Showing 33001 words to 36000 words out of 363274 words

Chapter 12 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2536

nan abubuwa yazanyi dasu " tona rami zakiyi ki binnesu da hannunki chewar hajj sadiya " to shike nan gobe zanje ta bayan gidan nan na binnesu,sai maganar Safras da zulaihat chewar aunty amarya " eh shima sai bayan sallah dan yache aikin nada matukar wahala kuma gashi sallah yakawo kai jamaa sunmasa yawa sosai kowache tana kawo kukanta asa mijinta tafito da ita sallan nan ta haɗu sosai, " mikewa Aunty amarya tayi tana faɗin bari nakawomiki kuɗin motakoh tanufi wajen Waldrop din kayan'sawarta

Misalin karfe 8 na dare gaba ɗaya family sun haɗu a palo suna chin abinchi kamar yadda suka saba " shiru kakeji bakajin karar komai sai karar spoon, bayan sungama chin abinchin ne " mai martaba yayi gyaran murya yasoma magana yau azumi saura kwana 33 yakamata kufara fitto da kayan abinchi kuna rabawa al umma san nan kuma gaba ɗayan mu zamuje umrah, saiku shirya, akoi mai magana " shiru palan yayi " diyana che tache Abba inasan da'sallah inje kauye ingano yaya bello " wani kallan banza yusuf ya wurga mata akule yafara magana au yanzu duk azabar dakukasha sake tunanin kauyenma kuke ke nan " mai martaba yayi murmushi yana faɗin to kai ina ruwanka kasan tsakaninsu da bello'ne to barikaji zasuje kuma kuzaku kaisu kukulamin dasu har sudawo " afusache don yamike zaibar palan " sai ina chewar Ammi " shiru yayi baiyi maganaba kuma bai dawo ya zaunaba " mai martaba yayi murmushi yache to ki kyalesamana jeka abinka ammafa kashirya dan dakai zaku kaisu diyana kauye " batare dayache koh uppan ba yayi waje " kallan Ammi mai martaba yayi chikin harchen fillanchi yake faɗin ki kyalesu inamusu hakane ko zansamu zuchiyar nan tasu taragu inba hakaba akoi matsala " jinjina kai Ammi tayi tana faɗin eh hakanma yana da kyau ai gara murinka koyamusu sanyi kobayawane " mikewa Aryan yayi yanufi waje har yakai bakin kofa saikuma yajuyo yana kallan diyana a nitse da sexy voice nashi nan yafara magana kisameni a ɗaki inzakizo kikawomin coffee yana kaiwa nan yawuche " gaba ɗaya palan mamakine yakamasu baranma yusuf suda sukasan hali, "nan take zahra jikinta yafara rawa ta kalli diyana tafara magana kasa kasa chikin harchen fillanchi wayache kiche zakije kauye to wlh yau babu ruwana dan zaki karɓi hukunchi " murguɗa baki diyana tai tamike tayi waje " baki sake zahra ke kallanta azuchiyarta take tunanin lallai diyana inaga darabon zakisha bugu kilama harda karaya,"
Da ɗai ɗai suka bar palan gaba ɗayansu kowa yanufi bangarensa


Zaune take a gaban murhun wuta tana kokarin hurawa innar buba tashigo gidan da sallama inna ta amsa mata sallamar,tamata iso zama innar buba tazo tayi kusa da inna suka gaisa " innar buba tafara tambayat inna wai har yanzu habiba baki samu kuɗin bane nifa wlh nafara karaya " aa karkikaraya dan kuwa nasamu natara dubu 5 yanzu kuma anjima zansake zuwa tallah kinga da kuɗin sun kai dubu 10 sai muje koh kiɗan kara hakuri kinji chewar inna " to badamuwa allah yakaimu nibari nazo nakoma gida dan mai dubawa buba kafarsa zaizo anjima chewar innan buba " inna habiba tache yajikin nashi " innar buba ta amsa da sauki sosai wlh dankuwa kafar tafara komawa dai dai " mashaa allah chewar inna " to habiba sai kinshigo tafaɗi hakan tana kokarin mikewa, har kofar gida inna habiba ta rakata san nan ta dawo


*💫STAR LADY💫*



*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai




*Episode7*



Zaune suke a palan Ammi suna hira nan fa zahra take fada musu komai na gidan
Zahra tache karku yarda kuyi wani laifi yanzu dankuwa shekaran jiya su yaya prince suka dawo baruwanku da kowa a gidan nan dan wlh duk yan gidan nan mugaye ne yaya Khalid ne kawai mutumin kirki dan haka karku kula kowa duk abunda kukeso ku tambayeni yauwa kuma inkun gaishesuma basu amsaba karkudamu kuma karkuyi wata maganar dan basa amsa gaisuwar kowa sukam haka suke
Diyana tache to tunda basa amsa kaisu basai mu kyalesuba dole sai mun gaishe sune
Zahra tache keeee. lallai da zafinki kikazo tab ai wlh idan sukazo suka wuche baki gaishesuba nan ma hukunchi zaki karɓa inkuma kingaishesu bazasu amsaba to zamanki lafi shine ki gaidasu koda basu amsaba karkidamu " yauwa kunga wandayake zaune a kujeran gefen Ammin ɗazun din nan koh wan nan mai kama da Hiyana
Da sauri Hiyana tache daman akoi mai kama dani a gidan nan ne " Zahra tache eh mana ai shine ya zauna kusa da Ammi sunansa yaya prince to dashi da yaya Aryan da yaya yusuf da yaya Fahad wlh karku yarda hanya ta hadaku inba hakaba zaku jijiki basu da kirki Zahra zata sake magana taji takun tafiya a tari ta mike tawatsa dakinsu da gudu dankuwa tasan irin wan nan takun mutun ukune kawai a gidan nan keyinsa " Don, Aryan , Yusuf shiyasa ta gudu dan batasan haduwa dasu
Suna ganin Zahra ta gudu suma suka mike da gudu sukabi bayanta
Yana shigowa ya tsaya shiru yana tunanin tabbas yaga wulkawar abu kuma kamar inuwar mutun wuchewa chikin palan yayi yasamu waje kan kujera mai zaman mutun daya ya zauna
Yachiro wayarsa yafara daddan nawa kana yasa akunne jimkadan sai yache gani nanfa a palo banji me akacheba a dayan bangaren ba kawai naga ya katse kiran
Fitowa Ammi tayi daga chikin betroom tazo ta zauna a kujera mai zaman mutun ɗaya a nitse Safra yache inawuni Ammi ta amsa masa da lfy yache yamukaji da hakuri tache hakuri yazama dole yache allah yajikansa da rahma amin Ammi amsa kana tache daman kuɗi nakeso kabani su farida zasuje suyiwa kannenka sayayya " shiru yayi bai chekomaiba kusan 10 mnt tukun nan yache
Ammi dan allah wai meyasa bazaki sabaki a magaAnar nanba nifa bazan iya mulkiba kinsanfa shugaba da adalchi da tausayi
akasan shi to nikuma sojanefa
Ammi baki sake take kallansa tache au kai bakada tausayi ke nan shiru yayi bai tankaba saima mikewa dayayi yanufi hanyar fita yana fadin Fahad zai kawo miki kuɗin
Ammi dai ido tazuba masa har yafita tukun nan ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuchiya afaili tache nida kaina nasan ba iya mulkar mutane zakayiba saboda wan nan irin hali naka bakayi kala da shugabanniba kadaifi dachewa da rike bindigar amma ni babu ruwa kaine zabin mahaifinka bazan chanza masa zabinsaba sai dai inshiyaga dama ya chanzaka da kansa amma zantayaka da adduar Allah yasa kar abaka mulkin nan dan in akabaka mutane zasusha wahala, zata sake magana sai taji alamar tafiya shiru tayi tana sauraran mai shigowa
Aunty farida che tashigo bakinta dauke da sallama da fara'a Ammi ta Amsa mata sallamar
Shigowa tayi ta zauna a gujerar da Prince yatashi kana tache Ammi barka da hutawa anche kina nemana gani
Ammi tache yauwa sayayya nakesan kuje kiyiwa su Diyana dan kinsan basuda kaya to kisaya musu duk abun daya dache
Aunty farida tache to inasuke suzo muje tare koh dan muzabi size dinsu dakuma colours din dasuke bukata
Ammi tache aa kuɗan jira kadan kanin naki yache zaibawa Fahad kuɗin yakawomin
Aunty farida tache aa basai ankarbi kudi wajen prince ba suzo mutafi kawai ni zan dauki nauyi sayayyar
Ammi tache aa farida kada na daura miki nauyi da kinbari shidai yakawo kuɗin nafisan yamusu da kansane dan kuwa duk wani responsibility su yadawo kansa shi zai dauki komai shiyasama banbiya kuɗinba nache yabiya
Aunty farida tache Ammi dani da prince duk ɗayane idan nabiya kamar shine yabiya kuma kamar yadda nakewa Zahra sayayya da kuɗina suma haka zanmusu saboda yanzu dasu da Zahra duk dayane awaje na
Ammi tache to shike nan badamuwa kuje din
Aunty farida tache Ammi dan allah inaneman alfarman kisa baki mai martaba yabani Diyana wlh tashiga raina ina kaunar yarinyar san nan kuma dan allah kutaimaka kubawa mardiya lamrat takuma da ita Abuja tunda kunga ita Allah bai bata aihuwaba
Ammi tache kwarai ina matukar tausayin mardiya musanman idan kuka haɗu yadda take matikar son junior batasan yayi nisa da ita wani lokachin har kwalla nakemata amma bayadda zanyi inraba marayun allah nan Feeda tare suka taso komai tare suke dukda shekarunsu ba ɗayaba amma dai zan gwada kinji
Aunty farida tache eh Ammi akoi chiwokam murabasu amma dan allah taimaka mana zakuyi muda bamuda yaya Ammi tache to zanyi magana da mai martaba da daddare
Dukyadda mukayi zakiji
Aunty farida tache to saikuma maganan prince Shima dan... Bata kai karsheba Ammi tache kingane tashi kutafi adawo lfy tana kaiwa nan tamike tanufi dakin su Zahra dan takirasu
Girgiza kai Aunty farida tayi tache Ammi " Ammi kinasan samana chiwon kai amma a hankali zanshawo kankine
Fitowa Ammi tayi rike da hannun Amrat su Diyana na biye dasu abaya diyana da hiyana hijabai sukasa zahra kuma abaya tasa da gyalensa sunyi kyau sosai amrat da lamrat kuwa blaus ne ajikinsu mai kyau sai dan karamin gyale dasuka yafa akamsu
Mikewa Aunty farida tayi san nan tache muje koh tayi maganar tana kokarin riko hannun Diyana
Suna fita kai tsaye parking space suka nufa da sauri driver yazo ya bude musu motar hiyana da diyana da zahra suka shiga mota ɗaya
Aunty farida kuma takama hannun amrat da lamrat suka nufi wata motar suka shiga
suna shiga wayar aunty farida yafara kara da sauri ta dauki call din tache hello daga ɗayan bangaren yache inakikene insan muyi maganane
Aunty farida tache gani nan yanzu nafito zamutafi shopping kazo karakamu mana sai muyi maganar a hanya " yache aa bazanjeba amma barinasa sojoji surakaminke saboda tsaro" dariya Aunty farida tayi tache kai dai prince allah bansan irinkaba mutunne bayasan shiga jamaa to shike nan tunda bazakajeba saina dawo saimuyi maganar koh zata sake magana ke nan taga waso sojoji guda 4 a gabanta chiki har da abdol
Tache laaaa yanzu muna waya yaushe kayiwa sojojin nan magana
Prince yache lokachin danache bari na hadaki dasu mana alokachin na dannamusu kararrawa dasu nanki
Dariya Aunty farida tayi tache to shike nan ngd saimun dawo
Yache kikula mana da kanki tache to tunkafin takarasama ya katse kiran
Juyowa tayi tabawa driver umarnin sutafi
Abdol chikin harchen turanchi yache madan inbadamuwa barini naja motar dan oga yache nabaki kulawa sosai
Aunty farida tache to badamuwa " fita driver yayi yabawa Abdol wajen yashiga sauran sojoji ukun kuma suka shiga wata motar natake suka kunna motar suka miki hanya sai gate " sojojin dake wajen suka bude musu pakekiyar gate din suna fita suka miki hanya
Aunty farida tachewa Abdol to aibaka tambayi ina zamujeba
Abdol yache oga yariga yashigarmin inda zan kaiku a chikin wayata
Shiru Aunty farida tayi tana kallan ikon allah tana jiran taga inda za'a kaisu
Kai tsaye wajen wani katafaren shopping Abdol yashiga yayi parking a parking space nawajen yafito yabudewa Aunty farida tafito kana takama hannu amrat ta tsaya saida su zahrama suka fito sukazo inda take san nan suka nufi chiki Abdol yabi bayansu sauran sojojin suka rufa musu baya Abdol yache su koma wajen mota sujirasu

Kaya dayawa Aunty farida tafara ludan musu kuma tache suma suzaba duk abun dasuka ga yamusu su dauka " Zahra kam duk abun datagani mai dan kyalkyali sai tache wan nan zayyiwa Hiyana kyau ta dauka mata sunyi sayayyar kayan sawa dayawa san nan sukaje wajen takalma da jaka suma dayawa suka dauka suka koma wajen kana nan kaya Hiyana naganin breziya tafa boye fuska Zahra nata mata dariya
Aunty farida kuwa chewa take My Diyana kemafa kin kai sa bra ba Hiyana kawaiba dan kema naga ba bayaba wajen chikar halitta rufe fuska Diyana tayi da hannunta tana murmushi
Amrat ne tayi magana da fullanchi tache zata sha ruwa Aunty farida tache ku fassaramin metache " dariya Zahra tayi tache kai Aunty farida yakamata kema kikoyi fillanchi ruwafa tache zatasha
Aunty farida tache to daga yau hausa zamu rinka yimata dan itama ta iya hausar to waima ya akayi ku kuka iya hausa ita bata iyaba
Hiyana tache mu munazuwa tallan nono ne a chan akoi hausawa suna zuwa saye itakuma kullum tana gida tana aiki bata zuwa ko ina " a gida kuma ba mai jin hausa sai fullanchi kawai shiyasa bataji
Aunty farida tache to yanzu dai hausar za'ana mata har ta iya to kawai sukache san nan sukachigaba da sayayyar su
Bayan sungama daukan bra da pant suka wuche wajen dankunne da sarka nanma dayawa aunty farida ta dauka musu har da gold saida sukachika keken zuba kaya uku da kaya tukun nan Aunty farida tache ya isheku ne kokuma akoi wani abun dakukeso " da sauri Hiyana tache ya isa " Aunty farida tache aa kuduba da kyau dai " hiyana tache allah ya isa haka nan " Aunty farida tache to shike nan kutura kayan muje wajen biyan kudi harsun kai wajen biyan kudin kuma sai Aunty farida tache inazuwa chikin shopping din tashiga bangaren always tanufa ta daukoh guda 6 ta dawo ta zuba musu a chikin kayan
Diyana sarkin baki tache aunty menene wan nan kamar breadi Aunty farida tache nakine ke da hiyana da zahra kuma ba bread bane always ne " Diyana ta mai mai ta su nan always to me akeyi dashi ko chi akeyi diyana ta tambaya.
Aunty farida dai taga alamar kamar diyana bata fara period ba saitache mata inmunje gida ki tambayi zahra zata fada miki to kawai diyana tache
Nanfa aka fadamusu bill na kuɗinsu Aunty farida ta chiro ATM nata tamikamusu suka chiri kudin san nan aka samusu kayan a leda Abdol yafara kwasan kaya shida yaran shagon suka kai mota
Aunty farida kuwa takama hannun diyana sukayi waje su Zahra suka rufa musu baya
Aunty farida tache Zahra da lamrat da hiyana suje su shiga motar da takawosu itakuma zata shiga motanta itada diyana da amrat . Tana kaiwa nan tashige chikin motar rike da hannun diyana amrat ma tashigo ta zauna kusa da diyana su
zahra kuwa suka nufi motarsu suka shiga nantake sojojin suka tada motochin suka nufi gida
Suna isa gida kai tsaye bangaren Ammi suka nufa a palo suka sameta nan suma suka baje kolinsu suka fara nunawa Ammi kaya. Ammi kam sai sannu da dawowa take musu tana sawa Aunty farida albarka takuma yaba kayan sosai tache su tattara suje su shiryasu a indaya dache, haka suka kwashi kayan sukayi dakinsu dashi

Aunty farida tadawo da hankalinta ga Ammi tache Ammi gobefa zan koma Mai duguri
Ammi tache ai naga wan nan karanma anbarki kindan dade " Aunty farida tache eh wlh shiyasa nakesan komawa dan kar a hanani zuwa sallah kinga azumi yakusa " Ammi tache ai garakam kikoma kije kikula damijinki yanzu dai kije ki kwanta ki huta a daki sai zuwa dare makarasa hirar
Mikewa Aunty farida tayi tana chewa to Ammi dan allah dai kiyi kokari kishawo mana kan mai martaba daya taimaka yabamu diyana da lamrat
Ammi tache to zanyi kokari . Betroom din Ammi aunty farida tashiga ta haye gadanta ta kwanta bajimawa barchi ya dauketa


Zaune suke a tsakiyar gado gaba dayansu hiyana tache aunty zahra dan allah inasan kifara koyamin karatu kinji lokachin muna kanana bappa yana koyamana karatu har munyi nisa danni har nakai izu 10 a karatun qur'ani kuma inasan in iya karatun qur'ani sosai
Zahra tache zan koyamiki hardana bokoma bana qur'ani kawaiba harda addoe dasu hadisai kuma akoi malamin dayake zuwa yana koyamin karatun islamiya kullum dayamma yanzu tare zamuna zuwa ya koyamana
Diyana tache yauwa nima inaso aunty zahra " zahra tache ai gabadayanku ma yazama dole kukoyi karatu yanzuma daga gobe zanfara koyamuku " harsuna hada baki wajen chewa to


Misalin karfe 8 na dare gaba daya family sun hadu a palan mai martaba
mai martaba da don da aryanne kawai basa wajen shiru kowa yayi daga masu daddanna waya sai wayanda sukayi tagumi suna jiran fitowar Abba
Aunty farida che ta kalli Fahad tache wai inasu prinse ne kullumfa sune suke bayan zuwa wajen nan " Fahad yayi shiru kamar bazai tankaba kusan 2mnt tukun nan yache nimafa tun dazun damuka rabu bansake shiga wajensuba
Ammi tache au ashe zaka tankamata ai nazachi bazakayi maganaba mutanene yadda kasan wasu kurmaye aimusu magana sunaji amma bazasu amsaba kukan wlh bakuji dadin halinkuba " Fahad dai shiru yayi kamar baijin me Ammi ke chewaba
Aunty farida tache kai Ammi hakafa akesan namiji yakasanche ba mai surutu barkataiba " harara Ummi ta watsawa aunty farida kana tache aidaman ke'ki'ke kara injizasu dan kuwa ke awajenki komai sukayi dai dai ne basa laifi " shiru aunty farida tayi bata tankasuba sai sukaji muryan mai martaba yanachewa aa karku dakurawa first born dina ku kyaleta haka nan irin wan nan faɗa haka
Ummi tache ai daman bakinku daya zama mai martaba yayi yana faɗin eh dai munji babu ruwanki farida dawo nan kusa dani
Mikewa Aunty farida tayi takoma kusa da mai martaba ta zauna
Mai martaba yache Amrat ummu waru ( amrat tashi kizo) mikewa tayi taje zaunar da ita mai martaba yayi a kujerar kusa dashi aunty farida kuma tache diyana taso kidawo kusa dani mikewa diyana tai takoma kusa da ita
Zahra'kam ko ajikinta dan ita koma kusa dawa zama zatayi amma yanzu da hiyana sukazo tare suke komai dan haka yanzuma suna zaune kusa da juna
Takun tafiya sukaji wanda kobasu juyaba sunsan takun manyan boss ne nantake palan ya nitsu tsit wasuma da kyar suke numfashi chiki har da zahra da umar
Su hiyana kam ko ajikinsu dan basumasan masu shigowarba
Kai tsaye kan table din suka nufa suna sanye chikin fararen jallabiya dukkansu sai kamshi sukeyi kamar anyi barin turare ajikinsu zama sukayi " don ya dauki bottle na ruwan dake kusa dashi ya bude ya tsiyaya ruwa a cup yasha san nan ya ajiye ragowar a kusa dashi nan take kannen nasu suka fara gaidasu amma babu wanda ya amsa a chikinsu saida kannen nasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login