Showing 216001 words to 219000 words out of 286946 words
dawo ta sanarwa Shattima.
“Ki ce jekadiya tace ta dubo ta gurin babanta ko taje can”
“Okay”
Ta juya ta fita, shi kuma ya zauna bakin gadon ya kurawa abincin da Fadime ta ci ido, haka nan kawai yake jin rashin natsuwa. Jekadiya da kanta ta je ta duba bangaren da aka sauke su Bappa ta tambaya ko Fadime na nan suka amsa mata tun da yamma da wata hadima ta zo ta tafi da ita bata dawo ba, bata ce musu komai ba ta dawo ta sanarwa Nana, cike da Mammaki Nana ta shigo ta fadawa Shattima.
“Ya bata can sun ce wai tun yamma da wata hadima ta fita da ita bata dawo ba”
Shattima ya mike tsaye still yana jin rashin natsuwa.
“Bata dakin Ammy?”
“Daga can na fito fa”
Shiru yai yana tunanin inda zata shiga, ba gani take ba balle yace ya fita wani gurin. Fita yai dakansa ya saka Jekadiya da wasu hadimai nemanta, wasa wasa har 10 na dare ba a ganta ba, duk inda ya kamata da inda be kamata ba duk an duba har bangaren Hajiya Babba sai da Shattima ya tura a duba ko tana can, daga baya ya koma yana tambayar waye da waye ya shigo cikin gidan. Duk wanda ya ganta da yamma nan zai fadi cewar ya ganta Jekadiya sai nanata take ita ta kai mata abinci ma kuma bata ga fitowarta ba. Sosai hankali Shattima ya tashi wata kila ko dansa ya bace ba zai shiga wannan tashin hankalin ba, babu abuj da yake ji kamar mahaifinta da ke ta shirin tafiya gobe tare da ita, me zai fada musu? Ya za su kalli abun? Ya za su ji? Anya ma za su yarda da shi?
“Jekadiya”
Jekadiya ta matso da sauri.
“Ranka ya dade”
“Address din da na baki last time, kin gane gidan su Hajiya Karama?”
“Eh an gane ranka ya dade har an kirata”
Ta amsa da sauri.
“Ki je da dogarai ku duba yarinyar a can”
Jekadiya ta mike tsaye da sauri ta fita zuwa aikin da Shattima ya saka ta, shi kuma ya nufi dakin Ammy rai ba ce, yana shiga ya zauna a kan kujerarta yana kallon wani bangare na dakinta.
“Kana tunanin za a sace ta ne?”
“Maybe saboda ta saka rayuwarta a hadari, kuma idan Hajiya Babba ta ji ko Iya ba za su kyale ba, ni yanzu babu wanda na ke ji kamar mahaifinta”
“Bana tunanin Hajiya Babba zata ji, saboda ba ayi zancen a gabanta ba, ko a gaban wani nata, Nana ma ban labarta mata ba, sai dai ko Iya ita ma kuma bana tunanin za ta iya shigowa har cikin gidan nan ta saci yarinyar, amman na san tabbas za ta ji zafin tona mata asiri da tai ga kuma abun na saka aka mata a dazun domin ganewa idan da gaske mayyar ce kuma na tabbatar”
Shattima ya kalleta.
“Me kika mata?”
A natse ta labarta masa komai.
“Yeah maybe ita ta sace ta saboda ta ji zafin abun da akai mata”
Ya ciro wayarsa, ya shiga neman wata number after a few seconds ya aikawa number kira.
“Galadima a duba security cameras da suke gidan nan a ko'ina, a duba idan wata bakuwar fuska ta shigo yau, kuma idan ka ga wani abun da baka yarda da shi ba ka sanar min, wata yarinya ta bata bakauniya ka bincika mana ko'ina”
“Tau ranka ya dade”
Ya sauke wayar yana jin wani karin tashin hankalin na kusantarsa.
SIRLEEM POV.
Sai da rana ta fito sannan ya tashi Falmata, cikin wani irin nauyin bachi da ya cika mata ido da kuma nauyin kunyarsa ta farka ta dan daga idon kadan ta kalleta sai ta sake rufe idon. Murmushi yai ya sumbacin goshinta ta yaye bargon da ta rufa da shi ya saka hannunsa biyu ya dauke ta cak, be sauke ta a ko'ina ba sai bandaki, ita kan gaba daya ma ta kasa kwarran motsi domin jikinta har yanzu yana amsa mata ga kunyar Sirleem da take jin kamar masa ta bude ta shige ciki ta huta. Ruwan zafi ya hada ya gasa mata jikinta sannan ya zuba mata tai wanka ta daura tawul ta fito tana ta kokarin danne kukanta domin har ga Allah bayan dukan da Baba yai mata har ya kusan karya mata kafa bata taba karo da wani abu mai zafi da wahalar da mai rai ba irin na jiya. Ko da ta fito ya shimfida mata carpet ya aje mata wasu tufafinta, yanayin yadda tafiyarta ta canja kadai abun tausayi ne. Ba dan ta so ba ta bar shi ya taimaka mata ta saka tufafin da su kadan suka mata yawa.
“Za ki iya yin sallah a tsaye?”
Ya tambaya yana kallonta fuskarta, tausayinta yasa ya ji kamar ya yayi mata sallah. Kai ta daga masa ta kabbarta cikin karfin hali tai sallah, bayan ta gama kuma ta ji zama na neman gagararta, wani iri zafi da yaji take ji a kasanta kamar an yanka gurin, a hankali a hankali take share hawaye tana ta sauke ajiyar zuciya. Sirleem ya matsa kusa da ita ya jata jikinsa ya rumgumen yana shafata a hankali.
“Im sorry”
Ya fada can kuma ya tsaki yana jin haushin rashin hakurinsa. A jikinsa tai bachi sai maida numfashi take a hankali, abun da bata taba ba a jikin wani, shi ma kuma abun da be taba ba ya rumgume mace har tai bachi kamar yadda yai ma Falmata.
Fuskarta yake ta kallo yana jin wani irin tausayinta da kimarta na kara shiga idonta, yatsunsa biyu ya saka ya shafa fuskarta yaja hancinta kadan.
“Pretty girl”
Ya furta yana murmushin farincikin da be san ta ina yake zuwa masa ba. Tashi yai tare da ita ya kwantar kan gadon ya lullubeta yai kissing din kumatunta sannan ya dauki wayarsa a hankali ya dauke ta hoto, sannan ya fice daga dakin, saukowa yai kasa yana kiran wani abokinsa.
“Bilya how far”
“Good ya kake?”
“Im good very good”
Ya fada yana murmushi.
“Dan Allah wa ka san ta kware a iya kwalliya a duk garin Yola, kuma wanda zata iya home services?”
“Akwai su da yawa, Amaryar za ayi ma?”
“Yeah yau za ayi Walima a nan, so ina son ta fito ne sosai, na yi magana da mai kaya tace yau zata kawo da rana”
“Amman Sirleem baka ganin Walima a gidan zai haifar maka da matsala? Za a iya gane kai ne fa”
“No ai ba zan bar wata alama ba, ita ma kuma na fada mata kar ta fadawa kowa, daman dai ina son mutanen da basa son cigabanta ne su ga a inda ta tare, that's all”
“Okay ba matsala lemmi ask my Sis ka san su ne yan gari”
“Okay idan ta fada maka sai ku yi magana da ita, ta zo misalin 3pm”
“Ba matsala angon boye”
Sirleem ya sauke wayar yana dariya, kicin ya shiga dakansa ya shirya musu abun karyawa daman duk wani abun bukata tun daga kan abinci har abun sha da kayan amfani ya zuba a kicin din. Sai da ya gama sannan ya shigo ya tashe ta a hankali yana kissing dinta kama ya samu sweet, a saman gado a jera mata abun karyawa yana feeding dinta a hankali, sai ya tabbatar ta taune sannan yake saka mata wani a baki. Bayan sun gama ya shiga yai wanka ya saka kananan kaya ya zo kusa da ita ya zauna yana janta a jikinsa kamar zai shigar da ita.
“Zan fita yanzu, na san kawayenki za su zo ganin daki, ban da fadawa kowa wanene ni pls”
Ta daga masa kai tana jin kamar tai kuka.
“Ki kula da jikinki idan zan dawo zan biyo miki da wani magani okay”
Nan ma kan ta daga masa sannan ya sumbance ta ya fita. Hakan ya bata damar karewa katon dakin kallo tana mamakin ace wai ita ce a ciki.
ZAINAB POV.
Tana zaune falon har akai sallah magariba sannan ta tashi ta shiga cikin domin yin sallah. Iya na ganin haka ta tashi da sauri ta shige dakinta ta maida kofar dakin ta rufe har da makulli, sannan ta nufi wardrobe ta ta bude ta dauko tukunyar kasar nan mai jan kyalle ta kara bakinta tai magana da muryar da ita kadai zata iya jinta, sannan ta kara kunnenta ta saurari abun da ake fada kamin ta maida tukunyar a mazauninta. Ta duka karkashin gadonta ta dauko wayarta ta bude ta dauko kurwar daya daga cikin kurwa biyu da suka rage ta warware zaren da yake kai sai ga wata yar abu ma kamar tsokar danyen nama karami yana numfashi, rufe hannunta tai ta janyo wani bakin mayafi ta rufe hannun dake dauke da kurwa, sai kurciya ta bayyana ta cikin bakin mayafin yana ta fisge fisge alamar lafiyayya ce mai jini a jika, dukawa ta sake yi wata robar ta janyo ta bude ta dauko wata tsohuwar kaya ta saita bayan kurciyar ta bangaren hannunta na dama ta caka mata ƙayar, take kurciyar ta zabura ta sai ta lafe, wanda hakan yai daidai da zaburar Maijidda dake zaune a dakinta tana duba wasu kayan na order da kawarta ta turo mata. Iya ta maida kurwar ta nade sosai sannan ta dauko wani karamin gwangwani ta kunna aci balbal din jiki ta kifa wani kwano ta dora kurwar a kai ta tura gwangwanin karkashin gado ta tura kwanon saitin wutar ta yadda kurwar zata azabtu, ta kara kurwar a kam wuta, sannan ta sake saka kayar ta soka ta gefen tsokar dake nade ta bangaren damanta daga kasa, can kuma ta tashi ta nufi inda tukunyar nan take ta dauko ta kar bakinta, sai da tai kirarin data saba sannan ta fadi kalar ciwon da take son turawa Maijidda.
Gaba daya sai Maijidda ta rasa natsuwarta ga wani uban zafi da ya sako ta gaba, duk ac dake dakin sai ta ji wani irin zafi ya taso mata, haka dai ta daure tana duba kayan kamin idonta ya fara cika da hawaye saboda azabar ciwon kai, aje wayar tai tana tana jikinta da yai mugun zafi kamar kyankyason wuta, ga bayan ta ta bangaren hannunta na dama sai ciwo yake kamar an soka mata abu a ciki, da zafin ya fara mata yawa sai ta gane ba daga dakin ba ne daga jikinta ne, kamar mahaukaciya haka ta fita daga dakin ta nufi kitchen ta bude firiza ta dauko kankaran ta fasa a roba ta dawo ta dakinta ta shiga bathroom ta surka kankarar ta cire tufafin jikinta ta watsa ruwan kankarar tana jin kanta kamar zai bare, daker ta daura zane ta fito da gudu zuwa dakin mahaifiyarta tana kuka.
“Momy zafi na ke ji sosai, kaina ma ciwo yake kamar zai bare, kuma nan ma ciwo yake min sosai”
Ta nuna bayan kafadarta, ba karamin tashi hankalin Hajiya Talatu yai ba, daman can mace ce mai shegen son yaya balle kuma Maijidda da ta fi kwanta mata a rai fiye da sauran.
“Subhanallahi, me kika sha?”
“Ban sha komai ba, ban ci komai ba”
Ta fada tana lumshe ido tsabar ciwon kan da take ji. Hajiya Talatu ta kai hannu ta taba jikin yarta sai ta ji shi ba zafi.
“Kuma jikinki babu zafi”
“Akwai zafi Momy kaina”
Ta dafe kan tana kuka sosai.
“Yusra, duba driver waje idan baya nan ki kira Haroon yanzu muje asibiti”
Daker Maijidda ta iya saka tufafinta har suka shiga motar Haroon din ya ja su zuwa wata private hospital Annuri, kamin su isa asibitin Iya ta janye kurwar Maijidda jikin wutar wanda hakan ya bawa jikinta damar karbar zafin da kurwar ta dauka, sai zafin ya maye ilahirin jikinta, Hajiya Talatu na tabawa ta ji yayi zafi sosai. Ta samu kula ta musamman kasancewar asibitin wanda ta saba zuwa ce kuma asibiti ce ta masu nera, duk wanda ka gani asibitin babban mutum ne ko kuma dan babban mutum dole a kula da kowa yadda ya dace. Gado suka bata bayan sun tabbatarwa Hajiya cewar taifot ce, allurar suka mata sannan suka saka mata drip, hakan yasa ta dan samu sauki har bachi yai gaba da ita. Sai a lokacin hankalin Hajiya Talatu ya kwanta domin da farko har ta fara jin tsoro tana tunanin ko abun da suka saka ayi ma Fadime ne ya dawo yarta, ko kuma saboda zancen aurenta da Baba Waziri yai ne da Shattima yasa it ma zata leka kiyama.
Zaunawa tai a kujerar dake dakin ta majinyata tana kiran mijinta ta shaida masa abun da ke faruwa, bayan a sauke wayar ta kalli Haroon dake tsaye ta ce.
“Ka tafi gida, ka farawa Yusra da Nazma su shirya komai na kwana sai ka kawo wata a cikinsu ta kawo min”
“A nan zaki kwana?”
“Dole ai, maybe gobe su sallame ta idan ta samu sauki, ka tafi kawai ka fada musu an ba mu gado”
“Okay”
Ya fada sannan ya juya ya fita, fitarsa tai daidai da shigowar kiran Hajiya Babba a wayar Hajiya Talatu, da muryar da za ta karantar da Hajiya Babba damuwarta tai picking call din.
“Hajiya Talatu? Haka aljannun nan suke aiki kamar yankan wuka? Yanzu nan Shattima ya turo a duba masa yarinyar wai ta bata a ganta ba”
Hajiya Talatu ta zaro cikin wani irin jindadi take ta manta da wani damuwar ciwon yarta.
“Alhamdulillahi abun nema ya samu, dauke ta su kai kenan? To ai haka ya fi ba ganta ba balle wata maganar ta fito”
“Wallahi ni ma haka na ce, amman fa tsorona daya kar ta dawo ko kuma ta fadi masarautar nan a dawo da ita”
“Aa haba Hajiya, ai ke ma kin san maganin biri karen maguzawa, ai ba za su kaita inda zata iya dawowa ba, tun da har mun fada musu asiri ne ba ma son ta tonu dole su san yadda za su yi da ita, ni ai murna ta zo min a wani yanayi ga ni a asibiti Maijidda ba lafiya wai tafot ne”
“Subhanallahi Allah ya bata lafiya, agaishe ta da gobe zan shigo na dubata”
“Amin Amin Hajiya na gode sosai”
Ta sauke wayar cikin wani irin farinciki marar misaltuwa.
***
Hajiya Babba na aje wayar ta kalli Jurry da ita ma murmushin jindadi take za ta yi magana sai ga Sirleem yayi knocking kofar sannan ya turo ya shigo. Hakan yasa Jurry saurin mikewa tsaye ta fice ba tare da ta gaishe shi ba, domin ita har yanzu fushi take da shi saboda marin da yai mata kwanakin baya akan Falmata.
Shi dai be kula ta ba ya zauna gaban Hajiya Babba dake ta yakar hakora kamar wanda akai wa gafara.
“Sirleem sai yanzu”
Ta fada tana kallon yadda fuskarsa ke ta annuri kamar ba shi ba, har wani kyalli yake.
“Barka da dare Hajiya”
“Yauwa, ya jikin?”
“Alhamdulillah”
“Ka je asibiti?”
“Eh sun ba ni magani”
Ta yi shiru har na wani lokaci shi kuma sai sake saken yadda zai shera mata wata karyar yake so that ya samu ya sake kwana a gidan amaryarsa.
“Alhaji Kabir ya kira ni, ya ce ka same shi da maganar ka na son a mika maka ragamar mahaifinka a hannunka”
Ya dan shafa kansa.
“Eh tun kwana bayan nai masa magana, yace min na jira ayi a gaban kowa kuma yace zai hada wasu takardun ya hannata min, ya ma ba ni wasu and i think yanzu ya kamata na rika natsuwa ina duba komai yadda ya kamata, jiya a gidan na wuni duba su sai gashi dare ya zo da fever”
“Ayyah, dole ai saboda baka saba ba, amma da sannu komai zai zama kamar an saba din, ya fada min zai tara kowa saboda a zama shaida, kuma yace na saka ranar da nake ganin ya dace a yi launch din new manager a babban kamfanin mahaifinka, na saka karshen watan nan”
Sirleem ya kalleta da sauri.
“Hajiya karshen watan nan be yi wuri ba? Sai kace abun da za a gudu?”
“Me ye abun sauri a dukiyarka? Shekarana nawa suna juyawa? Sai yanzu da lokacin karba yai za a ce an yi sauri? No karshen watan nan ya wadatar ayi biki a mika maka ragamar kamfaninka a hannunka da ma sauran kamfanonan da gidanjen da komai ma”
“To Allah yasa hakan shi ne mafi alheri, kuma ya bani iko kula da ita yadda ya dace”
“Ameen haka na ke son ji, Allah yai maka albarka”
“Ameen”
Ya fada yana mikewa tsaye.
“Ni zan koma can, Hajiya na fi jin zakewa a gidana gaskiya, ko ba komai zan samu na maida hankali kan abubuwan da suke gabana”
“Rantse min ba Mansura ta zo garin nan ba”
Kamar abun wasa sai ya fara dariya.
“Wallahi Hajiya bata zo ba, Mansura tana Kaduna Wallahi”
“Shikenan Allah ya tsare ka kula da kanka”
“Ameen sai da safe”
Ya fice cikin jindadi, Hajiya ta bar shi ya tafi ne kawai saboda ita ma tana cikin wani farincikin, kuma tana son ya maida hankalin kan abubuwa da ke gabansa kamar yadda ya fada, ba dan haka ba babu abun da zai saka ta kyale shi ya kwana a gidansa shi kadai.
TUMBA POV.
Ko da aka isa da ita asibiti bata cikin hayyacinta, gaba daya hankalinta ya bace, duk wanda zai ga halin da aka shigo da ita sai yayi tasbihi ya kawar da ido, domin kafar da babur ya buga gaba daya ta cire a hannu a ka iso da ita, ga naman fuskarta ya kwaye gaba daya baka ganin komai sai fatar can ciki mai jini wanda bata da kyau gani, hannunta na dama ma ya karye sai dai shi be cire ba sakamakon motar dake bayansu da bugu babur dinsu ita da Mai babur din sukai sama ita ta fada jikin wata motar, wanda hakan ya sa wani mai babur din ya bugeta babur din kuma ya fada kanta, shi kuma mai babur din da ta hau ya fada gefe, sai yai hanzarin tashi da jimuwar da yai, ganin yadda ta Tumba take sai ya saka ya manta da na shi ciwon, da taimakon wasu mutane da kuma jama'in dake kula da titi aka kawo su asibiti, ba dan suna da tabbacin ita Tumba din tana da rai ba, Likitocin ne suke tabbatar da tana da rai sai dai tana cikin mawuyacin hali.
A take aka hau neman yan'uwanta cikin mutane da suka kawo ta, kowa yace be santa ba, yar jakar kudinta ma an dauke tun a can gurin da hatsarin ya faru balle a binciki wayarta ko wani abu da zai bada