Showing 84001 words to 87000 words out of 286946 words

Chapter 29 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

958

yi dake, ni da na dauke ki kamar Mamana ina tunanin komai ke zaki min ko tufafi zaki iya siyamin amman sai fara saka min da wannan, yanzu fa ma yunwa nake ji”

“Karka sake ce min Nana Hajiya”

“Indai kina son na rika ce miki Hajiya sai dai ki biya”

Da sauri Nana ta kalleshi ta cikin madubi.

“Eh lallai kai baka ma da wayo, ai wanda ya dauke ka aiki ka zama yaronsa”

“Eh amman ai idan mutum yana aiki a gidan masu kudi gata ake masa, balle ke Nana da kike yar gata ina jin kamar ke dai aka haifa ko?”

“Ban sani ba, kai ka cika gulma da tambaya”

Murmushi yai be sake ce mata komai ba.

“Ni bani da kudi yanzu kuma karka kai ni school ma fada maka”

Ta fada ganin ya dauki hanyar makaranta har suna kusan isa.

“Miyasa baki son makaranta Hajiyata?”

“Haka nan dai bana so?”

“Wani abu ake miki a makarantar ne?”

“Ba abunda ake min bana son zuwa dai sai na rika jin kamar zan yi kuka bana son school ni”

Juyowa yai ya kalleta ta wani hade rai ta turo baki kamar zatai kuka.





FADIME POV

Tun cikin dare ta labartawa Inna wanda ya zo yai mata juyen gida.

“Inna na fara farinjini ko?”

Inna dai bata ce mata komai ba sai kallonta take da fitilar kwan dake haskata.

“Kina jin wani ciwo?”

“Aa”

“To ki yi addu'a kije ki kwanta”

“To Inna ki min addu'a ni wuya take bani har na manta da wasu addu'oin ma”

“To yayi kyau”

Ta mike tsaye ta dauki kyandir daya ta kunna ta nufi bukkarsu, tana shiga ta dauko littafinta ta fara rubuta abubuwan da suka faru sannan ta aje ta kwanta ba tare da tayi addu'ar ba. Can cikin dare ta fara jin ana wasa da bukkar ta fara ihunta kamar yadda ta saba tana kiran Bapppa sai da ya taso ya shigar da ita bukkarsu sannan aka samu zaman lafiya.
Washe gari sai ta farka cikin jindadi abubuwa biyu, Amo zata je da ita birni a yau kuma jiya an mata juye ta fara farin jini kenan, ko karyawa ba tai ba taje gidansu kawarta Ma'u ta labarta mata abunda ya faru jiya da dare sai wani shauki take yana jindadi. Sai da hantsi ya fito sosai ta dawo gida ta sha kokon da Inna da dama, ta dauki tulu zata je deban ruwa.

“Fulani ki kula kin san kullum kika je sai wani abu ya faru ko?”

“Aa zan yi addu'a babu abun da zai faru”

“To Allah ya tsare”

“Amin”

Ta kallame tulun ta bi hanyar, kana ganinta kasan tana cikin nishadi domin farincikinta ya kasa boyuwa sai far'a take. A maimakon ta isa gurin ruwa kai tsaye inda wasu yan mata biyu suke deba sai ta nufi gurin duwatsun kamar ta san Wasim na tsaye a gurin yana jiranta, tana hangoshi ta karaso kusa da shi da sauri tana murmushi.

“Kai dai jiya... An tashi lafiya dai”

Har ta fara bashi labari sai kuma ta tuna cewar bata gaisheshi ba, wani zancen bata kaunarsa na abun da yai mata duk ya kau saboda farincikin an mata juye.

“Lafiya kalau”

Ya amsa yana kallon cikin idonta kamar zai cinyeta.

“Jiya wani yai min juye”

Yayi murmushi har lokacin kallonta yake wani irin mayen kallo da yake saka shi nishadi da annashuwa, tana matukar burgeshi gashi yadda take abubuwanta tana saka shi nishadi.

“Kin jindadi?”

“Eh sosai mana, sosai ma ai na fara farin jini a haka kenan ko?”

Ya gyada mata kai yana murmushi.

“Kila son ki yake”

Ta yi dariya.

“Amman ai ina da miji dan birni”

“Idan shi ma dan birni ne fa”

“Aa dan kauye ne”

“To idan wacan ba mijinki ba ne fa?”

“Ai zan taba hannunsa na ji ko da sanyi, taba ni na ji”

Ta karasa tana mika masa tafin hannunta dake bude, kallon hannun yai ya sake kallonta.

“Idan na taba ba kiji sanyi ba fa?”

“Shikenan”

“Aa ba shikenan ba, ba zan hakura ba”

“Kamar ya?”

Ta tambaya da dariya dan bata gane nufinsa ba. Sai ya lakaci hancinta yana murmushinsa mai kyau.

“Kamar haka”

Ta taba hancin tana dariya, dariyarta ce tasa ya kara fadada murmushinsa yana kallonta cike da burgewa.

“Je ki debi ruwanki, zan je garin mu sai anjima”

“To Bye Bye good bye”

Ta daga masa hannu sannan ta juya da tulun ta nufi gurin ruwan ta fara deba. Ba laifi ta dibi ruwan da dan yawa ba ta kai gida, tana shiga Amo na shigowa gidan rike da kwayar da ta aro makota.

“Fulani ina kika fito?”

“Ruwa na debo”

“To tahi ki sirya yanzu zamu tafi”

Ta fada cikin rashin jindadin rashin sani zata tafi deban ruwa da sai tabi bayanta ta ga abunda take a dajin, amman ai akwai gaba bayan deban ruwa tana zuwa kiwo ai, ya ma fi dadi shi da take zuwa da yamma.
Ko da goma tai Fadime ta shirya cikin atamfarta ta karamar sallah ta saka yello Hijab ta fito da sauri domin Amo na waje tana jiranta. Inna dake aikin kirbin dawo (fura) a tsakar gidan ta kalli Amo cikin rashin jindadi tace

“Amman Malam be ce aje da ita ba Amo”

“Haba dai Inna Fadime yanzu tafiyar zuwa birni sai an fada masa? Ai cikin hikima zaki ce masa rakiyata tai ba sai an fada masa abun da zai kai mu ba”

“To Allah ya dai ya tsare, Fulani ki yi addu'a”

Amo ta kalli Inna da sauri ta rufe ta da fada.

“Kamar ya tai addu'a sai kace wanda zai je gurin mugun abu, idan baki yarda da zuwanta ba tai zamanta a gida, daga ina nema mata abokin rayuwa sai abu ya zama matsala”

“Amo addu'a ai tana da kyau ga musulmi ba dan fatan wani abu ya faru ba”

“Ke wuce muje”

Fadime ta fice da sauri Amo ta bi bayanta, Inna ta bisu da kallo tana addu'ar Allah ya tsare mata yarta, bata son zuwan a ganinta be dece ma ace an tafi da ita ba wai dan wanda ke sonta ya ganta abun be ma bada kala ba kuma ba al'adarsu ba ce.

Tafiyar awa daya da mintuna arba'in a mota suka iso ciki gari, Amo bata fita daga motar ba sai da ta laso kurwar macen dake kusa da ita ta nade a zane sannan suka fito ita da Fadime suka kama hanyar gari. Sai da ta fara biyawa ta guraren da take sayarda danyen manshanunta sannan suka shiga cikin tsakiyar garin, Fadime har ta fara gajiya dan bata saba da tafiya mai nisa ba, ko a kauyensu idan Inna ta aike ta nesa bata zuwa dan bata saba dogon yawa ba, gashi rana sai dukansu take yar hodar da ta shafa ma duk ta goge.

“Ni dai na fara gajiya”

“Ai mun kusa isa, bari na shiga gida nan”

Fadime ba dan ranta ya so ba ta bi bayanta suka nufi wani madaidaicin gida Amo ta kwankwasa, yaron gidan ya fara bude gidan ya leko.

“Waye?”

“Fadawa Innanka tana siyen manshanu”

Yana juyawa Amo ta laso kurwar yaron, a maimakon ta saka ta a zanenta ta kulle ko a jakar kudinta ko ta jimketa a hannu sai ta duka ta saka ta a karkashin kafarta gashi talkamin ya dauki zafi, aiko yaro kan ya karasa ya fadi tsakar gidan ya fara birgima yana rike kai. Mahaifiyarsa ta fito da sauri tana tambayar ba'asi, kamin ya leko waje ta ga Amo tsaye tana lasar baki.

“Hajiya kina siyen mansanu?”

Aljanun da suke kan matar sun fi karfin na Amo, a take jikinta ya bata cewar Amo manya ce, kamin tai wani unkuri aljannun suka fara takawa kanta suna kokarin riko Amo.

“Sake masa kurwarsa”

Kamin Amo ta kuce daga rikon matar Fadime har ta cire talkaminta tana shirin gudu, Amo ta juyo da sauri da zimmar gudu mata ta biyota kanta babu ko dankwali tana fadin.

“Sake masa kurwarsa”

Mazan dake unguwar suka taso da sauri suka nufo inda Amo take wasu na fadin matar musa police ce miya faru, ita kuma bata fasa fadin abunda take fada ba, sai kuma ta fadi ta birkice tana ihu aljanun suka taso da gasken gaske, a take wani makocinsu ya daga waya ya kira mijinta ya fada masa abunda ke faruwa.

“Daga na kwankwasa kofar gidan yaro ya leko nace ya fada mata tana siyen mansanu sai kawai ta leko wai na sake masa kurwarsa”

Amo na gama magana wani saurayi ya dauke ta da mari.

“Irin ku ne masu shigowa cikin gari kuma maita ko?”

Ba kadan taji zafin marin ba, amman karfi hali irin na maita ba zai barta ta nuna ba, kuma ba tai niyar sakin kurwarba. Fadime dake tsaye gefe ta shafa fuskarta tana jin kamar ita aka mara, ga mutane maza da mata sai fadi suke matar Musa Police ce, gudun kar ace tare suke yasa Fadime ta fadi a gurin ta fara karyar aljanu tana birkice ido.

“Ta kamani ta kamani Wayyo kurwata”

Wasu maza suka nufita ta sauri suka dauko ta suka aje karkashin wani ice sannan aka dauko yaron daya ki dawowa hayyacinsa suka aje kusa da Fadime, suka dauko itace dayan ya bugawa Amo a kafa.

“Tsallaka su sai kin tsallaka su, ko mu kashe ki Wallahi”

Amo mamakin abun da Fadime tai mata ya fi na abun da mutanen suka mata, a dolen dole suka cilastata ta cire tufafin jikinta ta koma daga ita sai vest da under skirt, ta ware kafafuwanta ta tsalaka yaron ba tare da ta taba shi ba, domin idan taba shi kurwar ba zata dawo ba, amman idan bata taba shi ba kurwar duk inda take a jikinta zata fado kasa ta shige jikin mai ita.

Tsallaka uku tai ma yaro sai ya mike tsaye kamar a firgice yana neman mahaifiyarsa, sannan aka cilastata ta tsallaka Fadime, ita ma uku tai mata sannan Fadime ta mike tsaye ta fara neman talkaminta da ta saki.

“Ina talkami gida zanje?”

“Zaki iya tafiya?”

“Eh”

“Ina ta hadu dake? ”

“Kan hanya tace na zo na nemo mata canji”

A nan mutane suka saka salati ana ta nanata maganar, daman masu manyan wayoyi tuni suka fara dauka, mazan nan duka hau dukan Amo kamar an aikosu amman ko alamar hawaye babu a idonta balle tai kuka idonta ne dai suka kara rinewa da ja, sai kallon mutumen da ya mareta da farko take tana jin zafin marin har yanzu.

Fadime na daukar talkaminta ta mike hanya, ba dan tasan inda zata ba ita dai burinta ya cika tun da ba agano tare suke ba, har da hadawa da gudu sai wagen bayanta take har ta kawo titi tana kokari karya kwana wata farar mota mai bakin gilashi ta dan bugeta kadan, abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa sai kawai ta fadi a gurin tana ihun kafarta.


SHATTIMA POV.

Yana kallon wayar tana ringing kamar ba zai daga ba, har sai da ta kusa yankewa sannan ya danna picking ya saka a speaker.

“Hello Shattima ina airport”

Jimmm yai kamar be ji abun da Zainab take fada ba sannan ya mike tsaye rike da kofin lemun tsakin.

“Gani nan zuwa”

Ya nufi kitchen ya aje kofin, sannan ya dawo dakin ya dauki wayar ya kira Ra'ees, bugu daya ya dauka domin ya san Shattima be son jira.

“Takardun suna hannunka ne?”

“Yeah gani tare da su”

“Zan biyo yanzu na karba”

Ya saka wayar aljihu ba tare da ya kashe ba, sannan ya dauki keys dinsa ya fice. Yana saukowa kasa ya shiga farar motarsa dake fake a gurin ya danna horn kamin ya isa gate har mai gadin ya bude masa gate. Kai tsaye ya nufi unguwarsu Hajiya Asiya yayar Ra'ess dan karbar takardun a hannun kanenta kuma amininsa. Kadan kadan yake tukin amman hakan bd hana shi bugun wata matashiyar yariyar ba, wacce ke sanye da atamfa da yellon Hijab, gilashin motarsa ya sauke yana jin ihunta tana fadin kafarta, kamin yai wani unkuri har ta mike tsaye ta nufo inda yake cikin masifa

“Kai baka ga ka kade mutum ba?”

Ido ya sakar mata yana ta kallonta da mamaki, ya kasa cewa komai yarinyar da za a kade imlndai har da gaske ta ji ciwo ai ba zata iya tasowa tace masa ya kadeta ba.

“Wayyo kafata”

Ta fada da kuka shi kam kallonta kawai yake kamar dan kallonta kawai akai shi.

“Ko kurma ne kai baka magana”

“Ina yi”

Ya amsa ta yana lumshe ido ya bude, sai da ya amsata sai ta ji kamar ba shi ba, because be cika magana any how ba duk kuwa da kasancewar kadeta yai. Samun kansa yai da bude motar ya fito ya duka yana kallon kafarta.

“Ciwo sosai”

Ta fada kamar zata yi kuka, kansa ya daga ya kalleta.

“Muje na kai ki asibiti?”

“Ko ba kai ni asibiti ba ka siya min kaza da yoghurt kawai sai ka bani kudin mota ko ka kai ni garin mu dan Allah”

Ta fada tana hade hannayenta alamar rokonsa take, sai ya mike tsaye yana gyada mata kai, ya kai hannunsa ya bude mata gidan baya sai ta shiga da sauri.

“Na gode”

Ya rufe sannan ya shiga yaja motar zuwa gate din su Hajiya Asiya, sannan ya ciro wayarsa ya tura masa Ra'ees sako cewar yana waje.

“Mu nan da muka zo ban san kowa ba, gurin wani muka zo”

Fadime ta fada masa ba tare da ya tambaye ta, kallonta yai ta madubin gaba be ce komai ba, kuma daman ba zai ce din ba tun da surutu be sha masa kai ba. Fadime na hakimce cikin motar ta hango Ra'ees ya fito a gate din dake gabansu. Ba shiri ta gwalo ido waje.

“Laaaaa Wallahi shine shi ne wanda muka zo nema”

Ta fada cikin wani irin jindadi tana dan kare fuskarta. Nan ma dai Shattima kallonta kawai yai. Ra'ees na isowa ya bude motar ya shiga ya zauna ya ja ganbun ya rufe yana mikawa Shattima takardu yana masa bayani, sai Fadime tai dan tari kadan shi kuma ya juya ya suna hada ido ta sakar masa murmushi, a take yaji mararsa ta cika da fitsari.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un dan Allah ki yi hakuri na jawa kaina bala'i”

Gaba daya kallon aljana yake mata, ganinta a motar Shattima, bayan yasan Shattima be taba saninta ba, a iya tunaninsa shi kadai yake ganinta ma. Hakuri da ya bawa Fadime sai ta ga kamar yana nufin tai hakuri ba zai aureta ba, sai kawai ta fashe da kuka, nan shi ma ya saka kuka.

“Wayyo Allah dan Allah ki yi hakuri ki yi shiru”


Wani irin rawa jikinsa yake yana jin cewar ya saka aljana kuka. Ita ma kukan take shi kuka ita kuka. Shattima kasa hade dariyarsa yai har sai da ya dora kansa kan sitarin motar tsakar dariyar da ta cika masa ciki.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660 *


23

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

Shattima kasa hade dariyarsa yai har sai da ya bude motar ya fita ya jingina da motar ya rike cikinsa. Fitar Shattima ce tasa Ra'ees ya hankalto da ya bude motar ya fita shi ma, kamar kyaftawar ido haka ya fice daga motar ya rufe, sai kuma yai tsaye ya kasa tafiya, gaba daya gani yake kamar mafarki yake, taya yarinyar dake kauye zata shiga a motar Shattima? Bayan kuma Shattima be santa ba?
Dariyar da Shattima yake ne yasa shi dawowa hayyacinsa har ya kalli Shattima da shi kansa zai iya rantsuwa be taba ganin dariyarsa kamar haka ba. Shi kan sam be ga abun dariya ba dan ya san me ya ji a lokacin da yake je kauye kuma ya san abun da ya gani a yanzu, a tunaninsa Shattima yana masa dariya ne saboda ya fashe da kuka ba tare da dalili ba, dan a iya tunaninsa shi kadai yai arba da Fadime a gidan baya.

“Man this is not funny, ni na san me na gani Wallahi, kuma na san me na ji”

Ya fada muryarsa na rawa, can dai ya ji kamar be gansu ba ya fara karanto ayatul kursiyu ya shafa ma kansa zuciyarsa sai bugawa take da karfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito.

‘Ba dan dai aljanu suna da cuta ba, ai ba wani abun nai mata ba, neman aure kawai naje kuma bama nawa ba, rabon ayi, shine kuma zata rika bina ina ganinta why? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’

Cikin ransa yake ta wannan sake saken yana jin kamar ya zuba da gudu ya shige gida ya bar Shattima a gurin.

“Ra'ees ban tab daukar tsoron ka ya kai haka ba”

Shattima ya fada har lokacin dariya yake, ban ya wacce yai har ta soma saka masa tari.

“Ba zaka gane ba ne Wallahi.... Ka ga me na gani wai?”

Ya fada yana zare ido kamar zasu fito tsabar tsoro.

“Ba yarinya ba ce?”

“Ka ganta kai ma?”

Ra'ees ya tambaya yana wani zuro kai, dan ya tabbatar idan da gaske Shattima ne ko kuma aljanun ne suka sake masa siffar Shattima, daman can Ra'ees matsoraci ne sai dai yanzu abun ya fi kamashi, domin be taba jin mutum da muryar saniya ba sai da yaje garinsu Fadime. Shattima sai da yai da gaske sannan ya iya gintse dariyarsa.

“Easy Ra'ess wannan yarinyar nemanka ta zo”

Ra'ees ya ji kamar ba shi ne ba, wani sanyi ya taso tun daga kan dan yatsan kafarsa har cikin kansa, ya share fuskarsa yana ta faman haki kamar wanda yai gudu ya gaji.

“Ni abun da nake son na gane, kai ma ka ganta ne ko ni kadai na ganta? Me zai kawota a motarka? Shattima wai kai ne dai?”

Shattima ya daga kansa sama yana kallon hadarin dake haduwa a garin yana murmushi wani iska mai dadi na shiga ta hancinsa.

“Yanzu nan na hadu da ita, kadeta nai my mistake”

Ya fada bayan ya sauke kansa. Be da bukatar yai masa dogon bayani domin ya fahimci Ra'ees be shirya saurarensa a yanzu ba, kallo daya zaka masa ka karanci irin tsoro da tashin hankalin dake tare da shi. Sai kawai ya koma cikin motarsa ya rufe gambu, Ra'ees dan dukowa yai ya leka cikin motar a lokacin kan Fadime na cikin Hijabin tama kuka kamar wacce akai wa mutuwa. Da sauri ya dauke kai ya matsa jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login