good ina mai tabbatar miki abun da ki ka ji game da naki ƴaƴan bai kai rabin abun da iyayen ki suka ji ba saboda ke kin dawo kin samu ƴaƴan ki cikin koshin lafiya su kuma iyayen ki har yanzu suna cikin zulumin da tashin hankali wallahi gara ace musu mutuwa ki kayi sun ga gawar ki nan zasu iya mantawa amma ɓata fa ki kayi awajen su ina da tabbacin har yanzu suna sa ran zaki dawo kin ɓata komai Fateema duk halin da su Hiyana suka shiga ashe kece sula to yanzu dai komai ya wuce tun da duk mai afkuwa ta afku ki shirya da kai na zan yi waya wa mahaifin ki dan muna da kyakkyawan alaka da gaba ɗaya saraku nan Africa za'a shirya mana tafiya da kai na zan kai ki, ki nemi gafara ina da tabbacin baban ki yana raye maman ki ne dai bamu sa ni ba sai munje kije ki shirya gobe goben nan zamu yi tafiyar sassafe" ya kai karshen maganar tare da mukewa ya bar wajen. Sosai Ammi ta kara mata faɗa da nasiha akan ba'a bijirewa umarnin iyaye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login