Showing 321001 words to 324000 words out of 363274 words

Chapter 108 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2620

wata 3 zuwa sama haka ita ma Auta cikin ta zai kai 2 Month"waro ido waje bgs yayi yana kokarin yin magana sukajiyo kakarin amai na Diyana wucewa bgs yayi ya koma part nasu yana faɗin"Ana kiran ka aciki"cikin sauri Aryan ya shige cikin bedroom nasu a tsakiyar ɗaki ya sameta ta duƙa tana tikar amai da alama aman yafi karfin tane ta kasa isa toilet cikin sauri ya karisa wajen tare da ajiye jakar da bgs ya bashi a gafe yasa hannu ya ɗagata cak suka nufi toilet gaba ɗaya ta ɓata masa jiki da amai dan har suka isa toilet bata dai

na tikar amai ba. A tsakiyar toilet ya sauke ta yana kokarin wucewa ya haɗa mata ruwan wanka ta kankame sa dan jiri take gani kukan ta sa masa tana faɗin"Yaya Aryan zan faɗi"tayi maganar cikin kasalalliyar murya riketa yayi da kyau ya ɗagata ya ɗaurata saman gefen baf ɗin wanka cikin sauri ya fara haɗa mata ruwan. Bayan ya gama haɗa ruwan yana kokarin ɗagata amai ɗin ya sake dawowa da karfi ta fara kwara amai ɗin a cikin baf ɗin wankan gaba ɗaya ta ɓata ruwan wankan tana kokarin faɗuwa saboda aman ta yaci karfin ta yayi saurin rikota yana faɗin"Sorry mai jidda"wahalallan kuka ta sa masa tare da riko shi kam tana mai da numfashi,kallon cikin ruwan wankan yayi kafin ya dawo da kallon sa kanta ya rasa ya zai yi ya zubar da ruwan ya haɗa mata wani dan aman Abincin da taci jiya da daddare tayi shiru sukayi dukkan su biyu shi yana tunanin yadda zan yi da amai nan ita kuma tana fama da murɗan da cikin ta keyi

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


[8/10, 6:16 PM] SAFIYYA: 💋 Duk Karfin Izzata 💋


💋The talent troupe writer's 💋


Wanna Page ɗin naki ne Dear ta Aunty Amyra KUKAN ZUCI All the best my Dear fatan samun nasara da cimma burin na Alkhari love you lodi lodi 🥰💔🔐

By
Star Lady


Page 55


......ganin ba zai iya gyara Toilet ɗin bane yasa ya ɗauke ta cak ya saɓa ta a kafaɗar sa suka fito waje ya wuce da ita ɗayan bedroom ɗin a nan ya haɗa ruwa mai zafi ya gasa mata jiki ya cire kayan jikin sa da ta ɓata masa shima yayi wanka ya ɗauro towel Sanna ya naɗota a towel suka fito waje saman gado ya kwantar da ita sanna ya koma bedroom nashi ya ɗauko phone nashi ya kira jourfree akan yazo ya gyara masa ɗakin ya ɗauka mata kaya tare da kayan sanyi ya fito ya dawo ɗayan bedroom da take ciki kamar yarda ya barta haka ya dawo ya same ta ɗagota yayi ya sanya mata kaya yana faɗin"Sorry my jidda"shiru tayi bata yi magana ba sai nishi take kamar wadda tayi gudu ta gaji"In kawo miki tea"cikin sauri ta girgiza masa kai alamar a'a"To me zakici in kawo miki?"girgiza kai tayi da kyar ta iya cewa"ba bu" "No my jidda ni ban yarda ba dole ki ci wani abun"kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin"Ni to ka kawo min nono da fura" "Tirkashi nono da fura kuma jidda? Ina zan samo nono da fura kuma?" "Ni shi nake son sha kuma na kauyen mu na shanun bappa" "My jidda kiyi hakuri ki sha Yoghurt kinji ba bu fura a nan ban taɓa gani ba ko nema zan yi ban san ai na zan nemo ba" "Ni gaskiya yaya Aryan shi nake so idan ba haka ba ba zanci komai ba"dafe kansa yayi aran sa yana tunanin in da zai samo nono kuma har da fura wai kuma na shanun bappa tirkashi,ganin ya shiga damuwa ne yasa ta yunkura ta mike zaune ta kwantar da kan ta a bayan sa cikin shagwaɓa tace"yaya Aryan ka bar shi kawai kaji na koshi"juyowa yayi ya rungumeta yana faɗin"Aa my jidda dole za'a ne mo shi kin ji"ya kai karshen maganar tare da ɗauko wayar sa ya laluɓo number Aunty farida ya fara kira yana murmushi. Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tana faɗin"Hello Aryan" "Aunty farida ya kike ya Junior da dadyn da?" "Suna lafiya ya Diyana da sauran yan uwan naka?" "Suna lafiya Albirushirin ki Aunty farida"cikin sauri tace"goro"ko kaɗan bata kawo cewa Diyana na da ciki bane tafi tunanin karin girma ya samu awajen aiki. "Aunty farida my jidda na da ciki sati biyu"mikewa Aunty farida tayi tsaye cikin sauri tace"Alhamdulila Alhamdulila Allah hu Akbar dan Allah Aryan ka dawo min da ita nan sai ta hai hu kaji"Aryan na kokarin yin magana Diyana ta fasa ihu tare da tashi daga jikin sa tana faɗin"ciki kuma nashi ga uku wayyo Allah Ummi na shike nan mutuwa zanyi wayyo na mutu na lalace ni wallahi ba zan Aihu ba dan mutuwa ake idan za'a Aihu ai na gani a film jinin mutun karewa yake wayyo Allah shike nan ni kam zan rabu da su Hiyana shike nan tawa ta kare innalillahi wa inna ilaihir rajiun"mutuwar zaune Aryan yayi yana ganin ikon Allah ya rasa ta ina zai fara bata hakuri ya kasa magana ya kasa cire wayar da yake da Aunty farida daga kunnen sa sai magana Aunty farida take tana faɗin"Aryan ka bata wayar bari nayi magana da ita"amma ina Aryan bai jin me take faɗe ba hankalin sa na kan Diyana dake neman tarwatsa masa zuciya yadda yake son cikin nan tace bata so kai ina ai ba zai yiwu ba. A sukwane ta mike tana kokarin sauka daga gadon da alama ta ruɗe cikin sauri ya ajiye wayar saman gadon ya riko ta yana faɗin"My jidda ki dawo cikin hankalin ki saurare ni"kokarin fisge jikin ta take tana ihu tsakanin ta da Allah tana surutai"Ai tun da mukayi Aure nace maka ni bana son Haihuwa dan na gani a Tv idan kutun zai aihu jinin sa na karewa ya mutu shine zaka sa na haihu dan baka sona ko? Mugu kawai kuma ko na mutu ba zan yafe maka ba"fusa iya fusata Aryan ya fusata a zuciye ya ɗaga hannu zai wanka mata mari a zafafe ta ɗago ido tana kallon sa suna haɗa ido yaji ya kasa marin nata cak ta tsaya da kuka da surutan da take ta zuba masa ido kamar mai jiran saukan mari kasa yayi da hannun sa murya a shake saboda ɓacin rai yace"My jidda I'm so sorry I.... Bai kai karshen maganar ba ta fasa ihu ta cigaba da surutan nata kaman mai aljanu ba karamin mamakin tane ya kama shi ba wayar sa ya ɗauko a ransa yana faɗin"nasan maganin ki" katse kiran Aunty farida yayi ba tare da ya mata magana ba ya laluɓo number Ummin su ya fara kira wayar na ringing har sai da ya kusa katsewa sanna hajjiya Fateema ta ɗaga cikin girmamawa yace"Ina kwana Ummu" daga ɗayan ɓangaren Hajj Fateema ta amsa da"Lafiya lou Alhadulillah ya kuke?" "Lafiya lou Ummi daman ina son kiyiwa jiddan magana ne" shiru Diyana tayi tana sauraron sa tana son jin dawa yake waya "Me deejahn tayi?" Hajj Fateema ta tambaya kasa yayi da kai kamar yana gaban ta cike da girmamawa ya fara magana "Daman mun samu karuwa ne take ta kukan wai bata so nayi nayi taki shiru taki sauraro na" zubur Hajj Fateema ta mike zaune daga kwanciyar da take a saman kujera tana faɗin "eyeee ba shakka ina take bata wayar" juyawa yayi ya mika mata wayar kallon sa tayi tana faɗin "Waye ne?" mamaki Aryan yake Diyana mai kukan da ba hawaye sai tayi kukan ta har tayi shiru bazaka ga hawaye ko ɗigo ba. Shiru yayi bai mata magana ba ya sa mata wayar a kunnen ta cikin tsoro tace"Waye ne?" daga ɗayan ɓangaren Hajj Fateema tace"Uwar ki ce" jin muryan Ummin ta yasa ta waro ido waje sosai tana kallon sa ciro wayar yayi daga kunnenta ya ɗaura mata a hannun ta ya mike ya fice daga ɗakin cikin tsoro ta mai da wayar kunnen ta ta tattara nitsuwar ta tace "Ina kwana Ummi" a kule Hajj Fateema tace"Wai deejah me matsalar ki ne? Eh wato ke baki jin magana ko" murya na rawa tace "kiyi hakuri Ummi wallahi ni bana so cikin ne" "What? Deejah ni kike faɗa wa baki son ciki eyee,ba'a Aihuwa ku na haife ku a'a lallai Khadijah kin girma to wallahi ki kiyaye ki bar mijin ki ya samu kwanciyar hankali ina cewa last Month na gama case naku akan gudun shi da kike shine yanzu kuma zaki fito masa da wata iya shegen ko to wallahi ina sa shi ya ɗauko ki ya kawo min ke dan ina ga kina bukatar na dawo dake cikin hayyacin ki" hawaye ta fara yi dan duk duniya ba abun da take tsoro biyun Ummin su cikin raunaniyar murya tace "Dan Allah Ummi kiyi hakuri zan yi duk abun da kike so amma ina tsoron cikin ne ranar na gani a Tv da matar tazo Aihuwa dr yace jinin ta ya zube duka ya kare ta mutu shine nake tsoro" sai yanzu Hajj Fateema ta fahimci in da matsalar take ba tsanar cikin Diyana ke yi ba tsoron haihuwar take dan haka sai ta sassauta murya cikin muryan rarrashi ta fara magana "Deejah ki na ji na ko! idan kin ga Mutun ya mutu kwanar sane ya kare ni meyasa na haife ku kuma ban mutu ba saboda kwanana bai kare ba dan haka ina son ki sani ba sai Aihuwa ba kina kwance saman gadon ki lafiyar ki kalau ma mutuwa tana iya ɗaukar ki wasu ma abinci suke ci mutuwa ke ɗaukan su kuma shi haihuwa bashi da wata matsala kin ji ko? Ke dai kiyi ta addu'ar Allah ya baki ƴa'ƴa masu Albarka karki ji wani tsoro kinji deejahn bappa" dariya Diyana tayi tana faɗin "to shike nan Ummi zan rinƙa yin addu'a,ina su Ammi?" "Ammi suna palon Abba suna yin breakfast nima tafiya can zanyi yanzu sai munyi waya" bata jira amsar Diyana ba ta katse kiran ajiye wayar Diyana tayi saman gadon ta diro kasa ta fice daga ɗakin ta nufi asalin bedroom nasu.

Nan ta isko Aryan yana zaune bakin gado ya buɗe jakar da bgs ya bashi yana duba takar dun jin shigowar ta yasa ya ɗago kai yana kallon ta karisowa tayi kusa da shi ta zauna tana faɗin "Yaya Aryan me kake yi" kallon ta yake ya kasa magana kamar ba itace yanzu nan tace kar ya sake yi mata magana ba har da ce masa mugu ganin yayi shiru bai tankata ba yasa ta anshe takardun hannun sa ta ajiye a gefe ta faɗo jikin sa tana dariya tana faɗin "Yaya Aryan me ya faru kake ta kallo na kaki yin magana"rungume ta yayi sosai yana ɗan murmushi yana godewa Allah daya basu Hajj Fateema a matsayin suruka kuma uwa "Tabbas da Hajj Fateema na nan da jidda ta tafi haka hankali yanzu gashi cikin yan mintocin da basu fi goma ba ta saita min jidda ta wadda ba dan ita ba da sai mu kwana mu wuni rikicin nan ba zai kare ba daga karshe sai ran kowa daga cikin mu ya ɓaci" yayi nisa cikin tunani yaji hannun ta cikin rigar sa tana shafa lallausan gashin kirjin sa kallon face nata yayi kafin yace "tashi ki zauna muyi magana" ba musu ta mike ta zauna da kyau tana kallon sa ɗauko takar dun data anshe daga hannun sa yayi ya miƙa mata yana faɗin "wannan takarda wani Katafaren gidan gona ne dake us Bgs ya baki kyau ta a matsayin gift na cikin dake jikin ki sai kuma wanna ma kullin motar irin na sister daman tun da naga ya bada Oder motocin guda shida iri ɗaya na kawo a rai na ku ya sayawa ashe ko haka ne ke ɗaya sister ɗaya auta ɗaya matar Yusuf ɗaya matar Fahad ɗaya ina ga ɗayan kuma na matar da Ahmad zai aura ne idan mun haɗu a palo anji sai ki masa godiya amma kin san me? idan Allah ya bamu baby boy sunan bgs zamu sa idan kuma mace ce sunan Ammi" cikin sauri tace "A'a sunan Aunty Amarya dai dan Allah" har cikin ransa yaji daɗin hakan sai kuma mood nashi ya sauya dan ta fama masa wani ciwo shiru yayi bai sake magana ba yana jin zuciyar sa na masa zafi a duk lokacin da ya tuna yadda karshen mahaifiyar sa ta kasance sai yaji ya tsani duniya gaba ɗaya ganin ya sauya ya shiga damuwa yasa ta faɗo jikin sa tana faɗin "Yaya Aryan ya batun nonon da furan kuma?" Kallon face nata yayi yana faɗin "tashi ki shirya muje mu nemo in da yake ai dole little bgs ya sha nono ko kuma" saurin rigashi tayi tace "ko kuma little Aunty Amarya" murmushin dole yayi kafin yace "to koma waye dai jeki shirya kizo mu tafi" mikewa tayi ta nufi dressing room har ta kai bakin kofa zata shi sai ta juyo tana faɗin "Yaya Aryan idan na Haifi maza yan biyu dan Allah kasa sunan yaya Prince da sunan yaya Aiman kaji" wani mugun raɗaɗi yaji zuciyar sa na masa ɗaga mata kai kawai yayi ya kasa magana Diyana ta tayar masa da zafi biyu lokaci guda,mikewa yayi ya kwanta yana tunanin rayuwar da sukayi da Aiman nan take idon sa suka sauya sukayi ja cije laɓɓan sa yayi yana jin mutuwar Aiman ta dawo masa sabuwa. A wanna hali Diyana ta dawo ta same sa ta shirya cikin dogon riga abaya baki ta sanya gyalen rigar a kan ta ba ƙaramin tsorata tayi da ganin yana yin saba hayewa gadon tayi tana faɗin "Yaya Aryan lafiya" mikewa zaune yayi yana kokarin ɓoye damuwar sa yace "Muje ko" bai jira amsar ta ba ya miƙe ya ɗauke ta cak suka nufi wajen. Bai dire ta ko ina ba sai cikin motar sa sanna ya shiga ya tayar da gudu suka fice daga gidan suka tafi neman fura da nono.

Misalin karfe 5 na yamma zaune suke a ɗakin su saman katafaren gadon su.
Hiyana na sanye cikin guntun wandon jeans blue zuwa goiwa da yar riga mai guntun hannu fari tas tayi kyau sosai kan ta ba ɗan kwali ta zuba lallausan bakin gashin ta nan har baya tana zaune a gefen sa ta ɗaura kyawawan fararen kafofin sa a kan cinyar ta tana jan yatsun kafar nasa tana mammatsa masa su yayin da shi kuma yake sanye cikin wandon sojoji guntu zuwa guiwa da farar singlet ya baza lallausan bakin gashin kansa bai ɗaure ba yayi kyau sosai kamar shi yayi kan sa ya ɗaura system a kan cin yar sa yana aiki. Cike da so da kauna sa cikin shagwaɓa tace "Yaya Prince yatsun kafan kan nan suna min kyau sosai" ba tare da ya ɗago kai daga aikin da yake a system ɗin ba yace "okey ma" waro ido waje tayi ta ɗaure fuska tana faɗin "Ni ce ma?" Cigaba da aikin sa yayi yana faɗin "Oh sorry ma" "Uhm Uhm shine zaka sake cemin ma ɗin kuma" sai lokacin ya ɗago ya kalleta yace "Oh I'm sorry ma man tuwa nayi" gunkule hannu tayi zaka kai masa dukan wasa a kirji yayi saurin mike wa yana faɗin "I said sorry ma" da gudu ta mike ta nufesa ɗaga ta yayi cak suka nufi wajen yana faɗin "Lokacin training yayi ma" kukan shagwaɓan ta sama tana faɗin "Ni ka sauke ni mun ɓata tun da ni ce ma" rungume ta yayi cikin shagwaɓa ya kwai kwayi maganar ta yana faɗin "Ni ka sauke ni mun ɓata tun da ni ce ma" "Allah yaya Prince bana so" sake kwaikwayar maganar nata yayi yace "Allah yaya Prince bana so" ya kai karshen maganar dai dai ya sauke ta awajen motsa jikin nasu bubbuga kafa tayi a kasa tana yarfe hannu tana faɗin "Allah bana so ni ka dai na kwai kwayon magana ta" bubbuga kafa shima yayi ya yarfe hannu ya sake kawai kwayon maganar nata yace "Allah bana so ni ka dai na kwai kwayon magana ta" yana magana fuskan sa a ɗaure sosai ɗaure fuska tayi ba tare da ta sake magana ba ta nufi hanyar komawa cikin ita a dole tayi fushi cikin sauri ya jawota jikin sa ya rungumeta yana faɗin "Oh my Eshat idan kikayi fushi dani ya kike so nayi da rai na to na tuba ba zan kara ba" ɗaga kafar ta tayi dan ya fita tsawo sosai ta sa hannu taja dogon hancin sa tana faɗin "Allah yaya Prince ni ban san waya koya maka neman tsokana ba" "wash Allah" ya furta yana ɗan shafa hancin nashi da ta ja,dariya tayi tana faɗin "Soja na kuka dan naja hancin sa" kama hannun ta yayi dukka biyu ya rike da hannun sa ɗaya yasa ɗayan hannun nasa yaja dogon hancin nata ita ma yana kallon face nata "ihu ta saki tana faɗin "Na tuba ashe da zafi" Cool murmushi ya saki tare da kara jawota jikin sa yana faɗin "Soja kam bashi da jini a jiki ne da ba zai ji zafin abu ba idan an masa" turo baki bayi tana kokarin yin magana yayi saurin matso da bakin sa sai tin kunnen ta yana faɗin "My Eshat give me a hot kiss kafin mu fara training kinji? Ɗago ido tayi tana kallon sa kashe mata ido ɗaya yayi tare da ɗaga mata gera ɗaya turo baki tayi tana faɗin "To ai sai ka ɗaga ni tsawona zai iya kamo bakin naka" tun bata gama rufe baki ba ya ɗaga ta cak ya ɗaurata saman sofa dake wajen tare da ɗan rangwafo da kan sa yana shafa bayan ta da hannun sa ɗaya a hankali ta kawo dan bakin ta dai dai sai tin nashi cikin nitsuwa ta kama lallausan lips nashi na kasa ta fara kissing kamar jira


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login