Showing 162001 words to 165000 words out of 286946 words
suna nan da yawa ga wandanda suke bincike sun san haka, ban fara rubutun nan ba sai da nai bincike. Ban sani ba ko son rai ne ya raya muku jifata da wadannan mugayen kalaman ko kuwa hassada ce saboda na fallasa sirrin maita? Ko kuma tsantsar jahilci da rashin iya magana? Ko ma dai minene ni dai na bar mutum da Sarkin da baya bachi baya angaje, Allah kenan ina rokonsa ya saka min tun a duniya kuma yai mana shari'a da ku a ranar da gaskiya bata boyuwa.
Special thanks to my lovely fans, i sincerely thank you, friends and loved ones, for ur support and encouragement. Love you to moon and back đź’ť
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
40
FADIME POV.
Wasim ya kai kunnensa saitin bakinsa a karo na biyu ya rada mata.
“Idan na baki magani kin sha zaki yarda ki zauna?”
Ya fadi hakan ne kawai dan ya kwantar mata da hankali ba dan yana da maganin da zai bata ba, shi kanshi ba da shiri ya zo ba. Sai ta girgiza kai da sauri.
“Aa ni ban yarda ba”
“Idan kina can zasu taba miki ido ne, kuma da zarar hakam ya faru kin rasa idon gaba daya kenan shiyasa na kawo ki nan”
“Zan fada musu kar su taba idon, yanzu kam Wallahi gaskiya zan fadawa Bappa ba zan sake boye komai ba”
Rasa yai yadda zai yi da ita, ba zai maida ita a can ba, domin ya san sai iyayenta sun taba idon nata, duk da ya san abu ne mai wahala ta yarda ta zauna a nan ko da tana gani balle bata gani.
“Iya ki ce min wani abu mana”
Maganar da Zainab tai yasa ta Fadime ta kara kame Wasim ta rike kamar ta shige cikinsa ta kara fashewa da kuka.
“Kana jin mayun biyu ne, Wallahi raba za su yi”
Kallonta Zainab tai cike da takaici kamin ta dauke kai ta nufi kofar fita daga falon ta fice gaba daya. Sai da ta fita sannan Iya ta kalli Wasim cikin tsoron mutuwarta ta ce.
“An min sako ne?”
“Ba a miki sako ba, zuwan kaina ne amman duk ranar da akai miki sako, kin sani na mutuwarki ne Iya, kuma be zama lallai ki san hanyar da sakon zai rikeki ba, ban san miyasa kika zabi zama dabam da mutane ba, kin ki ki amayar da kankarar maitar dake cikinki, kina ta bibiyar halittarki kina ci”
“Ban ci kowa ba, face na kusa da ni, iyalin wani mutum na ke bibiya, na cinye mata yanzu kuma na cinye yaya, maitar da nake ta cikar buri ce Wasim ba ta cinye duk wanda be ji be gani ba, kowa yana da dalilinsa na yin maita, wani saboda ya samu amfanin gona, wani saboda yai arziki, wata saboda kishiya ko makiya, har yanzu mutanen da nake ci wadanda suke shan gabana ne suna kokarin tare min cikar buri”
Ta fada jikinta na rawa, Uffan Wasim be sake ce mata ba, ya zauna a kujerar dake kusa da shi Fadime na rike da shi.
“Kai ka makantar da ni?”
“Me zai saka nai miki haka? Baki yarda ba zan iya bari a cutar da ke ba?”
“Zaka iya Wallahi tun har ka sace ni ka kawo ni gurin mayya”
“Bana da gurin aje ki ne sai nan, idan na koma dake garin mu wata karim fitinar ce, daman na fada miki matukar na fitar da ke b tare da izinin Babana ba wani abu zai iya samunki, amman kika dage akam sai na fito da ke, kin ga abun da hakan ya haifar saboda kin dage, a yanzu ma idan kika dage zaki rasa idonki har a bada, idan na fada miki abu ki rika yarda da shi, ki saka a ranki Wasim yana kaunarki, ba zai bari wani abu ya taba ki ba, ba zai taba cutar dake ba”
Ya fada hannayensa duka biyu shimfide a fuskarsa, yana mata maganar cikin kyakkyawan lafazi da kwantar da hankali.
“Daga danginki ma ban bari an taba ki ba balle daga ni? Ki yarda da ni Fateme Wasim ba zai taba cutar da ke ba”
Hawaye ya sauko a blind eyes dinta.
“Amman Inna da Bappa za su yi ta nemana, kuma ba zan samu natsuwa a gidan mayu ba, miyasa zaka tafi to? Ka tsaya a nan mana”
“Zan tafi na nemi gafarar mahaifina ne, ba zuwa zan yi dan na zauna ba, ina son ki dawo kamar da”
Ta sassauta rikon da tai masa tana kuka.
“Yaushe zaka dawo anjima ko gobe?”
“Anjima ina dawowa zan dauke ki na maida ke gidan iyayenki”
“Idan zan yi fitsari waye zai kai ni?”
Wasim ya kalli Iya
“Ita”
Iya ta girgiza kai da sauri tana matsewa jikin ginin. Fadime ta fashe da wani irin kuka.
“Idan ka dawo ka ga na mutu, kace Bappa da Inna su yafe min, kuma ka fada musu gaskiyar abun da nai”
“Zan dawo na same ki lafiya, duk wanda ya ci ki, ya ci mutuwa”
Ya sumbanci goshinta.
“Bude baki”
Ta bude sai ya saka yatsunsa biyu ya cikin bakinta a saman halshenta ta lakato yawun saman halshen ya bude nasa bakin ya shafa a halshensa. Sannan ya mike tsaye a hankali ta yadda ba zata iya jin motsinsa ba ya fara takawa da baya baya tana kallonta har ya fice daga dakin.
A harabar gidan ya samu Zainab tsaye tana kallon gate kamar mai jiran shigowar wani, hawaye sai sauko mata suke. Zuwa yai daidai ita ya tsaya sai ta juyo ta kalleshi, for the first sai ta ji bata jin tsoronsa sai ma kwarjinsa da ya cika mata ido.
“Ya akai ka gane gidan nan?”
“Ta hanyar zaren da na daura miki a hannu”
Ta dago hannunta ta kalli zaren.
“Kana da alaka da ni kenan, shiyasa ka gane cewar ni jinin Iya ce”
“Na gane ke jinin iya ce saboda na gaisa da ke, ba dan na san asalin cewar ke jinin ba ce”
“Sai yanzu na gano dalilin daya sa kace na ci naman nan, kuma na ci be mun komai ba, amman baka fada min ka santa ba”
“Ta taba baki labarina? Ko ta taba baki labarin tahirinta a can?”
Ta girgiza kai alamar a'a.
“Bata fada min gaskiya ba, kuma ban san dalilinta na yin haka ba, tunanina yana tafiya ne akan abun da ta shimfida min a kwakwalwa, shiyasa ban damu na zafafa bincike ba...”
Ta ja wani dogon numfashi ta sauke, ta kalleshi.
“Amman da gaske tana maita?”
Ta tambaya cike da fargaba da kuma tsoron irin amsar da zata fito daga bakin Wasim. Shi ma kallonta yake na yan dakiku kamin ya daga mata kai.
“Abun da ya rabota da garin kenan, saboda mu bama maita kuma ba mu yarda mu zauna da maye ba, ko da jininmu ne”
Da sauri ta daga kanta sama sai kuma ta sauke kasa tana hawaye, ji tai ina ma ace bata tambaya ba, wani irin kuka ne ya zo mata sai tai saurin rufe bakinta. Wasim ya cire hular kansa ya kai hannu ya janyo Zainab sai ta dora kanta akan kafadarsa ta fara rara kukanta a hankali, Fadime ma tana can cikin falon tana yin nata. Sai da Zainab tai kuka sosai sannan ta daga kanta daga kafadarsa.
“Im sorry”
Ta fada still crying idonta har ya fara ja, be ce mata komai ba yana ta kallon kyakkyawar fuskarta, har sai da ta sake kallonta.
“Ki kula min da Fateme saboda ke ta shiga wannan halin”
Juyawa tai ta kalli kofar falon da take jiyo kukan na Fadime, juyowa tai da zimmar yi masa magana sai ta ga babu kowa a gurin. Da sauri taja baya gabanta yai mugun faduwa.
HAJIYA BABBA POV.
A lokacin data fadi ba Suma tai ba, faduwa tai a kasa saboda jikinta ya kasa daukarta zuciyarta kuma ta buga irin bugun da ba a son zuciya tana yi. Da sauri aka dauke ta aka dora akan gado aka nufi ICU da ita, ba karamin kokarin likitocin su kai ba kamin su samu taimaka mata komai ya dawo normal, sai da suka mata allura mai karfi sannan ta samu tai bachi.
Wata yar kawunta aka bari tana jinyarta, su kuma yaran yayarta suka dauki gawar Hajiya Hansai suka tafi da ita gida, sai da suka isa sannan suka samu labarin rasuwar Talba, a lokacin ne suka gane dalilin faduwar Hajiya, a take aka tashi wasu family zuwa Yola domin yin jana'iza.
Haka Hajiya ta kwana ta wuni bata san inda kanta yake ba sai washe gari, shi ma ta farfadi ne kawai ba dan tana jin wani kuzari ko lafiya a jikin ba.
Bata komai sai kallon mutane da kuma bin dakin da kallo, idan ta fara tunanin abun da ya faru sai ta ji tunanin ya mata nauyi kamar zata soma, sai da suka bata magani suka mata allurar sannan ta samu sa'ida sai dai duk da haka bata iya kuka ko yin magana idan tana bukatar wani abu sai dai ta nuna da hannunta, ba dan ta kurmance ba sai dan magana tana mata nauyi a baki yanzu, bata aikin komai sai sauke numfashi da karfi kamar wata mai tsoho ciki. The following day suka sallameta, sai ta koma gidan Hajiya Hansai cikin yayanta ana ta mata gaisuwa, abun sai ya zame mata biyu ta rasa da wanne zata ji mutuwar yayarta wacce ita kadai ta rage mata ko kuwa na danta namiji guda daya da Allah ya bata, ko kuma rushewar burikanta? Abubuwan nan uku sai suka taru suka tokare mata zuciya. A gidan ta wuni duk wani mai rabon yayi mata gaisuwar Hajiya Hansai yayi mata, washe gari ta bi jirgin safe zuwa Yola ita da wasu yan'uwanta hudu, sai da jirgin ya sauka yola ta kira direbanta ya zo ya dauke su sannan mutuwar ta fara tabata, bata yarda ta rasa danta ba har sai da motarsu ta nutsa kai cikin Masarautar, arba da fara yi da manyan manyan motoci na alfarma, ga taron mutane a harabar masarautar ban da cikin fada.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah haka ka kaddaro min”
Ta furta tana fitowa daga cikin motar, matan da ke tare da ita suma kuka kamar ita, kallo sai ya koma akanta masu ganin tausayinta na yi musamman wadanda suka san mutuwa biyu akai mata ba daya ba. Tana shiga bangarenta sai aka bare da sabon kuka, kamar a lokacin akai mutuwar babu jin komai sai kukan rashin mamaci, a lokacin ne ta fara jin kamar ace zata iya ta dawo masa da ransa, sai dai bata da rabon sake ganinsa ma, domin tun ranar da abun ya faru aka kai shi makwancinsa ma gaskiya bayan an masa wanka da sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Yaranta daga Karima har Juwairiyya da Kausar kuka suke sosai, su kansu sun san sun fi rashin dan'uwa kuma jigo a rayuwarsu.
“Na yafe maka Talba, na yafe maka duk abun da kai min a cikin rashin sani ko kuskure ko ganganci, Allah ya yafe maka ya karbi bakuncinka”
Shine abun da Hajiya take fada tana wani irin kuka na fitar rai.
“Jama'a kana naka Allah na nashi, ashe Talba ba zai yi aure ya aje yara na gani ba, ashe rayuwar da Allah ya bashi ba mai yawa ba ce, Wayyo Allah mutuwa bata yi ba”
A gaba daya falon babu wanda be yi kuka ba, tausayin Hajiya ya kama su, sakon mutuwa kenan mai sanarwa jiki da ruhi da hana zuciyar walwala ta rike buri ta tarwatsa farinciki.
Gasuwar sai ta zama biyu, idan an yi ta bangaren Hajiya Babba sai a nufi gurin Ammy ayi mata nata, wasu kuma sai su fara yi ma Ammy sannan su iso bangaren Hajiya Babba. Hajiya Talatu ta dawo kusa da Hajiya Babba ta zauna tana ta bata hakuri da kalamai na kwantar da hankali.
Har akai sadakan ukun Hajiya bata iya cin komai ruwa da dan abu mai kamar ruwa kamar lemu ko fura, cikin kankanen lokaci kibar nan ta zube ta koma kamar ba ita ba.
FALMATA POV.
“Lafiya miya faru?”
“Komai ma ai ya faru Malam, yarinyar nan ta zama abun da ta zama bata min komai sai keta, ga halayen banza data kirkirawar kanta, yanzu na tashi da kafafuwa naje gidan Inna wuro na fada mata idan ba a biya albashin ta kirani da kaina na karba ko kuma ta karba ta kawo min ba sai an ba Falmata, ai sai ta bani bakin labari wai Falmata taje cikin gidan ta saci sarkar matar sarki ta miliyan uku, kuma ta saci yan kunnen yaran da take reno, shine fa suka koreta, amman da yake yarinyar ta kware a iskanci sai ta kama bakinta tai shiru bata fada ba, ashe duk kwana kin nan wani guri take zuwa tana wuni ba gurin aikin ba, ina ganin mai napep din da yake zuwa yana daukarta shine yake zuwa da ita can wani guri suna shashanci, nan gaba kadan yarinyar nan ciki zata kwaso maka”
“Miliyan uku? Fulani ke yanzu kin san ki saci abun miyan uku? Ina kika kaita?”
Baba ya fada yana dafa kirjinsa cike da mamaki da kuma tsoron kar ta ja masa zuwa gidan yari.
“Tace ai sun gane shiyasa suka karbe sarkar suka koreta, muna cikin zancen aka kirata wai yaran sun mutu”
A lokacin ne Falmata ta samu labarin rasuwar su Labib, a take ta ji wani irin tausayin yaran ya kamata har shakuwar da tai da su sai ta dawo mata sabuwa. Bata ankaro ba ta ji Baba yayi cikinta da duka, duka bana wasa ba domin katon icen girkin ya dauka ya rafka mata a kafafuwa, sannan ya shiga dukanta ta ko'ina gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, duk da bashi da tabbacin idan gaskiya Tumba ta fada masa, be tsaya ya saurari Falmata ba. Sai da yai mata lis da kuka kamar zai kasheta sannan ya bar ta a gurin kwance ko motsin kirki bata iyawa.
“Ni dai Wallahi da zaka dauki shawarata kamata yai ka aurar da ita kawai ka huta, tun da mutumen yace baya son komai, ba sai an kai auren nan nesa ba, daman can saboda aikin nan ne yasa na zabi lokacin yanzu kuwa tun da ba aikin kuma gashi ta fara lalacewa ai ka aurar da ita kawai ka huta”
“Haka zan yi, idan ban yi haka ba ba zata bari hankalina ya kwanta ba, miliyan uku fa? Kiranshi zan yi a waya idan ya zo zan ce masa an canja lokaci”
“Eh Wallahi ni ban ki an maida shi nan da sati daya ba ma, a daura auren ya dauke ta can mu huta da fitina, tun har Allah ya hutar da kai yace baya son komai”
Baba ya nufi inda ya barar da jakar buhunsa ya dauka ya shige dakin cike da takaici sai huci yake.
A waje Falmata ta kwana saboda bata iya komai sakamakon dukan da Baba yai mata, gashi bata da gatan da wani zai rikata ya shigar da ita dakin ko ya kawo mata abun rufa, ta zazzabi ta kwana sai nishi take kamar mai shirin haihuwa, ko'ina a jikinta zafi yake mata, bata ko iya motsa kafarta ta dama domin a gurin Baba yafi dukanta.
Washe gari da safe Baba ya kira surukin nasa mai suna Malam Mansur, ya sanar masa yana son ganinsa, sai ya fada masa cewar ya tafi kauye gurin wani sha'anin sai dai idan ya dawo zai zo. Da haka su kai sallama Baba be fada masa komai ba saboda ya fi son ganinsa face to face.
Da daker da shudin goshi Falmata ta samu ta shiga bandaki tai fitsari ta fito tai alwala ta shiga dakin tai sallah, sannan ta zube a gurin kwance ta fashe da sabon kuka tana tausayin kanta. Babu abun da yafi tsaya mata a rai kamar maganar auren da Tumba tai, wanda Babanta ya hau kai ya zauna, bata sani ba wata kila shi ma tsohon mai duka ne kamar Babanta, wata kila shi ma be da hali mai kyau, idan taje can wata kila wata wahalar zata sha, a nan zai zauna da ita ko a kauye? Tana jin lokacin da Baba ke fadawa Tumba cewar kar ta sake bari ta fita daga cikin gidan ta ji wani sabon kuka ya zo mata, shikenan ba zata sake zuwa gurin Momy ba, ba zata sake ganin Sirleem ba, sai ta ji wani sabon bakinciki ya sallamo mata, wasu hawayen suka fara zubo mata.
SHATTIMA POV.
Jirgin safe ya bi, ya sauka a Yola in time sai dai ko da ya isa an yi ma yaransa sutura da kuma dan'uwansa har an bar masarautar da su. Ya tarar da masauratar cike da mutane masu amsar gaisuwar da kuma amsu zuwa yi, manyan mutane suka rika zuwa gaisuwar, duk da kasancewar ba kowa ya san Talba ba, domin ba kasafai kake ganinsa a harkokin gidan ba.
Washen gari ranar da akai sadakan uku yana zaune Dakin Ammy, bayan wasu yan gaisuwar sun fita, suna magana akan mutuwar Talba da yadda ta zowa kowa a bazata, Ammy ta dauko zancen yaransa Labib.
“Tun da yarinyar nan ta tafi sai su zama wasu marar lafiya, da ko har walwala suke suna wasansu, nan da nan sai ciwo ya dawo sabo”
“Ina ta tafi?”
Ya tambaya ba tare daya kalli Ammy ba.
“Sata tai”
“Sata?”
Sai da Ammy ta dauki lokaci kamin ta labarta masa abun da ya faru.
“Ta taba daukar wani abu a nan kamin nan”
“Ba zamu iya ganewa ba, tun da ba tsare ta ake ba”
“Amman an bata kudin aikin da tai?”
“Bata dawo ba ai, tun da suka tafi can bata sake dawowa ba, amman Jekadiya tace min wai Sirleem ya fita da ita har ya mari Juwairiyya”
Shattima ya sake kallon Ammy da mamaki yana tuna wacan ranar.
“Sirleem”
Ya furta a hankali.
“Ammy baki yi tunanin akwai abun da zai iya saka yarinyar sata ba? Tana cikin halin rayuwa na san tahirinta, wata kila ta yi satar ne saboda ta taimaki kanta, Akwai inda sata ya halatta fa, Idan har da gaske ta yin, wata kila kuma shari ne kawai”
“To wa zai mata sherin?”
“Sirleem mana, so that ya samu ta bar gidan, shi kuma yana da damar yin komai da ita ”
Ammy ta masa wani kallon mamaki.
“Ban san