Showing 309001 words to 312000 words out of 363274 words

Chapter 104 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2567

su sa ran zai ɗaga musu hannu ko makamancin haka dan idan da sabo sun saba da halin sa na ko in kula.
da gudu wani jibgegen soja fari tas daya maye gurbin Abdol ya buɗe masa mota ya shiga da ita a jikin sa da gudu jibga jibgan sojojin suka koma cikin motocin su suka tayar suka figi dankara dankaran motoncin da gudun gaske suka bar Airport ɗin suka nufi gida
wayar sane ta fara kara tana neman agaji yana rungumi da Eshat ɗin sa yana jin wayar na kara har sai da ta kusa tsin kewa sanna ya ɗauka ganin sunan my dad my everything yasa yayi saurin picking call ɗin tare da manna wayar a kunnensa yana faɗin"hello Abba"daga ɗayan ɓangaren Abba yace"Safras ina humair?"kallon kyakkyawar face nata dake kwance saman faffaɗar kirjin sa yayi kafin yace"I'm so sorry my Abba"cikin sauri Abba ya ciro wayar daga kunnen sa dan ya tabbatar da bgs yake magana ba wani ba mamaki ne ya bayyana akan face na shi lokaci da ya tabbatar da bgs yake waya zancen zuci ya fara yi"yau Safras ne da cewa sorry kai ina ban yarda shi bane idan ma shine to gaskiya ina bukatar kallon face nashi dan na tabbatar da ba abun da ya shiga kan shi ni dai tun da na haifi Safras ban taɓa jin yace wa wani ɗan adam yayi hakuri ba Allah mai iko Allah mai canza bawa aduk lokacin da ya ga dama kai Alhadulillah Allah shine abun godiya"jin Abba yayi shiru yasa bgs yace"naso nazo na baka hakuri akan laifin dana maka a baya amma time ya tafi yanzu kuma na kara wani laifi kan laifi na tafi da Eshat I'm sorry ka tayani bawa Ammi hakuri"Abba ya kasa magana"eyee yau Safras ne tun baa ce yayi laifi ba ya ansa laifin sa ya bada hakuri Allah mai iko gaskiya ba zan taɓa manta wanna rana ba"danna recording na wayar sa Abba yayi kafin yace"gaskiya kayi laifi tafiya da ita da kayi kaga bata gama samun lafiya ba gashi kuma kama criminal zaka je yi zata rabama hankali waje biyu kana kokarin kama criminal sanna kana tunanin ta me yasa ma bazaka tura yaran ka su kama mutumin nan ba?ka kafe dole sai da kanka zakaje" "No Abba ina son kama shi da kai na saboda dalilai biyu na farko koma waye ne nasan ina da kusan ci da shi ya san abubuwa sosai akai na na biyu kuma mutun ne mai haddari na kasa da kasa ban son laifi na ya shafi wani soja ba inna tura yara sai in ga ba zasu iya min abun da nake so ba kuma zai iya fin karfin su dan yana da jama'a sosai ban son sanadina akashe soja ko ɗaya batun tafiya da Eshat kuma ina baku hakuri zan san yadda zan yi" "Allah Ubangijin ya kare min ku kuyi aiki lafiya ku dawo lafiya" "Amin ya Allah my Abba amma Abba why kake mamaki haka" "ni nace maka ina mamaki?"kallon face ɗin hiyana dake ɗan motsi yayi kafin yace"Abba ba iya aikin soja kaɗai na iya ba na iya karantar yanayin ɗan adam koda bamu tare innaji muryan sa ban san me ya baka mamaki ba amma acikin voice naka na fahimci kana jin mamakin"murmushi Abba yayi yana faɗin"sai kun dawo Allah ya tsare min ku"yana kai karshen maganar yayi sauri ya katse kiran mai da wayar gefe bgs yayi ya ajiye dai dai lokacin sojan dake tukasu ya danna hancin motar su cikin katafaren gidan su tun da aka wangale katafaren gate ɗin gidan nasu ya ke kallon Aryan dake tsaye a harabar gidan shi da Hisham mamaki ne ya kama shi"yaushe Aryan kuma ya dawo uk?"ya tambayi kansa yana cikin mamaki sai ganin Aryan yayi ya buɗe masa kofar mota cikin zolaya yace"barka da zuwa ango"harara ya watsawa Aryan kafin ya zuro kyawawan kafafun sa dake sanye cikin Booth kalan kayan sa waje yana kokarin fita motar hiyana ta farka tare da waro idon ta a kan kyakkyawar face nashi mikewa tayi daga jikin nasa tana mutsuke ido zuba mata ido yayi yana kallon ta shi kuwa Aryan wayar sa ya ɗauko ya fara yi musu video kasa kasa bgs yace"sannu da tashi sarkin barci"ɗan karkato da kai Aryan yayi yana faɗin"bgs ka rinƙa magana da ɗan karfi dan maganar ta fita a video"wani mugun kallo bgs ya wurga masa wadda yasa shi kawar da wayar ba shiri fitowa daga cikin motar hiyana tayi ta sunkuyar da kai kasa tana faɗin"ina wuni yaya Aryan" "lafiya lou sister ya gajiyar hanya?" "Lafiya lou yaya Aryan ina diyana?""tana cikin gida tare da Ilham matar Hisham"da sauri hiyana ta wuce cikin gidan,fitowa shima bgs yayi da karfi Aryan ya sara masa yana faɗin"sir munyi nasarar isa hotel ɗin a lokacin da ya dace kuma munyi nasarar kama yaran mutumin sai dai shi baya nan tun shekaran jiya sukace ya bar hotel ɗin mun tambaye su in da yake sunce suma basu sani ba baya taɓa faɗa wa kowa in da yake sai dai in shi yake son ganin su sai ya kirasu awaya yace su zo waje kaza zai basu aiki ɗaya daga cikin suma ce mana yayi baya tunanin wanda suke haɗuwa da shi shine asalin mai gidan nasu saboda muryan wanda suke waya da shi daban wanda kuma yake zuwa wajen su shima muryan sa daban hakan yasa suma suke tantama anya shine asalin wadda sukewa aiki kuwa" "yau wace rana Aryan yayi abun arziki"da mamaki bgs ke kallon sa"Aryan yaushe kazo kasar nan har kaje kayi wanna aikin" "lokacin da kaje cin amarcin ka mana sai in tsaya jiranka babban criminal irin wanna ya cubce mana" "yau dai kayi abun arziki"hararar wasa Aryan ya wurga masa kafin yace"sir zan iya tafiya?"wucewa bgs yayi ya nufi cikin gida yana faɗin"aa karka tafi ka kwana awajen"yayi maganar cikin tsokana bayan sa Aryan yabi yana faɗin"na shirya mana fita ni da kai da baby's namu dan mu kai su yawo fatan ba zaka ki zuwa ba"shiru bgs yayi bai tanka ba har suka shige cikin gida
dai dai zai shiga palo ba shiri yaja birki ya tsaya chak a bakin kofar palon ya kasa shiga sakamakon hiran da diyana da hiyana keyi a cikin palon kusa da shi Aryan yazo ya tsaya sukayi shiru suna sauraron diyana na yiwa hiyana lecture. Zaune saman sofa hiyana da diyanar suke suna fuskantar juna diyana ta tsantsara make up sosai a face nata tana sanye cikin wasu shegun riga da wando sun kamata sosai ta zuba lallausan bakin gashin tan nan har gadon baya tana tsotsar sweet mai tsinke wani pitinannen kanshin turare ne ke tashi a jikin ta kamar anyi ɓarin turare ta tasa hiyana a gaba tana bata kalan nata lecture zuba mata ido kawai hiyana tayi tana mamakin diyana ko waye ya koya mata dukka wanna abun oho katse mata tunani diyana tayi da cewa"Aunty hiyana ki dai na mamaki na in dai kika zauna da Aunty farida to fiye da haka zaki koya wlh,yanzu dai duk bama wanna ba dan girman Allah Aunty hiyana ki rinƙa yin make up sosai ki ajiye ustazancin nan ki fara kashe yaya Prince da wanka kananan matsastsun kaya ki rikita masa tunani ya zama komai yake ke yake tunani kingane ai?"kallon Aryan bgs yayi ya masa alama da ido irin wato"kai ma haka take rikita maka tunani kenan?"Aryan na son yin magana amma bai san su diyana suji dan yana son ji har karshen zancen nasu yana son jin amsan hiyana shidai bgs maman kin diyana kawai yake wai yar yarinyar nan hartasan rikitawa namiji tunani ita kuwa diyana cigaba da lecture ta tayi abun ta hankalin ta kwance take tsaro magana ɗaya bayan ɗaya"dan girman Allah Aunty hiyana karki sake sakawa yaya Prince atamfa ko dogon riga ko lace idan dai ba fita zakuyi ba kinji me aunty Farida tace mu zama karuwai a cikin gidan mazajen mu"tushe baki Aryan yayi saboda dariya data cubce masa shi kanshi bgs sai da yayi ɗan murmushi gefen fuska wai karuwai oh wanna yarinya"kin san me Aunty farida ta faɗa min? kowani namiji da kala abun da yafiso a tattare da mace amma mafi yawancin maza sunfi son breast na mace tom ki tsaya ki nitsu ki gane me yaya Prince yafi so a jikin sai kifi gyara masa wajen idan ba haka ba wlh Aunty farida tace Aure zai kara daga yau zan fara koya miki make up kuma wlh yaya Prince yana bala'i son mace mai make up dan akoi ranar da Aunty Zahra ta miki make up ina ganin sa yayi ta kallon ki sosai sanna kuma ko ban faɗa miki ba kin sani yaya Prince yana son kamshin turare ga turaruka mai daɗi da Aunty farida ta sa aka kawo mana daga Maiduguri daga ke har lamrat da Zahra ba wanda ya ɗiba amrat ce kawai ta ɗauka ita lamrat dan iskanci har wani cemin tayi turaren wari yake mata ita turaren jikin yaya Yusuf kawai take so ni zata gwadawa iya soyayya hmmm ta tambayi yaya Aryan ya bata labarin rikitashi da nake"girgiza kai kawai bgs yayi dan diyana ta fara wuce tunanin sa shi kuwa Aryan ya toshe baki saboda dariya diyana na neman kashe sa da dariya"Allah Aunty hiyana kamar yadda ake faɗe gaskiya ne wlh dukkan mu kin fimu kyau nesa ba kusa ba ke da bappa da Ammi da yaya Prince kike kama ni kuma da Ummi nake kama sanna wlh gaskiya ne kin fimu murya mai daɗi baki da yawan magana amma wlh idan kikayi magana ko macece a kusa dake sai taso ki sake magana dan ɗaɗin muryan ki ni kai na ina son sauraron voice naki to inaga namiji nasan kinfimu ilimin addini kin san abun da ya dace kiwa mijin ki to amma meyasa baki amfani da ilimin baki?me yasa baki yiwa yaya Prince abubuwan da Allah yace mace tama mijin ta?wlh da bakin shi ya faɗa min yana son ki tun lokacin da nake faɗa wa su Abba abubuwan da yake miki na mugunta yaya Aryan ya kawo min waya nayi magana da shi naki sai da muka koma ɗaki na ansa wayar nayi magana da shi shi da kan sa alokacin yace mi yana son ki kuma zai kula da ke na daina damuwa to kin gani ya kamata ke ma ki fara bashi kulawa ta musamman"dogon numfashi hiyana taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin tace"nima inason sanya kanana kaya na masa kwalliya amma wlh kunya nake ji sosai ba zan iya ba"mikewa diyana tayi tana taku da kyar saboda ta kalmin da ta sa mai shegen tsinine sosai kusa da ita ta dawo ta zauna tare da tafa kafaɗar ta tana faɗin"Aunty hiyana ki daure ki ajiye kunya nasan kunya abune mai kyau a musulci amma ki daure ki ajiye kunya saboda bata da wata fa ida tsakanin mata da miji kuma wlh maza basu san mace mai kunya a ɗaki kinji na faɗa miki idan kika tsaya kunya nan zakiji yaya Prince ya tafi neman wadda bata jin kunya kinga yanzu yaya Aryan ya shirya mana fita tun ɗazun ya faɗa min karfe 8 na dare zamu fita zan miki kwalliya sosai kuma ni zan baki kayan da zaki sa amma kimin alkawari kowani kaya na baki zaki sa"hiyana na kokarin yin magana bgs ya shigo dan ya lura hiran sun nan ba mai karewa bane ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce ya haura sama Aryan na shigowa diyana ta mike ta tafi da sauri ta faɗa saman faffaɗar kirjin tare da shagwaɓe murya tana faɗin"oyoyo yaya Aryan na"murmushi yayi tare da rungumeta yana faɗin"oyoyo my malama sarkin lecture sannu da kokari"miƙewa hiyana tayi cike da jin kunyan rungumar juna dasu diyana sukayi a gaban ta ta wuce ta haura sama.
tsayuwa tayi a palon su tana ganin yadda aka canza komai na palon kamar ba shiba an zuba sabbin furniture an sauya komai an kawata palon iya kawatuwa tasha mamakin tana tunanin Allah kaɗai yasan dukiyar da aka narkawa palon nan a hankali ta taka ta nufi asalin bedroom nata
chak ta tsaya a bakin kofar tare da sa hannu ta murje idon ta dan ta tabbatar gaskiya idon ta ke gane mata ne ko ko karya an kwashe komai na ɗakin ta an zuba mata sabbi komai na ɗaki fari tas aka zuba mata an sauya mata gado an sanya mata katafare mai girman gaske sabanin na da da bai da girma sosai kallon manya manyan trolley da ke gere gefe guda tayi manya manyan trolley shake da kaya dozin 2 guda 24 kenan manyan ciki ma sun kasa rufuwa gaba ɗaya saboda cika da sukayi da kaya a hankali ta zura kafar ta ta shiga cikin ɗakin bakin katafaren gadon ta dake shin fiɗe da white bed sheet mai mugun laushi ta zauna tana bin ɗakin da kallon kara waro ido tayi lokacin da idon ta ya sauka kan makeken hoton ta dake manne a bango tana kwance saman faffaɗar kirjin bgs tana barci shi kuma yana kallon kyakkyawar face nata mikewa tayi cikin sauri ta karisa wajen tasa hannu ta shafa hoton dan ta tabbatar ba mafarki take ba tunani ta farayi"ko yaushe yaya Prince ya ɗauki hoton nan har ya kai aka wanke masa oho",juyawa tayi ta nufi dressing room nata tun a bakin kofa tayi mutuwar tsaye tana kallon yadda aka shirya dressing room ɗin shake da kaya da jakunkuna takalma agogo sarkan gold masu kyau da tsada sai ɗaukan ido suke ga manya manyan perfume masu kyau da tsada komai an shirya shi a gidan sa daban karisawa tayi ciki a hankali take taku kamar ɓarauniya kallon wajen jera kaya tayi mamaki ne ya kara kamata a ranta tace"kenan gaskiyan diyana yaya prince yana son kananan kaya sosai gashi su kaɗai ya sanya aka jera min anan gaskiya ya zama dole na rinƙa sa masa dan yayi farincikin kamar yadda nima yasani farinciki"tana cikin tunani idon ta ya sauka kan dangareriyar waya kirar I phone 14 pro tare da key motar Mercedes-Benz a kusa da wayar a saman drawer dake wajen hannun ta har rawa yake wajen ɗaukan wayar ta kunna harken screen ɗin a cike take da charji anyi setting na komai harda sim card a cikin ta shagala da kallon wayar kira ta shigo cikin wayar yar tsorata tayi dan batayi tunanin za'a kiraba kyakkyawar fiskar bgs ne ya bayya akan screen ɗin cool murmushi ta saki kafin ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunnen ta cikin nitsuwa tace"Assalamu alaikum" "idan kin yi sallar issha ki shirya Aryan ya shirya mana fita" "yaya Prince"sai kuma tayi shiru ta kasa magana"lafiya Eshat menene?" "dama am daman"kasa magana tayi sai in da in da take masa"ok i think maganar zatafi fito idan gani gaki kiyi sallar mangariba ki kawo min hot milk idan kin zo sai ki faɗa min maganar ko?"cool murmushi ta saki kafin tace"ina son ka sosai my Habibi" "my Eshat murmushi na miki kyau sosai idan ina ganin murmushi ki bana sanin lokacin da nima nake murmushi" "yanzu yaya Prince a ɗaki na ɗin ma sai da kasa camera?" "Ai ya zama dole na sa miki camera dan na rinƙa ganin duk abun da baby na ke yi"hannu ɗaya tasa ta rufe fuskar ta ta fito daga dressing room ɗin tana murmushi ta faɗa saman katafaren gadon ta cikin shagwaɓa tace"amma yaya Prince ai kai baka son yimin murmushin kuma murmushi kafa yafi na kowa kyau a duniyar nan" "lokacin sallah yayi idan kinzo zan miki murmushi sai kimin video ki ajiye kiyi ta kallo dan a shekara sau ɗaya nake murmushi"dariya tayi mai ɗan sauti kafin tace"nikam zaka rinƙa yimin sau goma a rana ai ko?" "Tashi kiyi sallah dan mangariba shot time yake da shi in kin kawomin hot milk ma karasa magana"yana kai karshen maganar ya katse kiran tare da ajiye wayar ya fito suka wuce masallacin su shida Aryan mikewa ita tayi ta nufi toilet kallo sosai ta tsaya tayiwa toilet ɗin dan shima an canza komai an sanya mata katon show glass an shake mata shi tab da shampoos da mayukan gyaran gashi masu matukar kyau da tsada ta shagala da kalle kalle da taɓe taɓe a toilet ɗin har su bgs suka dawo masallaci jin diran motocin su yasa tayi saurin cire kayata ta fara wanka sauri sauri ta ɗauro alwala ta fito ɗaure da kyakkyawar farin towel mai taushi a kirjin ta shiru ta tsaya a tsakiyar ɗakin tana tunanin inda zata samu hijabi da manyan kaya tasa tayi sallah gaba ɗaya kayan da bgs ya sa aka sanya mata a dressing room nata kananan kaya ne kuma ba hijabi aciki.
Juyawa tayi ta nufi wajen trolley da ke jere gefe guda dan ta duba ko zata dace ta samu manyan kaya
da kyar ta iya jawo trolley ɗaya babba na kasa ta kwantar ta buɗe ta tafara dubawa tayi saa domin gaba ɗaya akwatin cike yake da jallabiyoyi da hijabai dariya ne ya kubce mata lokacin dataga abun da aka rubuta a jikin akwatin"only for prayer""wato dai da gaske yaya Prince bai san manya kaya har da sawa arubuta min only for prayer to In Sha Allah saboda sallah kawai zan rinƙa sawa"ta kai karshen maganar tare da zaro leda ɗaya na jallabiya da hijabi ta maida sauran tayi tayi ta rufe akwatin ta kasa dan kayan sun cika sosai daman da kyar aka iya rufewa bai ma gama rufuwa gaba ɗaya ba ganin bazata iya rufewa bane yasa ta mike ta barsu awajen ta shin fuɗa dadduma ta sanya jallabiyar da hijabin ta tada sallah a nitse.
duk abun da take bgs yana kwance saman katafaren gadon sa yana kallon ta ta cikin system nashi daga shi sai shot da singlet asalin kyakkyawar surar jikin sa a bayyane.

Bayan ta idar da Sallah ta wuce dressing


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login