Showing 126001 words to 129000 words out of 363274 words
da kanshi ya kai diyana class nasu wato primary 5 ko da tashi class ɗin gaba ɗaya students ɗin sun zuba mata ido suna kallon ta, ba karamin rikitasu kyan diyana yayi ba mu samma blue eyes nata dake ɗaukan ido gashi tasha kwalliya sai dai bata sa jambaki ba, amma idan kaga ɗan ƙaramin bakin nan nata ka rantse tasa pink janbaki, daga masu chewa Wow, sai masu chewa Masha Allah
kujerar tsakiya Hm yace taje ta zauna.
diyana ko baki baya shiru idan aka mata abun da bata so chikin iyayi da yanga tace "uncle wlh ni kujerar gaba nakeso bazan iya zama awani kujeraba idan ba gaba ba, toma ai kujerer baya na dolayene, " da mamaki yan class ɗin suke kallonta dan sun san gaba ɗaya school ɗin ana mugun tsoron Hm dan baya wasa da ɗalibai, gaba ɗayan su, sun zubawa Hm da diyana ido suna jiran suji wani amsa zai bata.
Chikin nitsuwa yace "to shikenan jeki zauna a kujerar gaban, ke saudat tashi ki koma kujerar tsakiya ki barmata na gaban, subhanallah gaba ɗaya yan class ɗin mamaki yadda Hm yayiwa diyana magana suke, kowannen su ya shiga tunanin wacece diyana? Yar wacece a kasan nan? Domin Hm ko ƴaƴan chikin sa baya raga musu, amma ko wache ta kuduri niyar tambayar diyana idan Hm ya fita.
Haka ko akayi Hm na ganin diyana ta zauna a kujerar yaja hannun junior suka fita waje.
Suna fita yanmata kai har da maza suka fara tururuwa zuwa wajen diyana, domin tambayar ita yar wacece, gaba ɗaya student dake class ɗin bazasu fi su 30 ba domin a school ɗin ba'a haɗa yara dawa a class ɗaya kowani class suna da A & B har C ma
Shiyasa basu dayawa sosai gaba ɗaya students ɗin sun taso suka nufi diyana ban da yarinya ɗaya wadda ke zaune shiru tana binsu da ido, kallo ɗaya zaka mata kuma kagane tana chikin damuwa da alama kuma yaran class ɗin suna kyarar ta basa sonta, dan ga idon ta nan chike tab da kwalla.
Ɗaya daga cikin students ɗin ne ta miƙawa diyana hannu, tana faɗin "sannun ki da zuwa ni dai sunana Maryam zamu iya zama friend"? Dayake diyana ma yar ji da kai che ba kowa takewa magana ba sai wadda ta ga dama, shiru tayi kamar bata san da tsayuwar mutane a kusa da ita ba,
Basuyi mamaki ba dan a yadda suka kallon diyana, dole yar wata hamshakin mai kuɗin ne ko yar shugaban kasa koma dai yar sarkin Makka, dan a ganin su kyan diyana ya wuche ache mata yar Nigeria, ga fatar jikinta tayi luwai luwai kamar na jarirai, haka dai sukayi ta mata surutai da tambayoyi amma diyana ko ta ɗaga ido ta kalli ɗaya daga chikin su, saima fitar da chocolate tayi daga school bag ɗin ta, ta buɗe tafara sha,
ganin ta manna musu hauka sai shan chocolate take yasa wasu daga chikin su suka koma ma zaunin su, sauran kuma suna tsaye, wata daga cikin su ta dubi diyana tace "haba baiwar Allah ya kamata ki kulamu mana
.......chikin tsawa da tsiwa batare da ta ɗago ta kallesu ba tace "dan Allah ku tafi ku bani waje, tun raina bai ɓachi ba, jin hakan yasa duk suka suka nufi wajen zaman su, dan suna tsoron yiwa diyana wani maganar saboda basu san wacece ba karsuje su taɓo abun da yafi karfin su, kuma ayadda suka ga Hm na mata magana hakan ya kara tabbatar musu, diyana ba daga karamin gida ta fitoba.
Wan nan kenan ya kamata mu waiwayi garin Yola tun da muna kusa dasu kunga tsakanin yola da Maiduguri banisa sosai
Yola
Zaune take a tsakar gida ta rasa meke mata daɗi, sai faman juyi take saman ɗan chinyayen tabarman ta, da duk ɓera ya gwaguyesa, jitake kamar hanjin chikinta zasu tsinke saboda yinwa da take ji ga chiwo da chikin nata ke nata gashi gidan nata ba komai bare ta dafa, gani take duniya na juya mata, duk ta rame lokachi guda ta chanza kamar ba itaba.
Da sallama hasana matar yaya Bello ta shigo gidan, wani kallo uku goma inna ta wurga mata kafin tace "munafurchin me kuma ya kawoki gidan nan"?
Tsugunnawa har kasa hasana tayi chikin ladabi tache ina wuni goggo habiba, chikin tsiwa Inna tace "idan ban wuniba zaki ganni ne" mikewa hassana tayi ta karisa wajen tabar man da innar ke zaune ta ajiye mata ɗan buhun dake hannunta tanan faɗin "gashi hamma Bello ne yace na kawo miki" bata jira amsar inna ba ta fice daga gidan da sauri
babu ko kunya bare tsoron Allah, Inna ta jawo buhun ta buɗe, ɗanyar gyaɗa ne da kuma gwaiba, dayake farkon shigowar damuna che akoi kayan lambu sosai, chike da zumuɗi tasa hannu ta ɗauki gwaiban tafara chiki tana ɗan murmushi,
sai da ta chinye gwaiban tas san nan ta miƙe da kyar ta nufi kichin tafara kokarin hura wuta dan ta dafa gyaɗar.
KANO
Misalin karfe 4 na yamma hiyana che zaune a gefen gadon da Yaya Ahmad ke kwanche tana ɗan tofa masa addu'oe a hankali, shi kuma ya zuba mata manya manya fararen idon nan nashi yana kallon ta
Cikin sanyin murya tace "yaya Ahmad ya kakejin jikin naka, abun mamaki sai taga ya ɗanyi murnushi, ya lumshe mata ido ya sake budewa, wani cool murmushi ita ma ta saki ganin yaya Ahmad ya fara samun sauki har ya fara murmushi, chigaba tayi da tofa masa addu'oe da take,
Almost 10mnt ta ɗauka tana masa addu'a, san nan ta ɗago tana kallonsa tace "yaya Ahmad zan chigaba da zuwa ina maka topin addu'a har na tsawon kwana 7 san nan zan haɗa maka ruwan addu'a mai karfi da kaina, ina sa ran kafi na gama topa maka addu'oe da zan maka na kwana 7 ɗin nan In Sha Allah zaka fara chin abin chi ta yadda ina kawo maka ruwan addu'a zaka sha, kuma da yar dan Allah kana sha zaka samu lfy, murmushi ya kara sakar mata alamar yaji daɗi, itama ta sakar masa murmushi san nan ta miƙe ta nufi waje.
Aunty Amaryan
Tsaye take a gaban miro tana waya da hajj sadiya
"Haba hajj sadiya wlh nache miki ban san ya akayi hakan ta faruba Amma dai zan sa musu ido yanzu" daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace "to wlh hajj Hajara gara tun dare bai mini ba kisan abunyi, bakiga da gagarabadau ya kirani faɗan da yake tayi bane yace wai tayaya za'ayi muyi sakachi har wata tana kokarin kunche masa aiki, kuma yache wlh yarinyar bazai iya yimata komai ba shiyasa da taje tana kokarin yiwa shi Ahmad ɗin addu'a aljanun suke ihu sun kasa yimata komai,saboda askar ɗin datake, idan bamuyi da gaskeba tofa tana gab da kunche aikin nan kuma tana kunchewa inba muyi saa ba to kan ɗaya daga chikin mu zai dawo.
Dafe kirji Aunty amarya tayi kafin tace "munshiga uku hakan ma bazata faruba wlh in dai Hiyana che daga yau bazata sake shiga in da Ahmad yake ba zan mata iyaka da shi, ba zan bari ta ƙara koda ganin saba"
"Yauwa hajj Hajara kiyi kokari dan Allah" "to kawai Aunty amarya tace sanna sukayi sallama ta ajiye wayar saman mirrow ta chigaba da gyara fuskar ta, tana tunanin yadda zata ɓullowa hiyana
To jama'a kwanaki sunja lokachi ya tafi a yau diyana ta chika sati 1 da kwana 3 a gidan Aunty farida Maiduguri
Yauma kamar kullun ta tsara kwalliyar ta kamar yadda ta saba tayi kyau sosai ga wani giba da ta ɗanyi sosai ta chiko ta ko ina, shap nata ya kara bayyana ga wani kyau da fatar jikin ta ya yayi, ya kwanta sumul sumul kamar fatar jariri, sai kyalli take ta ko ina, sanye take chikin wani haɗadɗiyar wandon jeans blue da t-shirt baki, ba karamin kyau kayan suka mataba sun zauna a jikinta sosai ta saki lallausan bakin gashin nan nata har gadon baya sai sheki yake, ta baza takartun makarantar ta a tsakiyar babban palon kasa tanayin home work, sai faman taunar chingum take kas, kas, kas, abunta
Da sallam ɗauke a bakinsa ya shigo palon, a sukwane diyana ta ɗago kai dan voice nashi da tayi, da sauri ta miƙe ta nufesa tana faɗin ƴa...✍️
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*💫STAR LADY💫*34
💖The Talent Troupe Writer's 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
*Episode 3️⃣5️⃣*
.........da sauri ta miƙe ta nufesa tana faɗin "yaya Aryan kai... Bata kai karshen maganar ba ta ɗakata kuma chikin sauri ta dakata daga nufarsa da take, jiki ba kwari ta juya ta koma wajen books nata ta zauna ta dukar da kai ta chigaba da abun da take.
A hankali chikin nitsuwa ya fara magana "me yasa kuma kika juya kika fasa karasowa" batare da ta ɗago ta kallesa ba tache "saboda kai ba yaya Aryan ɗin bane, da mamaki Aiman ke kallon ta, chikin mamaki yace "ya akayi kika iya gane chewa ni ba Aryan bane? bayan ko iyayen da suka haife mu in dai ba tare suka ganmu ba, basa iya banbanta mu, sau dayawa Abba na kirana da sunan Aryan haka zalika ya kira Aryan da sunana muna kama sosai bamu da wata bambancin"
Cikin sauri batare da ta ɗago ba tace "wlh kuna da banbanci sosai ma kuwa,
Karisa shigowa yayi cikin palon ya zauna saman sofa mai zaman mutun 2 yana faɗin "to menene bambanci namu?, Har lokachin diyana taba ɗagoba tana duke da kanta tana ta rubutu a chikin book nata, shikuwa Aiman ya kafeta da Ash eyes nashi sosai yake kare mata kallo
Kanta na kan takar dar da take rubutu tafara magana "yaya Aryan ya fika dogon hanchi, hanchin sa siririne sosai, san nan yafi ka manya manyan ido kuma shi idon shi yayi kalar ash sosai, sannan yana da ɗigon baki a ta gefen sagen sa, bakin sa yayi red sosai, kuma yafi ka dogayen yatsun kafa, gashin kansa yafi naka tsantsi da kuma baki, kuma... Bata karisa maganar Aima yace "ke ya isheni haka, a yaushe kika kare mana kallo har haka kuma shi Aryan ya fini komai ke nan? Ni babu abun da na fishi?"
Still dai bata ɗago kanta ba tace "aa yaya Aiman, akoi abubuwan da kafishi mana sosaima, gyara zama Aiman yayi kafin yace "ok ina jinki faɗamin ni kuma dame dame na fishi"
"Kafishi katon hanchi mana domin shi yaya Aryan hanchin sa, siririne kuma dogo sosai kai kuma naka dogone amma kuma kato, san nan ka fishi katon kafa, shi kafarsa karamine kai kuma naka kato, ka fishi katon kai, ka fishi jiki, kuma muryan yaya Aryan, ɗan siririne kai kuma naka iri na wanchan yaya Umar ɗin ne kato kuma .... "Ke dalla kiyi mani shiru idan muryana katone ya akayi dana yi sallama kika kasa gane ba Aryan bane? Ya akayi lokachin da kika ɗago kika ga fuskata baki gane ba Aryan bane? sai da kika zo kusa dani
"Ai saboda ina sunkuye da kai na kasane ne shiyasa naga kamar yaya Aryan ne, wlh da ina a tsaye ne na ganka bazan che yaya Aryan bane, saboda kuna da banbanci sosai kuma ai don na daɗe banji muryan yaya Aryan bane shiyasa naji kamar shine"
"Ok to ya isa ina Aunty farida" "Aunty farida bata nan taje shopping" "waya miki kwalliyar nan" ya tambaya yana kare mata kallo from head to toe, sai lokachin diyana ta ɗago kai chikin zumuɗi tace "ni nayi yaya Aiman, nayi kyau ne? "Murmushi yayi kafin yache sosai ma my sister, ai daman ke kyakkyawa che, da sauri diyana ta miƙe ta dawo kusa da shi ta zauna tafara magana
"Yaya Aiman kasan me, batare da tajira amsar sa ba ta chigaba da magana "yan school namu kowa chewa yake wai ina kama da laraba ina da kyau sosai" "eh mana sister ai gaskiya suka faɗa miki kinma fi larabawa kyau ai" murnushi tayi sosai wadda yasa har dimple nata ya lotsa, shi kuwa Aiman ya zuba mata ido kawai yana kallonta daga samma har kasa
"Yaya Aiman ina yaya Aryan yake? ya akayi kazo kai ka ɗai? "Abba ne yace nazo Aunty farida nason ganina, san nan kuma yaya Aryan yana gida" "to yaya Aiman ka kiramin shi awaya inason yin Magana dashi" "ok kawai Yaya Aiman yace san nan ya fito da wayarsa daga aljihun wandon jeans dake jikinsa, ya kunna hasken screen ɗin wayar, ya shiga contact yana neman layin yaya Aryan.
Da sallama Aunty Farida ta shigo palon hannunta riƙe da manya manyan ledoji shopping, da sauri Aiman ya ajiye wayar sa ya miƙe ya nufi Aunty farida ya ansa mata ledojin yana faɗin "Wellcome Aunty babba" "Aiman ka iso kenan? "Eh yanzu na shigo,
Zama sukayi saman kujera ɗaya mai daman mutun 3, nan suka fara gaisawa
"Yaya Aiman kazo ka kiramin yaya Aryan ɗin mana" chewar diyana, waro ido waje Aunty farida tayi chike da mamaki tache "ke wani yaya Aryan ɗin kuma wato yanzu diyana duk maganar da namiki bata shiga kunnen ki ba koh?
Turo baki diyana tayi chikin shagwaɓa tace "kiyi hakuri Aunty farida na mantane shiyasa, amma ba zan sake ba" subhanallah ido kawai Aiman ke binta dashi yama kasa magana kawai kallon ɗan karamin bakin nan nata yake baya majin me take faɗe shidai bakin kawai yake kallo.
"To tashi ki kwashe books nakin nan ki mai da ɗaki kizo mu shiga kichin yau da kaina zan yiwa yaya Aiman girki kizo kema ki tayani, da sauri ta miƙe chike da zumuɗin zata shiga kitchin yau.
tattare books nata tayi ta maida chikin jaka ta ɗauki jakar ra nufi stair ɗin.
KANO
wani zazzaɓi mai zafin gaske ne ya rufeshi, sai rawan sanyi yake, ga ash eyes nashin nan sun chanza sunyi jaa sosai gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi, zaune yaƙe saman sofa ya dafe kansa da hannu ɗaya, yayi shiru kamar mai tunani.
Almost 10mnt yana wan nan yanayin, a hankali yasa hannun ya ɗauko wayarsa dake gefe guda, kunna hasken wayar yayi ya chire password ɗin san nan ya shiga contact, layin Aunty farida yayi dealing ya fara kira, ringing ɗaya Aunty farida tayi picking tare da faɗin "hello Aryan"
Da kyar ya iya buɗe baki, baka jin voice nashi ma sosai ya fara magana "Aunty farida y kk" , subhanallah! Aryan baka da lfy ne? Yana ji voice naka haka? Tayi maganar a ruɗe "Aunty Farida Abba da Ammi suna neman kasheni da kansu" "A uzubillahi!! haba Aryan me suka maka haka? har zakache suna neman kasheka"
"Aunty farida sun ɓoyemin matata wlh ina sonta ina san ganin ta, ina chikin damuwa Abba yaki faɗamin in da take Ammi kuma bata isa ta faɗamin ba saboda dole tabi umarnin Abba, pls Aunty farida kisa Abba ya dawomin da ita in dai ba so kuke ku kashe niba, kin san yadda nakeji a chiki zuchiyata kuwa? Ya karisa maganar chikin rau'nanniyar murya
Wani irin farin cikin Aunty farida taji, jitake kamar ta zuba ruwa a kasa tasha dan daɗi yau Aryan da bakinsa yake faɗin zai iya mutuwa a kan mace, lallai diyana kin chiri tuta waiii, jin Aunty farida tayi shirune yasa yace "Aunty babba ko kema kina bin bayan Abba ne? Da sauri tace "a'a Aryan yanzu kasan ya zamuyi kaje ka sanar da Abba kana sonta kuma Auren ta zakayi nan ba da dadewa ba, nasan kana faɗa masa haka zai dawo maka da ita"
Dogon numfashi yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin yace "No Aunty farida ni bazan faɗawa kowa ina sonta ba kema na faɗa mikine dan keche sirrin mu kuma pls kada ki faɗawa kowa, har sai ɗan uwana ya samu matar da yakeso shima sai a haɗa Auren nu lokachi guda.
"Aryan idan fa baka faɗawa Abba chewa Son ta kake ba wlh zai iya bawa wani bare Aure'n ta"
Chika tsawa Aryan yace "No Aunty farida hakan ma ba zai yiwuba ni dai kawai yanzu kiwa Abba magana ya dawo da ita san nan kuma karki faɗa masa nache ina Son ta" to shikenan Aryan, ɗazun nan ma Aiman ya shigo" "ok to Aunty Babba kinga kwakwalwa Aiman na gab da samun matsala saboda rashin lfy Ahmad shiyasa ma muka zaɓi mu turashi wajen ki wata kila idan baya ganin Ahmad ɗin, zai iya mantawa da wasu abubuwan, pls Aunty farida bama sai na faɗa miki ba karki barshi ya rinƙa zama shi ka ɗai bare ya samu daman yin tunani gida ki mantar da shi komai, ki lallaɓa ki samo masa mata a cikin family mijin ki, ki haɗasu dan a haɗa Auren mu gaba ɗaya zanso hakan"
"Eh hakan zai yi daɗi kam zan yi iya bakin kokarina, Khalid da Yusuf su already suna da natan su, saura Shi ogan naku da Aiman da