Showing 180001 words to 183000 words out of 286946 words
ai za su kira tun da Shatu tace ka bada number wayarka”
Cewar mamansu Ramla. Bappa ya amsa mata cike da gamsuwa.
“Haka ne kuma da zancen ki, amman dai idan kana jin mu bawan Allah ka daure ka kawo mana ita, mu kuma ba zamu nema mata maganin komai ba”
Inna ta daga kai tana kalle kalle kamar ance mata zata ganshi.
HAJIYA BABBA POV.
Tun rasuwar Talba Hajiya ta koma kamar wata marar lafiya, bata da kuzari walwalar duk ta gushe kullum tana dakin sai idan za ta yi wani abun sannan ta fito waje, zuciyarta ta saka sakin tunanin Talba, ba mutuwarsa take ji ba kamar rushewa al'amuranta, gashi a da tana tunanin zata fi Ammy gado ko da Mai Martaba ya rasu, saboda Talba yana a matsayin Shattima Juwairiyya da Karima kuma suna matsayin namiji daya sai Kaunar dake matsayin Nana, yanzu kuma sun za daya tun da Talba ya tafi, Sirleem kuma ba zai gaji Mai Martaba tun da ba dansa ba ne, Tunanin hakan yasa tun farko ta zo a haihu da yara a gidan amman be bata da yawa ba, sai ya bata hudu, namiji hudu mace uku.
Ga burin da take da shi na son Talba ya samu sarauta yanzu ya kau, sai abubuwan suka taru suka mata tsaye a zuciya ko abincin kirki bata iya ci. Tana zaune tana ta tunanin duniya Sirleem ya turo kofar ya shigo yana sallama, sai ta amsa masa da muryarta dake karantar da shi tsantsan damuwar da take ciki, kusa da ita ya zauna yana jin babu dadi a yanayin da ya same ta, domin duk dan kwarai ba zai so ganin mahaifiyarsa a cikin damuwa ba.
“Hajiya...”
Juyowa tai ta kalleshi cikin kwanakin nan naman fuskarta ya sauka fiye da da, ma'ana ta yi rama sosai.
“Sirleem kana lafiya?”
“Lfy kalau ya jikin?”
“Alhamdulillah, magana nake son yi da kai, magana ta karshe ba shawara zan baka ba umarni ne”
Tun kamin ta karanto masa abun da take so gabansa ya fadi.
“Minene Hajiya?”
“Bana son wakar nan da kake yi, kaskanci ne a gareka da mu da kowa ma naka, bana son wakar da kake, baka rasa komai ba a duniyar, me zai kasa ka zabi waka?”
“Waka sana'a ce Hajiya”
“Na yarda sana'a ce, amman ba ga dan babban mutum kamar kai ba, mu ya kamata ace muna kyautatawa mawaka muna musu alheri muna basu dukiya, kai fa idan ana son kiranka kai kayatar a taro ko biki, ina jin zafi kuma kaskanci ne a gareka a matsayinka na a gola a gidan Sarki kuma dan former vice president, abun da ko wane dan babban mutum yake a yanzu kokarin yaga ya yi kamar ubansa ko ma ya wuce ubansa, ka yi karatu a waje kai fa engineering ka karanta miye hadinka da waka? Why? Bana so kuma ina mai umarta ka daina, kai kadai ka rage namiji a yanzu, so nake ka zama babban mutum kamar mahaifinka ba mawaki ba”
Tun daga cikin kansa ya ji wani abu na taso masa yana saukowa har kasan kafafuwansa, be taba jin nauyi wani abu a duniya kamar maganar Hajiya a yanzu ba, sai yaji kamar ta dauki wni katon dutse daya fi garin Kano girma ta dora masa a kai. A duniya babu abun da yake so yake jindadin yinsa kamar waka, ya dauke a amatsayin sana'a kuma abun da ke bashi farinciki da sayyana a cikin al'umma, mahaifinsa ya bar masa dukiya da kamfanona masu yawa amman kanen mahaifinsa yake kula da komai shi kuma ya maida hankalinsa gurin wakar. Sanin kansa ne Hajiya bata son wakar tun farkon tashinsa ta kyale shi ne kawai saboda yana ra'ayin abun, yanzu kuma ta masa mai gaba daya wanda be san ta inda zai fara ba, the most painful part is tace masa umarni ne ba shawara ba.
“In dai hakan zai faranta miki rai, kuma ya saka ki koma da walwala kamar dai, na miki alkawari zan tattara duk wani abu daya shafi waka na aje a gefe, zan maida hankali gurin dukiyar da Daddy ya bar min inshallah”
Ta yi murmushi daman ta san indai har ta bawa Sirleem umarni ba zai iya tsallakewa ba, ba kamar Talba ba da bata isa tai masa haka ba, har sai idan abun ya biyo da son zuciyarsa.
“Allah ya maka albarka ta taimaka maka, ai kara ka maida hankali tun wuri domin nan gaba kadan kenen mahaifinka zasu iya cewa rabin dukiya ta su ce”
Shi dai be ce nata uffan ba ya mike tsaye ba dan yana da tabbacin ta kare maganarta ba sai dan yana jin duniyar tana juya masa a yanzu. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta bar shi ya tafi ne kawai saboda ta san abun da ta dora masa mai nauyi ne, ba zata bijiro masa da zancen Mansura da Falmata ba a yanzu sai hankalinsa ya kwanta, daman kuma ba fasa shiga malamai zata yi ba.
Karamar wayarta ta dauka ta aikawa Hajiya Talatu kira, sai da wayar tai daf da katsewa sannan Hajiya Talatu ta dauka tana randaga sallama.
“Hajiya Talatu ban ji ki ba”
“Yanzu yanzun nan na fito wanka Hajiya, gidan zan zo amman kamin na iso bari nai miki albishir, na yi magana da matar nan laraba tace min zata zo, kin ga sai mu je gidansu Hajiya Uwani tun da yafi sirri, idan kuma kina ganin ba matsala bace idan ta zo gida sai ta tsaya bangare mu yi duk abun da zamu yi”
“Aa bana son zancen Hajiya Uwani, zuwa gidan ai tonon asiri ne, kara dai inda kike tun da Hajiya Mairo ba shigo miki take ba”
“To ba Ba matsala sai ayi haka din”
“Ya maganar wacan Malami kin tafi?”
“Eh na tafi, shi ma ya duba mana yace yarinyar ma aure za ayi mata, Na Mai Martaba ma ya bada magani a kawo miki ki bashi wai a abinci ya ci, na fada masa a warware kullin, Nana kuma ya bada wata laya yace a samu katon dutse a saka karkashi idan za a saka a ambaci sunanta sau uku, ya tabbatar min da an yi haka ba zata iya fadawa kowa ba ko da kuwa an dora mata wuka a wuya ne”
“To yayi kyau ba sai kin kawo min ba, ki samu dutsi a can ki yi, ko kuma ki saka wani wanda kika yarda da shi yai, ai kara a warware kam tun da mai gaba data ta afku, Allah na tuba ko mutuwa yai a yanzu ai Ammy da Jarma ne ke da harka”
“Shine ai, ita da su kowa wane murna zai yi tun da danta take zaton a bawa Jarma kuma kan sa zai yi wa yaki”
“Hmm Ai indai ina da rai Wallahi Shattima ba zai yi sarauta ba, ko Jarman idan ya samu ai ba gata zai mana ba, ni Wallahi har gani nake kamar da sa hannun Jarma ko Ammy a mutuwar Talba, ko tsawa suna iya tura musu ko kuma ayi wani abun jirgin ya fadi”
“Tsab za su aikata, musamman ma Jarma, ko da yake ita ma Ammyn ba kanwar lasa ba ce tun da gashi ta mallakewa kowa ta kama komai ta rikr sai yadda tace ake”
“Hmmm ai wannan matar ko? Allah kadai yasan irin tsafin da take takama da shi, ke kina ganin wani abu kin san ba banza ba ne, wai ya maganar auren Maijidda?”
“To har yanzu dai be sake ce min komai ba, kin san daman wannan bokan na can ya fadi cewar ba za ayi auren ba, ban sani ba ko dan an yi mutuwar nan ne ko kuwa saboda na yi yaji ne, ko kuma Ammy ta sake masa wata shawarar oho”
“Allah dai ya rabaki da wahala, wannan ai kisan kai ne za ayi miki da ya, Allah dai ya kyauta”
“Ameen Hajiya sai na shigo, yanzu da na gama shiri”
“To sai kin iso, daga nan ki ji yadda muka yi da dan gidanki Sirleem”
“Au to gani zuwa yanzu kuwa”
Hajiya ta sauke wayar tana dan murmushi da be kai ciki ba.
SHATTIMA POV.
Sake fita yai ya dauko key wata motar ya saka ta tashi, har sai da ya juya kanta ta kalli gate, sannan ya fito ya riko Fadime ya fito da ita a motar da take cikin ya saka a wacan Fadime na zaunawa Motar ta mutu, zagayawa yai ya shiga driver side ya kunna ta ki tashi, haka yai juyin duniya motar ta ki tashi. Can wani tunanin ya zo masa sai ya fita ya zagaya side din Fadime ya cireta a motar ya sake zagayowa ya shiga yai mata key sai mota ta tashi.
“Oh... ”
Ya furta sannan ya fita, a kunne ya bar ya sake zagayawa ya saka Fadime sai motar ta sake mutuwa.
“Miyasa motar take mutuwa?”
“Saboda kina ciki ne”
Ya amsa yana jinginawa da kujera yana kallonta.
“Wallahi ba dai ni ba, sai dai idan daman can motarka bata da kyau”
“Duka motacin uku?”
“Na sani ko mota daya ce kake juyani kana min wayo”
Yayi murmushi duk da baya cikin yanayin nan.
“Yanzu ba wannan ba, idan tafiyar da ke ba zata yiyu ba, ki zauna sai naje na fadawa iyayenki idan ma kama na zo tare da su sai na kawo su”
Ta lake kafada.
“Wayonka kenan? Wallahi ni ba zan yarda ba, ka bar ni a wannan gidan Allah kadai yasan zuciyar mutum...”
“Ni ma ba nan zan barki ba ai, masarauta ki zauna tare da mutane”
“Masarauta?”
“Eh”
“Gidan Sarauta kenan fa?”
“Yes”
Ta wara ido kamar tana gani har da sy bude baki jin an ambaci masarauta, sai dai tunawa da Wasim ya kaita gurin mayya yasa ta hade jindadinta.
“Gurin wa zaka kai ni?”
“Ammy”
“Ita ma tsohuwa ce kamar Iya?”
For the first time Shattima ya daka mata tsawa.
“I will slap your mouth, and Ammy mahaifiyata ce, so control your tongue, kuma matar sarki ce karki je kina mata zuba anyhow take zaki ji mari, ba zata dauki abun da nake dauka ba”
Ta kara fito da idonta waje kamar za su fado.
“Kai kenan dan waye?”
“Dan Babansa”
Ta yamutsa fuska.
“Kenan kai agola ne ko?”
Kai ya girgiza be sake ce mata komai ba, ya kai hannunsa ya murda key motar sai ta tashi.
‘Oh’
Ya fada a ransa kamin yai danna horn ya nufi gate, kamin ya karasa mai gadin ya bude masa gate din. Sai da suka hau titi Fadime tace.
“Akwai nisa sosai?”
“Ko mu wuce airport din da motar ta tashi”
Yana fadar hakan motar ta fara fisga tana gaba da baya, take Shattima ya fara addu'a.
“Aa mu dai fara zuwa gidan Sarkin, Sarki fa, gobe sai mu tafi gida, ka daina wannan abun da kake da mota bana so”
Ta turo baki gaba, ya dan wara idonta yana kallonta kamin ya dauke kai yai murmushi yana cigaba da karanta addu'o'insa. Sun isa cikin masarautar lafiya kalau, a harabar Ammy yai fakin sannan ya zagayo ya budewa Fadime ya fito da ita. Sai da ya rufe motar sannan ya kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata.
“Dan Allah karki gisgani a gaban mutane kinji? Zan siya miki kaza da yogurt”
Ta washe hakora.
“To...”
Ya kama hannunta suka nufi hanyar shiga ciki yana daure fuska kamar ba shi ba. Sai da suka fara hawan stairs din sannan tace.
“Me muke hawa?”
“Ciki zamu je, pls ki daina yawan min magana, da tambaya any how a gida ma ina amsa miki ne saboda muna mu kadai ne amman nan akwai mutane, daman can bana son yawan magana sai dole”
“Tsoron mutane kake ji? Ko kuma magana ciwo take maka?”
Ya daga hannunsa kamar ya kai mata rankwashi a ka sai kuma ya fasa, ya shareta kawai suka cigaba da tafiyar, ta kofar fadar Ammy ya shigo hakan yasa shi shiga bangaren kai tsaye, sai dai yana shigowa cikin falon hadiman dake ciki suka fara mika masa gaisuwa daman tun a bakin kofar shigowar wasu hadiman maza dake tsaron kofar suka gaishe shi. Fadime sai ta ji wani girma da kwarjini ya kamata duk da kasancewar bata ganin mutanen kuma bata san da waye Shattima ba. Bata dai ce masa komai ba har sai da taji sun bude daki sun shiga mai cike da sanyin ac ga kamshin turare kamar kamfanin turare.
“Daki muka shigo”
“Eh”
Ya amsa ta dan dole.
“Na ce dan sun ga Mamaka tana auren sarki shiyasa suke ta gaishe ka ko?”
Shattima ya kalli Ammy dake zaune tana cin abinci ita na ta kalleshi sai kuma ta kalli Fadime, be dai ce mata komai ba har sai da ya zaunar da Fadime shi ma ya zauna.
“Ammy ina kwana?”
“Lafiya kalau an tashi lafiya?”
“Alhamdulillah”
Yana rufe baki Fadime ta mikawa Ammy gaisuwa.
“Ammy ina kwana?”
Sai bayan few sec Ammy ta amsa mata tana ta mamakin inda Shattima ya samo ta daga ganinta dai bata gani.
“Lafiya kalau”
Fadime ta dan jingina jikin Shattima tana masa rada baki bude hakora har kunne tsabar far'a.
“Ita ce matar sarkin ko?”
Shattima kasa ce mata komai yai sai kallon Ammy yai, Ammy ma kallonsa take, yana yunkurin magana Nana ta turo kofar dakin shigo, a dayan barensa ta zauna cike da damuwa.
“Ya Shattima good morning”
“How are you?”
“Im fine, Ya ka ce zaka yi wani abu amman shiru”
“Nana i said i will karki damu”
“Akan Sardauna ko? Ko Hajiya Babba?”
Ammy ta tambaya, Nana ta juya ta kalleta.
“Aa Ammy akan makaranta na ne”
Sai kuma ta juya ta kalli Shattima.
“Ina saurare dan Allah Ya Shattima, kuma Jekadiya tace na fada maka Falmata na waje tana jiranka”
Ya gyada mata kai sannan ta tashi ta fice.
“Ammy...”
“Ina zuwa”
Ammy ta fada sannan ta mike tsaye ta nufi bandaki, budewar da Fadime ta ji an yi sai tai zaton ko Ammy ta fita daga dakin ne.
Sai ta kai bakin kusa da Shattima.
“Ta fita? Wani abu zan fada maka”
“Aa ta shiga bandaki ne”
Ta yi shiru can kuma tace
“Na fada maka wani abu? Wallahi na taba jin sunayen nan Nana, Falmata, Shattima, da wani namiji ko wa ko Jarumi ko waye suka zo gurin boka tare da wata yarinya da wata Hajiya ko wa? Har da sunan wannan maman taka Ammy, kuma da Nana har da Sardauna Wallahi, har aka ce ana son a rufe bakin Nana wai ko kar ta fadi me, ita kuma wannan Hajiyar dayar tace bata son ayi aurenta da wani sai bokan yace mata ai ba za ayi auren ba, har ya bata magani yace ta bawa yarta ta sha wai idan maye ya ci ta ya ci mutuwa, har da wata mai irin sunana Fadime, ita wannan matar sunanta Hajiya Babba, wai tana son a kashe dan sarkin kuma da sarkin... Har da irin sunanka a ciki Shattima na rantse da Allah kau”
Ba Shattima ba har Ammy dake bandaki tana jinta kasancewar bandakin a bude yake. Shattima ya gyara zamansa yana kallonta da mugun mamaki.
“Da gaske? A ina?”
“A gidansu Wasim gurin kakansa boka Wallahi kuwa, har da wani wai saka shi ya so Nana, ka bani kur'ane zan rantse maka, Allah ubangiji yasa Wasim ya zo Wallahi gabansa akai zai ce maka ba karya nai ba, ba a ma dade ba ana gobe Wasim zai maida ni gida, har take cewa ko nawa ne zata kashe kuma ko miye zata yi, kuma yace mata akwai tafiyar da ba dawowa”
Ammy ta fito daga bandakin ta tsaya jikin kofar.
“Wacece wannan?”
Shattima ya kalli Fadime kamin ya kalli Ammy.
“Fadime...”
Fadime ta sha jinin jikinta tunawa da abun da ya fada mata cewar Ammy bata son yawan surutu zata iya jin mari.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
46
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Tana nasa kafarta cikin gidan tai arba da wasu dangin mahaifiyarta da suka zo daga kauye, a jiya ma wasu sun taho saboda bikinta da Baba ya aika musu. Cikin rashin walwala ta gaishe su kana ganinta kasan bata cikin jindadi domin alamunta da mu'amalarta ya nuna haka, ko kadan bata son auren da za a daura mata da tsohon nan ta daure ne kawai saboda ta bar komai a hannun Allah, hakan yasa bata labartawa Tumba zancen da Shattima yai mata ba, cewar idan tana ra'ayin komawa aikin ta sanarwa Jekadiya a sanar masa. Ba fata take ba sai dai tasan komawa aikin ba shi da wata fa'ida a gareta domin Tumba ce zata mori kudin ba ita ba, kuma bata san iya abun da zai sake faruwa ba wata kila nan gaba kadan ma za a iya cewa ta kashe mutum.
Dakinsu ta shige ta zauna, tana ta hango muutanen dake tsakar gidan, tana jin wani abu marar dadi yana mata yawo a zuciya, ta wani bangaren tana jin kamar ta bijirewa Baba, sai dai idan tace ba zata auri wanda ya zaba mata ba wa zata aura? A yanzu bata san wani tsayentsayen Saurayin da zata gabatar a matsayin miji ba, domin duk masu nemanta mata ne masu planning din aure ba dan sun shirya ba.
“Falmata ta zo Tumba na magana”
Wata kanwar mahaifiyarta ta fada mata, sai ta amsa tare da mikewa tsaye ta fito zuwa tsakar gidan, ganin bata tsakar gidan yasa ta nufi dakinta ta daga labulen ta shiga da sallama.
“Ke”
“Na'am”
“Nawa Shattiman ya baki?”
“Wallahi be bani komai ba”
“Karya kike, to kiran me yake miki?”
“Tambaya yai akan yaransa, yace ko naga wata alama ta rashin