Showing 144001 words to 147000 words out of 286946 words

Chapter 49 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

956

alaka da lalata min aiki? Wai ko dai Jarma ya bata ni a gurinku ne?”

“Karki saka mana wasa a nan! Kin zo da bukata kuma an fada miki gaskiya, sai kuma ko kawo shakku? Kin san inda kike kuwa?”

Wannan karon mai fassarar ne yai maganar yana dakawa Hajiya tsawa, tun kamin bokan ya fadi komai. Hajiya ta natsu ba dan ta rasa abun fada ba sai dan tana tsiron kar a mata wata illar, tun a gurin zuciyarta ta fara yi mata kwankwanto.

Bokan ya jimke empty hannunsa, yana budewa sai ha wani kullin magani. Ya mikawa mutumen, shi kuma ya mikawa Hajiya Talatu.

“Ki ba yarki wannan magani da ci da nama, in har matar da take kudirin kasheta ta ci ta, to ta ci mutuwa”

Hajiya Talatu ta mika hannu ta karba da mamaki.

“Wace mata ce?”

“A masarautarku take, tana nan tare da ku, yanzu haka kurwar Maijidda tana hannunta, ba Maijidda kadai ba har da Mai Martaba da yayan Shattima biyu”

Wannan karon Hajiya Babba ce take masa kallon mamaki.

“Wacece ita kuma? Daga ina take? Me muka mata?”

“Ba ku mata komai ba, ita ma tana da burin Sarautar ne kamar ku, abu n karshe da zan fada miki shi ne ga tafiya nan da babu dawowa”

Hajiya Talatu da Hajiya Babba suka kalli juna kamin Hajiya Babba tace.

“Wa kuma zai yi tafiyar? Yaushe za ayi tafiyar?”

Be ce mata komai ba, ya buga ruwan dake cikin kwarya a gabansa.

“Ki aje mana kudin aikinmu, kudin dabba zaki aje, wacan ma ta aje mana kudin dabbar mu”

“Yanzu babu wani taimako za a iya min kenan? Ku taimaka min mana haba”

Cewar Hajiya tana kokarin fashewa da kuka, domin a maimakon ta samu warakar ciwonta sa aka kara daɓa mata wuka a ciwon, abubuwan daya fada mata sun saka tana jin kamar ta haukace, domin a ganinta tayi tafiyar banza ne, tun daga Yola har Katsina gashi babu biyan bukata. A dolenta ta aje masa kudin sa 100k ta fita Hajiya Talatu kuma ta aje masa 120k har suka bar dakin Jurry bata ce uffan ba, kamar wacce aka daurewa baki.
Bayan sun fita Wasim ya kalli Kakansa yace.

“Miyasa zaka musu aiki bayan kace zai taba yarinyar? Gashi ka ba dayar magani?”

“Wasim Rau... Kai kadai nake da shi a matsayin jika, ba zan yi abun da zai taba farincikinka ba, idan har ban bata maganin mutuwa ba, tabbas bayan yarta wannan yarinyar ce a ta biyu, domin ita kadai take da irin tsafinmu, wanda zata iya kama kurwar yarinyar nan, saboda bata da tsaro”

Wasim ya sake kallon Fadime da mamaki, Fadime na ganin haka ta saka kuka.

“Ni dai na ba ni yau? Ko dai ni ce suke cewa?”

“Ina masa magana ne a kan yadda za ayi a fitar da ke daga nan ne?”

Wasim ya fada mata a kokarinsa na kwantar mata da hankali.

“Okay tau, ayi sauri ku cigaba da maganar, daman babu kyau mace da namiji suna kebewa a daki daya haramun ne a addininmu”

“To da muka kebe me muka yi?”

Ya fada yana daga mata gira.

“Ai mu ba yan iska ba ne ba zamu yi komai ba, amman dai ya kamata na je gida wata kila ma Baba ya dauka kona mutu”

Wasim be ce mata komai ba, sai kallonta yake yana murmushi, ta dayan bangaren kuma yana mamakin yadda wata alaka zata shiga tsakaninta da wadannan mutanen. Hannunsa ya kai ya shafa fuskarta.

“Zan maida ke gida ki kwantar da hankalinki”

“Tau”

Ta amsa masa tana kallon cikin idonsa.

“Baka fada min yadda alaka zata shiga tsakaninta da su ba?”

Wasim ya fada da yarensu yana ba tare daya kalli kakansa ba si cigaba da kallon Fadime yake, sosai yake jin idan wani abu ya same ta ba zai yafewa kowa ba.

“Idan wani ya taba ta, ba zan raga masa ba, ba zan saurari kowa ba”

Ya sake fada sai dai wannan karon yana kallon Kakansa. A nan ma kakan be ce masa komai ba.

“Gobe zan maida ita gida bana son wani abu ya sameta”

“Ba zamu sake yarda ka sake nisa da mu ba, ba zamu yarda ka dauki wata al'ada da dabi'u kamar wacan karon ba”

Shine abun da kakan ya fada masa da yarensa.

“Wacan karon ra'ayin Iya na bi, wannan karon kuma ra'ayin kaina zan bi, ba zan yarda wani abu ya taba yarinyar nan ba”

A nan ma kakan be sake ce masa komai ba, Wasim ya mike tsaye yana rika wuyan hannun Fadime, ko sau daya be tana mantawa ya rika tafin hannunta ba.

“Zo muje waje ki sha iska”

“Kuma ina son nai sallah yanzu anyi la'asar ko?”

“Eh”

Ya amsa mata tare da jan hannun nata suka fice, bayan dakin ya zagaya da ita inda ruwa suke tai alwala daman a nan da saba yin alwalarta, idan ta gama sai ya dauko mata wani babban mayafin da suke rufa da shi ta nade jikinta ta yi sallah, mutanen dake harabar gurin sai su yi ta kallonta suna ganin ta yi wani abu na dabam.



FALMATA POV.

Da yammar ranar Momy ta saka mai gadinta ya nemowa Falmata Napep tai jinga da shi akan nawa zai rika kaita kullum yana daukota ya fada mata, tun a ranar ya fara aikinsa domin shi ya maida Falmata gida a ranar, tun 8pm ta koma gida ba kamar yadda Shattima yace sai 10pm zata rika komawa gida ba. Da sallama ta shiga cikin gidan, Umma ta amsa mata sama sama.

“Tau kin ma huta mika mata bokitin ta dauko ruwan”

Naja ta jefa mata bokitin, sai Falmata ta kai hannu ta dauka ta juya ba tare da ta shiga dakin ba. Kai tsaye ta nufi gurin fanfon bohore din tana ta tunanin abun da Sirleem yai mata a yau. Kamar daga sama ta ji an dabata, tana juyowa sai tai arba da kawarta Khadija, da sauri Falmata ta rumgume ta.

“Khadija oyoyo”

“Hmmm amarya kin yi wuyar gani”

Khadija ta rada mata a kunne sanin lalurar kawarta.

“Amarya kuma? Aiki ne baya barina zama kullum idan na fita 7 bana dawowa sai 9 yau ma saboda na samu matsala ne shiyasa na dawo da wuri...”

A natse Falmata ta labartawa Khadija abun da ya faru da kuma irin taimakon da Sirleem yai mata.

“Wai da gaske Sirleem din dana sani Falmata?”

“Wallahi shi”

“Allah sarki Allah ya saka masa da alheri, shekaran jiya aka kawo mana chewing gum dinki an rana a unguwa amman ke baki ba mu na ki ba”

“Cingan dina kuma?”

“Eh”

Khadija ta daga mata kai.

“Ni aka ce kuma?”

“Naja fa ta kai mana shi, aka ce naki ne amman tace auren ba yanzu sai kaka ta yi”

“Auren wa?”

“Na ki”

“Ni...?”

Ta sake nuna kanta.

“Ni ban yi maganar aure da kowa ba ba a fada min komai ba”

“Wai da gaske kika? To Wallahi an raba cingan din aurenki yau kwana biyu”

Khadija ta fada da mamaki. Take idon Falmata ya cika da kwalla.

“Baba be fada min komai ba, Umma ma bata ce min, kuma ni ban yi maganar aure da kowa ba, taya za a bada aurena ban sani ba?”

Ta fashe da kuka.

“Ko dai ba ni aka ce ba?”

Ta sake tambaya.

“Idan kinje gida ki sake tambaya, amman tabbas ke aka ce, sai dai idan baki sani ba”

“To wa aka ce za a aura min?”

“Ke da zaki aure shi baki sani ba balle mu da aka bawa minti, idan kin je gida ki tambaya”

Da sauri Falmata ta share hawayenta ta dauki bokinta ta watsa da gudu fanfon, ta ci sa'a babu mutane sosai, nan da nan ta cika bokinta ta dauka ta dora a akai, bata ko lura da kawayenta dake bakin fanfon ba suna mata magana, tana tafiya hawaye na mata zuba, ruwa data debo na zuba, kamin ta isa gida har ta matsu. Bata ko yi sallama ba ta fada cikin gidan ta sauke bokinta, bata yarda da juyo ba sai da ta share hawayenta, sai kuma ta rasa wa zata tambaya tsakanin Tumba da Naja, me zata ce? Guri ta samu saman tabarmar da Naja take zaune ta zauna tana da kokarin gintse kukanta, sai da Tumba ta shiga daki sannan Falmata ta kara matsawa kusa da Naja.

“Naja wai da gaske an raba minti aurena?”

Naja ta kalleta tana kyalkyalewa da dariya.

“Eh mana, Baba ya miki miji wani tsoho mai hurhura”

“Tsoho kuma?”

Falmata ta dafa kirjinta tana jin wani sabon kuka na zo mata.

“Yaushe? Ni ban tana zance da wani tsoho ba”

“To shi ya ganki ya zo yai magana da Baba akan yana son ki, kuma Baba ya bashi dan ya kawo minti tun shekaranjiya an raba, ai yau zaki ganshi tun da kin dawo da wuri”

“Da gaske dan Allah Naja?”

“To karya zan miki? Tambayi Umma ki ji”

Ta karasa tana mata dariyar mugunta, kamar hadin baki sai ga yaro yai sallama yana fadin.

“Wani tsoho yace yana sallama da Falmata”

Falmata ta juya da sauri ta kalli yaron, kamin ya juyo da sauri ta kalli Umma kamar wacce ta rude.

“Je kace gata nan zuwa, yau kam ya taki sa'a ai”

Falmata ta lumshe ido sai hawaye masu zafi suka hau mata zuba.

“Tashi kije ana sallama dake a waje, idan kin dawo ki zo na fada miki sakon Malam”

Kamar an dasata a gurin haka ta ji, ta kasa motsawa sai hawaye take. Can kuma ta mike tsaye ta saka talkaminta tana jin kafafuwanta na mata mugun nauyi. Kadan kadan take tafiyar kamar wacce aka cewa ida ta leka waje wani abun tsoro zata gani. A hankali ta nasa kafarta waje ta fara kallon damanta kamin ta kalli hagunta sai ganin tsoho tai sanye da manyan kaya rike da yar leda, gulob din su na waje na haska shi kasancewar akwai wutar nepa. Gaba daya furfura ta rufe masa fuska har baka iya shaidar yadda kamaninsa suke, ga wani baki a hannunsa da jikinsa da fuskarsa kamar na dauda.

“Wayyo Allah... Wayyo Allah...”

Falmata ta fada tana rabawa jikin ginin tana kuka.

“Lafiya dai?”

Ya tambaya da shakakkar muryarsa yana dan lekota. Ita kam bata ji me ya fada ba ma, sai rare kukanta take a hankali ga shi daman kunnuwan ba lafiya ne da su a balle ta ce taji abun da yake fada. Ban da kuka babu abun da Falmata take, tun yana tsaye har ya gaji ya zauna a timitin dake kofar gidansu, can kuma ya ciro wata tsohuwar dari biyu ya mika nata tare da ledar hannunsa.

“Ga wannan ki shiga da shi ciki”

Falmata ta kasa karba kuma ta kasa daina barin kukan ta kuma kasa barin gurin, risinawa yai kasa ya aje mata ledar.

“Mu kwana lafiya, zan yi magana da mahaifinki”

Binsa tai da kallo har ya karya kwana sannan ta juya ta shiga cikin gidan ba tare data dauki kayan ba. Gaban Tumba taje ta risina tana kuka.

“Umma me na muku? Me na muku zaku bani tsoho? Me nai”

“Ke...! Muma a matsayin iyayenki mun miki zabi na gari har kika tambayar mu? A yadda kike yar kurmar nan wa zai aureki? Dan kin samu ma tsohon yace yana so? Duk masu zuwa gurinki ba da gaske suke ba, da sun turo, amman shi yana zuwa yasa aka kirani ya fayyace min komai, kuma ya nuna da gaske aurenki zai yi, shiyasa na fadawa Mahaifinki kuma ya aminci, na san daman irin wannan fitsarar za ki yi shiyasa na hana mahaifinki ma ya ji ta bakinki, yanzu dai an raba cingan shaidar an tsayar miki da miji, har kauye an kai, idan kasa zaki watsawa mahaifinki a ido to Bismillah gaki ga guri, kin san dai zai iya korarki ko ya tsine miki albarka, daman yace na fada miki daga yau kar ya sake ganinki da kowa a waje, dan karki maida mu yan iska a rika cewa mun miki miji kuma muna barinki kina tsayuwa da wasu a waje...”

Tun da Tumba ta fara maganar bata tsaya ba sai da ta kai aya. Naja ta kyalkyale da dariya.

“Iye matar tsoho, amman yace dabam zai aje ki fa”

Falmata ta kai hannunta ta dafa zuciyarta tana jin wani irin abu yana mata yawo.




HAJIYA BABBA POV.

“Ni ban ga anfanin wannan zuwan na mu ba, a maimakon ayi mana maganin matsalar an kara banbaro mana wata”

Cewar Hajiya cikin fada tana jin kamar ta kama bokan ta masa shegen duka.

“Gaskiya kam, be mana komai ba akan matsalar, sai nake ganin kamar yana mana boyeboye”

Cewar Hajiya Talatu bayan ta aje kofin ruwan da yake hannunta.

“Ni ma ai shi na gani, wata kila dai Jarma ya siye mu gurinsa ne, ga alamar aiki kina gani har suna fadar abun da ya kawo mu da kuma sunayenmu amman ya ki yarda yai mana aiki”

Hajiya Babba ta sake fada.

“Amman ko yanzu zama be gan ni ba, Wallahi a zan kyale ba, idan shi baya yi ai ba a rasa masu yi ba, sai wani yi mana bazarana yake da cewar wai sua da tsaro, ko me yake nufi oho”

“Addu'a wai ko?”

Hajiya Talatu ta amsa ta.

“Ni ba zan yarda abubuwa su lalace min ba, na zuba ido komai ya kubuce min”

Duk abun da suke Jurry dai bata ce komai ba sai cin naman kazarta take wanda Hajiya Amutu ta saka aka soya musu.

“Mutum ya taso tun gari wa gari amman babu biyan bukata sai bakinciki”

Jurry ta kalli Hajiya.

“Hajiya ki aje maganar komai for now, bari har mu koma gida lafiya, yana ta fadar akwai tafiyar da ba dawowa what if yana nufin zamu mutu ne”

Da sauri Hajiya Talatu da Hajiya Babba suka kalli Jurry.

“Kuma fa haka ne?”

Hajiya Talatu ta fada, sai Hajiya Babba tai karaf tace.

“Ai ba shi ne Allah ba, be isa ya mana komai ba Wallahi, yayi kadan kuma lafiya zamu koma gida, kuma da yardar Allah sai kudirina ya cika, ki ma daina kawo mana wannan maganar”

“Bari dai har mu isa gida tukuna, ni Wallahi na tsoro ta sosai, kuma da alamar kamae akwai abun da yake rufewa”

Jurry ta sake fada.

“Ni fa abun da ya fada ba zai saka na ki neman wani taimakon ba, ai a san inda rana zata fadi ba, Allah kadai ya san ida za a dace, bayan bakar wahalar matar nan da na sha, yanzu kuma ace na rasa komai, ita fa silar mutuwar aurena, yanzu igiya daya ta rage min da Mai Martaba, sai kuma na saka mata ido tana jindadin rayuwa ni ina a matse”

“Ai ba son ta muke ba, kuma ni van baki shawarar ki kyale ba, amman dai ki yi hankali da wannan Jarma, dan ina ganin shi ya saka aka ki mana aikin nan”

Hajiya Babba ta kalli Hajiya Talatu wacce tai magana.

“Shi ne mana, ai shi ma burki zan taka masa, duk wanda yace zai tari gabana ba zan bar shi ba, kina ji har da wata wai a Masarautar ita ma tana son Sarautar waya sani ko Ammy yake nufi”

Hajiya Talatu ta rufe baki da mamaki.

“Zai fa iya yuyuwa haka din ne, waya sani ko ita take cinye matan Shattima? Wannan matar fa zata iya daukar maita domin ta mallaki komai, kuma gashi ta yi har da mijina”

Hajiya Babba ta tabe baki.

“Ai ni na san wacece Ammy, muguwar mata ce Wallahi, zata iya komai”

Wayar Hajiya Babba ce tai ringing, sai da ta fara kai dubanta kamin ta kai hannu ta dauka, ganin number Mansur second son din Hajiya Hafsa babbar yayarta.

“Salamu alaikum Mansur”

Sai ya amsa daga dayan bangaren.

“Na'am Hajiya ya gida?”

“Lfy kalau ya Hajiya?”

“Wallahi gata nan ba lafiya, jikin yayi tsanani sosai yanzu haka muna asibiti, shiyasa ma na ce bari na kira ki?”

“Subhanallahi me ya same ta?”

“Hawan jini ne ya taso sai numfashin nata na dan sarkewa, kuma bata iya motsa hannun”

“Tun yaushe?”

“Jiya dai abun ya fara amman yau yafi tsanani yanzu haka bata san inda take ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, gashi bana gari Wallahi, amman gobe zan dawo zan iso Kaduna inshallah Allah bata lafiya”

“Amin Amin Allah kawo ku lafiya”

Ta sauke wayar cike da damuwa domin ita kadai ce yar'uwar data rage mata a raye wanda take kallo tana jin sanyi.

“Wai Hajiya ce ba lafiya suna asibiti?”

“Subhanallahi ba a rabu da Bukar ba kuma a haifi Abu? Wannan abu Allah ya mana saukinsa, abubuwa sai faruwa suke marar dadi, daman bata da lafiya ko da kika cewa Mai Martaba ita zaki je dubiya”

“Wallahi lafiyarta kalau, wai abun jiya ya fara zuwa yau”

Ta sauke ajiyar zuciya tana kara jin abubuwan sun mata nauyi fiye da da.

“Ina ganin ni Kaduna zan wuce kai tsaye in yaso sai ku ku wuce Yola, zama ai be gan ni ba”

“Ki tafi Hajiya, ni kuma zan yi duk abin da ya dace da yardar Allah zan kara bincika mana wani wajen”

“To Hajiya Talatu dan Allah ayi kokari”

“Karki damu Hajiya kamar dai baki san wacece ni ba”

“Allah ya kyauta”

Shine kawai abun da Jurry ta fada ta mike tsaye ta fice daga dakin.



_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
37

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*



FADIME POV.

Sai da ya zauna sannan ya aje mata akushi dake cike da kayan marmari.

“Yau ka ce zaka kai ni gida”

Ta fada tana kallonsa.

“Eh amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login