Showing 180001 words to 183000 words out of 363274 words

Chapter 61 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2544

manne a kirjin'sa, a hankali yake shafa bayan ta yana mata raɗa a kunne tun Zahra na share sa har ta fara biye masa suka chigaba da zubawa juna kalaman love.

Maiduguri Nigeria


Ahzan ne zaune saman karfet a betroom din mum ɗin sa yayin da mum ke saman gado suna hira
"Ahzan kana ganin hakan shine dai dai? "Eh mum ya kamata mu taimaka mata" "amma Ahzan abun ne da ban mamaki anya Dr walid bai yi kuskure ya baka result na wata ba, a mai makon na Ummi dan ni dai ban ga alamar Ummi na bukatar aure ba" "mum baki ji Dr yace yanzu ne abun ya fara kamata ba idan ta kara 1 week ba tare da an mata aure ba, shine abun zai bayyana karara kuma kinga idan hakan ta faru ba zanji daɗi ba" "Ahzan Hanan fa zata girmi Ummi sosai dan yadda nake ganin Ummi ba zata wuchi 16 years ba kawai tana da wadatatchen halittace, ni anawa ganin idan ma hakane to chiwon hanan ya kamata ya fara kamawa ba Ummi ba" "mum kowa da kike gani a duniyar nan da irin tasa kaddarar, ai wanna chiwon bai bi ta shekaru ba" "hakanne Ahzan kana da gaskiya to shikenan zanyiwa dadyn ka salim magana" "to mum amma fa karki sanar da kowa batun chiwon nata dan kar su fara magana akai" "ai wannan abun kunya ne baki ba zai iya faɗi ba" "yauwa my mum san nan kinji Dr yace kar a wuche 1 week baa mata Aure ba idan aka wuche za'a samu matsala, ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bani ba shi yasa ma na yanke shawarar Auren ta kawai, dan in shere mata hawayen rashin iyaye" "In Sha Allah zaka samu ladan hakan" "Allah yasa my mum, amma mum yana ga baki shirya zuwa wajen aiki ba jiyama fa baki jeba lfy" "wlh Ahzan gaba ɗaya jikina a mache ne bana iya komai sai kwanchiya kawai" shiru Ahzan yayi yana tunani a ranshi "kai gaskiya maganin na aiki da kyau am sorry mum ba zaki iya komai ba kwakwalwan ki ma bazata yi aiki ba bare kiche babu irin wan nan chiwo a duniya, dole sai abun da na tsara miki shi zaki yi, bazaki iya fita ko nan da tsakar gida ba har sai an ɗaura Aure na da Ummi dan karki bata min shiri nasan kina fita zaki samu lbr ana neman Ummi dan haka babu in da zakije sai bayan Aure, shima dady salim yanzu zanje nayi maganin sa dan idan yazo kawai ya amince da zanchen Aure na da Ummi, babu wan da zai zo gidan nan da sunan yazo biki salon suga Ummi, su tonamin asiri Auren sirri za'ayi
"Ahzan tunanin me kake? Da sauri ya dago kai tare da mikewa ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "babu wani tunanin da nake mum ina tausayin yarinyar ne kawai" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, gyara kwanchiyar ta mum tayi a saman gadon ta ta lumshe ido ta chigaba da barchinta da ta fara.


KANO

da sallama ɗauke a bakin sa Aryan ya shigo fada, kallo ɗaya Abba dake zaune kan kujerar sarauta ya masa ya kau da kansa gefe dan bai san ganin Aryan a chikin wannan hali kwata kwata, saman kujerar kusa da Abba yaje ya zauna "Aryan yaushe ka dawo? "Yanzu na dawo Abba" "to ya ake chiki Allah dai yasa diyanar ce" "aa Abba ba ita bace, wadda suke magana a kanta wai mahaukachiya che wani ya buge da mota to kaga ita kuma ai ba mahaukachiya bace shiyasa ban ma bi ta kan maganar tasu ba ina jin hakan nayi dawowata kawai" "eh lallai Aryan na yarda kana chikin matsananchin tashin hankali wadda yasa baka iya tantanche abubuwa" juyowa Aryan yayi da kyau yana kallon abba kafin yace "Abba me yasa kace haka? "Eh mana Aryan idan ba kana chikin tashin hankali ba, ai da ka daɗe da gano in da diyana take" da sauri Aryan ya kara waro idon sa waje yana kallon Abba "ta yaya kenan Abba kamin bayani" "lokachin da farida ta kira tana sanar mana da diyana ta bata kai kayi picking call din amma tashin hankali ya hanaka kaji bayanin da farida tayi kafin ɓatar diyanar" "Abba pls tell me wani bayani kuma tayi!? "Chemaka tayi diyana ta tafi babu ɗankwali babu mayafi babu ta kalma ta bar wajen, to kaga bazaka nemi diyana a chikin masu hankali ba sai dai a dubata a sawun marasa hankali, idan kayi tunani mai yuwuwa wayan chan mutanen suna da gaskiya domin babu yadda za'ayi suga hoton diyana su che itache kai kuma ka che ba ita bace ko da blue eyes nata zaka iya ganeta chikin sauki kawai dan ayanzu baka da nitsuwa ne, shiyasa Amma abun da nake so da kai yanzu ka tattara nitsuwar ka waje guda, ka dawo asalin Kga da na sani kayi aiki da kwakwalwan ka dan samun nasara ina taya ka da addu'a tare da fatan awanan karon kayi nasara"

a sukwane Aryan ya miƙe ba tare da ya sake magana ba ya nufi hanyar fita fada, taku yake da sauri sauri, wayar sa ya chiro, ya kunna hasken screen ɗin ya duba time 7pm contact ya shiga sauri sauri ya fara kiran layin Shahram, kira ɗaya Shahram ya ɗaga chike sauri da bada umarni Aryan yace "ka sanar da commissioner ya rikemin wayan nan mutanen, san nan ka shiryamin tafiya gobe karfe 7 ina son tai mana a Maiduguri" yana gama faɗin hakan batare da ya jira amsar Shahram ba ya katse kiran part na Ammi ya nufa

Da sallama a bakin sa ya shiga betroom na Ammi zaune take saman Throw pillow tana shan fura ganin shi yasa ta ajiye furar a gefe chike da kulawa ta amsa masa sallamar tare da tambayar yaushe ya dawo, sauri sauri yace mata "yanzu" Ammi zata sake magana ya rigata da chewa "Ammi ina son ganin drowar sa kayan yarinyar nan "diyana? Ammi ta tambaya tana kallon sa sosai "Eh ita inane wajen sa kayan ta yake? "Yana ɗakin su kayan na chan yadda suka bari ba a taɓa ba" tun Ammi bata karisa maganar ba ya juya ya fice ya nufi ɗakin su Hiyana, jakar da ya bawa diyana lokachin da ya dawo saudia ya ɗauka ya fice daga ɗakin, kai tsaye Part nashi ya koma

Yana shiga betroom nashi ya ajiye jakar saman mirrow ya nufi toilet dan yin wanka


Uk

8pm dai dai hiyana ta fito part nasu ta nufi kitchen already jourfree ya gama shirya abinchin Bgs dauka kawai tayi ta komo part nasu gaba ɗaya a takure take dan ji take kamar tsirara take tafiya kayan sun kamata sosai, da sallama ta shiga betroom ɗin yana zaune saman sofa yana waya da wajen aikin su ga dukkan alamu magana yake akan sojojin su da yan ta adda suka kama yana chikin bachin rai sosai, saman table dake gaban sa ta ajiye masa abinchi chikin sauri ta juya zata fita dan kar ya ganta ba hijabi muryan sane ta katse ta yace "ke zonan!? Chikin sauri ta dawo ta tsugunna a gaban sa ta sunkuyar da kai kasa dan kunyar kayan jikin ta takeji, alama ya mata da hannu akan tayi sarving nashi, da mamaki ta ɗago tana kallon sa, taga bama ita yaƙe kallo ba, chikin sauri ta ɗauko plate ta fara zuba masa abinchin tana gama zubawa bata lura da hannun sa dake saman hannun kujerar ba ta ɗora plate din awajen saman hannun nashi, wani wawan mari ya sakar mata, tare da binta da harara chikin tsawa yace "get out" da gudu ta miƙe ta fice daga ɗakin tana kuka, katse wayar da yake yayi ya ajiye wayar a gefe, chike da ɓachin rai ya miƙe ya fice daga ɗakin ya nufi waje, Hiyana na ganin fitar sa ta dawo ɗakin ta kwashe kayan abinci gaba ɗaya ta mai da kitchen tana dana sanin abun da tayi yau itache rana ta farko da yaya prince zai fara chin abun da ya fito daga hannun ta amma gashi saboda zumuɗi ta bata hakan, dawowa tayi saman doguwar kujera ta kwanta ta lumshe ido tana tunani har barchi yayi awawon gaba da ita


12:30Am

Bgs ya dawo chikin gidan kai tsaye part nasu ya nufa, dai dai zai shiga betroom nashi yaji mutun na numfashi da kyar da kyar kamar wadda aka shake, gashi palon akoi duhu wutan a kashe yake, kunna wutar wayar sa yayi haske ya gauraye wajen, juyawa yayi ya nufi in da take kwanche ta takure waje guda, sai rawan sanyi take, a hankali ya kai hannun sa saman wuyar ta jikin nata yayi zafi sosai kamar wuta hannu ɗaya yasa ya dauke ta chak, ya nufi betroom nashi da ita

Jin mutun ya dauke tane yasa ta waro manya manyan blue eyes nata da kyar dishi dishi ta fara gani ta kasa gane wanene ya dauke ta kokarin kwache kanta take ta fara fisge fisge da iya karfinta, chike da jin haushin hakan ya.....



Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu🤪🤪


NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)



💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 14*


.......Chike da jin haushi hakan ya yakacheta daga jikin sa zaiyi wurgi da ita, kalaman Fahad suka fara masa yawo a kwakwalwa kalman Ammi ta karshene ta dira masa a rai in da take chemasa idan har ya kuntata wa hiyana to yasa a ranshi tamkar ita ya kuntatawa, tuna hakan ne yasa ya mai data jikin sa ya rike ta da kyau chike da bachin rai ya daka mata tsawa "zaki min shiru ne ko sai nayi wurgi dake! Jin voice na shi yasa ta nitsu tsit dan ita bata taɓa tunanin shi bane tayi tunanin wanine yazo sache ta shi yasa take kokarin kwache kanta.

saman ka tafaren gadon sa ya kwantar da ita tare da mikewa ya ɗauko Box ya dawo saman gadon, magani zazzaɓi ya fitar ya ɓalli guda biyu, chikin sanyin murya yace "gashi an sa ki sha" jikin ta na kerma ta sa hannu zata ansa zubawa hannun ta ido yayi da mamaki yake kallon yadda hannun nata ke kerman tsoro, ɗaugo idon sa yayi ya fara kallon ta from head to toe gaba ɗaya jikin ta kerma yake hannun ta ya kasa tsayawa waje guda ba lallai idan ya sanya mata maganin a hannun ta ta iya kaiwa bakin ta ba, mikewa yayi ya koma falo ya ɗauko ruwa mai sanyi tare da glass cup ya dawo ɗakin a gefen gadon ya zauna ya balle bakin roban ruwan ya zuba a glass cup ɗin, zama yayi da kyau ya sa hannu ɗaya ya ɗagota, kasa kasa yace "buɗe bakin ki" da kyar ta iya sai ta kerman da bakin na ta keyi ta bude masa, sanya mata maganin yayi sannan ya kafa mata glass cup ɗin a bakin ta, sosai ta sha ruwan sai da ta shanye dukka, san nan ya chire mata cup ɗin a baki ya mai da ta ya kwantar, ya mike ya mai da cup ɗin da roban ruwan saman table ɗin tsakiyar ɗakin, toilet ya nufa.

Wanka yayi ya fito ɗaure da towel a kugun sa, a gurguje ya shafa mai tare da fesa perfume nashi mai bala'i kamshi da daɗi, dressing room ya nufa, jim kaɗan ya fito sanye chikin kayan barchi masu kyau da tsada ga laushi fararen tas riga da doguwar wando, saman katafaren gadon sa ya haye, ya kwanta hannu yasa saman drawer ya ɗauki remote ya kashe wutan ɗakin ya mai da remote ɗin ya ajiye, ya kunna wutan gefe da gefen gadon masu bada haske blue da green, addu'ar barchi yayi ya shafa, sannan ya juyo ya ɗan kalli in da hiyana ke kwanche yadda ya kwantar da ita ko motsawa ba tayi ba, hannun sa ya kai saman goshin ta ba laifi jikin nata ya fara sanyi, dauke hannun sa yayi ya juya ya bata baya yana fiskantar gabas ya ja blanket zuwa saman chikin sa, tare da lumshe ido, asuba ta gari.

1:30am hiyana ta farka daga barci dishi dishi ta fara gani goge idon ta da kyau tayi domin ta tabbatar wa kanta shin muryan mutun take jine ko dai aljani ne mai wannan karatun dan ita dai a chikin bil adama kam bata taɓajin voice mai daɗin wannan ba, mikewa tayi zaune a saman gadon, tafara bin ɗakin da kallo.

mamaki ne ya kamata yaushe ta zo ɗakin nan kuma? Waya kawota? Dan ita jiya kwata kwata batama san in da kanta yake ba, yan waige waige ta fara yi tana neman ta in da take jiyo wannan kira'an Alqur'ani mai bala'i daɗin, karaf idon ta ya sauka kan shi yana zaune saman dar duma yana rike da Alqur'ani mai girma yana karatu, tasha ruwan mamaki wai daman yaya prince ɗin nan ya iya karatu? wai da gaske ne daman yana da imani? Ashe yasan Allah? Ashe yasan in da gabas take? ai na ɗauka shikam in ban da bindiga ba abun da ya sani, da wani zuchiyar sa kamar na Abu lahabi, duk girma da kima da mutunci da fiyayyen halitta manzon rahma yake da shi sai da abu lahabi, ya rinka kokarin kashe sa, to haka yaya prince ka ke duk mai mutunchi da imani da kima wadda Allah ya ɗaura maka responsibility sa a kanka komai kyaytatawar da zai maka sai ka nemi ka masa rashin mutunchi kai mutun baya taɓa kyau tata maka ko mai aka maka laifi ne, tayi nisa chikin tunani da take kamar daga sama har tsakiyar kanta taji voice nashi "ke sauka kije ki kawomin Black tea mara sugar! Chikin sauri ta diro daga gadon ta nufi waje mai da kanshi yay kan karatun da yake ya chigaba.

Jim kaɗan sai gata ta shigo rike da Cup mai shegen kyau gefen sa tazo ta tsugunna murya na rawa tace "gashi nan yaya prince" ko kallon in da take bai yi ba, shiru shiru sai zuba kiraar karatun qur'ani kawai yake tun hiyana na sa ran zai ansa har ta chire rai ta gaji da tsugunno gashi ba wani isshen lfy ke gareta ba, Almost 30mins tana tsugunne a wajen har barchi ya ɗan fara ɗaukan ta, slowly ya sa hannu ya ansa cup ɗin, da kyar ta iya mikewa sai kuma ta kasa komawa saman gadon nashi ta kwanta, gani take kamar idan ta hau zai mata tsawa yace ta sauka, shiru tayi tana tunanin ta haune ko dai ta koma Palo, dan bata son tsawan nan da yake mata ko kaɗan, daga karshe dai ta yanke shawarar komawa saman sofa set dake chikin ɗakin dan tana ganin hakan ne ɗan dama dama.

Saman doguwar kujera ta kwanta ta lunshe ido, har barchi ya fara ɗaukan ta sanyi mai karfi ne taji ya fara ratsa gaba ɗaya jikin ta, takurewa tayi waje guda, sai rawan sanyi take, har karfe 2:45am ba abun da kakeji a chikin ɗakin sai karan hakoran ta dake kakkarwa suna haɗuwa da juna
mikewa yayi ya mai da Qur'an mazaunin sa bayan ya gama karatun dawo yayi ya naɗe daddumar ya nufi gadon sa, hayewa yayi ya kwanta yaja blanket zuwa dai dai chikin sa, ƙaran sautin haɗuwar da hakoran ta keyi ne suka takura masa, chikin tsawa yace "ke zaki dai na damuna ne ko sai na ɓallaki!? Da sauri ta sanya hannu ta toshe bakin ta ta dungule waje gida, rmt ra ɗauko ya kara gudun Ac sosai ya mai da ya ajiye, ya ɗan kara hasken din light dake gefen gadon ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba da shi.

Hiyana kuwa barchi ya gagara, sai juyi take saman kujera sabon zazzaɓi ne ya rufe ta tun tana iya hakuri har ta fara kuka kasa kasa, gashi yace bai san jin karan sautin hakoran tama bare kuma kuka sosai ta toshe bakin ta, ta rasa in da zata sa ranta, shiko sai sharara barchin sa yake a haka har asuba, bata yi barchiba tayi kukan ta kasa kasa har ta gaji tayi shiru, tana jin sa ya tashi yayi wanka ya shirya chikin jallabiya fara ya fice ya nufi masallaci, yana fita ta chire hannun ta daga bakin ta, ta saki wani marayan kuka da kyar ta tashi ta nufi toilet na shi sauri sauri tayi wanka da ruwa mai zafi sosai, ta fito ɗaure da towel nashi ta nufi Palo, kamar zatayi kuka lokachin da take duba kayan da zata sanya dan tayi sallah gaba ɗaya babu kayan arziki, daga rigar da wando masu kama da 1 sai doguwar riga mara hannu, ji take kamar taje ta dauko Zahra ta mata mugun duka dan haushi, da kyar ta samu wani bakin wando da rigarsa fari mai hannu ɗaya, hannun ɗayan ma ɗan siriri da shi da babu duk ɗaya ne, komawa tayi chikin ɗakin sa da sauri ta sanya kayan ta ɗauki blanket na shi ta rufa a jikin ta daga kanta har kasa ta shin fiɗa daddumar tayi Sallah, tana idarwa ta mai da blanket ɗin ta naɗe daddumar, ta ɗauki Cup da yasha black tea da daddare ta fice daga ɗakin ta mai da kitchen, tunani ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login