Showing 48001 words to 51000 words out of 286946 words
hankara ta ji an taka burki da karfi wani abu ya bugeta ta fada can gafe, da sauri ta rike kafarta da bata warke daga daurin da Baba tai mata ba, yau kuma ta sake jin ciwo a kafar, da sauri Sirleem ya fito daga motar ya karaso inda take.
“Ba ki ji ciwo ba? Ina ta horn ba ki lura ba”
Baki sake take kallonsa idonta kamar za su fito gaba daya ta manta da wani ciwo a kafa, ta masa yardar Sirleem take gani da gaske shi? Ko mai kama da shi.
“Sannu ba ki ji ciwo ba?”
Yana tambayarta ta kuma ta kasa amsawa sai kallonshi take tana ganin abun kamar a mafarki, daman kuma ba jinsa take ba tun sai an yi da karfi take iya ji.
“Hey”
Ya kada mata hannunsa a fuska sai a lokacin ne ta dawo hayyacinta, a lokacin ne mutane suka fara taruwa kallonsa da kuma ganin abun da ya faru. Rawa jikinta ya fara yi idonta ya cika da kwalla bata san lokacin da ta riko hannunsa da sauri ba.
“Dan Allah kai ne Sirleem M2 ko kama ce kawai”
Kallonta yake for few seconds sannan ya ce.
“Ni ne”
Tana kallon yadda bakinsa ke motsi da yadda ya nuna kansa ta san magana yai, amman bata ji komai ba saboda be yi da karfi ba, gashi kuma tana son jin muryarsa.
“Bana ji sosai sai ka fada da karfi, dan Allah kai da karfi na ji muryarka kanji”
Ta sakin hannunsa tai ta rike kafafunsa ta fashe da kuka.
“Ni ne”
Ya amsa mata da karfi yadda zata ji, ta ji muryarsa sai dai akwai banbanci a tsakanin muryarsa ta cikin waka da kuma ta zahiri, amman tabbas kamaninsa da wacan Sirleem din ba su da banbanci tun daga kan sajen har farin da tsaye da iya wanka.
“Wallahi ina matukar son ka, ni masoyiyarka ce sosai, ina kaunar wakokinka, ban tunanin Allah zai hada ni da kai cikin sauki haka ba, na gode na gode da ka kade na yafe maka na yafe maka Wallahi ina kaunar sosai”
Jikinta har rawa yake sanadin kallonsa da take, hawaye kuma suna ta aikinsu a fuskarta, har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba.
“Ko dai mafarki na ke yi”
Ta tambayi kanta tana taba fuskarta, sai yai murmushi ya cire facing cap din dake kansa ya saka mata akai saman Hijabinta, yana girgiza mata kai alamar a'a ba mafarkin take ba fuskarsa da murmushi. Hannunta ta kai ta cire hular daya saka mata ta rumgune hular tana kuka, a nan wasu suka fara tsaki suna fadin wai abun ta yayi yawa sai kace wacce ta ga wani sahabi ko Annabi, ita kam ta san me take ji a kan Sirleem kuma ganinsa da tai a yau yasa ta kasa yadda ma a duniya take. Hannu yasa aljihunsa ya ciro wallet dinsa ya ciro kudin da za su kai 5k ya mika mata, sai tai saurin girgiza kai.
“A a ni bana son kudi, na gode da ka kide ni, na gode na yafe maka”
Kai kawai ya kada mata daman kuma be jin zai iya kara ce mata wani abu tun da sai an yi magana da karfi zata ji, sai ya sara mata ya nufi motarsa ya bude ya shiga masu aikin daukarsa a hoto suna ta yi, da kallo ta bishi har ya tashi motar ya hau titi. Sannan ta mike tsaye ta saka hullar cikin hijabinta tana jin wani irin farinciki a ranta marar misaltuwa. Gaba daya ta manta da wani tunani da bacin rai, sai laleben hular dake kamshin turarensa take tana jan numfashi tana saukewa, yadda zata labartawa yan islamiyarsu da kawarta labarin yadda ta ga Sirleem yau kawai take tunani, har ta isa masarautar murmushi be gushe daga fuskarta ba, ji take kamar yanzu komai ya faru. Zancen wani haduwa da Iya da fargaban da take samunta idan zata shigo gidan duk ta manta sai murmushi kawai take tana jindadi a ranta. Door bell ta danna sannan ta samu guri ta zauna a gurin tana jiran a bude mata kofar, after like ten minutes aka bude kofar.
Mikewa tai tsaye sai tai arba da Iya hakan kuma ba karamin fadar mata da gaba yai ba, a take murmushin fuskarta ya gushe, Iya sai kallonta take irin kallon nan da ke nuna mata komai na jikinta har yadda jini yake gudana a jijiyarta, Falmata ta yi kasa da kanta ta saka cewa Iya ina kwana balle tace ta bata hanya ta wuce. Ba kallon bakinciki abun da ya faru kawai take mata ba har da na kurwarka dake ta yawa a saman kanta kamar fara, irin ta ce mai wuyar kamu, kurwar da ke yin kasa mai kamar hawainiya ita tafi saukin kamu sai kuma wacce take yawo a kasan kafafuwan mutum, wanda wani lokacin kasan kafafuwan mayu suke kallo su kama kurwar mutum. Akwai wance take kamar tantabara ita ma tana da wuyar kamu sai dai bata kai mai kamar fara ba wacce ke fira.
A take jikin Falmata ya fara wani tsamtsamtsam wanda hakan ke bata cewar ba mutumen arziki bace, a take ta fara karanta addu'o'in da ta iya, sai iya ta kauce mata da sauri tana mata alama da ta shigo da hannunta. Ita kuma tai saurin ficewa daga falon, sai da Falmata ta juya ta kalli ficewarta sannan ta juyo ta nufi hanyar dakinsu yan uku, tana ta mamakin yadda Iya ta rikirice saboda Addu'ar da tai.
‘Idan zan sake zuwa sai na samu furen tumfafiya na hada da goro na zauna’
Ta fada a ranta dan ta taba jin Tumba na fadar indai mutum yai haka yai arba da maye ba zai iya kallonsa ba. Yau ma bata tararda yaran ba, daman haka ya fi mata dan bata son tai wani abu ace ta yi ba daidai ba. For the first time yau tana ta ji tana sha'awar yin shara tana kirar suratul Baqara, surar da idan ka karanta shaidane sai yayi wata daya kamin ya sake shigowa gidanka, idan kuma ka karanta ayoyi goma na farkon surar a kullum, to kana cikin tsaron Allah babu wani abun da zai same ka, maita ko aljani ko wani shari kuma zaka wuni cikin nishadi.
Daga alif lam min ta fara karatun cikin muryarsa mai dadi da kwantar da hankali ga saukarda natsuwa kasancewar qur'ane take karatu, a yanayin yadda ta kare a kirar ma sai ka dauka wata balarabiya ce ba fulani ba. Har ta yi aikin ta gama karatunta take sai da ta gyara komai tsaf sannan ta fito ta janyo dakin ta rufe ta fito daga corridor, bata wani tsaya kula wadanda suke falon ba ta sa kai zata fice, sai Ammy ta kira wata mata dake zaune kasa tana kallon tv.
“Salamatu kira yarinyar can”
Jikin Salamatu na rawa ta kwalawa Falmata kira tana mikewa tsaye ta nufi inda take.
“Ke...
Falmata ta juyo a tsorace gabanta na faduwa, ita dai tsoron ta kar ace ta yi wani abu.
“Na'am”
Ta taho da sauri ta zube kasa ta gaishe da Ammy kamar yadda ta lura da mutanen gidan na yi, ko daga kai ta kalli Ammy bata yi saboda tsoron irin an talaka a gaban sarki. Sai ta karaso sannan Ammy ta yi murmushi kadan tana kallonta cike da burgewa, yadda ta ji tana karatun ya matukar burgeta ga natsuwa da kuzari aiki da take ganin kamar yarinyar tana da shi, ina ma ace Nanarta ce a haka.
“Duk abun da na ce ki rada mata a kunne”
“To ran ki ya dade”
Salamatu ta amsa, sai Ammy ta maida dubanta gurin tv kamar ba zata ce komai ba, ba dan komai ba sai dan isa da kasaita irin ta matan sarakuna musamman idan suna cikin talakawa. Falmata kan cikinta sai kadawa yake tana ta tunanin abun da tai ba daidai ba.
“Ya sunanki?”
Salamatu ta rada mata, sai Falmata tai saurin amsawa muryarta har rawa take kana jinta kasan tana daf da fashewa da kuka.
“Falmata”
“Shekarunki nawa?”
“Cikin ta sha bakwai”
“Kina zuwa makaranta?”
“Eh islamiya, bana boko”
“Saboda me?”
“Ba a saka mu ba”
Ko wace tambaya sai Ammy ta bada tazara take yinta kamar mai tunanin wace tambaya zata mata ko kuma mai hutawa sannan yai wata tambayar.
Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, daman can Falmata shi take jira sai ta tashi da sauri ta fice daga katon falon jikinta har rawa yake.
Sai da ta fice sannan Ammy ta kalli Salamatu.
“Tashi ki nemo min Gambo”
“To ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya da imani”
Da sauri Salamatu ta fice daga falon, ba a dauki lokaci ba sai ga Gambo ta shigo ta zube kasa ta kwashi gaisuwa.
“Gambo yarinyar nan da kika kawo tana da halin kwarai ko?”
“Wallahi ranki ya dade ba zan dauko sheri na kawo a cikin iyalanki ba, ina wace ni, Wallahi sai da na duba na dubo na zabo sannan na dauko ta, kaf a unguwar nan ba yarinya matashi kamar ita wacce tai kunya da tarbiyar Falmata, Allah ya mata natsuwa da kamala, ga ilmin kamar ruwa, sai dai ace ba tai boko ba amman na muhammadiya kam babu abun da bata sani ba”
Ammy ta yi shiru har na wani lokaci sannan ta ce.
“Ma-sha-Allah, ina son ki fadawa iyayenta za ta rika wuni nan tana rainon su Labib”
“To ranki ya dade, yadda kika ce haka za ayi, yanzu ma daga nan can zanje na isar musu da sakon Hajiya, Allah ya kara miki imani”
Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, sai ta mike da sauri ta fice.
*** *** ***
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya bayan Jarma ya gama yi mata bayanin salin inda garin yake, da kuma abokinsa da zai musu jaroganci.
“Jarma ina tunanin kai ya kamata ka fara zuwa, domin kai ka fada masa matsalar ta yarka ce, ganina zai iya gano wani abu, sannan ba zai yiyu na shirya tafiya a yanzu ba, kai ma kuma a nemeka a rasa cikin masarautar nan, za a fara zarginmu”
Jarma ya jinjina kai.
“Na yi wannan tunanin Hajiya, sai dai jin cewar ba a musu sako sai dai mutum yaje da kansa yasa dole ne mu yi tafiyar a tare”
Hajiya ta yi shiru na wani lokaci kamin ta kalleshi ta ce.
“Zuwana kamar zuwanka ne Jarma, domin bukatar da nake da ita ita ce a kanka, idan ka je ka ga guri sai mu shirya wata tafiyar daga ni sai kai mu tafi ba tare da abokin ka ba”
“Abokina amintaccena ne Hajiya karki samu damuwa da shi”
“Bana saurin yarda da mutane kai ma ka sani, kuma ka san Shattima a can yake aiki, zai iya ganinmu”
“Haba Hajiya ya za ayi mu yi saken da Shattima zai gan mu sai kace wasu yara dai?”
“Baka san gayyadar da Zainabu ta tara ba ne, shi kanshi ba dan sa ido ne lamurran gidan nan”
“Zan fara zuwan kamar yadda kika bukata, daman can na yi tunanin fara zuwa ni kadai”
“Haka yayi, ka karanta musu komai idan ka je, idan zai yiyu ka shirya tafiyar nan a cikin satin nan”
“Assabar din nan zan tafi In-Sha-Allah, Allah dai ya bamu nasara”
“Amin”
Hajiya ta amsa tana kashe ido daya. Hannunta ta kai ta dauko wayarta ta soma neman number Talba, ta san ko yana a gari ba saba shigowa ya gaishe ta ba kamar Sirleem amman rashin ganinsa kwana biyu yasa ta damu. Ring biyu ya daga, sai da suka gaisa sannan ta ce.
“Talba ina ka shiga kwana biyu?”
“Ina nan”
“Kwana biyu baka saka mahaifiyarka a ido ba, kuma hankalinka kwance”
“Hajiya idan wani abu ya same ki ai dole a sanar da ni, na san lafiyarki kalau ai”
“Kana da labarin dai za a daura auren Teema ko?”
“Yeah na sani”
“To kai nake son ka wakilci mai martaba”
Ya zare ido kamar tana gansa.
“Wane irin ni kuma Hajiya, kin san ban saba shiga irin abubuwan nan ba, kuma dai ga Baba Waziri ga Baba Jarma ga Shattima sai ace sai ni?”
“Yanzu ina son ka fara shiga, duniya ta san da kai, wannan umarni ne ba shawara ba, idan ka shigo zan mu tattauna akai ya kamata ka fara mika hannu ana yin komai da kai”
“Gaskiya Hajiya ba zan iya ba Wallahi ban saba wannan ba”
“Shiyasa na ke son ka saba din ai”
Ta kashe wayar bata ma tsaya jiran abunda zai fada ba. Idan ba tai da karfi ba, ba zata samu abun da take so ba, a komai sai Ammy ta tura danta ko'ina shi ake gani ita ba a san da nata dan ba, tana ganin yanzu ya kamata ta zage dange tai da gaske kar a mata yar gidan jiya.
*🐄🐄 FULANI 🐄🐄*
By Khadeeja Candy
*14*
Gaba daya ta koma kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da suka zo gidan Waziri haka take zama wata saliha, bata sakewa har sai sun bar gida, wannan karon kuma zuwan gaba daya tai dan bata san ranar komawarta ba.
Gashi nan tana jinta kamar tana gidan yari, domin yaran Baba Waziri basa fita ko'ina daga makaranta sai gida sai kuma wata hidimar idan ta tashi, gara ma a can masarautar tana iya yin karyar zuwa wani guri Ammy ta barta ko ta samu Sirleem ya fita da ita ko Hajiya Karama, nan fa? Gaba ta kasa sakewa ko breakfast bata fitowa ayi da ita kamar yadda aka saba yi tare da kowa sai ta shige cikin daki ta zauna ita kadai sai idan an kawo mata nata abun karyarwa haka ma da rana, gashi nan dole ne taje makaranta kuma school bus din da bata so ce take kai ta kullum ta dauko ta.
Gaba daya ta rasa yadda za tai, wata zuciyar na raya mata ta ari wayar wani ta kira Hajiya Babba ta fada mata dan ita kadai ta ke da tabbacin zata taimaka mata ta cireta daga wannan kangin.
Misalin karfe biyu da yan mintuna Motar Hajiya Karama ta shigo gidan, ta window Nana ta leka tana hangota ta sauka saman gadon da sauri ta fita a guje har tile din na kokarin zameta ta fadi. Zainab na kokari rufe motarta sai ga Nana ta fito da gudu ta zo ta rumgume ta, Zainab ta saka dariya tana cire gilashin idonta.
“You miss us right”
“Yes Hajiya Karama ki ce Ya Shattima am sorry kuma zan ce ma Ammy sorry pls ya maida ni gida”
Zainab ta taba kumatunta tana mata dariya.
“Shattima ma baya garin nan, ya koma aiki”
“Ni bana son nan Hajiya dan Allah”
“Dukanki suke?”
“No”
“Tau why? Kanen mahaifinki ne Nana yayansa kuma yan'uwanki ne, ni kaina idan na gaji da zaman gidan can wani lokacin a nan nake zuwa na kwana biyu sannan na koma, a gida nan ma ina da gata komai kike so za ayi miki, komai kike so shi zaki ci to miye matsalar ki Nana?”
“Ba a zuwa ko'ina kuma dole sai an je school both islamiya and boko”
Zainab ta rika fuskarta.
“Can baya na san kina son makaranta yanzu miyasa ba ki so?”
“Ni dai bana so kuma, kuma.... Ni bana son na gama bokon saboda kar na auri Sirleem”
Kyalkyalewa Zainab tai da dariya.
“Saboda ba ki son Sirleem sai ki lalata karatunki? To idan ba ki son zuwa makaranta ai sai ya ce ayi muku auren da wuri, Nana ki kwantar da hankalinki idan ba ki son babu dole ki bada lokaci kawai zan yi supporting din ki na hana auren Sirleem”
Nana ta zare ido.
“Har da Hajiya Babba ma za ta goya min baya ko? Shikenan ma na huta”
“Ya za ayi Hajiya ta goyi bayanki, ki ki auren danta na cikinta? Ke har yanzu ba ki da wayo?”
“Ai tana so na”
“Amman ta fi son danta dake, ki daina wannan tunanin, yanzu dai zuwa nai na ganki kuma na dauke ki muje mu sha ice cream dan san kina so”
“Yes yes, amman kina shiga cikin gidan nan Hajiya Maryam ba zata bari ba, zata ce Baba Waziri yace kar na je ko'ina”
“Okay je ki dauko veil ko hula mu je”
Da gudu Nana ta juya ta koma dakinta dake cikin gidan ta dauko wani karamin veil ta saka a kanta, ko da ta fito har Zainab ta yi reverse ta bude nata front seat. Da sauri ta shiga Zainab ta fara tukin tana kai hannunta ta dauki kwakwarda ke gefenta ta ci sai kuma ta dauko wata ta mikawa Nana, ita kuma ta karba ta fara ci, tafiyar ta su ba tai nisa ba Nana ta hango AA tsaye kusa da wani gida mai karamar kofa yana waya.
“Hajiya tsaya tsaya tsaya....”
Da sauri Zainab ta taka burki ganin yadda Nana ke kokarin tsayar da ita kamar ta ga wani abu. Sai da Zainab ta faka motar sannan ta bude ta fita, AA na hangota ya yanke wayar da yake tana kallonta gabansa sai faduwa yake, wata zuciyar na raya masa cewar ya gudu, ko kuma ya shige cikin gidan ya boya. Wata kuma na ce masa ya daure, dan murmushi da Shaukin da ya hango a fuskar Nana yasa ya dan ji kwarin guiwar tsayawar.
“AA AA”
Ta fada tana jin kamar ta rumgume shi. Shi kuma ya kasa amsawa sai kallon motar da ta fito yake, sai da Zainab ta sauke gilashin motar ya ga macece sannan hankalinsa ya dan kwanta.
“Me kika zo yi nan? Waya ce miki ina nan? Biyoni kika yi?”
“A a ba mu fita ni da Hajiya Karama shine na hango ka na ce ta tsaya”
Ta fada tana kara matsawa kusa da shi kamar ta rumgume shi wani irin shauki take ji idan ta ganshi.
“Nan ne unguwar ku?”
Ya tambaya yana zaro ido wata zuciyar na ce masa ashe baka tsira ba.
“A a nan gidan aka kawo nan dai, wai bana jin magana shine za min horo”
“Kamar ya?”
“Wai saboda gidan ba a zuwa ko'ina kuma dole aje school, shiyasa aka kawo nan”
“Wane gida?”
“Wacan gidan mai Ash da white paint”
Kai tsaye ya san gidan Waziri take nufi, baki sake ya ce.
“Gidan Waziri?”
Ta gyada masa kai.
“Ya kike da shi?”
Shiru tai tana kallonsa sai kuma ta fara dariya.
“Ina ruwanka kai me kake a unguwar?”
Ya dan shafa kansa yana