Showing 267001 words to 270000 words out of 286946 words

Chapter 90 - Fulani Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

896

suna shiga falon yan jikokin gidan suka fara musu sannu da zuwa, sai ya rika daga su yana saukewa, sannan ya shiga ciki ya gaisa da wadanda suke manyansa Falmata ma ta gaisa da su kana ya nufi bangaren da dakin Hajiya Babba yake, domin bangare aka ware mata mai komai a ciki har da yar aikinta ita ke mata komai har abinci hakan kuma idan akai na gida gaba daya za a dauko a kawo mata a falonta. Kausar da Karima dakinsu daya, Jurry ce kawai ke da daki dabam saboda yanayinta. Da sallama ya shiga Kausar din ta amsa masa tana murmushi kana ta kalli Falmata.

“Anty Fateema sannunku da zuwa”

Falmata ta washe mata hakora tana jin girman da ta bata har cikin ranta.

“Kauwa Kausar ya gida?”

“Lafiya Kalau”

Kai tsaye Sirleem ya wuce dakin Mahaifiyarsa, Falmata kuma ta zauna a falon tana kallon katon Plasma, Kausar taje ta dauko mata ruwa da lemu ta aje mata.

“Ga ruwa na san dai kun ci abinci”

“Alhamdulillah, na gode”

Kausar na ta kokarin janta ta fira ita kuma ta kasa sakewa sai jifa jifa take saka baki a maganar, har Sirleem ya fito ya kira ta ta shiga ciki su gaisa da Hajiya. Kamar dai wacan karon wannan karon ma da dan tsoro Falmata ta shiga cikin dakin ta gaisa da Hajiya Babba, sai ga Hajiya Babba na amsa mata kamar ba ita ba, sai dai kam ta kurawa Falmata ido sai kallonta take, (Hausawa sun ce dan hakin da ka rena...) Tana cikin dakin Karima ma ta shigo suka gaisa a mutunce, sannan tai musu sallama ta fito, sai da Sirleem ya koma ciki yai mata sai da safe sannan ya fito suka kama hanyar gida shi da matarsa.

FADIME POV.

_1 Months later..._

Inna ba ta labarta mata komai ba har aka fara gyaran gidan, mutane sai murna suke shigowa suna musu da Allah sanya alheri, suna fadin Fadime ta janyo musu alheri ta taimaka musu, ba karamin farincikin Fadimr takr ba, ganin za ayi musu gida irin na zamani, sai dai hakan be hana ta shiga damuwa ba, kusan kullum sai ta yi ma Inna maganar Shattima tana fadin matarsa ta huta, kaza da kaza. Inna dai bata ce mata komai sai da aikin yai rabi, wanda hakan yai daidai da tafiyar da za'ayi Yola, a tunanin Fadime tare za a tafi da Inna da Bappa sai ita, domin a da har kirarin cewa take ita ba zata je ba, sai da Inna tace idan ya ji ba zai jidadi ba bayan duk hallacin da yai mata kuma zata ja ya bata da ita har abada kamar yadda Wasim yai, hakan yasa ta janye kudinta na cewa ba zata je ba, sai dai har ga Allah ba dan tana son zuwa ban saboda Shattima zai auri wata ba ita ba, hakan yasa bata ma sake bin ta kan wayarsa ba. Sai da ana saura kwana biyu su tafi sannan ta fada mata ba da ita za'ayi tafiyar ba.

“Saboda me Inna?”

Fadime ta tambaya tana kallon Inna da ke murmushi.

“Tare za ku tafi da su, Su Uwani da Dije, mu zamu zo daga baya ne”

“Miyasa to?”

“Su suka ce a kawo ki da wuri wai akwai yan abubuwan da za ayi miki kamin lokacin biki”

Ta turo baki gaba.

“Bana so, waye yace haka?”

“Matar Sarkin ita ta fada min da kanta a wayar Bappanki, ta fada abubuwan da za'ayi amman ban rike sunanayensu ba”

“Ni dai bana so abar ni sai kun tashi tafiya sannan”

“Gyara fa za ayi miki”

“To lalacewa nai balle a gyara ni, ni dai a kyale ni bana so”

“Kin taba ganin anyi amarya babu gyara?”

Inna ta fada da dariya, sai Fadime tai mata wani kallo na mamaki, can kuma zuciyarta ta raya mata zolayarta Inna take.

“Inna Wallahi bana son haka, zan miki addu'a Bappa ya karo wata Wallahi”

Ta fada har idonta na cika da hawaye wai ita ala dole ta ji haushi. Inna ta yi dariya.

“Wollah ba wasa nake miki ba, amman idan kin je can ai za ki yarda”

“Inna ban gane ba, yi min da hausa”

Ta fada tana dukawa gaban Inna tsabar son ta ji komai, Inna ta yarfeta da hannu.

“Ke ar kina Fulani kina fadin ayi miki da hausa, arrrr Fulani da abun kunya”

“Eh na ji, fada min wacece Shattima zai aura?”

“Ke ce mana, ba shiyasa za a tafi dake jibi ba”

“Ya za'ayi na yarda?”

“Na taba miki karyar?”

“Aa”

Ta girgiza kai. Inna ta soma bata labarin tun a lokacin da Mai Martaba ya nada wasu mutanen ciki har da Waziri suka zo neman aurenta cikin sirri ba tare da duniya ta sani ba, kuma Bappa ya sallama musu ba tare da ya nemi izininta ba, akai komai a sirrance domin su a can basa son a bayyana Bappa ma a nan baya son a bayyana hakan yasa babu wanda ya sani sai yan'uwansa. Inna ta yi zaton Fadime zata tashi ta fara rawa ne tana murna saboda jindadi, amman sai ta ga akasin haka a gurin yarta, wai yau Fadime ce ta saka hannu ta rufe fuskarta da sunan kunya.

“Wallahi Inna kunya na ke ji”

Ta fada wani kalar dadi na rufeta, Inna dai ta yi dariya tana girgiza kai

“Ashe kina da kunya”

Fadime ta tashi ta bar gurin da gudunta, ba Inna kadai ba har Bappa sai Fadime ta koma tana jin kunyarsa, fadar irin murna da dadin da take ji za'a mata aure kan har ba ya misaltuwa, tun ranar ta fara ayyana irin yadda za a rika bata girma idan ta auri Shattima, ta dayan bangaren kuma tana misalta yadda za ta yi girki.

“Da safe in ce masa ina kwana”

Ta yi dariya tare da rufe ido duk kuwa da kasancewar ita kadaice a sabon dakin na Inna.

“Da rana na dafa masa taliya ko shimkafa da miya ko wani abun na kawo masa lemu da ruwa, na ce sannu da zuwa”

Ta yi wani murmushin jindadi, sai kuma ta mike tsaye tana gyara sabon gadon Inna na masu karamin karfi.

“Kullum na gyara gadona na yi shara na goge komai, idan ya dawo na ce sannu da zuwa, da dare na hau gadona na kwanta shi kuma na shimfida masa bargo,.... Aa be dace ya kwanta kasa ba, sai dai ya kwanta a gado ni sai na shimfida bargo na kwanta a kasa”

Ta rumgume hannayenta tana jin kamar ga nan ma dakin mijin, ko dan damuwar da mata suke idan za su tafi su bar iyeyensu Fadime bata yi.

“Ita kuma Ammy kullum zan gaishe ta na duka mata har kasa, ko Nana da take kanwarsa duka mata zan yi ai ance ayi ladabi da biyayya...”

Haka tai ta surutunta tana misaltar yadda za ta yi idan anyi auren, tun daga ranar bata sake gaishe da Inna a tsaye ba sai dai ta duka har kasa haka ma Bappa, kuma bata yarda ta hada ido da su domin indai kunya ce tana jin kunyarsu a yanzu kam. Ana gobe za ayi tafi Inna tace ta je tai ma kawayenta bankwana amman kar ta fada musu komai, haka Fadime taje tai musu bankwana da sunan zata tafi Yola bikin Shattima, a kasan ranta sai fadar take wai sai dai kawai su ji ta auri dan sarki. Inna Uwani da Inna Dije a gidan suka kwana domin Ra'ees ya fadawa Bappa cewar da sassafe zai zo ya dauke su.
Cikin daren Inna ta ja Fadime gafe tana mata nasihar da ta saba mata tun a lokacin da aka saka mata rana, cewar ta natsu ta daina abubuwan da take, kuma ta rike addu'a ban da raina mutane surutun nan da take kamar an bude redio.

“Kina gani dai Allah ne ya kai ki wannan matsayin ba dan kin isa ba, kuma duk wanda yake cikin gidan sarauta zaki ganshia natse, ba kamar ke ba, kina musu hauka za su koroki ki dawo ruga”

“Aa duk watsar da komai zan yi, ba zan yi komai ba na natsu zan yi biyayya”

Fada sosai Inna tai mata irin na ya da uwa, sannan ta motsa mata fura ta bata ta sha, Fadime ta je ta kwanta babu komai a ranta zai zumudi kamar wanda aka cewa ana zuwa za a daura mata auren, mafarki babu kalar wanda ba tai ba. Washe gari sun da asubar fari Inna ta shirya musu abun karyawa tana ta tunanin Fadime a ranta irin kewar da zata yi amman Fadime hankalin baya kan Inna, Bappa ma sai da yai mata nasa fadan ya ja mata kunne sosai sannan yai mata albishir da gafararsa na abubuwan da tai ta masa na bacin rai. Misalin 8am Ra'ees ya iso ya daukesu zuwa Katsina sannan su wuce airport, Inna da Bappa suka tsaya suna ta kallon motar har sai da suka daina hangota sannan Inna ta share hawayen idonta ta koma cikin gida tana jin kamar ta fashe da kuka, zuciyarta ta cika.

SHATTIMA POV.

“Amaryarka ta iso”

Ammy ta fada da murmushi a fuskarta, Shattima ya aje cup din hannunsa yana murmushin jin kunya

“Ammy har da ke?”

“Ramawa na yi, ni ma dazun Mai Martaba yake zolaya ta wai ana masa kuri za'ayi sabuwar in-law, na ce masa lallai kam wannan Amaryar ta fi saura domin ina son yarinyar sosai da sosai Wallahi ta kwanta min rai kuma ta mana komaia rayuwa”

Shattima ya fadada murmushi yana shafa kansa.

“Mai Martaba dai lafiya ta samu”

“Wallahi yanzu kam Alhamdulillah sai dan abu ba a rasa ba, gashi har yana fita abu kamar wasa”

“Daman ai komai yai farko yana da karshe, sai a cigaba da addu'a”

“Haka ne kam, addu'a kuma ai ta zama dole, daman can Mai Martaba baya wasa da addu'a ni ma kuma ina masa, ai da baya addu'a da abun be zo a haka ba, kasan wani lokacin ko da addu'a abubuwan su kan samu bawa saboda an rubuto masa hakan sun kafi na haife shi”

“Haka ne Allah yasa mu dace, amman ita ba nan zata sauka ba?”

Ammy ta yi murmushi domin ko fito kai tsaye ya mata magana ba ta san wa yake nufi.

“Kai da ganinta yanzu ai sai an kai maka ita”

“Tooo”

Ya mike tsaye yana cigaba da murmushi.

“Nana ta min maganar graduation dinsu, wai a Abuja za su yi”

“Eh ta fada min ni ma nace ban yarda ba, yayi nisa duk abun da za a ce sai an bar Yola anje wani guri ayi sa ban zan bari ba”

“Ni ma ban bata shawara ba gaskiya, mace kiwonta ake, na ce mata dai zan yi magana da ke, zan fada mata kin ce ba ki aminta ba”

“Haka ya kamata Allah ya muku albarka”

Ya amsa da Ameen sannan ya fice daga dakin sai zuba kamshin turare yake.





_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
65

*Khadeeja Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

A harabar makaranta yake tsaye, yana sanye da bakin wando sai rd T-shirt da black shoes, a saman T-shirt din ya dora rigarsa sanyi irin mai kaurin an hannunsa sanye da safa kansa ma sanye hula, waya ce makalle a kunnensa sai faman murmushi yake kana ganinsa ka san yana cikin farinciki.

“Yanzu kun yarda ku yi a Yola kenan?”

“Eh dolen mu ai, because most of us iyayenmu ba su yarda ayi a Abuja ba”

“Good hakan ya fi duk da na san kuna da family a can amman dai kara komai ayi a gaban iyaye”

“To yanzu ai karatu zanje India a gabansu zan yi?”

“Wannan yana da banbanci, kuma idan sun barki kin je hakan na nufin sun yarda da ke kenan kuma hakan ba zai baki dama ki yi rayuwar da kike so ba, kuma ita fatar ba za ki ba mu kunya ba”

Ta yi murmushi yana juyawa saman gadon da take.

“Zan yi karatu sosai, kuma ba zan yi wani abu da zai tsaba tarbiyarta ba, ba zan ba ku kunya ba”

“Thank You”

“Ur Welcome”

“Bari na barki yi bachi saboda na san nan dare ne ko? Nan kuma rana”

“Yeah 1am ma ta kusa”

“Oh Wow kai ki kwanta kar Ammy ta ji kina waya da ni”

“To sai miye ai ta san muna waya, ta san ina kiranka ai kuma kana kirana”

“Yeah zata san muna gaisawa ai”

“Gaisawa kawai?”

Yayi murmushi.

“Yeah gaisawa kawai, domin bana jin idan ta san akwai wani abu a tsakaninmu zata bar mu mu cigaba da mu'amala”

“Saboda me?”

“Saboda yanayin rayuwata da taki ba daya ba ne, mu'amalarmu ma ba daya ba matsayinki yana da nisa da ni, kuma kina sama da ni sosai a komai n rayuwa idan aka cire shekaru”

“Shikenan?”

“Yeah”

“Hmmmmmm sai da safe”

“Goodnight...”

Sweetheart, ya karasa a zuciyarsa sannan a sauke wayar yana kallon hotonsa dake screen din wayarsa, babban yatsansa ya saka yana shafa screen din sannan ya daga kansa yana karewa makarantar kallo, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin wai shi ne yau a uk yana karatu cikin turawa abun da be taba mafarki ba. Duk iya fatan samun kudin da yake da misalin arzikin da yake karatunsa da burinsa a Nigeria ne, but look at him a kasar waje da sunan karatu karatun da zai inganta rayuwarsa. Tafiya ya fara yi yana tuna yadda rayuwa ta kasance musu before now, but komai ya canja cikin kankan ne lokaci.

“Arziki kashi...”

Ya furta yana kara yarda da kalmar nan da hausawa kr cewa idan Allah ta so ka tsinuwa zai baka, kuma dare daya Allah kan yi bature, lokuta ta dama ta inda baka yi tsammanin abu ba yake zo maka, domin be taba tunanin sanadin Nana zai samu haka ba, a iya tunaninsa zai samu yan kudaden a hannunta ne sai ya taimaki kansa da yar'uwarsa sai ga shi sanadinta an masa komai kuma an yi ma yar'uwarsa, farinciki na farko da ba zai manta da shi ba shine kudin da Shattima ya saka masa a account one million, a daren ranar kasa bachi yai yana ta ganin kamar karya ne one million in his account! Shi da ko 100k be tana ajewa a ciki ba, dai gashi an masa kyautar 1m. Daman tun da Nana ta fada masa ya tura account din yakr rike da wayarsa ko kara yaji sai ya duba sai ya ga sakon mtn, kudin be shigo account dinsa ba the following day, a ranar kasa yadda yai a farke yake, ya tisa Anty a gaba wai ta mare shi ko zai yarda.

“Wane irin mari kuma?”

“Dan girman Allah ki mare ni Anty”

Anty tai tsaye tana masa kallon mamaki.

“Sardauna ince dai ba wani abu ka sha ba?”

“Ni dai ki mare ni dan Allah”

Shiru Anty tai tana kallonsa kamin ta matsa baya.

“Gaskiya akwai abun da yake damunka Sardauna”

“Kai Anty dan Allah ki mare ni”

Ganin ba marinsa za tai ba yasa ya juya kamar zai fita sai kuma ya juyo.

“Anty yau yau ce? Ba mafarki na ke ba? Shiyasa na ke son ki mareni na tantance”

Anty na jin haka ta san kudin ne suka iso domin ta san da labarin izuwarsu, sai ta matsa kusa da shi ya ware hannunta iyakar karfinta ta zabgamar mari mai dan karen zafi, har sai da yaji wani shockin kamar na wutar lantarki, a nan kam ya yarda ba mafarki yake ba gaskiya domin da mafarki ne da yanzu ya farka.

“Na rantse da Allah da abokina ne yai min wannan marin yau sai mun yi dambe da shi”

Anty ta saka dariya domin ita kanta da tai marin ta ji zafi balle shi da aka mara.

“Ai dan ka tabbatar ba mafarki bane gaske ne miliyan sun shigo”

Sai gashi yana murmushin ya duka yai ma Allah sujudar godiya, tun a ranar ya rabawa abokansa da yan uwa 100k ya bawa Anty 500k ya rike 400k. A week later Ammy ta saka Nana ta kira shi ya zo ta hada shi tare da mutanen da Mai Martaba ya wakilta suka kai shi million quarters aka nuna masa gidan da Mai Martaba ya bashi, sai ya rasa bakin godiya, ba tabbatar da gaske ba ne sai da aka ba shi keys din gidan da takardu, ba shi kadai ba Anty ma kuka ta rika shi ganin katon gida mai gate da manyan dakuna da falo, ko'ina an gyara furniture ne kawai ba a saka ba, daman duk wanda ya san unguwar ya san yadda gidanjen unguwar suke da kyau da tsaruwa, ba su da wani girma sosai sai dai an musu tsari mai kyau ta yadda kowa zai iya zama ciki, 500k din da Sardauna ya bata ta siya gado da duk wasu abubuwa na bukata, abun ka da mai nema ko sati ba a kara ba ta tare a gidan tare da Sardauna da dakinsa ke daga waje kamar na saukar baki, mutanen unguwa da yan'uwa sai murna ake musu. After komai na karatu ya kammala Mai Martaba ya kira Sardauna da kansa suka ga juna ya sake yi masa kyautar kudi mai yawa kuma ya karbi account dinsa ya bawa Waziri, saboda a rika tura masa kudi time to time na karatun da yake, duk wani abu na biza da komai Mai Martaba ne ya biya kudi akai masa har komai ya zama ready.
Ana saura Two

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login