Showing 216001 words to 219000 words out of 363274 words
wani dangareren sarkan gold ne wanda ya ansa sunan shi gold ne awajen,mai matukar kyau da tsada sai ɗaukan ido yake ɗago kai Abba yayi ya kallin diyana da ta kwantar da kanta jikin Ammi tana kuka kasa kasa "my daughter ga sadakin ki 100m shine kuɗin sadakin ki daga mijin ki" hannu Ammi ta sanya ta ansa ta sanyawa diyana a tafin hannun ta tana faɗin "an sa ki gani my diyana" kuka kawai take taki kallon sarkan buɗe ɗayan kwalin Abba yayi ya miƙawa Aryan ansa Aryan yayi ya fito da wasu kananan Fararen box masu bala'i kyau daga chiki buɗe ɗayan yayi dan kareran diamond ring ne wadda ya amsa sunan sa diamond sai kyalli yake yana ɗaukan ido ring ɗin ɗauke yake da harafin A ajikin sa ta tsakiya ajiyewa yayi a gefe ya ɗauko ɗayar box ɗin ma ya buɗe shima ring ne irin ɗaya da wan da ya buɗe da farko komai nasu ɗaya sai dai wanan ɗauke yake da harafin D a jikin sa ɗago kai yayi ya kalli diyana dake ta faman kuka kasa kasa yace "my jidda tashi ki zo"tashi tayi tazo gaban sa ta tsaya dan saman sofa mai zaman mutun ɗaya yake zaune hannu ya sanya ya nuna mata saman chinyar sa akan ta zauna satar kallon su Abba tayi kasa kasa yana kallon chikin idon ta miƙewa Abba yayi yana faɗin "zama chikin turawa ya ɓatamin ƴaƴa basa kunya ta yanzu kwata kwata" ya kai karshen maganar tare da fice palo chikin sauri su Ammi suka bi bayan sa taɓe baki Haidar yayi ya fice shi da Omar suna mamakin yaya Aryan
Aryan Kamar jira yake su Abba su fita ya jawota jikin sa yana faɗin "my jidda ya isa kukan nan haka kwantar da kanta tayi saman kirjin sa kasa kasa tace "yaya Aryan kukan ne ai yaki tsayawa" hannu ya ɗaura saman face nata yana goge mata hawaye yana faɗin "to ya isa karki bari hawayen ya sake fitowa kinji? Gyaɗa masa kai kawai tayi ta kara lafewa a kirjin sa hannun ta ya riƙo ya sanya mata diamond ring mai tambarin harafin A sanan ya miƙa mata mai tambarin harafin D yace ta sanya masa ansa tayi ta sanya masa a ya tsan sa na kusa da karamin ba karamin kyau ring ɗin ya musu ba kamar dan su akayi shi
Kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace "my jidda tashi muje na baki abinci" maƙe kafaɗa tayi chikin shagwaɓa tace "aa na koshi yaya Aryan" jan karan hanchin ta yayi chikin wasa yana faɗin "idan baki chiba zan miki Allura" chikin sauri tace zanci to amma kaɗan" ba tare da ya sake magana ba ya miƙe ya saɓata a kafaɗar sa tana faɗin "yaya Aryan dan Allah ka sauke ni zan tafi da kafana" bai tan ka taba ya wuche ya ɗauki Box na sarkan sadakin ta da sauran kayan ya fice daga palon kai tsaye part na shi ya wuce
Masu karatu mu damalmale da ku a soyayyar Habibi da jiddan sa gobe idan mai dukka ya kai mu su habibi yau abun nema ya samu 😹😹
Ina muku fatan alkhari masoyana masoyan Duk Karfin Izzata fatan Allah ya chika muku burin ku na alkhari
Ina miko gaisuwa da jijjina gare ku
Aunty Asma'u
Aunty Hauwa'u
Maman Twins
My mum
Dr Aisha
Aisha
Hauwa'u yar adamawa jinin yola
Sister Halima
Sister Deeja
Aunty Amira
Nana farida
Deenat Ahmad
Maman Amir
Hafsat Rabi'u Abubakar
Da duk sauran wayan da ban samu daman kiran sunan su ba ina godiya ina ganin comments na ku ya sanyani farimciki da nishaɗi yana rage min kishin hiyana da nake ki dan na lura hiyana ta fara shisshigewa masoyina 🥲
Pls a bani hot🔥 comments
💋Duk Karfin Izzata 💋
💖The Talent Troupe Writer's 💖
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Maman Shureim gaba ɗaya wanan page ɗin na kine more love 🥰
Book 2
Page 23
Uk
4:40am ya farka daga barci slowly ya waro idon sa waje kyakkyawar face nata ya fara chin karo da shi ba karamin kyau hasken blue light na ɗakin ya ma face nata ba, barcin ta take chikin kwanciyar hankali ya ɗan ɗauki mintoci yana kallon face nata kafin ya miƙe zaune tare da zuro kafafun sa kasan kagon gently ya miƙe ya fara tafiya toilet ya nufa brush yayi sannan yayi wanka ya fito ya shirya chikin fara jallabiya ya fice daga ɗakin ya nufi masallaci
Yana fita ba jimawa ta farka da kyar ta iya buɗe idon ta dan barci bai ishe taba kiran Sallah ne ya tashe ta mikewa tayi ta nufi toilet jim kaɗan ta fito ɗaure da towel jallabiyar sa ta sanya ta sanya karamin hijabi tayi sallah zama tayi saman dadduma bayan ta idar da sallan ta fara yiwa diyana addu'ar Allah ya bata lfy sai karfe 6am dai dai ta tashi daga kan daddumar ta naɗe ta mai da mazaunin sa
Toilet ta fara wanke wa kafin ta fito ta gyara masa ɗakin tsab ta sanya wani daddaɗar turare ɗaki mai bala'i kamshi sai da ta gama komai sanna ta wuce dressing nashi ta chire masa jallabiyar sa ta ɗaura towel ta dawo ta tsaya a gaban mirrow kallon kan ta tayi sosai kafin tace "Allah sarki yaya Prince wlh yanzu zan ɗaura ɗamarar ya kar ka a gidan nan domin son ka yana neman halakani dole nayi amfani da shawarar Aunty farida, da wanna tunani ta fara shafa body lotion nashi masu kamshi da tsada bayan ta gama ta nufi trolley ɗin ta sosai ta shiga wargaza kayan nata tana neman kayan da sukafi lallacewa wadda idan ka sanya zatayi kama da karuwar gaske koma abun da ya fi karuwa chan kasan babban trolley ta samu wasu wanduna da ba zasu wuchi chinyar taba da yan rigunan su masu kama da singlet ɗaga rigar tayi tana kallon rigar ba zata wuci chibiyar taba murmushi tayi ta mai da ta ajiye tana faɗin "wanna sai da daddare" kara watsa kayan tayi sosai wani shegen wando ta sake chin karo da shi shima ba zai wuchi guiwar ta ba sai dai shi rigar sa zata saukar mata zuwa marar ta da rigar da wandon duk jikin su robane, miƙewa tayi da su a hannun ta tana murmushin chikin sauri ta sanya su tanayi tana sanyawa Zahra albarka da addu'ar Allah ya bata baby mai kyau kamar yaya Khalid ɗin ta, sai yau taji daɗin kayan da Zahra ta zaɓa mata, sosai kayan suka kamata sunfitar mata da ainihin surar jikin ta ba karamin kyau tayi ba ta zama kamar waruwar gaske
bayan ta gama sanya kayan ta kwashe wayan da ta fitar ta mai da chikin trolley ɗin sanna ta nufi gaban mirrow wow ita da kanta tasan tayi kyau sai dai mugun kunya take ji yayay Prince yazo ya ganta a haka tara gashin kanta tayi ta ɗaure a tsakiya da gangan ta ɗauki perfume nashi ta sanya a jikin ta dan ta lura idan ta taɓa wani abu nasa hakan yana sa yazo jikin ta da niyar hukun tata saman gado ta koma ta kwanta tana tunanin ya kamata a che ya yaya Prince ya dawo yanzu, bata kai ga rufe tunanin nata ba sai gashi ya shigo kallon ɗaya ya mata ya kau da kai ya wuce ya nufi toilet har ya kai bakin kofar toilet ɗin ba tare da ya juyo ya kalleta ba kasa kasa yace "ki fitar min da kayan sawa da suka dace da ni" yana kai karshen maganar ya shege toilet ɗin tunani Hiyana ta farayi ki fitomin da kayan sawa da suka dace da ni kenan yana nufi wanda na fitar masa jiya basu dace da shi ba kenan? to ni ya za'ayi in san wan da suka dace da shi kai dole na tambayi Aunty farida ta faraɗamin wasu kayane sukafi dacewa in rinƙa fitar masa idan ya buƙaci dana fitar masan da wanna tunani ta miƙe ta shiga dressing room ɗin,wandon jeans baki da t-shirt ash ta fiddo masa da shi ta ɗaura saman gado ta wuce kitchen dan ɗauko masa breakfast
lokacin da ta dawo ɗakin har ya fito yana shiryawa godiya tayiwa Allah da ya sanya tafita kafin ya fito ba dan haka ba da zata iya sumewa dan shi yaya Prince ba ruwan shi bai san kunya ba zai iya shiryawa ma a gaban ta,bakaramin daɗi taji ba ganin yau ya sanya kayan da ta zaɓa masa
saman table ta ajiye masa trey mai ɗauke da kayan breakfast ɗin,tana kokarin zama saman sofa sai ta tuna massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa ta rinƙa taya bgs sanya kaya da sauri ta fasa zamar ta miƙe ta karisa wajen sa dai dai lokacin yana sanya buttin ɗin rigar, ba tare da tayi magana ba ta sanya hannu chike da tsoro kirjin ta na dukan uku uku ta fara tayashi sanya wa, kasa kasa yake satar kallon ta mamaki ne ya kama shi wato yarinyar nan ta dai na tsoron sa kenan,amma duk da hakan ya ji daɗi sosai har chikin zuciyar sa da ta taya shi sanya buttin ɗin afili kuwa ɗaure fuska yayi chikin tsawa yace "ke me haka!? Chikin sauri ta chire hannun ta daga saman rigar nashi da cool voice tace "kayi hakuri ba zan sake ba" ko kallon ta bai sake ba ya chi gaba da sanya buttin ɗin sa bayan ya kammala ne ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna da sauri ta karisa wajen ta fara sarving na shi sai da ta gama komai ta tura masa gaban sa sanna ta tsugunna chikin girmamawa tace "yaya Prince dan Allah ka kiramin Aunty farida" da hannu ya mata nuni da wayar sa dake saman bedside drawer ba tare da yayi magana ba miƙewa tayi ta ɗauko wayar ta dawo ta miƙa masa tare da ɗan tsayawa daga gefe layin Aunty farida ya kira wayar na fara ringing ya miƙa mata
Ansar wayar tayi ta nufi kofar fita dan ta koma palo bata son yaji me zatace tsawa ya daga mata wadda ya sanya ta juyowa ba shiri "in zaki je!? "Palo zanje" ta bashi amsa chikin tsoro batare da ya kalli in da take ba ya mata nuni da hannun sa akan ta wuce wajen hutawar sa tayi wayar achan,ba musu ta wuce ta nufi wajen already Aunty farida tayi picking call ɗin tun ringing na farko duk abun da ya faru a kunnen ta ya faru tana jin su, zaman saman sofan dake wajen hiyana tayi kafin ta manna wayar a kunnen ta ta fara magana
"Hello Aunty farida in kwana" "my Hiyana kina ji yanzu ba gaisuwa zamuyi ba kin ga wayar sa ne kuma lokacin tafiyar sa wajen Aiki yayi kawai muyi abun da ke gaban mu yanzu wani chi gaba aka samu"shiru hiyana tayi tana ɗan muku muku bazata iya faɗaqa Aunty farida chewar Bgs yayi kissed nata ba,jin tayi shirune ya sanya Aunty farida tace "my hiyana karki ɓoyemin komai ki faɗa min da wuri kinga bamu da time ko, sunkuyar da kanta kasa kayi tamkar Aunty farida na gaban ta chike da jin kunya ta fara bata lbr duk abun da ya faru tsakanin ta da bgs,murna sosai Aunty farida tayi kafin tace "yanzu bari na faɗa miki kayan da ya dace kirin ka bashi da lokacin da suka dace idan ya dawo aiki kinga yana bukatar ya huta ya sha iska to wannan lokaci kananan kaya zaki fitar masa dan su yake buƙata idan ya shiga wanka da daddare kiyi sauri fitar masa da kayan barci masu laushi kuma Prince ya fison abu fari komai nashi farine yana son kalan fari sosai sai ki kula da wanna ma idan da safene to kayan Aiki zaki fitar masa idan kuma ranar weekend ne to ki karanche sa shin yana fita weekend ne idan yana fita to kaya masu kyau da tsada zaki fitar masa irin jeans da t-shirt ba manyan kaya ba aikema ranar kinyi wauta Prince baya sanya kayan hausawa idan ba dole ba, abu na gaba idan kuma baya fita weekend to jallabiya zaki fitar masa sanan ki rinƙa rigasa tashi sallar asuba dan idan ya shiga wanka ki fiddo masa da jallabiya da zai sanye yaje masallaci,yanzu dai sai mu bari haka sai anjima zan kira ku ta wayar Auta akoi wani shirin da zamuyi kuma ki dage akan shawarar Khalid da Aryan yanzu ki mai da masa da wayar sa dan naga lokacin ya tafi zaije wajen aikin sa kar kije kiyi laifi rike masa waya da kikayi" miƙewa tsaye tayi kafin tace "to Aunty farida na gode sosai" "ba sai kin min godiya ba ke dai ki chigaba da yin abun da na faɗa miki In Sha Allah mun kusa nasara" a chikin zuchiya ta amsa da amin tare da chiro wayar daga kunnenta bata iya komai a wayar san nan ba dan haka bata katse kiran ba ta mai da masa da wayar yana zaume saman sofa kamar yadda ta bashi haka ta dawo ta same sa kusa da shi ta zauna tare da miƙa masa wayar tana faɗin "gashi yaya Prince Nagode" an sar wayar yayi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin,bin bayar sa da kallo tayi har ya fice, tana kokarin miƙewa sai gashi ya dawo ɗakin a tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da miƙa mata hannu sa alamar tazo ta ansa miƙewa tayi chikin sauri ta kariso wajen sa sim card nata ya miƙa mata tare da faɗin "now zaki iya kiran kowa sister ki ta dawo dai dai" yana kai karshen maganar ya juya chikin sauri tace "yaya Prince to dan Allah kasamin kati awayar" ba tare da ya juyo ba yace "akoi card a chiki" "to yaya Prince dan Allah ina neman wata alfarma ma" sai lokacin ya juyo yana kallon ta tare da dakatawa da tafiyar da yake takowa tayi a hankali tazo kusa da shi chikin sanyi murya tace "yaya Prince ina son abubuwa da ɗan dama ina son perfume ina son kayan sawa ina son...sai kuma tayi shiru ta fasa faɗe, kallon ta yayi from head to toe kafin yace "wayace ki sanya min perfume na? Waro ido waje tayi tana nadamar tambayar sa da tayi yanzu gashi ta tonawa kanta asiri, harara ya wurga mata kafin ya sake chewa "ki shirya muje" yana kai karshen ya juya "yaya Prince bani da kayan masu hankali a chikin akwatin wanda zan sanya na fita" "ki sanya jallabiya ta" ya kai karshen maganar tare da ficewa tsalle ta buga tana dariya da sauri ta wuche dressing room nashi ta ɗauko jallabiyar sa ta sanya jallabiyar ya fi karfin ta har jaa yake a kasa sosai itakam bata damu da yawan da jallabiyar ya mata ba sai murna take ta fito daga ɗakin baya palo dan haka sai ta wuche ta nufi harabar gidan
Yana zaune chikin motar sa sunyi reading tafiya da alama ita suke jira tsayuwa tayi ta rasa wani mota zata shiga chikin sauri Abdol ya buɗe motar ya fito ya buɗe mata gidan baya in da Bgs ke zaune,satar kallon sa tayi ta kasan ido taga ko ya kalli abun da Abdol yayi kuwa ganin ko kallon in da suke bai yi bane hankali sa na kan system dake saman chinyar sa, hakan ya sanya ta tako jiki ba kwari ta shiga kusa da shi ta zauna tana jiran taji me zai che rufe motar Abdol yayi ya buɗe gidan gaba ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar da matsanancin gudu suka bar gidan
wani katafaren shopping mall suka shiga bayan sunyi parking Abdol ya fito ya buɗewa Bgs ɓangaren sa sanan ya buɗe wa hiyana,kusan a tare suka fito sai kallon wajen take tana satar kallon sa gaba yayi ta bi bayan sa Abdol ya rufa musu baya tun kafin su shiga chikin wajen ya sanya face mark a face na shi
Suna shiga chikin shopping ɗin Abdol yayi saurin ɗauko masa kujera ya zauna tsayuwa hiyana tayi kusa da shi dan ita gaba ɗaya wajen ma tsoro yake bata da ɗan tsawa Bgs yace "ki wuce kije ki ɗauki abubuwan da kike bukata mana kina ɓatamin lokaci!" Tsuke fuska tayi kafin tace "ni wlh yaya Prince tsoron wajen nake ji ba zan iya zuwa ni kaɗai ba sai dai ka rakani" a sukwane ya ɗago kai yana kallon ta lokacin guda taji numfashi ta ya tsaya dan irin kallon da ya mata tsoro take kar yace an fasa sayan komai su koma gida,kallon ficekar hiyana Abdol yayi kafin ya juyo ya kalli Bgs chikin girmamawa yace "sir let me escort her tun da tana tsoro" wani mugun kallo Bgs ya wurga masa wadda ya sanya shi juyawa ba shiri ya ɗauke kansa daga garesu ya mayar yana kallon kofar shigowa,miƙewa bgs yayi yana faɗin "wuce a mai daki gida tun da ba sayyayyar zaki yi ba" yayi maganar tare da kama hanyar fita chikin sauri ta riko hannun sa tana faɗin "dan Allah yaya Prince kayi hakuri ka rakani karkace mu koma wlh ina bukatar kayan ne" ta karisa maganar kamar zatayi kuka juyowa yayi ya kalleta kafin ya saukar da kallon sa kan hannun sa da ta riƙe ganin hakan ya sanya ta sake masa hannun sa da sauri chigaba yayi da tafiya har ya fice daga wajen,tsayuwa tayi a ranta tana faɗin "yau zan gani rashin imanin ka ya kai ka iya tafiya ka bar ni a nan ne ko kuma akoi sauran imani a zuciyar ka kuma wlh ko kasheni zakayi bazan fita shopping ɗin nan ba har sai mun yi sayayyan nan bare ma ba abun da ka isa kamin yanzu dan Ammi ta sanar dani bazaka kara buguna ba wlh yau sai nayi maganin ka sai ka sauke girman kan nan naka yau" tana tsaye tana kallon su