Showing 147001 words to 150000 words out of 363274 words
kansa kasa yayi chikin raha yace "to Aunty babba gashi nan naji kunyar taki" tsaki Aunty salma taja chikin wasa tare da nufar kofar fita tana faɗin "ai, Ni ban soma Abba ya baku matan naku yanzu ba so nai ya bari sai nan da wata 2 masu zuwa" tana kai karshen maganar ta fice daga ɗakin
Dawo da kallon sa Khalid yayi kan Zahra dake ta faman sharɓan kuka, hannu yasa ya goge mata hawaye chike da so da kauna yace "my wife kukan me kuma ki keyi ne? Shiru Zahra tayi bata tan ka shi ba kuma bata dai na kukan ba, murmushi Khalid yayi tare da miƙewa ya naɗe hannun rigan sa ya duƙa ya ɗauke ta chak kamar yar baby ya nufi betroom nashi da ita
A tsakiyar katafaren gadon sa ya zaunar da ita tare da zama daga ɗan gefen ta ya kwan to da kan sa kan chinyar ta kasa kasa ya fara magana
"My wife wai kukan menen hakan? Baki san zama da nine? Sunkuyar da kai kasa Zahra tayi ta chigaba da kukan ta, "oh my god Khalid ya furta tare da miƙewa zaune yasa hannu ya ɗago haɓarta, chike da so da kauna yasa harche ya lashe hawayen nata tas tare da haɗe fuskokin su yana kallon chikin idon ta "now zaki yimin magana ne ko kuma dai sai na chiji ɗan bakin nan naki? Chike da shogoɓa tace "Ni Allah yaya Khalid bana so ka mai dani part ɗin Ammi na" murmushi yayi kafin yace "au shine dalilin kukan naki? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh "ok to bari zuwa gobe zan mai dake kinji amma yanzu tashi muje na miki wanka na shiryaki muje na baki abinchi a baki" turo ɗan bakin nan nata tayi chike da shagoɓa tace "ni na iya wanka da kai na ai"
"Aa ni gaskiya ban yarda ba kizo kawai muje na miki idan ke kikayi bazaki fita sosai ba, bata san lokachin da dariya ya kubche mata ba zuba mata ido yayi yana kallon yadda take dariya sai da tayi mai isar ta san nan ta raba fuskantar da nashi tana faɗin "to ai ni nake wankana tun dama chan kuma ina fita sosai ai a haka ma ka ganni kache kana so" ta karisa maganar tare da rufe fuskar ta da hannun biyu "eyeee a lallai my wife ta girma babu zan chen ɗaga kafa kenan" "ɗaga kafan me kuma dama ai ni ban che kaɗaga kafaba" "au haka kika che? "Eh mana yaya Khalid ni ban che ka ɗaga kafa ba to ma idan ka ɗaga kafar ka kai ta ina
Fisgota yayi da karfi ta faɗa kan kirjin sa, rungumeta yayi sosai yana faɗin "ai ko ba zan ɗaga kafar ba" ɗago da fuskan ta tayi daga kan kirjin nasa chike da shogoɓa tace "yaya Khalid ka kusa karyamin hannu fa Allah" "sorry my wife to muje na kai ki toilet kiyi wanka ko?tun da bakya so na miki, Ba tare da ya jira Amsar taba ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi toilet da ita.
A ɓangaren Yusuf kuwa Aunty Mardiya na fita ya matso kusa da Amaryan sa kasa kasa yace "my baby ya jiki? Kan ta a sunkuye tace "da sauki amma har yanzu kai na na min chiwo sosai" eyya sorry kinji In Sha Allah zai dai na yimiki chiwo yanzu dai ki kwanta ki huta bari naje wajen Abba a fada ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje ita kuma lamrat karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita
A ɓangaren Fahad kuwa
Koda Aunty mardiya ta shigo tare da Amrat shiru palon babu kowa kai tsaye betroom nashi suka shiga tare da sallama babu kowa a ɗakin sai dai karan ruwan dake tashi daga toilet da alama wanka yake
Karisawa su kayi chikin ɗakin a bakin gado Aunty mardiya ta zaunar da Amrat tace " amrat ki zauna kijira mijin ki yana wanka ne zan koma ɗakin Ummi kinji? Batare da tajira amsar amrat ba ta juya ta fice daga ɗakin.
Almost 20mnt Amrat na zaune shiru tana sunkuye da kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta, jin An buɗe kofar Toilet ɗin ne yasa ta ɗago kai tana kallon kofar tana jiran taga mai fitowa dan ita kwata kwata batama san wanene mijin nata ba
Ɗaure da farin towel mai laushi da kyau a kugun'sa ya fito bai ma lura da mutun a ɗakin ba kai tsaye gaban mirrow ya nufa, ganin sa haka yasa Amrat fasa ihu dan ba karamin tsorata da ganin halittar jikin sa tayi ba, A'sukwane ya juyo yana bin in da akayi ihu da kallo, da mamaki yake kallon razanan ne fuskar ta a nitse yace "ke wacece ke? Sai lokachin Amrat ta dawo chikin hayyachin ta da sauri ta miƙe tsaye ta kwasa da gudu ta nufi hanyar fita daga ɗakin taku biyu Fahad yayi ta damko kugunta ta baya tare da ɗaga ta sama ya dawo da ita chikin ɗakin wurgi yayi da ita a saman gadon chikin tsawa yace " wacece ke!? Me ya kawo ki ɗakin nan!?
Amrat ta gama tsorata murya ta har rawa yake ta fara magana "Aunty mardiya che ta kawo ni" " wacece ke!? "Sunana Amrat" shiru yayi yana tunanin chikin ran shi yana mai mai ta sunan Amrat tabbas na taɓajin sunan Amma na manta ko ai nane "to naji sunan ki Amrat me kika zo yi a ɗakin nan!? "Aunty Mardiya che ta kawo ni kuma tace na zauna na jira miji na ya fito sai yanzu Fahad ya tuno in da ya taɓa jin sunan lokachin da limamin babban masallacin juma'a yake faɗin an ɗaura Auren Fahad Abubakar Saraki da Amrat Ahmad guntun tsaki yaja tare da juyawa ya nufi gaban mirrow ya fara shafa mayu kan sa masu kamshi da tsada, Amrat kuwa shiru ta kwanta a saman gadon nasa ta runtse idon ta tana jiran taji me zai sake che mata
"Ke tashi ki shiga dressing room na ki ɗauko min kayan da zan sa dan ni yar Aiki aka kawomin da sauri Amrat ta miƙe chikin sanyin murya tace "yaya ina ne wajen kayan naka kuma yaya sunan ka, da mamaki ya ɗago yana kallon ta ta cikin mirrow wai yarinyar nan ko sunana ma bata sani ba amma Abba ya san yadda ya shiga ya fita ya haɗa mu Aure nan take kuma yaji wani irin tausayin yarinyar ya kama shi chikin sanyin murya yace "sunana Fahad ki buɗe wan chan kofar ki shiga zakiga kayan na awajen ki kawomin set ɗaya, chikin sauri Amrat ta nufi dressing room ɗin
Jim kaɗan ta fito hannun ta ɗauke da kayan nashi gaban sa ta dawo ta sungunna chikin nitsuwa tace "yaya Fahad ga kayan nan shiru yayi kamar bai jita ba, shiru ita matayi ta sunkuyar da kanta kasa tana jiran ya amsa kayan, sai da ya gama gyara gashin kansa san nan ya goma gefen gado ya zauna tare da miƙa mata hannu alamar ta kawo masa kayan, miƙewa tayi tana tafiya a hankali kamar bata son taka kasa, sugunnawa tayi a gaban sa tare da miƙa masa kayan, bin kayan yayi da kallo ba tare da ya ansa ba
"Waye ya koya miki zaɓen abu mai kyau? "Babu kowa ni da kai na na iya, shiru yayi bai sake magana ba yasa hannu ya Ansa kayan, shiru tayi ba tare da ta miƙe ba tana ɗan satar kallon sa "tashi ki zauna a saman gadon mana, ya faɗi hakan tare da miƙewa ya shiga dressing room ɗin bin bayan sa da kallo Amrat tayi har ya shige room ɗin san nan ta miƙe ta koma gefen gadon ta zauna.
Maiduguri
"Ahzan ai na ka buge wan nan kyakkyawar yarinya haka? Kuma ina iyayenta da yan uwan ta suke? "dady wan nan yarinyar fa mahauniya che bata da hankali" " aa Ahzan wan nan yarinyar ba mahaukachiya bace ka dubi jikin ta mana ka kalleta da kyau zaka gane hakan" "to dady Ni dai a yadda na ganta sai naga kamar mahaukachiya che "To mu bari ta farfaɗo tukun nan sai muji daga bakin ta ko? Yanzu dai bari naje na sanar da mom ɗin ka sai mu dawo gaba ɗaya dan ta chigaba da kula da yarinyar" to kawai Ahzan yace miƙewa dady yayi ya fice daga ɗakin, dawo da kallon sa Ahzan yayi kan yarinyar dake kwanche bata ko motsi sosai ya zuba mata ido chikin ran shi yana yaba irin kyawun yarin yar.....
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan Allah ya kaimu
NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*💫STAR LADY💫*4
💖The Talent Troupe Writer's 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
Book 2
*Episode 4*
KANO
washe gari tun karfe 7 Aunty farida Aunty salma Aunty mardiya suka shiryawa su hiyana ɗakin su da duk wani abun da mace zata buƙata an shirya musu, super market Aunty farida taje tayiwa hiyana sayayyan kanana kaya masu kyau da tsada Akwati 3 chike da kananan kayan ta kawo mata da kanta ta shirya mata a sip sosai tasake saka Hiyana a gaba tana bata shawara da kuma yadda zasuyi dan su samu su shawo kan Bgs, ba musu hiyana ta bawa Aunty farida goyan baya tare da mata alkawarin zata yi yadda tache ba karamin daɗi Aunty farida ta ji ba sosai ta sake karfafawa Hiyana guiwa tare da mata alkawarin zasu rinƙa waya kuma zata rinƙa taya ta yaki daga nata ɓangaren, Sallama sukayi dan yau zata koma Maiduguri, kuka Hiyana ta farayi dan tana ganin kamar idan Aunty farida ta tafi shike nan Yaya Prince zai kasheta, rarrshin ta Aunty farida ta shiga yi har ta hakura tayi shiru san nan Aunty farida ta tafi
Yau ta kama Monday Hiyana na zaune a ɗakin ta dan tun da aka kawota ko palo bata lekaba saboda tsoron kar ta haɗu da yaya prince, tayi light make up sanye take chikin doguwar rigar abaya baki ta yafa gyalen rigar a kanta, tayi tagumi ta zauna shiru tana tunanin ina diyana ta shiga awani hali take yanzu shin ta chi abinchi kuwa? Tayi nisa chikin tunanin da take sai taji an buga kofar ɗakin nata, wani miguwar faɗuwa gaba taji chikin sauri ta miƙe ta nufi kofar, batare da ta tambayi wanene bane ta murza key ta buɗe kofar wani dum dum taji gaban ta ya faɗi ganin Bgs a tsaye ya juyawa kofar baya ya zura hannu a aljihun kallon sa ta baya ta farayi from head to toe sanye yake chikin wando sojoji 3cuter da farin t-shirt mara nauyi zubawa gashin kan sa ido tayi ya tara ya ɗaure a baya sai sheki gashin yake sauko da blue eyes nata tayi kan wuyar sa, wani bakin lallausan gashi ne kwanche awaje har kusa da farkon bayan sa sai wani fitinannen kamshin yake zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikin sa dawo da kallon ta tayi kan ɗamtsen hannun sa dake chike kamar zasu fasa hannun rigar aranta tana faɗin idan yaya prince ya daki mutun da hannun nan tofa wlh ba zai tashi ba chikin sauri ta tsugunna kasa murya na rawa tace
"Yaya prince ina kwana shiru bai amsa ba kuma bai yi wani motsin da zai tabbatar maka da yaji gai suwar ba, tunani ta shigayi na mai mai ta gaisuwar ne ko kuma nayi shiru to idan nayi shiru kuma bai ji gaisuwar da nayi da farko bafa? Idan kuma na mai mai ta zai iya hukun tani kai bari dai nayi shiru ai ya ji fitowa ta bari naga me zai che shiru shiru Almost 5mins tana tsugunne, shi kuma yana tsaye ya bata baya yana kallon palon kasa, shiru shiru Hiyana har ta fara gajiya da tsuguno kafarta ta fara yimata zafi sai wani ash take faɗi, shi ko yana tsaye ko motsi bai yi ba
Juyawa yayi ya fara tafiya batare da ya kalli in da take ba sai da ya ɗan yi tafiya mai nisa ba tare da ya juyo ba yace "Abba na kiran ki a palon sa yanzu, yana kai karshen maganar ya sauka kasa ya nufi hanyar fita palon kasa cikin sauri Hiyana ta miƙe tana kallon sa sosai ta zuba masa blue eyes nata tana kallon yadda yake tafiya, sai da ya fice daga Palon san nan ta sauke ajiyar zuchiya a file ta fara magana "kai gaskiya yaya prince yana da kyau sosai Ni wlh ma gashin kan sa na burgeni ga hannun nan na sa shima burgeni yake sosai, ɗakin ta ta koma ta ɗauki hijabi babba har kasa ta sanya san nan ta fito ta sauko kasa ta fice daga palon ta nufi palon Abba
A bakin kofar shiga part ɗin Abba ta samu Bgs tsaye yana latsa waya, tunani ta shigayi to me ya tsayar da shi kuma a nan? Karisowa tayi wajen da yake ta sake sugunnawa tace "yaya prince ina kwana, ba tare da ya ɗago da fuskar sa daga kan wayar tasa ba ya daka mata wani mugun tsawa chike da izza yace "ke Ni zaki tsayar ina jiran ki!!? Chike da tsoro da karyewar zuchiya murya sai kerma yake tace "kayi hakuri yaya prince ban san Ni ka ke jira bane, dogon tsaki yaja tare da shigewa chikin part na Abba chikin sauri ta miƙe tabi bayan sa
Gaba ɗaya family sun haɗu a table ɗin chin abinchi
Abba na ganin Bgs da Hiyana sun shigo a tare ya fara murmushi yana faɗin "haka nake son ganin ku kowa ya shigomin shi da matar sa a tare shi yasa nache kuzo a tare, wani kululun ɓakin chiki Bgs yaji tazo masa har wuya jiyake kamar ya shake yarinyar nan ta mutu kowa ya huta wai ma ni ban ga abu da ya sanya Abba yake son dan gan tani da yarinyar nan ba
karisa wa wajen Table ɗin su kayi kujerar kusa da Aryan Bgs yaje ya zauna tsayuwa Hiyana tayi tama kasa zama dan tsoro, sai kallon su Zahra take ɗaya bayan ɗaya kowache tana zaune kusa da mijin ta ba karamin kyau hakan ya mata ba ji tayi itama tana bukatar zama kusa da mijin ta
hannu Abba yasa ya mata nuni da kujerar dake gefen Bgs ɗin yana faɗin "zo ki zauna kusa da mijin ki, jiki ta har rawa yake saboda tsoro gaba ɗaya palon sunyi shiru suna kallon ta ita kuwa zulaihat kallon Bgs kawai take tana yaba kyan sa chike da ɓachin rai Bgs ya miƙe yana faɗin "Abba ka dai na min hakan bana so! No need ma na ji dalilin da ya sanya ka kiramu na fasa yin 3 month ɗin yau jirgina zai ɗaga zuwa London" tun da ya fara magana gaba ɗaya family suka nitsu suna kallon sa yana kai karshen maganar ya juya zai fita chikin sanyin murya Ammi tace "Prince dawo ka zauna a sukwane Bgs ya juyo dan Ammi bata taɓa yi masa magana da sanyin murya haka ba kuma bata taɓa kiran sunan saba sai dai tace masa kai, lallai yau dole nayi abun da kike so my Ammi nan take yaji zuchiyar sa tayi sanyi juyawa yayi ya koma kujerar da ya tashi ya zauna, shi dai Aryan duk wan nan abun da ake bai ma san ana yi ba dan kwata kwata hankali sa baya tare dasu ya sunguyar da kansa kasa da alama tunani yake
"Hiyana zo ki zauna kusa da mijin ki chewar Ammi chikin rawar murya hiyana tace "Ammi ni bana jin yinwa zan iya komawa ɗaki? Gaba ɗaya su Abba sai da suka tausaya mata ban da zulaihat da Aunty amarya dake ta jin daɗi nuni da hannu Abba yayi mata akan tazo, ba musu ta karisa kusa da shi zata tsugunna yayi saurin dakatar da ita tare da kamo hannun ta ya zaunar da ita a saman kujerar dake kusa dashi "Abba wai me yasa ka kiramu ne chewar Yusuf dake zaune kusa da Baby Lamrat nashi, gyaran murya Abba yayi san nan ya fara magana
"Daga yau idan ba nawa matan ba karwan da ya sake zuwamin palo chin abinchin kowa matar sa ta rinƙa kai masa ɗakin sa, da sauri Yaya Ahmad yace "Abba ni da Umar da Haidar fa "eh ku ma ai na kusa yin naku bikin amma kafin nan kurinka zama a ɗakin ku mai Aiki tana kawo muku" Umar yayi sauri chewa "Abba dan girman Allah karka yimana irin Auren da kayiwa su yaya prince kabari mu samo matan m.. bai karisa maganar ba yayi shiru sakama kon wani mugun kallo da Bgs ya wurga masa dariya ne yaso kub chewa Zahra Amma sai tayi saurin damme wa hakan ya haifar mata da tari, tari take sosai chikin sauri Khalid ya ɗauko ruwan dake gaban Abba ya fara bata abaki yana faɗin "sorry my wife yana ɗan bubbuga mata baya
Wani kunya Ammi taji ya lullɓeta ji take kamar ta make Khalid, shi ko Abba sai murnushi yake ba karamin daɗi yaji ba ganin yadda Khalid ke kula masa da autar sa
wani dogon numfashi yaya Aryan yaja tare da miƙewa yace "Abba zan koma Maiduguri an jima amma a yau zan dawo, bai jira amsar Abba ba ya fice