Showing 84001 words to 87000 words out of 363274 words

Chapter 29 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2591

birki ya jaaa da maganar asukwa'ne ya daɗa waro manya manyan green eyes nashi yana kallon Ammi, data ɗaga yatsu biyar zata zabga masa mari sai kuma itama ta dakata tana kallonsa, chikin fushi Ammi tafara magana "to a nan aka haifi uwar idan mutanen garin nan dabbobi'ne to fa kasa har dani ina daga chikin dabbobi nima ko naso ko baka so nan shine tushen ka ta ɓangarena kuma ina alfahari da hakan,idan kaga dama katashi ka dakatar da ɗan uwan ka idan kuma bakaga dama ka barshi yayi kisan kai tana kai karshen maganar ta juya a fusache ta koma chikin gida,

dafe kai DON yayi yana faɗin "dan Allah Ammi kiyi hakuri na tuba, why why zan ɓatawa mahaifiya'ta rai sosai haka, har take kokarin yin abun da bata taba kotan tawaba mari Ammi, kuma ni NO yau gaskiya na kure ta, sosai dole naje na nemi yafiyarta ya karisa maganar yana miƙewa kai tsaye wajen su Aryan yanufa,yana taku irin na jaruman maza,
yana zuwa yasa hannu ya damki damtsen hannun Aryan ya jashi baya, a fusache Aryan yasake nufar buba gadan gadan, rikesa DON yayi yana faɗin "wai wan nan dukan na menene haka ya isa baka ganin ya suma ne wai ma me ya haɗaku kune, shiru Aryan yayi yakasa magana sai huchi kawai yake ga wani iska mai zafi dayake furzarwa daga bakinsa, hannunsa DON yaja har wajen mota, ɗauko robar ruwa DON yayi a chikin motar ya buɗe bakin robar ya miƙawa Aryan, ansan ruwan Aryan yayi ya kafa robar a bakinsa ya farasha, ganin yakusa shanyewa'ne yasa DON ya ɗauko masa wani yabuɗe yana jiran ya karisa shan'yewa, tas Aryan ya shanye ruwan, yayi jifa da robar, yasa hannu ya anshi wanda DON ke riƙe dashi ya duƙa ya zuba ruwan gaba ɗaya a tsakiyar kansa,shiru yayi Almost 7mnt sai faman furzar da wani iska mai zafi daga bakin'sa yake, ganin Aryan bai da niyar miƙewa yasa DON kamo hannunsa ya mikar dashi ya zaunar dashi chikin mota yana kallon face nashi "are U okey bro DON ya tambaya yana nazarin face ɗin shi, jinjina masa kai kawai Aryan yayi batare dayayi magana ba "me ya haɗaka da mutanen kauyen nan,har ka masa irin wan nan duka, a zafafe Aryan ya ɗago kamar wadda akawa allura yasake miƙewa yana kokarin nufar buba, da sauri DON yasake kamo hannunsa, yana faɗin "it's ok zo kayi zaman ka ya isa haka kodai so kake ka ɗau doka a hannun kane ya isa pls, da kyar DON ya shawo kan Aryan ya hakura ya kyale buba, shiru sukayi Aryan na zaune chikin mota DON na tsaye a kusa dashi yana kallansa, almost 15mnt san nan Aryan ya ɗago yana faɗin "ina su Ammi, wani dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace, thank God daka dawo chikin hayyachin ka, tsaki Aryan yaja kafin yace "ni bansan wulakanchi da che maka akayi bana chikin hayyachi nane pls ka faɗamin ina su Ammi "suna chikin gidan chan mana yayi maganar yana nuna gidansu hiyana da hannu, shiru Aryan yayi kamar mai tunani jingina kansa yayi da jikin kujerar motar ya lumshe ido, zuba mi shi wan nan manya manya green eyes nashi nan DON yayi yana ta kallonsa kamar mai son gano wani abu a tattare dashi.

A ɓangaren buba kuwa, a sume yake ga jiki duk jini, bello ya ɗauke sa Chak ya saɓasa a kafadar'sa yayi chikin gida dashi, saman ta burman dake shinfiɗe a tsakar gidan bello ya kwantar dashi san nan yakira hasana, yace ta kawo masa ruwa, da sauri hasana ta kawo ruwan a kwano bello ya ansa ya ɗiba a hannun'sa ya shafawa buba a fuska, shiru bai farfaɗo ba, sake ɗibar ruwan bello yayi yasha fa masa nan ma shiru, bai farfaɗo ba zuba masa ruwa mai ɗan yawa bello yayi shiru buba ko motsi baiyi ba, dukar da kai bello yayi sai tin kirjin buba yasa kunnensa dan yaji shin mutuwa yayi ne, tabbas zuchiyar buba na har bawa to amma an zuba ruwa an zuba bai farfaɗo ba, shiru bello yayi yana tunani a wan nan yanayi innar bello tafito daga bayi ta same'su chikin ruɗu da kiɗima ta nufe'su tana tana faɗin "bello me ka masa badai dukan'sa kayi ba "a'a inna bani na dake sa ba yan uwan'su diyana ne suka masa hukunchi "to yanzu bello ya zamuyi kasan, san dai bala'e mahaifiyarsa yanzu ko zamu tsallake inuwar mu bazata taɓa yarda ba kai ka bugesa ba, shiru bello yayi bai sake chewa komai ba ya zubawa buba ido .

A bangaren su Ammi kuwa zaune suke a tsakar gd diyana na kwanche a kan chinyar Aunty Farida tayi barchin wahala duk da an wanke mata goshin nata jinin bai daina zuba ba, miƙewa hiyana tayi tana faɗin "Aunty Zahra kizo muje ɗakin bappa,"to Zahra tace san nan ta miƙe suka nufi ɗakin bappa, kamar yadda suka bar ɗakin haka yake ba'a taɓa komai ba sai uban kura da datti da ɗakin yayi, nan fa hiyana ta shiga kakkaɓe kurar ta fito ta ɗauki tsintaiya a waje ta koma chikin ɗakin ta hau gyaran ɗakin

Gyara zama Ammi tayi tana fuskantar Inna tafara Magana "habiba kinsan kafin Ahmadu ya rasu babu Aure a tsakanin ku Koh, to yanzu mu ba wan nan che ta kawo muba, yanzu dai wan nan gida da kike chiki kirike mun barmi'ki, ki chigaba da zaman'ki a chiki da sauri Aunty Farida tace "Ammi ya zakiche kin bata gidan kuma ina che ae ba zai yiwu kiyi kyauta da dukiyan marayu, batare da izinin suba, murmushi Ammi tayi nasu irin na manya kafin tace "feeda wan nan dukiyar dakike gani bana su hiyana su kaɗai bane har da nawa a chiki nima ina da kaso, dabbobi 60 baban mu ya rasu ya bari ga filaye da gonaki, ba yadda za'ayi nayi kyau ta da abun da ba na waba Aunty farida zatayi magana hiyana tafito daga ɗakin bappa da gudu tana faɗin Ammi ki..
*💫STAR LADY💫*



*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*


*Episode 23*





Da gudu hiyana ta kariso wajen su Ammi tana faɗin "Ammi ki kalla, "manene wan nan kuma hiyana, Aunty farida ta tambaya da mamaki a fuskarta, da sauri Ammi tasa hannu ta ansa wani ɗan karamin tsohon a kwatine irin na ajiye abu mai mahim manchi "hiyana ina key ɗin a kwatin Ammi ta tambaya tana goge kuran jikin a kwatin, "nima ban gani ba iya wan nan kawai nagani "ok to kutashi muje mu duba key ɗin kuyi sauri dan karmu bata lokachi kunsan yau zamu koma tana kai karshen maganar ta miƙe,tanufi ɗakin bappa

a hankali Aunty farida ta sauƙe kan diyana daga kan chin yar ta ta kwantar da ita a kan tabar man ta mike itama tabi su Ammi binchike suka shiga yi a ɗakin bappa,su duba nan su duba chan, sun bin chika ko ina amma basuga key ɗin ba Ammi tace "muje kawai tun da babu key ɗin dan ajiye a kwatin a hannu na dan nasan abu mai mahim man chine Ahmadu yasaka a chikin wannan a kwatin,domin a kwatin asali na baban mu ne abubu masu muhimmanci ake ajiyewa a chiki tana kai karshen maganar tanufi waje, suka bi bayan ta har sum fita hiyana ta dawo da gudu ta ɗauki wata jakar bappa mai ɗan girma jakar chike take da Qur'ani da hadisan, ta karkaɗe kuran dake jikin jakar ta ɗaki tsumma da goge jakar tas san nan ta ɗauka ta nufi wajen, kuɗi Ammi ta ɗauko a jakar ta ta kirga 50k ta mikawa inna, sai washe baki inna take tana hannu ta amsa a zuchiyar ta, tana faɗin kuɗin zuwa wajen malam sun samu Ammi ta dubi Aunty farida tace "feeda ki tashi diyana mutafi Koh kinga rana nayi'fa, kuma mai martaba yace kar muwuche karfe 2 "a'a Ammi dan Allah kar a tasheta kingafa wahalar da yarinyar nan tasha hiyana kije ki kiramin Aryan ko prince ɗayansu yazo ya ɗauke'ta Aunty farida ta karisa maganar tana kallon hiyana, jiki ba kwari hiyana ta juya tanufi wajen a zuchiyarta tana tuno abun da DON yamata jiya, a tsorache ta karisa wajen motar nasu, zaune suke a chiki,sunyi shiru DON na latsa waya, Aryan na jingine da jikin kujerar mota idon sa a lunshe kamar mai barchi, jikinta har kerma yake ta karisa wajen su ta duka har kasa chikin sanyin murya da tsoro tace " yaya prince Aunty farida tace na kira ɗaya daga chikin ku, kamar basuji me tace ba, bawan da ya ɗago barema tasa ran zai mata magana, tsorone yasake kamata tashiga tunani, in tashi in tafine ko dai basu ji bane nasake mai mai tawa, chike da fargaban abun da zai biyo baya ta kuma chewa "yaya prin...bata kai karshen maganar ba Aryan yayi saurin che mata "kije ina zuwa dan yasan in ya bari ta karisa maganar DON zai daka mata tsawa ya firgitata,da sauri ta mike har tana kokarin faɗuwa takoma chikin gida,

Slowly ya buɗe idonsa tare da ɗagowa daga jingina da yayi da jikin kujerar, a nitse a zuro kafarsa waje kafin yafito daga motan gaba ɗaya, sai daya fito ya juyo ya kalli DON yace "bari naje naji menene yasa Aunty babba ke kiran mu, batare daya jira yaji me DON zai che ba ya nufi chikin gidan, dan yasan DON ba tan kashi zai yiba, da Sallama ya shiga chikin gida daga ɗan baya ya tsaya yana faɗin "Aunty babba lfy kike neman mu, "lfy diyana zaka ɗauka ka kai min ita mota tayi barchine kuma bansan a tashe'ta dan kukan da ta sha yaka mata ta huta "shiru ya ɗanyi yana kallan face ɗin diyana yadda jinin ke zuba kaɗan kaɗan ga wajen ya kunbura sosai, nan take yaji wani ɓachin rai jiyake zuchiyar sa na tafasa sosai tunani yake anya idan nabar wan chan kazamin yaran haka bai chucheta dayawa ba kuwa, "Aryan lfy kuwa Aunty farida ta tambaya tana kallon fiskar'sa ɗauke kai yayi daga kallon diyana ya dawo da idan sa kan Aunty farida "ba komai Aunty babba ya bata amsa tare da nufar inda diyana ke kwanche hannu yasa a aljihun'sa ya chiro hanky ya duƙa a hankali yafara goge nata jinin, mamakine yakama su Ammi musamman Zahra shiru sukayi suna kallon ikon god, Aunty farida kam sai murmushi take tana adduar Allah yasa Aryan ya kamu da sin diyana dan ita har cikin zuchiyar ta tana kaunar diyana sosai
ganin diyana na ɗan motsi tana kokarin farkawa yasa Aryan chire hanky ɗin daga kan goshinta,ya zuba mata ido sosai yana kallon ɗan tsagun dake kan gerarta ta raba gerar gida biyu, bakaramin kyau gerar ta masa ba wani dogon numfashi yaja kafin ya miƙe ya tsaɓeta a kafaɗarsa yanufi waje da ita

gaba ɗayansu suka rufa masa baya Ammi tana faɗin "to habiba mun tafi idan da rabo sake haɗu Allah ya haɗa fuskokin mu idan kuma babu to Allah yabamu dachewa tana kai karshen maganar tayi waje, ita dai Inna ko ajikin ta sae murna take tasamu kuɗin zuwa wajen malam

Chikin mota Aryan ya kai diyana ya kwantar san nan ya dubi Zahra da hiyana dake tsaye a bayan sa yache "ku koma ɗayan motar chan ku barta a nan ita kaɗai tun da barchi take, hannun hiyana Zahra ta kama suka nufi ɗayan motar, shi kuma ya juya ya nufi motar'su yadda ya bar DON haka ya dawo ya same'sa sai latse latsen waya yake, zama yayi a gefen sa ya kwantar da kansa a jikin kujerar motar yana kallon sama slowly ya lumshe manya manyan ash eyes nashi nan

"Ke zahra'u ina zaku je baga motar ku chan ba Ammi ta tambaya tana kallon su Zahra dake kokarin buɗe motar da yaya Aryan yace su dawo chikin ta tace "yaya Aryan yace mu dawo nan mu kyale diyana a chan tun da barchi take "ok to bari mu shiga gidan su bello, jin an ambachi sunan bello yasa Aryan ɗagowa tare da waro ido asukwa'ne, ɗaure fuska yayi sosai yafara magana "Ammi ki bari dai a kira bello yazo nan ya sameki ban yar da kuje gidan ba, sai lokachin DON ya ɗago green eyes nashi dan jin yadda Aryan yayi magana yasan ranshi a ɓache, zai yi magana sai ya jiyo Ammi na faɗin "aa Aryan ni ina mutunta mutanen garin mu dan na Aure jinin sarauta ba shi'zaisa na wulakanta mutane ba, innar bello ta girmeni sosai ita zanje zanje in gaisar, sai muyi magana da bello san nan ga bappa bello shima zan gai dashi, tana kai karshe maganar ta wuche tanufi gidan su bello da sauri Aunty Farida ta bi bayan'ta, Aryan kuwa kamar zai yi kuka saboda bakin chiki sai huchi yake,

wani iska mai zafi DON ya furzar daga bakinsa tare da juyo da green eyes nashi yana kallon Aryan calmly ya fara magana "kai me kake wani ɓata rai haka ae kaɗan ma ka gani in dai Ammi che Allah dai ya rufa mana asiri kar tache mu kwana a garin nan, wani dogon tsaki Aryan yaja kafin yace "wlh nima naji gaba ɗaya na tsani garin, da sauri DON ya juyo da kyau yana kallon Aryan from head to toe wani dogon numfashi taja tare da sauƙe ajiyar zuchiya, yayi shiri kamar mai nazarin wani abu "lfy kake kallona haka Aryan ya tambaya yana kawar da kai gefe "Aryan are U okey kuwa? Wai meyasa tun ɗazun ka keta wani fushi da ɓata rai ne?
Dawo da kallan sa Aryan yayi kan face ɗin DON ya ɗaure fuska sosai yace "wai ni prince wani irin iskanchin ne wan nan sai ka'rinƙa wani tambaya ta ina lfy ina lfy to am not okey haba dan Allah ni yarone, "yanzu nasake tabbatar wa tabbas akoi abun da ke damun ka daga magana sai fushi sai kache ba lfy ba "tsaki Aryan yaja a kule yace "to sai ka bincike ko wace chuta che ke damu naɗin ai, shiru DON yayi bai sake magana ba kuma bai dai na kallon face ɗin Aryan ba, ganin haka yasa Aryan juro kafarsa waje yana kokarin fata daga motar, da sauri DON ya rikoshi, "where are U going yayi tambayat still dai yana kallon face ɗin sa, wani dogon tsaki ya kuma ja kafin yace "wai dan Allah prince meyasa kakeson takura min ne, me namaka dan Allah ka kyaleni haba, ɗaure fuska sosai DON yayi yafara magana "saboda ina kaunarkar mana Aryan ka nitsu kadawo chikin tunanin'ka kabani hankalin ka bari'ma na maka wasu tambayoyi, kara ɓata fuska Aryan yayi yana kawar da kai gefe "me ya haɗaka da wan chan mutumin da ka buga har ya suma? Na biyu me ya fusata'ka chikin ɗan kankanin lokachin,bayan ni nasan baka sauri hawa haka, na uku meke damun ka, yau naga abubuwa dayawa a chikin kwayar idon ka, juyowa Aryan yayi da kyau ya rungumi DON yana faɗin "ban saniba my blood ban saniba wlh nima na rasa meke damuna kwata kwata gaba ɗaya sai in rinƙa ji kamar ba niba,ya karisa maganar chikin rau'nanniyar murya, hannu DON ya ɗora a saman bayan shi yana ɗan bubbuga shi a'hankali kamar karamin yaro yana faɗin "it's okay ya isa, nima nasan ba abun da kake ɓoyemin kuma babu wani abun da zaka iya ɓoyemin, kawai abunne yana bani mamaki gaba ɗaya ka sauya kuma nayi binchike a kan lafiyar ka baka da wata matsala duk wani binchiken daya dache nayi nayi, amma bawani abun dake da munka, inajin ba daɗi inganka hakan shiya nima abun yake damuna, ya karisa maganar yana raba jikin su, mayar da kai Aryan yayi ya kwantar a jikin kugerar ya lumshe ido yana mai ds numfashi, shiri DON yayi kamar mai tunani.



A bangaren su Ammi da Sallama ita da Aunty farida suka shiga gidan su buba da suri Inna bello taminƙe ta nufosu tana murnushi, "subhanallah Ammi ta furta ganin buba a kwanche ko motsi ba yayi da sauri ta karisa wajen tana faɗin "bello ku kai shi asibiti mana, shiri Inna yaya bello tayi tana mamakin kyawun hali irin na Ammi "zamu kai shi Ammi yanzu nake son tashi inje in kira mai mashin bello yafaɗa yana kokarin tashi "a'a dakata bello magana nakesan yi da kai daman, bayan mun gama maganar sai ka kai shi asibitin "to Ammi chewar bello yayi maganar yana gyara zaman'sa, kujeran katako innar yaya bello ta ɗauko wa Ammi da Aunty farida, ansa sukayi suka zauna suna fuskantar juna, Ammi ta fara magana "bello ka chigaba da kula da dabbobin nan inshaa Allah idan muka gama magana da Mai Martaba zamu wai waye'ka, san nan kabawa habiba shanu uku biyu mata da ɗaya namiji gonakin bappa kuma duk mun barma ka chigaba da amfani dasu gidan da habiba ke chiki mun bar mata, yanzu sauri muke lokachi ya kure banajin zamu sake zuwa nan kusa amma ko ban zoba duk shawarar da Mai Martaba ya yanke zan aiko ɗan aika,ya sanarma ta kai karshen maganar tana miƙewa, miƙewa Aunty farida ma tayi suka sufi hanyar fita su nawa Inna sallama, har wajen mota yaya bello ya rako su Ammi,
kuɗi mai yawa Ammi da Aunty farida suka bashi san nan Ammi tace "ka ɗauki buba ka kai shi asibiti yanzu nan "to kawai yaya bello yace tare da yajuya ya koma chikin gida, Aunty farida ta dubi Ammi tace "muje mana kodai akoi wani abune "a'a ban san meyasa basu tada motocin ba jeki tambayo yan uwan naki, wuchewa Aunty farida tayi tanufi motar su DON,Ammi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login