Showing 264001 words to 267000 words out of 286946 words
“To ya Sayyada”
Be yarda ta taka ta kafarta zuwa gurin motar ba, daukarta yai har gurin motar ta bude mata ta shiga sannan ya zagaya dayan side din ya shiga, be yi ma motar key ba har sai da ya saka yatsunsa cikin nata ya rike hannunta sannan ya fara tukin. Kamin su isa gida ya biya ta gurin wani katon shopping mall mai tsada na manyan attajirai yai ma Baba siyayya turare sannan ya dawo cikin motar ya sake rike hannunsa suka kama hanyar, kamin su isa sai ta rika jinta a wani yanayi na daban, wai ita ce zata je ganin gida daga gidan mijinta kuma tare da mijinta, so all her sad story ya zama story yanzu, take ta ji idonta ya cika da kwalla saboda canjin da Allah yai mata bayan dubun hakuri da wahalar da ta sha. A hankali ta kalli Sirleem sai shi ma ya kalleta sai turo mata bakinsa yai.
“Kiss me Kiss me”
Hannu ta kai ta buge bakin a hankali sai yai dariya ya kai hannunta saitin bakinsa yai kissing din hannun. Saboda yanayin unguwar yasa yai bakin waje ya dauko glass dinsa ya saka so that yayi badda sau, sannan ya bude motar ya fita ya zagaya bangaren Falmata ya bude mata ta fito, yai saka ma motar lock suka nufi hanyar da zata sada su da gidan yana rike da ledar turarun da ya siyowa Baba. A lokacin da suka isa bakin kofar gidan sai ya tsaya daga waje har sai da tai sallama ta fara shiga sannan ya shigo yana sallama da karewa gidan kallo.
Tumba na zaune bakin kofar dakinta rike da sandar da take dafawa idan zata tashi ko tai tafiya, sakamakon cirewar da kafarta tai sanadiyar natsarin da tai, ba a maida kafar ba saboda jijiyoyin su tsinke, daurin da akai nata a hannu ma ya kumbura sai ruwa yake mata, satin da daya asibiti ta dawo gida saboda babu kudin magani, a lokacin da ta dawo gida sai yan bani na iya suka rika duba mata ciwon suna kara janyo mata aiki, bayan ayi daurin aka dade ba a duba ba ko da aka kwance sai aka ga ya fara ruwa daurin ya lalace, haka nan dai da karfin hali da taimako aka koma da ita asibitin aka sake mata wani nan ma ba a dace ba, ta sake dawowa gida tana jinya, jikin nan nata duk ya zube ciwon ya janyeta har wani tsufan wahala ya taso mata.
Akwai hasken farin wata ga kuma gulof kasancewar akwai nepa amman hakan be wadatar da ita ba sai da ta dauki touch light dinta ta haska Falmata domin tantancewa.
“Falmata ke din ce da gaske?”
Tumba ta tambaya tun kamin Falmata ta karaso inda take.
“Na'am Umma ina wuni”
Ta tabe baki tana jin wani irin bakinciki ganinta cikin shiga mai kyau ga jikinta ma ya fara kyau.
“Hmmm ashe kina tunawa da ni? Ai mutunci da karamci be ce haka fa Falmata, saboda ba ni na haife ki ba, shiyasa kika ji zuwa ganina asibiti ko? Sai yanzu za ki dauko kafa ki taho dan ba ki da kunya, wato tun da mun aura miki tsoho mai nera kina can kina kwantawa a gado mai kyau kina yadda kike so sai ki watsar da mu”
Kamin Falmata ta yi magana Sirleem dake tsaye ya ce.
“Yanzu ma Baba muka zo gani, ina fatar yana nan”
Falmata ta kalleshi da sauri jin abun da ya fada, Tumba kuma ta sake daukar fitilarta ta haske shi.
“Wanene wannan? Kanen mijinki ne ko dansa?”
Falmata ta kalleshi sannan ta kalli Tumba ta ce.
“Mijina ne”
“Wannan...?”
Tumba ta tambaya da karfi har zawo na kubuce mata, ta sake haska fuskarsa da sauri tana ganin kamar ta taba ganinsa.
“Ke Falmata kalli fa wannan ki gani, mu da muka aura miki tsoro? Na shiga uku ko aljani ne dai”
Cewar Tumba sai wani maida numfashi take cikinta na murdawa.
“Wallahi mijina ne Umma shi ne kuka aura min”
Falmata ta fada, tana kallon Naja da ta shigo gidan da sallama, at first kallon mamaki ta fara yi ma Falmata, sai Sirleem ya cire glass din idonsa so. that Tumba dake haska shi ta tantance ko waye. Naja na kallom Sirleem dake tsaye tai baya baya, bata san lokacin da ta daka tsalle ta daki kirji tana fiddo.
“Umma Sirleem Sirleem M2 Wayyo na shiga uku Wallahi Sirleem M2”
Ya fada cikin rikicewa mai kama da hauka ganin celebratie a fili kuma a cikin gidansu, abun da ba ta taba tsammani ba.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
64
*Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Tumba ta fito da ido waje tana kallonsa, sai a yanzu da Naja take fadar sunansa ta gane ko waye duk da ba wani saninsa tai can sosai ba, sai dai tana ganin hotunansa da wakokinsa can sama sama.
“Sirleem dai mawaki”
Tumba ta fada tana nuna shi jikinta na rawa, kamar ta unkura ta tashi sai kuma ta saka tsabar mamaki da kuma rashin kafarta ta hadu.
“Allahu Abkar, to to to ni ban gane wannan abun ba, daman can shi ne yai siffar tsofi ko kuma babansa ne?”
“Shi ne dai”
Falmata ta amsa tana kallon Sirleem. Tumba ta girgiza kai tana kallonsa, domin a iya tunaninta sun aurawa Falmata tsoho ne kuma inda zata je ta sha wahala ashe gurin jindadi ta kaita ba tare da ta sani ba, daman can waya isa yai ma bawa abun da Allah be masa ba?
“Allahu Akbar Allahu Akbar, wani abu sai Allah, hakika abun da Allah ya rubutawa bawa be isa ya wuce shi ba, Wallahi yanzu kam na yarda”
Ta fada cikin kuka, tana kallon Baba da shigowar kenan rike da jakarsa ta zuwa kasuwa, Naja taje ta sauri ta karba saboda halayen kirkirin da ta kirkiro masa ganin ya fara wulakanta mahaifiyarta balle kuma ita, sai ya fisge abarsa ya karaso yana kallon Falmata.
“Wa na ke gani haka?”
Ya tambaya cike da far'a kamar ba shi ba, abun da Falmata ba tai tsammani ba daga gareshi.
“Ni ce Baba Sannu da zuwa”
Ta fada tare da kai hannu ta karbi jakar sai ya girgiza mata kai ya duka da kansa ya aje.
“Yanzu kuma Allah ya dauke miki wannan nauyin, dawainiya ta koma gurin mijinki”
Ya fada yana kallon yarsa cikin da farinciki da ya shafe shekaru be yi ba, Sirleem ya duka yana gaishe shi cike da girmawa tare da aje masa ledar turaren da ke hannunsa, kana ya kai hannu aljihunsa ya dauko kudo mai kauri ya saka a ciki ledar.
“Lafiya Kalau Wannan fa?”
“Wanda kuka aura min ne Baba”
Baba ya ja baya da sauri yana nuna Sirleem ganin zankadaden saurayi a gabansa bayan kuma shi ya san tsoho ya aura mata.
“Wannan? Ko dai idona ne ba su gani daidai kamar yaro na ke gani”
“Shi ne Baba”
Baba ya kalli Falmata wanda ta amsa masa cikin tsoro domin har yanzu be yarda ba.
“Ya akai ya zama yaro? duba dai”
Sirleem yayi murmushi tare da mikewa tsaye.
“Baba zan tsaya a waje Fatima za ta warware muku komai inshallahu”
Ya nufi kofa daga Tumba har Baba da Amaryar tasa kallonsa suke har ya fice. Baba ya kalli Falmata.
“Ban gane ba, daman can ke kin san yaro ne?”
Sai ta girgiza kai ta fara bashi labarin farkon haduwarsu har zuwa aure da abubuwan da suka faru, tun Baba na tsaye har kai ya dauko kujera ya aza ya zauna yana sauraren Falmata, tana fada Tumba na kuka Naja ma ta rafka uban tagumi tana kallonta. Sai da ta kai aya sannan Baba ya share hawayen da suka cika masa ido yana fadin.
“Allah ya dubi zuciyarki da maraicinki, da kuma halayenki na kirki da kika rike shiyasa ya bude miki kadan faga falalarsa da kuma rahamarsa, na sani na cutar da ke iyakar cutarwa, kuma har ga Allah bana jin dadin abubuwan amman ya zamin kamar dole na musguna miki, mahaifiyarki ma na mata...”
Ya fashe da kuka, daman tun da hankalinsa ya dawo yake cikin damuwar abubuwan da ya aikata, Falmata ma hawaye take, Tumba na kukan nadama da dana sani.
“Na tabbatar idan na mutu a halin nan, sai Allah ya hukunta ni domin yaya ma suna da hakki akan uwaye kamar yadda uwaye suke da hakkin akan yaya”
Falmata ya matsa kusa da shi tana hawaye.
“Ba halinka ba ne Baba, da can ba haka kake mana ba, idan har akwai wani hakki nawa da yake kanka Wallahi n yafe maka shi duniya da lahira, kuma ina rokon Allah wanda ke tsakaninka da Mama ya daukar maka, na jidadi Baba yanzu ka gane gaskiya”
“Hakika ba hali ba ne, halin wacan bakar matar ne, tun da ta shigo rayuwata komai ya lalace min, dangina ma yaushe rabon da na je ganinsu? Ta zallumci ni ta cutar da ni, na sa na ci amanar uwar yayana kuma na ci amanar yayana, Allah ya isa tsakani da ke Tummmba Tummmba Allah ya tsine miki albarka, yarana kuma da kike ikirarin ba ki iya zama da su zan dawo da abuna cikin gidana kina da rai zaki gan ni da wata matar na auro mai son yayana, ke kuma Allah ya tsine miki albarka, babu irin cin amanar da ba ki yi ma yarinyar nan ba, babu kalar sherin da ba ki mata ba, kuma ni ma kika min, ina jin son yata a zuciyata ina tausayinta amman ban isa na nuna ba”
Tumba ta hade hannayenta biyu tana wani irin kuka da bata taba mafarkin zata yi ba, domin ko a lokacin da hadarin ya faru hankalinta ya bace bata san zafin ciwon da bakincikin cirewar da kafarta tai ba sai daga baya, sai abun ya zame mata kukan zuci wanda ya fi na idanuwa zafi da bakinciki, domin ta rasa kafarta ga hannu kuma sai ruwa yake.
“Malam ka dubi girman Allah ka yafe min, dan'adam ajizi ne”
“Ajizo na ce Ajizo, da can ba ki san da haka ba sai yanzu da Allah ya kama ki? Ai ko wannan kadai ya isheki ishara, ga shi nan baki ga hannu ba ki ga kafa, kuma yarinyar da kike ma fatan sheri gata nan kin jefata cikin alheri ba tare da kin sani ba, ba ki isa ki hana abun da Allah yai mata ba, gashi ijaba nan kin gani Allah ya kaita a matsayin da babu wanda ya taba taka shi a cikinmu, Allah yai miki albarka Falmata ke kuma Tumba Allah ya tsine miki, kuma Wallahi babu ni babu ke daga yau daman can ba ni wani rabon mugun iri dake, ki hada komai na ki bar min gidan na saki”
Naja ta fashe da wani irin kuka ta rugo da gudu ta zube gabansa.
“Baba dan Allah kai hakuri”
“Ni ba ubanki ba ne, tafi can ki nemi ubanki kuma na kara mata saki daya ya zama biyu”
Tumba ta daga hannunta nan daya ta fashe da kuka tana ihun da duk wanda ke makotaka da su a kusa zai ji.
“Ba ki shiga uku ba, tukuna nan yanzu na kara miki wani sakin daya sai ki shiga ukun, kuma ina rokon Allah ya tsine miki albarka”
Falmata ta rufe baki da sauri jiki na rawa jin irin sakin da Baba ya jerawa Tumba a take. Kukan da take ne yasa makota suka rika shigowa suna tambayar ba'asi, Baba abun da Baba ya boye daga kan abubuwan da take saka shi yana yi har zuwa wanda take yi ma Falmata, sai a lokacin ne mutane suka san gaskiyar abun da yake faruwa, domin kowa yana mata kallon mutuniyar kirki saboda yadda take nunawa Falmata kauna a gaban idon mutane kamar zata hadeye ta, babu abun da ya bawa mutane mamaki kamar maganar auren Falmata, a nan wasu suka yarda domin kowa yayi mamakin jin Falmata zata auri tsoho yarinya kyakkyawa kuma mai kananan shekaru. Duk wanda ya shigo gidan ya ji abun da ya faru sai mamaki ya kama shi, gashi babu bakin bada hakuri domin mai faruwa ta faru Baba ya riga ya aikatawa Tumba mai gaba daya. Tumba kan kuka kawai take tana fadin ta shiga uku amana ta kamata, Falmata bata labarta musu wanda take aure ba balle su san fittacen mutum ne, sanin yaro ne yai shigar tsofi ma Baba ne ya fada, Naja kuma ana ciki kuka da jimamaki hakan yasa babu wanda ya san Sirleem ne, sai hakan be hanata zama abar kallo ba saboda tufafin jikinta da kuma gidan da aka kaita domin duk wanda yajr walimarta ya ga gida abun da ake kira da gida, har wadanda ba su je ba ma sun samu labarin irin gidan da aka kai Falmata.
Sai kusan goma na dare Falmata tai ma Baba sallama yana ta saka mata albarka, yana mata addu'a har da hawayensa har lokacin yana jin bakinciki da nadamar abun da ya aikata. Sai bayan da Falmata ta wuce ne ya duba kayan da Sirleem ya bashi ya ga turaruka masu tsada da kamshi gaske ga kuma kudin da za su haura 70k a ciki.
“Allahu Akbar Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar, Allah kai mata albarka”
Ya fada yana share hawayen idonsa. Falmata ta isa gurin da Sirleem ya aje motarsa tana hawaye, tana jin kamar ace mahaifiyarta tana raye ta ga wannan ranar, ta dayan bangaren kuma zuciyarta na cike da farincikin dawowar Baba a hayyacinsa, tana taba motar sai Sirleem ya mika hannunsa ya bude mata motar ta shiga ta zauna ta rufe. Sirleem na kallonta ya san akwai wani abu, hannunsa ya kai ya kama hannunsa ya dora a kirjinsa.
“Haba dai karki ce min tausayin matar can kike”
Ta kalleshi.
“Baba ya sake ta, ta rasa kafarta kuma hannunta yana ruwa”
“She get what she deserved”
“Rayuwa abar tsoro ce Baby, wani lokacin Allah yana kyale bawa yai ta abun da yake so, idan ya tashi taba shi kadan zai taba shi amman sai ya zama abun tsoro, duk da irin makircinta bata hana Allah yi min abun da ya kaddara min ba, kuma gashi ta fara riskar sakamakonta tun a yanzu bayan hukuncin da zata je ta tarar a lahira”
Ta lumshe ido hawaye na sauko mata.
“Daman duk wanda za ayi wa hassada ko kuma a cutar da shi, to zai yi ta samun cigaba ne, kuma zai ga riba hakuri a duniya kamin ya riski ladar lahira, I love you...”
Bude idon tai ta kalleshi sai ta ji wani irin farinciki ya lullubeta marar misaltuwa.
“Alhamdulillah”
Ta furta sai ya ari numfashinta.
“Yeah Alhamdulillah da Allah ya ba ni mata irinki”
Ta yi murmushi shi kuma ya tashi motar yana tukawa da hannun daya yayinda dayan hannunsa yakr rike da hannun babynsa, time to time yake kissing din hannun kamar wani abun da ya zame masa dole. A zatonta gida za su wuce kai tsaye sai ta ga sun dauki hanyar zuwa Family house din su Hajiya Babba wato inda take zaune a yanzu, this is the second time da zai kaita gidan bayan zuwansu na farko a lokacin da ake shirye shirye fitar da Hajiya Babba India, ya je tare da Falmata ya nemi yafiyarta Falmata kuma tai mata bankwana, a lokacin Falmata ta yi zaton Hajiya Babba zata mata wulakanci ne ko ta mata wani abun, sai dai babu ko daya ta kanta take ma, kana ganinta kasan tana cikin ciwo, a Lokacin kam Sirleem ya shiga cikin tashin hankali sosai wanda ya saka Falmata ita ma ta shiga damuwa ganin mijinta ma a cikin damuwar, kusan kullum idan ya taso daga aiki sai ya je gurin Hajiyar, kuma be fasa bacin rai ba saboda halin da ta koma, bata iya komai da sashenta daya, bakinta kuma yaki dawowa daidai, komai take ci sai ya zubo mata ta gefen bakin haka ma yawu ke sauko mata gwanin tausayi, gaba daya ta canja kamar ba ita ba, cikin kankanen lokaci jikinta ya koma kamar na tsofi, sau uku ana fitar da ita waje amman babu wani canji kuma idan sun auna basa ganin komai, Jurry kam sau daya aka fitar da ita saboda ciwon kan da ya saka ta gaba nan suka ce ba su ga komai ba, ana dawowa da ita sai abun ya kara kamar an takaloshi sai ya taba kwakwalwarta har ta kai tana yin wadansu dabi'u da halaye irin na masu tabin hankali, zata zauna ayi fira da ita cikin mutune sai dai da an fara zata fara barin zance tana dariya irin na masu fama da hauka, hakan ya saka komai na rayuwarta ya tsaya cak bata fita ko'ina daga gida sai gida.
Sirleem yayi bakin harabar katon gidan da ya kusa gida ukun wani mutum, sannan ya bude motarsa ya fita kamin ya zagayo har Falmata ta bude ta fito.
“Ba mu siya mata komai ba”
“Babu abun da babu a cikin gidan nan, babu abun da zata nema ta rasa, ni kaina wani lokacin sai na rasa abun da zan riko mata, saboda ba komai take iya ci ba”
Sirleem ya bata amsa sannan ya nufi kofar shiga Falmata na biye da shi a baya,