Showing 108001 words to 111000 words out of 286946 words

Chapter 37 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

933

Falmata ta mike tsaye ta nufi dakin yaran ta fara aikinta. Bayan ta gama aka kawo mata abun karyawa sai ta dauki tray ta fita waje can gurin Garden ta zauna ta ci abincin mai rai da lafiya, sannan ta dawo da kayan gurin data saba aje su ta dawo dakin yaran gurin rainonsu. Cikin kwana biyun nan sun fara sabawa da ita musamman Labib yadda yake far'a da zillo idan ya ganta sai ka rabtse da Allah daman can a hannunta ya bude ido, ita da su da gan game da an dace ne domin ita na tana son yara balle kuma wa'dannn da suka kwanata mata a rai, take wuni tare da su basa barin hannunta har sai sun yi bachi. Misalin biyu da yan mintuna wata hadima ta shigo dakin ta sanar mata cewar an mata izini fitar, a lokacin tana goye da Luma dake ta aikin kuka alamar bachi take son yi.

“Dan Allah kin san agogo ki duba min ko karfe nawa?”

“Eh biyu da minti arba'in da takwas”

Hadimar ta fada tana kallon agogon bangon dake dakin yaran.

“Na gode”

Falmata ta amsa ta, sannan ta dauko Labib da abun wasansa ta nufo falon Ammy da shi, Jekadiya na zaune falon tare da Iya, Iya na ganin Falmata ta yi wani abu da kai ta dauke fuska kamar ta ga kashi, gaban Jekadiya Falmata ta sauke Luma da Labib sannan tai mata sallama ta tashi, sai ta juya sannan iya ta iya dago kai ta kalli bayan Falmata domin a yanzu tsoron hada ido take da ita.

“Ni kam Jekadiya da ni ce, da n bawa Ammy shawara, Babban Mutum ya nemi matar aure ya huta da irin yaran nan yan kama guri zauna, ba a san halinsu ba”

Jekadiya ta yi murmushi.

“Ai ko matar aka kawo kin san ba su ke raino ba, dole mai raino za a dauka, kuma an kusa inshallah ni ma dazun Ammy take min albishir”

Iya ta gyara zama cike da son jin labari.

“An samo masa wata kenan...?”

“Eh inshallah”

“Allah yasa ma yar gida ace a huta, idan kuma ya kasa samun waje ba ga Hajiya Karama ba”

Jekadiya ta mata kallon mamaki jin furuncinta.

“Hmm ita ma wannan yar gida ce, tun da Mai girma Waziri ba bari ba ne”

“Eh haka ne, kam kai Mashallah Yar wajen Waziri ce kai mashallah”

Iya ta fada ba dan ranta ya mata dadi ba, zuciyata sai kokarin gano mata take wace yar Waziri a ciki.


**
Wajen gate din Falmata ta fito ta tsaya, tana ta raba ido, ta kusan minti ashirin a tsaye sannan ta hango Sirleem ya fito daga bangarensu cikin wata motar wacce ba ta jiya ba ash colar, tun daga nesa da gane shi ne domin ta dade da haddace fuskarsa sai da ya kawo kusa da ita sannan ya rufe gilashin motarsa ya mika hannunsa ya bude mata front seat sai ta zagaya ta shiga ya tashi motar suka nufi gate.

“Ina wuni”

Be amsa mata ba sai ya sakar mata murmushi yana cin apple.

“Bismillah”

Ya mika mata da dayan hannunsa dayan hannun kuma yana tuka mota da shi.

“Aa”

“Da dai kin ci ni da matsala”

Bata ce matsa komai ba, domin bata ji abun da ya fada ba, bisimillar da yai mata ma ta gane ne saboda ya miko mata.

“Zan kai ki na aje ne, saboda akwai aikin da zan yi idan kin gama sai Momy ta dawo da ke”

Ya rada mata.

“Tau”

“Fada min me kika yi har Babanki ya mareki haka?”

Ta yi shiru tana mursa yatsun hannunta.

“A lokacin da aka kore ni aikin a nan gidan ne, sai Umma ta ce ma Babana wai ta gan ni da wani mutum muna aikawa assha”

Ya kalleta yanayin yadda take maganar kadai ya isa ya sakar maka cewar tana daf da fashewa da kuka.

“Abun nan akwai ciwo sosai kazafi, bayan shi kuma aka hada miki da duka I'm sorry”

Bata ce masa komai ba, sai kokarin tare hawayenta take. Wannan karo daga muryarsa yai ta yadda zata ji.

“Shiyasa kika yi kokarin guduwa ko? Now i realize irin wuyar da kike sha a gidanku, amman kin san me?”

Ta girgiza kai.

“Idan kika yi hakuri wata rana zaki ga ribar hakuri, amman idan kika gudu zaki afka wata rayuwar ne da ba lallai ne ki dace hannun kwarai ba, kuma idan zaki yi aure ko kika haihu abun zai biki ya bi zuri'arki ne, ki bata future dinki ki koma dana sani”

Nan ma shiru tai bata ce komai ba, ido ya kura mata kamar ba tuki yake ba.

“Ya ma sunanki?”

“Falmata...”

“Kina da Kyau...”

Wani irin dadi ne ya lullubeta, an sha fada mata tana da kyau daga maza har mata yan'uwanta amman bata tab yarda da tana da kyau ba saia yau da Sirleem ya yabe ta, bata taba jindadi dan an fadi cewar tana da kyau a sai yau da Sirleem ya fada.

“Kina da Kyau”

Ya sake maimaitawa yana kallon pretty face nata.

“Da kin bi duniya zaki yi arzik ki samu duk abunda kike so, amman zaki rayu cikin kunci da nadama, just like Mansura, banbancinki da ita ke wahala ce tasa kika gudu ita kuma auren dole za ayi mata shiyasa ta gudu”

Ta dan dago kadan ta kalleshi cike da jin nauyinsa.

“Bata son shi ne?”

Ya tabe baki yana kallonta sai kuma ya kalli titi ya kwanto kamar saurayi da budurwa suna fira.

“Uhmm kusan haka, kin san su yarbawa idan akaiwa mace aure mostly su suke ciyardar mazansu, ita kuma tace ba zata iya wannan ba, hasalima bata son auren yarenta, daga haka ta gudu daga Ondo zuwa Lagos, sai ta fada hannun wani mawaki dan iska, shi ya koya mata iskancin har ya zame mata business, idan za ayi rawa ko wani abu da ita ake zuwa, ni kuma naje studio wani aiki sai na hadu da ita, ta fada min tana son waka kuma she's my big fan, hakan yasa na hada ta da wani manager na dake Kaduna, after ta zo Kaduna ta yi waka sai wakar ta karbu saboda ta fadi dalilin guduwarta, ba ni kadai ba mutane da yawa sun tausaya mata, at that time da muke magana da ita sai ta nuna min da ace zata samu ta gina kanta da zata daina karuwancin domin abun yana damunta, i like that girl saboda tana da addini but a lokacin can Zina ta zame mata ado, so i decided to help her sai na kama mata gida a Kaduna, na zuba mata komai a ciki saboda ita ta daina karuwancin, and i got lucky ta daina din, amman sai duniya ta dauki cewar na kama mata gidane saboda na maida ita karuwata, i face alot of challenges saboda haka har daga gurin Hajiya, to me taba mace rumgumarta gaisawa da ita ba komai ba ne a gurina, amman ban taba zina ba, har gaban Ubangijina zan fadi wannan, so kazafin da akai min ya min zafi amman hakan be saka na rabu da ita ba, ina ziyararta time to time, kamin na ankaro boom...! ta fada so na, a lokacin da ta tallata min kanta ba zan iya ce mata a'a, i accept it na saka ta istibira'i and guess what?”

Ya karasa yana kallon Falmata da murmushi a fuskarsa, sai kuma ya bawa kansa amsa.

“Sai Hajiya tace ba zan auri ta, saboda yare ce kuma karuwace sai dai na auri Nana, bana son ta amman haka na daure ina ta koyawa kaina sonta, saboda Nana bata daga cikin irin matan da nake so, ina son mace mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata ba irin Nana ba, kuma ni bana son farar mace a yadda nake fari sai na samu baka zai fi bada kala ai, ina son mace mai addini da natsuwa kuma black beauty just like you”

Ya fada daidai lokacin daya fakin harabar asibitin yana murmushi. Duk wani abu da Sirleem ya fada Falmata ta ji shi sai inda ya saka turanci ne kawai bata gane ba. Kallonsa tai kadan sai ta ji ya ji ya cika mata ido sosai har sai da gabanta ya fadi, sunkuyawa tai har ya fita motar ya zagayo ya bude mata side dinta.

“Ke baki ba ni labarinki ba”

Ya fada saitin kunnunta bayan ta fito motar.

“Ba ni da labari”

“No kina da your Family Papa Mama da kowa ma karatunki shekarunki and so on...”

“Ni...”

“Eh... ”

Sai kuma ta shiru bata sake ce masa komai ba har suka soma nitsawa cikin asibitin, a lot of people sai kallonsa suke wasu na gaisawa da shi ciki har da masu daukar hoto da shi.


Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
28

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

FALMATA POV.

Shine a gaba tana biye har suka shiga office din Momy, tsaye suka same ta basu baya tana sanye da rigar likitoci tana duba wasu takardu dake gabanta.

“Momy how are you”

“Fine kun shigo?”

“Eh amman nan zan barta akwai aikin da nake, idan an gama sai na aiko driver ya dauke ta”

“Okay you can go”

Ta fada ba tare da ta juyo ba, shi kuma be damu ba ya nunawa Falmata kujera.

“Je can ki zauna”

“Tau”

Sai da ta zauna sannan ya juya fice yana yi ma Momy sallama. After ya fice Momy ta juyo fuskarta shakaf da hawaye ta kalli Falmata tana kokarin danne kukanta, sai kuma ta zagaya ta zauna a kujerarta tana hawaye. Falmata dai sai kallonta take ganin babbar mace kamar Momy tana kuka. Kuka sosai Momy tai sannan ta saka tissue dake gaban teburinta ta goge fuskarta.

“Ya goshinki...?”

Ta tambaya da muryar kuka sai kuma ta sake fashewa da kuka. Ganin hakan yasa Falmata ta ce.

“Ko na kira Sirleem?”

“Aa, ba matsalar shi ba ce matsala ta ce ni kadai”

“Baki da lafiya ne?”

“Ina lafiya, kawai ina jin ciwo ne idan ana min gorin haihuwa, akwai ciwo a rashin haihuwa, idan na ga yara kamar ke ko kasa da ke ina jin kamar na sace, yan'uwan mijina da abokiyar zamana suna min abubuwa saboda ni ban haihu ba, kun zo a lokacin da wani abun ya bata min rai ne”

“Inshallahu zaki haihu, aure haihuwa, mutuwa duka lokaci ne”

Momy ta share hawayenta tana jin yadda kalaman Falmata suka saukar mata da natsuwa.

“Haka ne, haka mijina yake fada shi ma be cire rai da cewar zan haihu ba, ni ma ban cire rai ba ko dan rikon da nake ma Ameer ina fatar Allah ya dube ni ya ba ni haihuwa”

Ta karasa idonta na cika da hawaye. Sannan ta dauko takarda ta rike biro tana tambayar yadda Falmata take ji da kuma lokacin da abun ya fara, after ta yi nata bincike ta kira likitan kunne ya dubata ya rubuta mata magani, da kanta ta karbi takarda maganin taje ta siyo mata a pharmacy dake asibitin sannan ta dawo office din waya a kunnenta.

“To ka biyo ka sauke min bakuwa a Masarautar su Sirleem”

Tana fadar hakan ta sauke wayar ta mikawa Falmata maganin, kamin ta shiga mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi. After like thirty minutes Ameer ya shigo Office din, hannunsa rike da makullin mota.

“Tashi kuje shi zai sauke ki gida”

“Tau na gode Allah ya saka da alheri”

“Ameen, drive carefully”

“Okay Mom”

Ya amsata sannan ya juya suka fita tare da Falmata, a tare suka jera har gurin da ya aje motarsa, sai ya shiga sannan yai unlock din motar ta bude ta shiga.

“Ina wuni”

Ta gaishe shi ba dan ta san zai amsa mata yadda zata ji, bata a damu da sai ya amsa mata din ba, ta maida hankalinta gurin titi tana kallon motocin dake shigowa cikin asibitin a yayinda su suke kokarin fita. Lokaci zuwa lokaci yake kallonta haka nan yake jin takwanta masa a rai natsuwarta ya masa. Sau daya ta juyo ta kalleshi sai ya sskar mata murmushi ba ta sake kallonsa ba har suka isa bakin gate din Masarautar, sai da ta masa godiya sannan ta bude motar ta fita, be bar gurin ba sai da ta shige cikin Masarautar sannan yaja motarsa ya gaba. Cikin masarautar ta shigo rike da ledar maganinta dake cikin hijab, kai tsaye ta nufi bangaren Ammy, tana isa ta danna door bell din wata hadimar ta bude mata, babu kowa a katon falon sai ac da katuwar plasma, dakinsu yaran ta nufa, a hankali ta tura kofar ta shiga, sai ta samu Luma ta yi tana ta bachi, Labib kuma baya dakin, fita tai daga dakin ta sauka saka gaba daya ta nufi Garden daman da yamma haka a gurin take zama ko da yaran, balle yanzu da babu ko daya a hannunta.



SHATTIMA POV.

Ya farka da tunanin maganar da sukai jiya da Baba Waziri, babu abun da yafi tsaya masa a rai kamar maganar aure da kuma transfer, ba wai baya son zama kusa da iyayensa ba ne, irin halin da Mai Martaba yake ciki yana daga masa hankali gashi kuma idan yana gari dole ne sai an saka shi cikin harkokin sarautar. Sakon DSP Nura ne ya shigo wayarsa cewar police din daya bukata suna waje suna jiran Zainab, call list dinsa ya shiga ya kira Zainab ya sanar mata, sannan ya mike tsaye ya fito harabar gidansa, a zahiri motocin dake jera a harabar gidan yake kallo, abadini kuma zuciyarsa na can ta lula wani gurin da tunani. Juyawa yai koma ciki yana shiga ya tube tufafin jikinsa ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya sai kamshin turare yake kamar wani sabon ango. Keys dinsa ya dauka da wallet dinsa ya nufi motarsa Baba Adamu na ganin haka ya taso da sauri.

“Ran ya dade masarauta zamu je?”

“No zauna abun ka ni kadai zanje”

Ya furta yana bude motar ya shiga, kamin yai warming din motar har mai gadi ya bude masa gate. Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da masarautar daman can a ka'ida ba a masarauta yake kwana ba sai idan ta dauro, duk wani abun daya shafi masarautar yana nisanta kansa da shi domin ko kadan sarautar bata burgeshi. Tun daga babban gate din har cikin gida ake ta mika masa gaisuwa amman be amsa ko ka daya ba, daman can kasaita bata barinsa amsa gaisuwa balle kuma yanzu da tunani ya saka shi gaba. Yadda ya fito cikin motar yana takawa sai ka rantse da Allah ba zai mutu a saka a cikin kasa ba, kallo daya zaka masa kasan cewa jinin sarauta ne, domin sarautar ta nuna a tafiyarsa da maganarsa da isarsa da fuskarsa da kamalarsa ga wani irin kasaita a tafiyarsa kamar shi ne sarkin ma. Kai tsaye ya nufi bangaren Mai Martaba sai ya kararda shi yana bachi, hakan yasa ya dawo bangaren Ammy, sai da ya fara duban yaransa dake hannun Jekadiya sannan ya nufi dakin Ammy ba tare da ya tambayi mai rainonsu ba. Ammy bata dakin Sai Nana dake aikin mata abincike a wardrobe ganin Shattima yasa jikinta ya fara rawa.

“Ya Shattima sannu da zuwa”

“Yauwa Sis Morning baki je school ba”

“Eh sai gobe?”

“Why”

“Bana jin dadi ne, kuma na fadawa Driver yaje makarantar ya fada”

“Me ke damunki?”

“Fever amman an sha magani”

Tana amsa masa ta nufi kofa da sauri, shi kuma ya bita da kallo cike da kulawa. Tana fita Ammy ta shigo rike da plate din wainar kwai a hannunta.

“Morning Ammy”

“How are you?”

Ya dan tabe baki alamar ba Kalau ba.

“Tunani ko rashin lafiya?”

Ammy ta tambaya yana mika masa farantin.

“Tunani dai”

Sai tai murmushi.

“Waziri ba zai yi abun da zai cutar da kai ba, ni kaina na dade ina son ka dawo garin nan da aiki ka ki, yanzu kuma baka isa ka sabawa Umarninsa ba”

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon Ammy.

“Maganar Auren ma bana fatar ka saba masa, tun da har ya zabi rufe ido ya aura maka yarsa be kamata kace aa ba”

“I accept it”

Daga haka be sake cewa komai ba. Be koma bangaren Mai Martaba ba sai da suka fito daga sallah la'asar. Ko da ya shiga falonsa sai ya same shi a ciki zaune, ko'ina na falon duhu ne kamar dare, bayan kuma yamma ne akwai haske a ko'ina. Ganinsa a falo ma abun ma farinciki gurinsa domin a da kullum yana kan gado kwance, amman yau gashi akan kujera zaune. Kamin ya karasa kusa da shi yai masa sallama, Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Shattima, wanda siffarsa da ke shimkide a siffar Shattima kallo daya zaka masa ka san jini daya ne. Gaban Mai Martaba Shattima ya zauna yana murmushi.

“Barka da Yamma Mai Martaba ya kufan jiki?”

“Alhamdulillah”

Mai Martaba ya amsa yana ta kallon Shattima.

“N ga jiki ya fara kyau Alhamdulillah”

Shattima ya fada cikin jindadi, sai Mai Martaba yai murmushi ya ce.

“An samu shigowa?”

“Eh Baba Waziri ne ya kira ni jiya, akan maganar fitar da kai waje da kuma aurena da neman transfer”

A hankali Mai Martaba ya sauke ajiyar zuciya.

“Hakan yana da kyau, ni kaina aurenka yana cikin rai na, neman transfer ma yana kyau, domin kai ne babba a yanzu, sai dai magana fita da ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login