Showing 183001 words to 186000 words out of 286946 words
lafiya a lokacin da nake rainonsu, na fada masa”
“Ba ki fada masa za a miki aure ba?”
“Na fada masa”
“Be ce komai ba?”
“Eh”
“Ko dai ya baki wani abun kika boye?”
“Wallahi be bani komai ba Umma”
“To tashi ki tafi”
Falmata ta mike tsaye ta fito daga dakin, ta zabi yi ma Tumba karya cewar ta fadawa Shattima ne saboda kar ta cilastata tace sai taje ta fada masa saboda aba ta wani abun.
Kamar ko yaushe yau ma a cikin rashin walwala ta wuni, dambun masarar da akai ma kadan ta saka a cikinta, da dare ma sai da kanwar mahaifiyarta ta takura mata sannan ta ci tuwon shi ma kadan, ita dai sai kallonta take domin kana ganinta kasan bata cikin walwala.
“Falmata ko dai akwai abun da yake damunki...?”
“Babu komai Inna Laure”
“Idan akwai wani abun ki fada min, ni ma mahaifiyarki ce, ko da ba zan iya miki maganinsa ba, zan miki addu'a”
Falmata ta kwantar da kanta jikin Inna Laure hawaye na cika idonta.
“Ina tunanin Mama ne”
Inna laure ta dabata tana jin babu dadi.
“Ki yi hakuri, haka Allah ya kaddara, Allah yai mata rahama”
“Ameen”
Ta amsa hawaye na sauko mata. Suna zaune a waje ita da Inna Laure har kusan tara na dare, duk zaman da suke gurin idon Tumba na kansu, domin zuciyarta na raya mata Falmata zata iya fadawa Laure cewar bata son wanda za a aura mata, ko kuma tace tsoho ne. Sai dai Falmata bata ce mata komai akan haka ba. Tara da yan mintuna Baba ya shigo gidan rike da jekarsa ta zuwa kasuwa, baki har kunnen ganin yadda baki suka fara cika gidan, da wasa da dariya da far'a suka gaisa da shi, yana musu sannu da zuwa tare da tambayar mutanen kauye, duk suka amsa masa cewar kowa yana lafiya sai ranar daurin aure mazan za su zo. Sai da ya shiga dakin Tumba ya ci abinci sannan ya ciro kudin da tsohon ya bashi ya aje a gabansa yana fadin.
“Dazu da yamma nan, Malam Mu'azu ya zo tare da wani abokinsa, ya kawo min dubu ashiri, yace a be san zabinta ba be san zabinta ba, shiyasa be siye komai ba, amman a bata wannan kudin ta siye duk abun da take so, sannan yace gobe zai kawo sauran abubuwan al'ada yace wasu yan'uwansa za su kawo, kuma idan sun kawo za su tafi da wasu a duba inda za a kaita”
“Mashallah, amman yayi kokari, har dubu ashiri a wannan marar? Daga gani gaskiya mai rikon amana ne, kuma zata jidadi idan ta aure shi kai ai ko sarauyi albarka”
“Allah dai ya ba su zaman lafiya”
“Ameen Wallahi, ita ma Naja Allah ya kawo mata mai albarka”
Baba be sake cewa komai ba ya dauki dubu ashirin din ya mikawa Tumba.
“Gashi sai a siye duk abun da ya dace”
“Inshallah”
Tasa hannu ta karba tana far'a, abun nema ya samu daman shekaranjiya Falmata ta zo mata da 50k da Shattima ya bata da sunan aikin da ta yi.
SHATTIMA POV.
Jirginsu ya sauka Katsina ya sanarwa Ra'ees cewar ya iso, cikin kankanen lokaci Ra'ees ya iso da motarsa ya daukesa, a motar Shattima yake labartawa Ra'ees haduwarsu da Fadime sama sama, ba karamin mamaki Ra'ees yai ba.
“To yanzu na yarda mutum ce amman tana da aljanu gaskiya”
Shattima yayi murmushi yana ciro wayarsa daga aljihunsa na gaba ya duba kiran Baba Waziri dake shigo masa, hakan nan kawai ya samu kansa da faduwar gaba sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yai picking.
“Salamu Alaika Baba”
“Shattima kana lafiya?”
“Alhamdulillah”
“Yanzu Ammy take fada min cewar kaje Katsina?”
“Eh wani dan abu ne ya taso na gaggawa, amman gobe zan dawo da yardar Allah”
“To ka fara shirin aure, ina son karshen watan nan a kai karshen komai da yardar Allah”
Silently Shattima ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya amsa da.
“To Baba Allah ya nuna mana”
“Ameen”
Yaya Waziri ya ashe wayar, sai Shattima ya kurawa wayar ido yana ta kallonta kamar mai tunanin wani abu. Asibitin ya fara sauka ya shiga gurin Shugabansu suka gaisa sannan ya bukaci Number Bappa, a nan ne yake fada masa zuwan da Bappa ya sake yi har suka nemi yai masa uzuri har sai nan da sati daya. Shattima dai be yarda ya fada musu cewar yarinyar tana yola ba, domin ba kowa ne zai masa kyakyawar fahimta ba, ya fi son Fadime ta fadi komai da bakinta kuma a gaban idon kowa ta yadda zata wanke shi. Number Bappa ya karba a hannunsa sannan suka fito shi da Ra'ees zuwa cikin motar, tun kamin su bar asibitin Shattima ya kira Bappa a waya, sai da wayar tai ta ringing kamar zata katse sannan Bappa ya daga yana tare da sallama.
“Am Sunana Shattima, ni ne likitan da kuka barwa ajiyar Fadime ta bata, ina fatar ka gane?”
“Na'am na gane”
“Dan Allah kana ina akwai maganar da nake son mu yi”
“To a yanzu dai ina kasuwar Kaita, gurin sana'ata, wani abun ne”
Shattima yayi jimm yana tunanin ta Inda zai fara.
“Am daman ni mutumen Yola ne, idan baka manta ba, na fada maka cewar an min rasuwa kanena da kuma yayana”
“Haka ne Allah yai musu rahama”
“So naje gida gaisuwa, kuma na je gidan wata mata da zimmar yin wani abun, sai na ga yarka a gidan, and i try my best na ga na kawo ta a katsina amman abun ya ci tura, domin duk motar da na sakata da zunan zuwa katsina sai motar ta ki tashi, i decided na zo na sanar da kai so that idan ka aminta da ni sai ka bini mu je ka zo da yarka, nasan a yanzu ba lallai ne ka fahimce ni ba, amman ita zata muku bayanin komai”
“Yanzu haka ka ga Fulani da idonka?”
Bappa ya tambaya, Shattima ya amsa masa da eh duk da kasancewar be san ana kiranta haka ba sai dai ya san ita din yake nufi domin akanta ne suke magana.
“Eh”
Bappa yayi shiru daga dayan bangaren kamin ya sauke ajiyar zuciya.
“Yanzu haka Fulani tana Yola?”
“Tana can”
“To ka fada min inda kake zan zo na same ka”
“Okay idan ka shigo Katsina, ina unguwar Hill road GRA gida mai number 35, kuma zaka iya kira number wayata, idan kuma ka aminta da ni zan iya turo mota har inda kake a dauke ka”
“Aa zan shigo da kaina, zan kira ka”
“Okay”
Shattima ya sauke wayar sannan ya kashe kiran da kansa, ba dan komai ba sai dan yana jin mutumen daya kira din kamar yana da muhimmanci a gurinsa.
“Ina tunanin su da suke iyayenta za su iya zuwa da ita ba tare da wata matsala ba”
“To Allah yasa su aminta su bika din kar su dauka ko su ma siyar da su zaka yi”
Shattima yayi murmushi.
“Indai suna son ganin yarsu ai za su je”
“Kasan mutanen kauye suna tsoron na birni musamman ma su ji cewar nesa ne kamar Yola”
Shattima be sake cewa komai ba har suka shiga unguwarsu. A harabar gidan Ra'ees yai fakin tun kamin ya kashe motar Shattima ya bude ya fita ya nufi entrance din, a hankali ya tura kofar falon ya shiga zaunawa yai kan manyan cushion din ya kiran line Jekadiya. Bugu daya ta dauka da alama wayar tana hannunta.
“Ranka ya dade”
“Jekadiya yarinyar na kusa da ke?”
“Eh tana zaune kusa da ni ranka ya dade”
Kamin ya sake cewa komai ta kama hannun Fadime ta saka mata wayar.
“Ki yi magana Shattima ne yake kira”
Fadime ta kai wayar a kuje upside down, sai da Jekadiya ta gyara mata sannan ta fara magana.
“Hello...”
Samun kansa yai da murmushi ya ki ya amsa mata sai saukar muryarta a kunnensa yake cike da shauki.
“Hello”
Nan ma be amsa ba sai fadada fuskarsa yake da murmushi, kamar wata abokiyar wasarsa haka ya dauke ta. Ta cire wayar a kunnenta ta mika ma Jekadiya.
“Ki duba wayar ya yanke, ina ta magana ba a amsa ba”
Jekadiya ta duba wayar ta ga yana nan ta mayar mata a kunnen.
“Yana nan ki yi magana”
“Hello”
Sai a lokacin ya amsa.
“Cute ya kike?”
“Lafiya kalau, ka tafi gurin Babana?”
“Na yi waya da shi dai zai zo ya same ni?”
“Gobe zaku zo kenan?”
“Inshallah”
“To ka zo da wuri dan Allah”
“Gidanmu ya fara isarki ne?”
“A kasa fa nake ta zaune kamar almajira, kuma na ce ta boye ni a wani guri kar Hajiya Babba ko Iya su gan ki ta ki”
Shattima ya shafa fuskarsa yan murmushi.
“Kina da gaskiya, za a kai ki a boye yanzu kuwa, kin ci abinci”
“Eh an bani abinci na ci”
“To yayi kyau zan kira anjima kamin ki yi bachi”
“Tau, na bata wayar?”
“Eh bata”
Ta mika ma Jekadiya wayar
“Gashi yace zai fada miki wani abu”
Jekadiya ta karba ta kai a nata kunnen.
“Ranka ya dade”
“Jekadiya a kaita dakin Nana so that ta samu abokiyar fira, kuma dan a daina aje ta masa, a rika dorara a kujera”
“To ranka ya dade gan gama”
“Kuma idan an yi sallah ki ankarar da ita”
“To ranka ya dade inshallah Allah kara maka lafiya ”
Jin shiru yasa ta kashe wayar ta mike tsaye tana kama hannun Fadime.
“Ta so muje yace a kaiki dakin Nana”
“Wacece Nana?”
“Kanwarsa ce”
“A nan gidan take?”
“Eh”
Sai da Jekadiya ta isa da ita bakin kofar dakin Nana sai taja ta tsaya tana kwankwasawa. Nana ta bude kofar tana sanye da uniform dinta dawowarta kenan daga makaranta, sai da ta kalli Fadime sannan ta kalli Jekafiya.
“Ya akai?”
“Shattima ne yace a kawo ta dakinki t samu abokin fira”
“Wacece ita?”
“To nima dai bana ce ba Wallahi”
“To ta shigo”
Nana ta bude mata kofar Jekadiya ya shiga da ita ta zaunar har kan gadon Nana sannan ta juya ta fita.
“Ke makauniya ce?”
“Aa idon zai bude ai, Wasim yace min idon zai bude”
Nana ta fara kokarin cire rigarta.
“Waye Wasim? Miye sunanki?”
“Fateema, Wasim Sarauyina na ne...”
Da kadan da kadan Fadime ta labartawa Nana komai ciki har da labarin Hajiya Babba, Nana kam ta samu yar'uwa a nan ita ma ta dauko mata labarin abun da ya faru da ita da na Sardauna.
“Shi Sardauna nan Saurayinki ne?”
“Aa abokina dai”
“Kuma namiji? Mace da namiji suna abota?”
“Eh mana ai ba komai”
“Mu kam a kauyenmu ba ayi, kuma za a rika yi ma mace kallon yar' iska”
“Mu ai kin ga birni ne kuma ba wani abun muke ba, abota ce kawai”
Fadime ta yi shiru can kuma tace.
“Wai nan gidan kato ne?”
“Kai sosai masarautar ce fa”
“Mu ma Bappa an bashi sarauta a garinmu sarkin Fulanin yankinmu, ko Wasim ma dan Sarki ne sarkin garinsu, amman su garinsu basa son wuta basa son komai na zamani”
Haka suka kai firarsu, sai da lokacin sallah yao Jekafiya ta shigo ta kama hannun Fadime ta kaita bandaki, bayan ta fito ta kawo mata abinci.
***
Bappa na gama waya da Shattima ya rufe shagonsa yai ma abokan aikinsa sallama bayan ya sanar musu wani uzurin ne ya taso masa. Sai da ya hau achaba sannan ya isa tashar daya saba shiga mota zuwa garin bamdalo, ya kusan awa biyu a mota har sai da ta cika sannan ya suka kama hanyar gari.
Yana cikin motar sai sake sake yake a ransa, tunanin yadda zai bullowa lamarin yake, ya tafi garin Yola tare da Shattima ko kuma dai ya hakuri har sai Wasim ya dawo da ita da kansa? Har ya isa gida be raba dayan biyu ba tafiyar ko kuma barin, ta wani bangaren yana son tafiyar domin tahowa da yarsa sai dai kuma yana tuna maganar Wasim cewar yayi mata kafin da ko gawarta ba zata iya barin garin ba.
Ko da ya shiga ya samu Inna na shara, tana ganinsa ta san ba lafiya ba, domin ba kasafai yake dawowa da rana ba.
“Malam Lafiya dai?”
Ta tambaya bayan ta amsa sallamarsa, be bata amsa ba ya nufi kofar bukkarta ya tsaya, sai ta aje tsintsiyar hannunta ta nufi bukkar ta dauko masa tabarma ta shimfida masa ya zauna, sannan ta dauko kofi ta karkata tulun dake aje gefen zanar ta zuba masa ruwa ta kawo gabansa ta aje tana kokarin zauwa. Daukar ruwan yai ya sha kusan rabin kofi sannan ya kalleta ya ce.
“Dazun mutumen nan ya kira ni...”
Ya labarta mata komai ciki har da shawarar zuwa da yake. Inna ta sauke ajiyar zuciya kana ta kalleshi cike da damuwa.
“To Amman Malam ka manta abun dashi wanda ya dauke ta ya fada mana? Kana ganin idan kaje zata iya dawowa a nan ne?”
“Ni ma shine abun da ya tsaya min a rai, ina tsoron kar naje can kuma ya zama wata matsalar”
“Kuma mutanen birni ba abun yarda ba ne, idan ma zaka ce sai dai kaje tare da police, be zama lallai da gaske ya ganta ba, wata kila dai yana son yai wani wayon ne saboda ya batar da case din saboda ana ganin kamar zai bata mai suna, ba mu sani ba ko ya shirya wani abun ne”
“Kina da gaskiya, ni kaina ina jin tsoro, ba zanje ni kadai ba, zan je tare da Kawu dan Iroro, kuma tare da yan sanda”
“Kuma idan kun je kana ganin zata zo? Ni dai a tawa shawarar karka je ko'ina Malam mu bar wa Allah komai, na fi gamsuwa da bayanin da wacan matsafin yai min fiye da wannan, domin ya fada mana gaskiyar abun da Fulani bata fada ba, kuma tun da har ya ce ya mata kahin a can idam kun je ba zata iya zuwa ba, wata kila ma daga nan zai iya karawa da ita gaba,”
“To yanzu mu kyale ta kena?”
“Ni kam shi na ga yafi, abun d duk Allah ya rubutawa bawa be isa ya tsallake shi ba, na yarda d wannan shiyasa na fara kokarin cire damuwar a raina, indai Allah yasa tana ta rabon idom ya bude zai bude kuma idan da rabon ta dawo mana zata dawo, bana nema gurin kowa sai Allah”
“Kina da gaskiya, ni kaina na yi wannan, sai dai ina ganin kamar idan na kyale na yi sake tun har ance an ganta”
“Ganinta ba na tabbas ba ne, domin ba kai ka ganta da idonka ba, ko muryarta ka ji ba abun yarda ba ne, domin mutum babu abun da be iya ba, ni dai kam da za ka bi shawarata da ka hakura, ka saka number ta a inda ko ya kira ba zai same ka ba, kuma kar ka fada masa zancen yaron nan mai tsafi ”
“Tau mu dai gamu ga Allah, Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri, ni daman wannan maganar ce tasa na zo”
“Yanzu dai ka tashi kaje gurin Kawu dan Iroro ka fada masa komai ka ji shawararsa ”
“Haka za ayi, bari naje same shi a kasuwa na ji abun da zai fada”
Bappa na fadin haka ya mike tsaye, domin zuciyarsa ta fi natsuwa da tafiyar fiye da zama, taya za a ce ga yarka a can kuma ka watsar bayan kana cikin halin nema. Daga gidansa be tsaya ko'ina ba sai kasuwar bandalo gurin Kawu Dan Iroro, sai da suka zauna sannan Bappa yake labarta masa abunda ke tafe da shi, har labarin da Wasim ya bashi sai a lokacin ne Bappa yake labarta masa. Kawu ya jinjima lamarin yana kara girmama halin Fadime a ransa, ya san bata jin magana amman be zata rashin jin maganar ya kai haka ba.
“Yanzu ita Fadime halinta har ya kai haka?”
“Wallahi Fulani kam sai hamdala, shiyasa wani lokacin sai na ji kamar na kyaleta da halinta Wallahi”
“Gaskiya, ka tashi tsaye a akan yarinyar, idan ta dawo ka nemi wani ko a cikin yan'uwa ayi mata aure shi ya fi kwanciyar hankali, kuma ka tashi tsaye da yi mata addu'a”
“Kawu ina ganin da bana addu'a da abun da Fadime za ta yi sai ta fi haka, Wallahi ina bakin kokari akam yarinyar nan”
Kawu ya ja wani dogon numfashi ya sauke, sannan ya kalli Bappa ya ce.
“Wannan maganar ba abar a kyale ba ce, ka kira shi a waya, mu je gobe mu yi magana da shi fuska da fuska sannan mu sanarwa yan sanda ko wnai abu ne ka ga tare za mu je da su, ba wai mu kadai ba, kaga idan mu ka yi magaja da shi gobr jibi sai mu tafi garin”
“Haka ya kamata ni ma dai nace be kamata a kyale wannan maganar tun da har ance gata”
“Shiyasa na ke son a tafi garin ai, ba a barin abu sai dan dole, tun da shi be fada maka cewar ga ranar da zai dawo da ita ba, kuma kai baka san inda zaka sake ganinta ba, sannan wannan lamarin Allah kadai ya san gaskiyarsa sai kuma ita Fadimen idan ta so ta fada”
“Amman akwai kamshin gaskiya a maganar yaron nan, domin duk abunda ya fada min faru, wani ne kawai ba ni da tabbaci saboda bana a gurin, ba zan musa masa ba domin na san Fulani zata iya aikatawa”
“Fadime kam ta wuce tunaninmu, aure ne kawai zai saka ta hankali, idan Allah yasa komai ya warware sai ka samu wani ko a cikin dangi ka hada ta da shi”
“Ai haka zan yi da yardar Allah”
Bappa be bar gurin ba har sai da ya kira Shattima a waya ya sanar masa cewar gobe yana nan tafe.
ZAINAB POV.
Kamar marar lafiya haka ta wuni babu komai a cikin tunaninta sai Mahaifiyarta, domin a zuwa yanzu ta sadakar cewar laifin na mahaifiyarta ne da bata aikata ba, da Fadime bata ji komai ba har ta fadawa wani.
Saukowa tai da kafafuwanta daga kan gadon ta mike tsaye cikin rashin kuzari ta fita dakin zuwa dakin mahaifiyarta.
Iya na jin motsin an taba kofar tai saurin tura kwaryar dake hannunta karkashin gado ta ta juyo da sauri tana fuskarta kofar. Ganin Zainab ciki yanayi na damuwa da bacin rai yasa ta dan sake tata fuskar duk da kasancewar ita ma tana cikin nata damuwar.
“Zainab lafiya dai?”
Zainab bata amsa ba ta zauna bakin gadon, Iya yayinda Iya take zaune kasa.
“Ina son nai magana da ke Iya”
Iya ta gyara zama tana fuskarta Zainab da kyau gabanta na faduwa sai tsoron tambayar da za ta yi mata take.
“To ina saurarenki”
Zainab ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, can kuma ta bude soma magana cike da nauyin baki.
“Iya a baya ina miki kallon ke mahaifiyata ce, amman a yanzu zuciyata tana min kwankwanto, na kasa samun natsuwa