Showing 207001 words to 210000 words out of 363274 words

Chapter 70 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2605

karshen maganar tare da nufar in da hiyana ke zaune

ita dai tayi mutuwar zaune tana kallo ikon Allah, kusa da ita yaje ya zauna yana faɗin "hii baby" shiru ta yi bata amsa ba sai ma takure jikin ta da tayi tana kallon gefe, hannu ya kai yana kokarin kamo face nata ya juyo da ita bai kai ga taɓa fuskar nata ba yaji an yiwa hannun sa wani wawan damka

da sauri ya juyo, zaro ido yayi waje ganin yadda face ɗin Bgs ta sauya lokacin guda idon sa ya sauya yayi jaa

Da karfi Bgs ya murɗe hannun ya mai da ta baya ji kake kas kas kashin ya karye ihun azaba baturen sojan ya saki, da gudu ɗayan ya miƙe ya bar palon dan ya san halin Bgs, bugun mutuwa Bgs yayi wa baturen har sai da ya suma, a guje hiyana ta bar palo ta shige betroom jikin ta sai rawa yake,tsoro ya hana ta hawa gadon tsayuwa tayi a tsakiyar ɗakin, tana tunanin irin hukuncin da zai mata

Bayan ya gama sumar da baturen ne ya chiro wayar sa ya kira jibga jibgan sojojin dake tsaron gidan su kazo suka ɗauki sumammen baturen sukayi waje da shi,chikin zafin nama ya juya ya nufi betroom ɗin tana jin shigowar sa ta kwasa a guje ta nufi wajen hutawar sa, taku biyu yayi ya damko kugun ta ta baya chikin tsawa yace "me ya kai ki palo da har kika zauna a chan!!? Runtse ido tayi ta kasa magana dan ji tayi gaba ɗaya hanyar maganar ta ya toshe harshen ta ba zai iya motsawa ba, jiran saukan duka kawai take tsawa ya sake daka mata tare da juyo da ita suna fuskantar juna "ba da ke nake magana bane!!! Ɓari kawai lips nata keyi hakoranta sai karaf karaf suke suna haɗe wa da juna, ganin tsoratachiyar face nata ya sanya ya ɗan ji zafin zuchiyar sa ta ragu, dan ya lura ta gama tsorata ko magana ba zata iya ba calmly yace "Open your eyes" kamar jira take ya sake magana ta saki wani kuka mai ban tausayi da ratsa zuchiyar mai sauraro, chije lips na shi na kasa yayi da karfi yana ɗan shafa kan sa da hannu ɗaya kasa kasa yace "kukan me kuma ki ke? Sai lokacin ta samu damar buɗe baki ta fara magana "dan Allah yaya Prince kayi hakuri ba zan sake ba idan ba ka so ko palon ma ba zan sake zuwa ba dan Allah kar ka bugeni"

Kara chije lips na shi yayi da karfi ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa ya rungume ta da hannu ɗaya ɗayan hannun nasa kuma ya chusa chikin gashin kanta yana shafawa da Cool Voice yace "it's ok" shiru tayi ta kara lafewa a jikin sa kasa kasa yayi magana ɗago kai tayi dan bata ji me yace ba "yaya Prince banji me kace ba" shiru yayi yana kallon face nata sake mai mai ta maganar nata tayi nan ma shiru yayi bai yi magana ba slowly ya fatso da face nashi dai dai nata sunkuyar da kanta kasa tayi dan kunyar sa take ji,kwantar da kansa yayi saman wuyar ta yana shakan kamshin man tashin ta "wayace kimin amfashi da man gashi? Saxy Voice nashi ya daki dodon kunnen ta "kayi hakuri ni bani da shine kuma gashi na ya fara hardewa" shiru yayi bai sake magana ba chigaba yayi da yawo da face nashi samar wuyar ta kamar mai neman wani abun sosai yake shafa lallausan bakin gashin kanta da ɗayan hannun sa,ba karamin daɗin taɓawa lallausan fatar wuyar ta ya masa ba

Kokarin faɗuwa hiyana take dan gaba ɗaya ya kashe mata jiki kafofin ta ba zasu iya ɗaukan taɓa amma haka ta daure ta chigaba da tsayuwa dan tana tsoron yi masa magana, Almost 15mins suna tsaye sai shafa gashin kanta yake ya dawo da face na shi saman kanta yana shaƙar kamshin da kyau

Gangaro da kansa yayi kusa da kunnen ta yace "kije ki kawomin wayar ki" ya karisa maganar tare da sakin ta,da gudu ta wuce ta bar wajen ta koma palo


Masu karatu sai mun haɗe gobe idan mai dukka ya kaimu Nagode sosai da comments na ku kuma ina matikar jin daɗin comments ɗin Allah ya saka da alkhari

💖The Talent Troupe Writer's 💖




💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Wanna page ɗin nakine Aisha baita jidda My mum ina godiya da comments naki ina matikar farinciki da jin daɗi Allah ya bar zumunci ya barmin ke


Book 2

Page 21


____da sauri hiyana ta koma palo ta ɗauko wayar ta lokacin da ta dawo ɗakin zaune a bakin gado ta same sa gaba ɗayan kunyar sa take ji yanzu gaban shi tazo ta tsugunna tare da miƙa masa watar tana faɗin "yaya Prince gata" batare da ya kalleta ba yace "sim ɗin zaki chire ki bani" zaro ido waje tayi sai yanzu ta fahimci me yake son yi wato bayaso tayi waya dasu diyana ko,shiru tayi ta kasa ko da motsi dan gaskiya tun da diyana ta dawo bazata iya kwana ɗaya basuyi waya ba,ita yanzu ya zatayi, ganin tayi shiru bata chire sim ɗin bane ya sanya ya ɗago kai ya kalle ta yayi niyar yi mata tsawa amma sai ya fasa saboda tausayin ta dayaji musamman daya ga face nata yadda ya sauya lokacin guda kasa kasa da sanyin murya yace "chiro sim ɗin ki bani idan kina son magana da su sai ki kirasu ta wayata"sunkuyar da kanta tayi kasa kafin tace "dan Allah yaya Prince kayi hakuri ka barmin kaga kai wani lokaci baka dawowa da wuri kuma kullun da rana muna waya da Aunty farida da Ammi" kawar da kansa yayi daga kallon ta ya ɗaure fuska sosai ya fara magana "ba dan su Aunty farida zan ansa sim naki ba nasan ko nace karki kira yar uwar ki sai kin kirata kuma idan kikayi haka ba ke kaɗai ba kuna gefa Aryan chikin tashin hankali da damuwa sister ki bata da lfy idan taji Voice naki tana kara birkichewa Aryan kema nan ki zauna kiyi ta kuka mara amfani addu'a zaki mata dan haka bani sim ɗin,duk lokacin da kike son magana da su Aunty farida ki furta afili kina son yin magana da su duk in da nake zan jiki ko nayi ni sa zan sanya a haɗaki da su" jikin ta har bari yake wajen chire sim ɗin kamar zatayi kuka haka ta chiro ta miƙa masa chikin sanyi murya tace "to yaya Prince ina son ganin Aunty farida da Ammi wlh ina kewar fuskar su" shiru ya ɗan yi kafin ya mata nuni da hannun sa akan ta zaun na gefen sa a saman gadon ba tare da yayi magana ba,chikin sauri ta koma saman gadon ta zauna kusa da shi

remote ya ɗauko daga bedside drawer ya kunna makekiyar Tv dake chikin ɗaki tana sai tin gadon sa, Cameras da ban da ban ne a jikin Tv tafiya yake kai tsaye ya shiga Cameran gida zai wuce idon sa ya sauka kan wata tsohuwar Camera na ɗakin da Ahmad ya kwanta rashin lfy bai san ma ta ya akayi ta shiga Cameran ba, tsaki yaja yana kokarin fita dai dai idon sa ya sauka lokacin da hiyana ta fara yiwa Ahmad addu'a da tsawar da taji da duk wani abu da ya faru a ɗakin, dakatawa yayi ya fasa fita ya chigaba da kallon ita kan ta hiyana waro ido waje tayi ta chigaba da kallo dan ita kwata kwata tama manta da yaya Ahmad ya taɓayin wani chiwo a rayuwar sa tun daga farko har karshen yanar da Ahmad ya warke sai da suka kalla a tare

nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke lokacin da suka kammala kallo satar kallon ta yayi ta kasar ido yayin da itama take satar kallon sa tana jiran taji me zai che, shiru yayi yana tunani idan dai hakane zuchiyar yarinyar nan take bai kamata naki ansar ta a matsayin sister na ba,tabbas ko dan taimakon ɗan uwana da tayi ya kamata itama na fara tausayin ta na ɗauke ta kamar Zahra Auta, da wanna tunani ya fita Cameran ɗakin Ahmad ya shiga na gidan Aunty farida tare da ɗaukar wayar sa ya kira layin Aunty farida

lokacin da kiran Bgs ya shigo wayar Aunty farida tana bedroom, nata Camera kuma a iya palo Bgs ya sanya shiya sa ya kirata domin ta fito palo, zubur Aunty farida ta miƙe tsaye lokacin da ta ga sunan mai kiran ta dogon numfashi ta ja tare da sauke ajiyar a fili tace "yau kuma an tuna da ni kenan yau kuma ko meya sanya Prince ya kirani ko dai ya hakura ya sauko ya chireni a blacklist ɗin ne,jiki na rawa ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunne tana faɗin "hello" ba tare daya amsa ba yace "ki fito palo" yana gama faɗin hakan ya katse kiran, chikin zafin nama ta nufi palo jikin ta har bari yake ita duk tunanin ta yazo gidan tane dan bata taɓa tunanin akoi Camera a gidan na ta ba

pitowa palo tayi amma bataga kowa ba zama tayi saman sofa tana jiran taji me zai faru kuma gaba, massage ne ya shigo wayar ta tana dubawa ta ga Bgs ne ya turo mata, "kunna cameran system naki" abun da aka rubuta a sakon massage ɗin kenan tunani ta shigayi anya Safras lafiyan sa kuwa anya bai sha wani abun ba kuwa? Mutun ne kamar wani aljani bai da aiki sai bawa mutane umarni kamar shi ya haifesu to idan nace ba zan kunna cameran bafa dan iskanci tun yaushe bamuyi waya da shi ba amma ko ya tambayi ya nake, wani tunanin ne ya sake faɗo mata to idan abu mai mahimmanci zai nuna mata fa ai gara ta kunna cameran dan tasan shi dai Safras baya chewa ayi abu haka kawai sai da dalili, tuna hakan yasa ta miƙe chikin sauri ta karisa wajen table ɗin tsakiyar palon ta ɗauko system ɗin duk abun da take Bgs da hiyana suna kallon ta tana kunna system ɗin ta shiga Camera tana shiga Bgs yayi connecting nasu,

Aunty farida bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba ganin Bgs da hiyana zaune waje guda saman gado ɗaya kawar da kai gefe Bgs yayi yana faɗin "ya Junior? Ba karamin haushi Aunty farida taji ba wato ma ba zai gaishe ta ba sai ya wani kawar da kai yama faɗin ya Junior wai shin yaushe Safras zai chan za ne shikan a rayuwar sa, hiyana ce ta katse ta da chewa "Aunty farida ina wuni dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan hiyana lokacin guda ta saki wani Cool murmushi tana son suyi gulma da hiyana amma ba hali tana so ta tambayeta ya akayi suke tare waje ɗaya da Bgs bayan ada tasan ko fuskar hiyana bai san gani amma duk ba daman yin haka dan yana zaune ya chiro wayar sa yana latsawa duk da hankali sa na kan wayar sa yana jin duk abun da suke sosai hiyana da Aunty farida ke zuba hira suna dariya kamar wasu kawaye kwata kwata hiyana ta manta ma Bgs na jinsu ta saki jiki sai zuba hira suke sai da ya gaji sun chika masa kunne dan shi ba mai son surutu bane chikin sauri ya ɗauki remote yayi disconnecting da Aunty farida ko sallama bai bari sun yi ba

wajen Ammi ya shiga ya ha ɗasu da Tv palon ta dan a iya palo kawai yake sanyawa matan Camera kannan sa maza ne yake samu su har bedroom na su

Ammi na zaune a palo tana shan fura ga Tv a kunne tana kallon News, kamar daga sama taga kallon ya ɗauke sai ganin hiyana da Bgs tayi zaune a bakin gado,tasha ruwan mamaki amma sai ta ɓoye mamakin nata chikin farinchiki kamar bakin ta ba zai rufu ba tace "my hiyana a ɗo jam (my hiyana kina lfy)? "Lfy lau Ammi ina wuni? Ammi dai tama kasa yin wani dogon magana gaba ɗaya farinciki da murna ganin hiyana ya sanya harshen ta yayi nauyi "Ammi ya su yaya Haidar? Hiyana ta sake jefo mata tambaya
Sai lokacin Ammi ta samu damar chewa "my hiyana yaya jiffina oɗo wanna ma ko haɗi ko? to owala wanna ma dai dai a yacha am (my hiyana yayan ki ya sauko yana miki abun da ya dace ko idan fa baya miki ko yana miki wani abun da baki so to ki sanar da ni karki ɓoyemin kin ji) Ammi tayi magana chikin harshen fullanci ne dan bata son Bgs yaji me suke faɗe satar kallon sa hiyana tayi ta kasan ido dan ita dai tasan Bgs na jin fullaci ta taɓa jin sa yana magana da harshen fullanci a waya ko kallon in da suke bai yi ba latsa waya kawai yake kai kace kwata kwata baya jin me suke faɗe, jiki a mace hiyana tace chikin harshen fullanci "babu abun da yake min Ammi sai kyautatawa" sosai suka sha hira Ammi sai kawo mata zanchen Bgs take da fullanci hiyana na kakkauchewa dan karya mata hukunci

Daya ji hiran Ammi fa ba mai karewa bane sai ya kashe Tv nasu gaba ɗaya yana jan tsaki su mata basu da wata matsala a rayuwar su idan sun haɗu dai sai suyi ta magana ba hutawa, chikin sanɗa hiyana ta miƙe tana son ta zame ta gudu dan tasan duk abun da Ammi ta faɗa yaji kuma yanzu zai iya mata wani abun akan hakan duk abun da take yana kallon ta ta wutsiyar ido sai da ya barta ta kai bakin kofar fita chikin harshen fullanci yace "waru haɗo (zonan)" turus ta tsaya zuchiyar ta na dukan uku uku dan daman tasan yaji kuma tun da yaji ba zai kyaleta ba mutun kamar wani aljani ko waye ya koya masa fullanci ohon masa ko aina ya koya oho gashi fullanci nasa ma har yafi nasu hiyana fita,

jiki a mace ta koma ta tsugunna a kasa tana faɗin "damin ɗo (gani nan) kamar bai san da zaman ta awajen ba yayi shiru ya chigaba da latse latsen wayar sa tun hiyana na sa ran zai yi magana har ta chire rai kwatsam sai taji sexy Voice nashi ya daki dodon kunnen chikin harshen fullanci "or daman kin che wa Ammi ina miki wani abun kenan ko? To me nake miki faɗa min naji" girgiza kai ta farayi tana faɗin "aa yaya Prince wlh ba abun da kake min" wani mugun kallo ya jefa mata da manya manyan green eyes nashi nan wadda ya sanya ta haɗiyar yawun wahala da kyar

"baki che mata komai ba baza tace na rage muguntar dana ke miki ba ko? Daman ina miki mugun ta kenan ko? to faɗa naji wani mugun tan nake miki? Sunkuyar da kai kasa tayi chikin sanyin murya tace "kayi hakuri ba zan sake ba na tuba dan Allah karka hukun tani nayi alkhari ba zan sake ba" dogon tsaki yaja bai sake magana ba yayi shiru itama shiru tayi tana tsugunne almost 30mins suka kwashe suna zaune a wajen ko kallon in da take bai sake ba hiyana ji take kamar zata faɗi dan ta gaji da tsuguno tana tsoron ta tashi dan yanzu ma bata san hukuncin da zai mata ba,karta kara laifi saman laifi sai da suka kara 10mins a haka sanan Bgs ya miƙe ba tare da yabi ta kan taba ya fice daga ɗakin yana fita ta zauna dirshan awajen tayi zaman yan bori tana mai da numfashi

30mins da tafiyar Bgs sai gashi ya dawo chikin sauri tana zaune yarda ya fita ya barta ta shiga duniyar tunanin meke damun diyana saxy Voice nashi ne ya daki dodon kunnen ta "ke zonan!" da sauri ta miƙe ta karisa wajen sa saman gadon ya haye ya zauna a tsakiya tare da nuna mata gefen sa akan ta zauna, system na shi dake saman bedside drawer ɗayan side ɗin ya ɗauko ya kunna system ɗin sauri sauri ya na yi yina tambayar ta

"wani magani kika bawa Ahmad? Satar kallon sa tayi ta kasan ido kafin tace "ruwa addu'a" chak ya tsaya da latsa system ɗin ya juyo yana kallon ta dan shi a tunanin sa wani maganin gargajiya ta bawa Ahmad "ok to ya kamata ki sanya sister ki a addu'a domin itama kusan chiwon ta ɗaya da Ahmad" na rai na rai tayi da ido chike da tausayin diyana ta fara magana "to dan Allah yaya Prince kasa a mai da ni gida sai na mata addu'a kaji? "Ki mata addu'a daga nan ko ina take zai same ta"yana kai karshen maganar ya miƙe ya fice daga ɗakin yana jiyo sassanyar Voice nata tana faɗin "Allah ya tsare a dawo lfy" a chikin zuciya ya amsa addu'ar yayi ficewar sa, gyara kwanciyar ta tayi saman gadon tana kallon sama kamar mai tunanin wani abu,ko me ta tuna sai kuma ta miƙe da sauri ta shiga toilet ta ɗauro alwala tazo ta fara sallah a sujadar farko tayiwa diyana addu'a sosai da sosai tana addu'a tana hawaye sharshar ta daɗe awajen tana jerawa Allah kirari tana rokon sa daya bawa diyana lfy bayan ta gama ta made daddumar ta koma saman gado ta kwanta


KANO

Abba Aryan da wani Babban malami ne zaune a palon Abba suna tattaunawa akan abubuwan dasu suke faruwa a gidan lbr Abba ya fara bawa malamin tun farkon chiwon Ahmad da duk wasu abubuwan da suka faru a gidan har izuwa yau,dogon numfashi malam ya ja lokacin da ya gama jin bayanan Abba chikin nitsuwa da girma ya fara magana

"gaskiya kunyi sakaci tun farko kun riƙe boko sosai kun yasan da addini


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login